Chapter 13
BA SO BANE.
Story📃 writing
by
Hafsat waziri
Young talent writer's
•Yota•
Page 13
I Dedicate this book to
Nanakhadii 💅📕_
Karon farko daya ya buÉ—e idanunsa gaba É—aya ya zuba mata su ba tare da kiftawa ba.
Wani irin bugawa zuciyarta ta yi da ƙarfi sosai. Duk lokacin da zai ɗaga ido ya kalleta, sai ta ji irin haka. Amma na yau, na yanzu, ya fi na kowane lokaci tasiri a jikinta.
Bugun da zuciyarta ke yi ne ya sa ta É—an rikice.
Ko yaushe idan ya kalleta haka, wani irin kwarjini da ba ta iya bayyana asalinsa yake ratsa ta. Sai dai ta ƙi nuna hakan.
Cikin ƙoƙarin danne halin da zuciyarta da gangar jikinta ke ƙoƙarin shiga, ta ce cikin inda-inda,
"Wai... wai kai, me ka É—auki kanka ne? Kai da har ina magana kana tsaye kana kallona?"
Bai amsa ba. Bai kuma janye idanunsa daga kanta ba.
Cikin hanzari ta yi ƙoƙarin janye nata idanun daga kansa, amma ta kasa. Saboda wani irin riko da nasa idanun suka yi mata, kamar masu son isar mata da wani saƙo.
Cikin ƙarfin hali da son nuna masa sakonsa bai yi tasiri a kanta ba, ta janye idanunta a hankali tana hararar gefensa.
Ci gaba ya yi da kallonta na wasu daƙiƙu, sannan cikin natsuwa ya kau da kansa.
Ba tare da ya ce uffan ba, ya mayar da wayarsa cikin aljihunsa.
Karo na biyu kenan da abubuwanta suke son ba shi dariya. Sai kace wani Ala Musuru. Shi ina ya san abin da ta zo siya? Kawo su nan É—in da ya yi ma a bakin Ajmal ya ji. A hankali ya furzar da iska daga bakinsa tare da É—aga kai ya shiga bin abubuwan da ke cike a wajen da kallo. Ya rasa ta inda zai fara bin umarnin oganniyar tasa.
Sai dai tunawa da ya yi ita ɗin wace ce, ya sa ya sauke ajiyar zuciya a ɓoye. Mamallakiyar company ai tana da kuɗin siyan duk abin da ke wajen. Tuna hakan ya sa ya saki murmushin mutunta tare da girgiza kansa kaɗan.
Cikin nitsuwarsa ya miƙa hannu ya ja shopping cart ɗin.
Kamar wanda aka ce masa ya dauki duk abin da ke wajen an basa kyautar su. Haka ya dinga É—aukar duk abin da idanunsa suka gani yana jefawa cikin shopping cart É—in. Tun daga kayan girke-girke, Omo, chocolate, Pampers, sanitary pads da drinks.
Har kifin gwangwani na kamfanin S&S Sardines da aka jera tsaf a kan shelves bai bari ba. Ya dinga kwasarsu yana zubawa cikin babban shopping cart É—in har ya cika, wasu ma suka fara zubewa.
Tana tsaye tana kallon yadda yake yin duk wani movement nasa cikin nitsuwa da aji ba tare da hayaniya ba.
"Looks like he is used to shopping in supermarkets."
Ta faÉ—a a hankali tare da É—auke kanta daga kallonsa.
Mutanen da ke cikin supermarket É—in duk suka tsaya suna kallonsa cike da burgewa, ganin yadda yake ta siyayya kamar bai san zafin kuÉ—i ba.
Ummul, wadda ke tsaye nesa da su kaɗan tun ɗazu, tana ta saƙe-saƙen yadda za ta isa gare shi. Ganin yadda yake jidar abubuwa ya sa ta cika da jin daɗi tare da tunanin ta samu husband material. Wannan tunanin yasa ta sake daura aniyar ko ana ha maza ha mata, sai ta riɓisa.
Ganin ya gama É—aukar abin da zai iya yana nufowa wajen da take, ya sa ta É—auke kanta daga kallonsa a karo na ba a daÉ—i.
Tsurrr!
Ta ji ya turo shopping cart É—in zuwa inda take tsaye, wasu abubuwan ma har suna zubewa tsabar yadda suka cika.
'' done my boss ''
Ya fada yana bin kyakkyawar fuskarta da kallo.
Cikin takaici ta hararesa, ta zaro ATM card ɗinta daga cikin handbag. Ta riƙe katin tsakanin yatsu biyu, sannan ta miƙa masa.
Shi ma cikin irin nasa ji da kai ya miƙa hannu zai karɓa. Sai ta sake katin ya faɗi ƙasa da gangan.
A hankali ya ɗan zaro manyan idanunsa waje, kamar karamin yaro ya bi katin da kallo na wasu daƙiƙu, kafin ya ɗago ya kalleta. Ita ma ta kalli katin da ke ƙasa, sannan ta ɗago tana kallonsa, ta saki dan karami murmushi tare da ɗaga masa gira, alamar ya tsugunna ya ɗauka.
Bai ce komai ba.
Ya tsugunna a hankali zai ɗauka. Sai ya ji yatsunsa sun taɓa hannun mutum.
A hankali, cikin nitsuwa, ya É—ago kansa ya kalleta.
Idanunsu suka sarƙe cikin na juna.
Ta sakar masa wani shegen murmushi, murmushin nan nata mai jan hankalin maza.
Da sauri Abdul-Aziz ya miƙe tare da haɗe girarsa sama da ƙasa, kamar wanda ya ga babban abokin gabansa.
Cike da karairaya, ta miƙe da katin a hannunta, fuskarta ɗauke da murmushi yayin da ƙamshin turarenta ke ratsa shi.
"Excuse me."
Ta faÉ—a cikin murya mai taushi.
Mammy,
wacce ke tsaye a bayansu kamar wacce aka shuka a wajen, ta yi shiru yayin da duk ilahirin jikinta da zuciyarta ke rawa.
Ba ta san me yake damunta ba. Ba ta san dalilin da yasa take jin kamar tana ƙoƙarin losing herself ba. Ba ta san ma a kan wani dalilin ta shiga irin halin da take ciki a yanzu ba.
"Za ka min bayani idan har neman mata na É—auke ka ka yi? Yi nonsense kawai."
Ta ƙarasa maganar cikin tsananin ɓacin ran da ba ta san dalilinsa ba.
A hankali ta mayar da kanta kan Ajmal, dake wasa da katon teddy É—in da tun shigowarsu ya je ya É—auka.
Sai dai ko daƙiƙu goma ba su kai ba, ta ji ta kasa jurewa, saboda ji ta yi kamar idan idanunta ba sa kansu, wani abu zai iya faruwa.
Hakan ya sa ta juya tana kallon Ummul, wacce ke tsaye a gabansa har yanzu, katin na hannunta bai karɓa ba.
"I think this belongs to you."
Ummul ta sake faɗa da muryar da ta fi ta farko maƙalewa.
Ya kalli katin a nitse, sannan ya sake kallon fuskarta.
Ba tare da ya nuna wata alamar ɓacin rai ko rashin jin daɗin hakan ba, ya sa hannu ya zare katin daga hannunta. Cikin deep voice ɗinsa, mai saka mata bugun zuciya, ya ce,
"Thank you."
A taƙaice.
Ba tare da ya sake kallon inda take ba. Sannan ya juya wajen biyan kudin.
Nan take murmushin da ke fuskar Ummul ya ɓace ɓat kamar wanda aka yiwa layar zana.
Wannan shine karo na farko, da wani ɗa namiji ya taɓa tsallake tsarkonta.
A hankali ta juya suka haÉ—a ido da Habi, wacce ke tsaye nesa da su kaÉ—an tana kallon duk abinda ke faruwa.
"I think this belongs to you."
Ta sake matsowa kusa da shi domin ya ƙara shaƙar ƙamshin turarenta sosai, sannan ta miƙa masa katin.