Chapter 14
BA SO BANE.
Story📃 writing
by
Hafsat waziri
Young talent writer's
•Yota•
Page 14
I Dedicate this book to
Nanakhadii 💅📕_
“Never give up Ummul za ki iya. Yes i will! Maza da suka fi shi ma na ja su a ƙasa bare shi.”
Ta yi maganar cike da ƙoƙarin ba wa kanta ƙarfin gwiwa, idanunta ta lumshe yayin da ƙyaƙyƙyawar fuskarsa ke sake mata gizo.
A hankali ta buɗe su, a lokacin da tsoro da fargaba suka yi mata dirar mikiya, nan take murmushin da ke kan fuskarta ya dusashe.
“But... amma me yasa nake jin haka a kansa?”
ta faɗa a hankali, jikinta a sanyaye.
Ita kanta ba ta san wani irin abu ne take ji game da shi ba. Wani yanayi ne da bai taɓa samun ta ba.
A duk inda ta shiga, kallo ɗaya tak ya isa ya ɗauke hankalin duk wanda ta so. Ba ta taɓa wahalar jan hankalin kowa ba.
Amma shi fa?
A maimakon ita ta ɗauke hankalinsa, shi ne ya mamaye nata gaba ɗaya. A ɗazu da take kallonsa daga nesa, ta yi tunanin shi ɗin kamar sauran yake, but sai a yanzu da tazararsu bai wuce taku biyar ba, ta gane yana da bambanci mai yawa da sauran.
Wani irin kwarjini ne yake da shi da ya fi ƙarfin tunaninta. Ko da bai yi mata magana ba, yanayin fuskarsa da tsayuwarsa kaɗai sun isa su sa zuciyar mutum shiga wani irin yanayi.
Ajiyar zuciya mai nauyi ta sake saukewa a karo na uku, tare da ɗauke kanta daga kallon Habi ta mayar kansa.
Idanunta suka sauka kan kyakkyawar fuskarsa, wacce take a ɗaure babu alamar fara'a.
“Ki haƙura da shi kawai, Ummul.”
Ta faɗa a fili cikin sarewa da rasa ƙarfin gwiwa. Tabbas tana sonsa amma bata san ta ina zata fara ba.
“Shi ma mutum ne kamar kowa. Ba zan iya haƙura ba, wallahi. Duk wacce za a yi, sai dai a yi.”
Ta faɗa cike da ba wa kanta gwarin gwiwar da bata da tabbaci.
Da wannan tunanin ne ya sake bata wani sabon ƙarfin gwiwa da ya fi na farko.
Ta kafesa da idanunta.
A ƙoƙarinta na ganin sun haɗa ido.
Sai dai hakan ya gagara.
Saboda shi, tun kallon farko da ya yi mata ya ɗauke kansa, bai sake waiwayarta ko sau ɗaya ba.
Ganin har ya gama biyan kuɗin kayan da ya saya, ana musu parking za su tafi.
Ya sa hakan ya ƙara tayar mata da hankali sosai.
Babban damuwarta ma shi ne, ko sanin wanene shi ba ta yi ba. A tunaninta, ko ba komai idan ta san wani abu game da shi, nemansa ba zai mata wahala ba. But sai dai ta yaya? Mutumin da ko kallonta bai yi ba, bare ta sa ran samun number.
Ta lumshi idanunta tare da yin shuru tana tunanin yadda zata yi. Bata dade a haka ba bude idonta da sauri tare da sakin wani ƙaramin murmushin jin dadi.
A hankali ta shiga takawa cikin sanɗa, har ta isa bayansa ta tsaya a kusa da Afaf.
Ba ta ce komai ba. Ta tsaya tana kare wa yarinyar kallo. Ganin ba sa kama ko kaɗan ya sa ta ɗan tabe baki.
Cikin murmushin yaudara, da son ganin ta ja hankalinta ta tsuguna a gaban Afaf, wacce ke tsaye a bayansa. Tare da kama hannunta.
Da sauri Afaf din ta ɗaga kai tana kallonta, yayin da idanunta ke nuna tsoron Ummul ɗin.
Murmushi ta sakar mata mai cike da nuna kulawa.
“Hi beautiful baby, what is your name?”
Ta tambayi yarinyar, yayin da idanunta ke kanta. Duk wani hope nata a kansa yanzu yana kan yarinyar ne.
Afaf ta ƙwal-ƙwala idanu kamar mai shirin yin kuka saboda rashin sabo da mutane. A hankali Ummul ta sake matse hannun yarinyar da ke cikin nata tare da sake tambayar sunanta.
Cikin siririyar murya ta ce,
“My name is Zainab Umar Sa'ad Lekki.”
“Wow... Umar Sa'ad Lekki. What a good name...?”
Ta faɗa a cikin zuciyarta yayin da wani daɗi ke ratsata.
Ko ba komai, jin sunansa kaɗai ya sa ta ji burinta kashi saba'in ya cika.
“Nice name.”
Ta ɗan saci kallonsa.
Ganin ba ita yake kallo ba, ya sa ta mayar da hankalinta kan yarinyar. Duk da ta samu sunansa, hakan bai isa ba. A yanzu har da address ɗinsa take fatan samu.
“Kinason chocolate?”
Ta fada a lokacin da ta kokarin buɗe handbag ɗinta, ta ciro chocolate din tana miƙa mata.
Da sauri Afaf ta shiga girgiza kanta tare da makale kafaɗa alamar ba ta so. Ummul kuwa ta matsa lallai sai ta karɓa.
Hakan ya sa yarinyar ta fara kuka tare da matsawa baya ta shige jikinsa, tana rirriƙe hannunsa.
Jiki a sanyaye ta mayar da chocolate ɗin cikin jakarta. Tare da muke wa tsaye tana kallon bayansa.
Jin kukan yariyar yasa ya juyo ya
Sai dai ganin Ummul a tsaye a wajen yasa ya fasa maganar..
Tsaki ya ɗan ja a ƙasan maƙoshi yana ƙara tsuke fuska, ya ɗauke kansa ya mayar gefe.
Wannan kallon nasa ya sa Ummul ta sake jin shakkarsa.
Batare da ya sake kallon wajen da take ba ya kama hannun Afaf da niyyar fita daga cikin supermarket ɗin. Yayinda Mammy da Ajmal ke biye da shi.
Jin wayarsa da ke cikin aljihunsa yana ringing.
Yasa ya tsaya, yana yatsina fuska ya saki hannun Afaf, sannan ya zaro wayar.
Ganin Habu ne ma ke kirannasa, yasa ya ɗan ja tsakin da ya koyeshi a wajen oganniyarsa tare da kawar da kansa.
Ya ƙi ɗaga kiran.
Ya ci gaba da tafiya riƙe wayar a hannunsa.
Yana shirin wucewa kenan...
Ummul ta yi saurin matsowa kusa da shi, tana kokarin yi masa magana.
Tsabar yadda take saurin cin masa har kafaɗarta ta bugi hannunsa.
Wayar ta kuɓuce daga hannunsa ta faɗi ƙasa.
“Ya Salam...”
Ta faɗa a razane, jikinta na tsuma.
Da sauri kamar walƙiya ta tsugunna ta ɗauki wayar.
Ta miƙe tana tsaye a gabansa.
A karo na biyu kenan da suka tsaya suna fuskantar juna.
Cikin tsananin shakkarsa ta miƙa masa wayar.
A hankali ya rumtse idanunsa, sai kuma ya buɗe su a kanta.
Wani irin yankawa zuciyarta ta shiga yi da sauri-sauri saboda wani irin kwarjini mai cika idanu da ya yi mata. Amma saboda tsabar ƙarfin hali ta daure.
Mammy da ke binsa a baya ta tsaya tare da buɗe idonta tana kallon duk abin da ke faruwa.
Wani irin baƙin ciki da ɓacin rai suka sake taso mata.
Ta sauke idanunta ƙasa, yayin da zuciyarta ke ci da wutar masifar abin da take gani. Ita a ganinta, saboda ya rainata ne ya sa a matsayin mai aikin ta ya tsaya yana kula mata.
Ta ɗaga kai ta kalli Ummul da ta sunkuyar da kanta ƙasa, har yanzu wayar na hannunta yayin da zuciyarta ke bugawa da ƙarfi.
Tsabar tsoronsa da kwarjininsa da suka mamaye dukkan zuciyarta ya sa ta ji kamar ta yar da wayar ta gudu.
Amma saboda taurin kanta da kudirin da ta ɗaukar wa kanta, ta daure.
Cikin daburcewar harshe ta ce,
“I'm so... sorry. Dan Allah, Daddy Zeey... I just want your...”
Ba ta ƙarasa maganar ba.
Sai ta ji an fizge wayar daga hannunta da ƙarfi, har sai da hannunta ya yi ƙara.
A razane ta juyo.
Idanunta suka sauka a kan Mammy, wacce ke tsaye a tsakaninsu kamar boss.
Ganin irin kallon da Mammy ke mata ya sa ita ma ta tsuke fuskarta, tana jiran idan rashin mutunci za a yi a yi saboda yadda ta kware a kansa, ba ta tsoron uban kowa.
Ganin haka yasa Habi dake tsayenesa dasu kadan, ta ƙaraso da sauri tana rike hannunta Ummul din da ta cika fam saboda bakin ciki.
Mammy ta zare idanunta daga kan Ummul ta mayar kansa.
Shi ma ita yake kallo
Dama tijara ta yi niyyar masa, sai dai ganin yadda fuskarsa take a ɗaure kamar yadda ta saba gani, ya sa ta fasa.
Yana tsaye babu alamar komai a kan fuskarsa. Daga ƙarshe ma, kawar da kansa ya yi gefe, kamar ba saboda shi komai ke faruwa ba.
ganin kamar tashin hankali ne ke kokarin faruwa a wajen.
Yasa hankalin mutanen da ke wajen ya fara dawowa kansu,
Nan take wasu suka fara kus-kus din cewa, akan saurayi ne suke faɗan.