BA SO BANE?

Chapter 15

by @hafsatwaziri1122

BA SO BANE.

Story📃 writing
by

Hafsat waziri

Young talent writer's 

•Yota•


Page 15


I Dedicate this book to
 Nanakhadii 💅📕_



Tana niyyar barin wajen, ta juyo ta balla masa harara da jan tsaki tana faÉ—in,

"Follow now, womanizer kawai. Mtsssss"

Ta fice daga supermarket É—in fuu, kamar za ta tashi sama.

Da kallo kawai ya É—an bita har ta fita, sai kuma ya janye idanunsa ya mayar kansu Ummul da ke tsaye har yanzu.

A hargitse, Habi ta sauke kanta ƙasa saboda gwarjinin da ya yi mata.

Yayin da Ummul ke tsaye, ta yi shiru. Duk da tana da abin faɗa, sai ta zaɓi yin shiru saboda tsoron kar ya dizgata a gaban Habi.

Tana ji tana gani ya kama hannun Afaf tare da É—aukar Ajmal, suka bar gurin, aka bisu da siyayyarsu.

Wani irin ihun takaici ta yi tare da buga ƙafarta a ƙasa da ƙarfi.

A hargitse ta ce,

"Na rantse da Allah, ko mutuwa matarsa za ta yi, sai dai ta mutu, amma sai na aure shi."

Ta yi maganar cikin tsananin ɓacin rai, zuciyarta na tafasa saboda haushi da tsanar Mammy da suka cika zuciyarta.

Baki Habi ta taɓe ta ce,

"Ai na faɗa miki tun farko, kika ƙi yarda. Su fa mazan auren nan, duk yadda za ki yi ba za ki samu kansu ba, saboda matansu sun riga da sun gama da su. Ni gani ma na yi kamar ta riga ta mallake shi, tunda har umarnin da yasa meta a waje take ba sa, kuma babu musu ya je din."

"Ba mallake shi ta yi ba. Ko wankewa ta yi ta ba shi ya sha, sai sun rabu. Kin ji na rantse ko? Wallahi ban haƙura ba."

"Lallai kam, sai ki dage k..."

A zafafe ta É—aga hannu tare da faÉ—in,

"Mtsowww ya isa Don Allah, Habi, kar ki sake ba mini rai."

Ta wuce fuu kamar za ta tashi sama.

Baki Habi ta sake taɓewa tare da sakin munafukin munafikin murmushi, tana jin daɗin duk abin da ya faru yanzu, tare da addu'ar Allah Ya sa kar Ummul ta samu kansa. Saboda ta san idan har Ummul ta same shi, to ita samunsa zai yi mata wahala.

Ita yanzu har ta sa a bi bayansa, a gano mata inda yake.

Da wannan ta juya ta bi bayan Ummul da ta fita.

Mammy kuwa, tana isa gaban motar ta window ta yi hurgi da wayar. Tare da buɗe motar a fusace ta shiga, ta rufe murfin da ƙarfi kamar za ta ɓalla shi.

Kasa zama ta yi saboda yadda zuciyarta ke tafasa.

Ta zauna kusan mintuna biyar ita kaɗai a cikin motar, bai fito ba. Hakan ya sa ta kifa kanta a jikin kujerar motar tana tunanin irin wulaƙancin da za ta yi masa.

Tun da ya fito ta zuba masa ido tana kallonsa ta madubi, har ya iso ba ta sani ba.

Da kallo ta bi sa har ya shigar da yaran. So take ta yi masa masifa, amma yadda ta ga ya yi kicin-kicin da fuska ya sa ta ji duk ta rasa ƙarfin gwiwar cewa komai.

Shi kuwa, shigewarsa ya yi, ya zauna a mazaunin direba. Ko kallonta bai yi ba, kamar ma Allah bai halicci mutum a wajen ba.

Ya tada motar suka bar gurin.

Tafiya suke yi babu wanda ke magana a cikinsu. Duk da yadda masifa ke cinta a rai, amma ta kasa.

Gashi su Ajmal ma duk sun yi barci, hakan ya ƙara sa motar ta yi tsit sosai.

Cikin dakewa ta yi tsaki tare da mayar da kanta gefe tana kallon hanya, kamar wanda za ta wa magana yana waje, ta ce,

"Ko kunya mutum bai ji ba. A gaban mutane ma sai ya nuna kansa."

Kamar zai share, sai kuma ya yi magana cikin muryarsa mai sa Æ´ammata da yawa mutuwa a kansa ya ce.

"Abin kunya ya wuce wanda mutum ya yi a gaban kowa. Ina ruwanki da ita?"

Ya yi maganar ciki-ciki.

Ɗago kai ta yi da sauri tana kallon bayansa. Cikin ɓacin rai ta ce,

"Ni kake mayar wa da magana? Kai har ka isa ina magana kana yi? Waye kai? Mind you, kai fa kawai direba ne da ke jiran wata ya yi a biya ka salary ka je ka kashe tarin matsalolinka, sannan ka sake jiran wani watan.

Saboda haka ka kula da maganganunka. If not..."

Sai kuma ta yi shiru tana huci kamar wacce ta yi dambe.


"Otherwise, are you going to fire the employees?"

Ya yi maganar ba tare da ya juyo daga driving É—in da yake yi ba.

Cikin mamakin jin ya yi magana da Turanci, saboda dama a tunaninta ɗan ƙauye ne.

Ta ce,

"Har da kai zan haɗa na kora, womanizer kawai. Aikinka shi ne ka tuka ni, ka riƙe min jaka, kuma ka buɗe min ƙofa, ba neman mata ba. Idan har ka sake kallon wata da waɗannan idanun naka masu kama da na mujiya, sai na ɓatar da kai a duniya."

Ta faɗa cikin matsanancin ɓacin rai tare da dukan bayan kujerar da yake zaune.

Idan har su Afaf da ke barci sun motsa, to shi ma ya motsa. Balle ya nuna mata ya san da shi take ba.

Za ta sake magana, ya taka birki da ƙarfi.

Har sai da ta yi gaba ta yi baya da ƙarfi, ta buge kanta. Wayarta da ta jefa a kan kujera ta gangaro ta faɗi ƙasa.

Ai kamar an kunna famfo, haka ta dinga masifa kamar za ta ari baki. Muryarta har rawa take yi saboda kukan da ke ƙoƙarin cin ƙarfinta, tana dannewa saboda kada ya ji.

Shi dai yana zaune yana sauraren duk abin da take yi, amma ko sau É—aya bai nuna ya san ma tana yi ba, balle ya tanka.

Hakan da ya yi kuwa ya ƙara fusata ta da cimata rai, saboda ta tsani tana magana a yi mata shiru. Ita da har so ake ta yi mata masaga saboda a kula da ita. Amma shi babu ruwansa, bai ma kula da ita ba, balle ya ba ta haƙurin da take son ji.

Har suka isa company, ba wanda ya sake yi wa wani magana a cikinsu.

Sai ita da ta gama masifar ta yi shiru tana satar kallonsa lokaci zuwa lokaci.

Har wajen da bodyguards É—inta ke zaune ya gangara ya kashe motar.

Suna ganinta kuwa, gaba ɗaya suka miƙe jahpat har da da sauke ajiyar zuciyar ganin ta dawo lafiya.

Da sauri É—aya daga cikinsu ya zo ya buÉ—e side É—in da take.

Sai dai ko motsi ba ta yi ba, bare ya sa ran za ta fito.

Ganin haka ya sa ya ja baya.

Ƙin fita ta yi. Ita a dole sai ya fito ya buɗe mata.

Shi kuwa ya share ta kamar bai fahimta ba.

Aiko ta cika ta yi fam. Dama a ƙulle take da shi, ai ko ta fara zazzaga masa masifan da ta koya a jiya.

Sam hayaniya ba halinta ba ce, amma daga jiya zuwa yau ta zama ƙaramar mafaɗaciya.

Wani banzan kallo ta watsa masa, cikin É—aga murya ta ce,

"Buɗe min ƙofa mana!"

A hankali ya lumshe idanunsa. A ransa ya ce,

"Zata fasa min dodon kunne."

A zahiri kuwa, tsaki mai tsayi ya yi, fuska a haÉ—e.

Ya fita daga cikin motar, ya zagaya, ba tare da ya kalleta ba ya buɗe mata ƙofar.

Ko kallonsa ba ta yi ba. Ta fito ba tare da ta sauke handbag É—inta ba, ta wuce kamar za ta bankaÉ—e shi. Ya matsa da sauri.

Ganin ta shiga cikin companyn ya sa ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi sosai tare da murza goshinsa da hannu ɗaya, yayin da ɗayar ke riƙe da gwangwaninsa.

A hankali ya ce,

"Gaskiya kana ganin rayuwa, GiÉ—aÉ—o."

Ya yi murmushi mai kayatarwa, kamar wanda yake ganin abin nishaÉ—i.



"Idan kere na yawo, zabo na yawo, dole a haÉ—u."

Ya ƙarasa maganar tare da leƙa cikin motar yana kallon su Afaf da barcinsu ya yi nisa sosai.

Tsayuwarsa ya gyara yana tunanin yadda zai yi da yaran nan.

Ji ya yi masa tamkar ya tafi ya barsu a nan, amma sun yi barci kuma ba zai iya ba.

Ko ba komai, yaran sun shiga ransa, duk da ya san kila daga yau ba za su sake haÉ—uwa ba.

Ganin jakarta da ta bari a kan kujera ba ta ɗauka ba, ya sa ya yi ƙaramin murmushi yana kare wa ɗan madaidaiciyar jakar kallo.

Waige-waige ya fara yi ko zai ga Huba ko Adamu su taya shi É—aukar yaran, amma ba wanda ya gani.

Suhairat ya hango tsaye ita da wata ma'aikaciya suna jiran abin hawa.

Ya santa, but bai san sunanta ba. Hakan ya sa ya tsaya yana faman cizon lips.

Suhairat da ke tsaye kamar an ce mata ta juya, ta juyo da kanta saitin da yake.

Cikin sa'a kuwa suka haÉ—a ido.

Ganin ta gan shi ya sa ya yi mata alamar ta zo da hannu.

Tsananin mamaki da farin ciki suka kasa ɓoye akansu a fuskarta saboda jin daɗin yau shi ne yake kiranta.

Ta sansa anguwarsu É—aya ita da shi. Hasali ma, makwabta ne, tsakanin gidansu da gidan Baffa babu nisa.

Suna haÉ—uwa kullum idan ya je, amma ko kallo ba ta ishe shi ba, kuma ko ta gaida shi baya amsawa.

Wannan dalilin ya sa ta shiga kokonto, kila ba ita yake kira ba.

Hakan ya sa ta nuna kanta alamar, "Ni?"

Kamar a mafarki ta ga ya gwada mata kai alamar eh.

Ai da sauri ta sa hannu ta shiga gyara fuskarta tare da hijabin jikinta.

Jikinta har rawa yake yi, ta shiga takowa da saurin da ya fi kama da gudu.