PART 1 AI A JIKIN LEDAR BIREDIN AKWAI LAMBAR WAYAR SHI🤣 FATIMA DAHIRU
PART 1 AI A JIKIN LEDAR BIREDIN AKWAI LAMBAR WAYAR SHI
PART 1 🤣🤣AI A JIKIN LEDAR BIREDIN AKWAI LAMBAR WAYAR SHI🤣🤣
Haihuwa ce akayi mana a Kano, d'iyar wata 'kanwar maman mu.
Duka 'yan uwa da dangi muka had'u muna muhawarar yadda wannan tafiya zata kasance, ga rashin kud'i, kowa sai zullema tafiyar yake, wannan yace " ba shida kudi-wannan yace "Ai haihuwar ta ta farko dashi akaje suna.
'Karshe dai kowa ya kawo uzurin shi aka rasa masu zuwa, daga 'karshe dai aka yenke shawarar ni inje, tunda ban ta'ba zuwa ba kuma banda nauyin kowa.
Haka aka had'a gudummuwa mai d'ari biyar mai d'ari uku, aka tattaramin abinda zan kaima mai jego, a haka dai tafiya ta dawo kaina.
Zuwa can 'kanwa ta Shamsiyya ta ce "Ah! Ke kad'ai zakije suna, aiko zaki ci dad'i, don waccen haihuwar ta farko da tayi mukaje suna mu uku daga ni sai Asiya sai Raulatu ai munci dad'i, da safe fa shayi da biredi aka kawo mana, ai mujin ta manajan gidan biredi ne."
Na ce "Allah shine manajan gidan biredi?!"
Shamsiyya ta ce "Shine mana, ai a jikin ledar biredin ma number shi akasa, saboda shine manaja, gashi zaki soya ragon suna ke kad'ai, ai ba 'karamin dad'i zaki ci ba, don Allah ki d'an 'kullo min wani, yadda koda anzo an kasa na dangi, nawa ya 'kara yawa, kinsan kason naman nan fici-fici ake yinshi."
"Huwumh! Ke dai bari, ai harna 'kosa ranar sunan tazo, nama dai kam saina barshi.
Haka na gama shiri na tsaf! ana saura kwana biyu suna na shirya, na nufi Tasha, na hau motar zuwa Kano.
Kuna so kuji yadda wannan tafiya tawa ta kasance ? To inga ruwan comment da liking da sharing, masu copy and past ban amince ba, share kawai nace ayi.
Jama'a kwana biyu kunji ni shiru, to da izinin Allah yanzun kam na dawo, aci gaba da bani had'in kai musannan wurin yin share
Fatima Dahiru Funtuwa Binta✍