PART 1 😯KUN TA'BA JIN AN KAMA MAYYA A GRA?😯

PART 1😯 KUN TA'BA JIN AN KAMA MAYYA A GRA? 😯

by @fatimadahirufuntuwa

KUN TA'BA JIN AN KAMA MAYYA A GRA?

     Wannan tambayar da taita yawo a social media ta sa na tuno da wani labari daya faru a kaina, wasu shekaru can baya da suka wuce. 

    Yaro na ne ya fara rashin lafiya, zazza'bi haka da ciwon kai, aka bashi magani tsawon kwana biyu, jiki dai yana nan, sai aka kaishi kyamis, aka fara yi mashi allura, tsawon kwana uku, ciwo dai sai gaba yake, anata jiran sau'ki shiru.

     Bayan yayi sati d'aya kwance, ciwon yaci jikin shi sosai, don har ma kanshi da harshen shi ya kare, baya iya magana, komai ma bai san yanayi ba, a lokacin yaron bai wuce shekara bakwai ba.

    Da jiki yai zafi, sai mukace to a tafi asibiti, duk a tunanin mu idan akaje Asiti gado za'a bamu saboda yanayin yadda jikin yaron yayi sanyi.

   Innar mu ta d'auki yaro ta goya a baya, zuwa can bayan azahar sai gata ta dawo, wai basu basu gado ba, Allurai sukayi mashi da magunguna, har baban mu nata fad'a yana cewa  "Wannan yaron ruwa ya kamata a 'kara mashi, funda ko magungunan ma baya iya sha, don bai san ma inda kanshi yake ba, bai kamata ace ba'a  kwantar da yaron nan ba."

    Zuwa can bayan la'asar jikin yaro fa yayi zafi, sai aka kira wani likita mai kyamis nan cikin unguwar mu yake, shima yana taimakawa sosai.

   Yana zuwa kuwa ya ce "yaron nan ruwa yake bu'kata.

   Aiko ya jona mashi ruwan nan, muna zaune muna gadin shi, ruwa nata tafiya.

    Zuwa can gab! Da magari ba ruwa ya  'kare, a lokacin yaron ya iya bud'e idon shi ya d'an fara kuka. 

   Ai farkowannan da zaiyi, tunda dama kamar ya suma ne, sai ya fara da  gane-gane.

   'Kanwata Shamsiyya na zaune ya kalle ta ya fara magana  a hankali cikin zafin ciwo, ya ce  "Aunty Shamsiyya ga wani tsofo nan ya ma'kale a jikin ki."

      Shamsiyya ta ce  "Mee!?"

    Ya ce  "Wani Aljani ne gashi nan a jikin ki tsofo."

    Shamsiyya ta mi'ke tsaye ta daka tsalle, ta fasa ihu, tana innalillahi wai Aljani a jiki na! "

    Kai! Abu fa kamar wasa sai ya ce "Ga zomo nan zai shigo d'akin nan."  zuwa can kuma  "Ga mage nan ba'ka, ga bera nan ya shigo."

    Irin dai kana nan abubuwa haka ya rika gani, zuwa can daya fasa wata kuwa, ya mi'ke a tsorace ya ce  "Ga kura nan." ya rugo da gudu yana kankame mutane, abufa ya rikice sosai, muka fara yi mashi addu'o'i, Iklas- Fala'ki-Nasi-Ayatul kursiyyu, kowa na karanta abinda yazo bakin shi ana tofa mai, amma yaron nan bai daina gane gane ba.

    Tun muna d'aukar abin kamar wasa, har muma jikin mu yayi sanyi muka tsorata, ganin yadda yaron ya gigice da irin tsoron da ake ba shi.

   Zuwa can ba sai masu iskokai suka fara tashi ba, ni kaina ban san inada Aljanu ba sai ranar, yo tashin hankali ya'ki karewa.

   Aljanu fa suka hau, akai turanci-akai yarbanci - akai inyamuranci, yaron nan bai daina gane-gane ba, saima abinda yayi gaba.

   Da aka gama tashin iskokan abin dai ba sau'ki, sai aka yanke sharar aje wurin malami a anso taimako.

IDAN NAGA RUWAN COMMENT DA LIKING DA SHARE INCI GABA DA BAKU LABARIN, IDAN BANGA NI BA KUWA GASKIYA SAI KUN JIRA.