NANNY(MAI RENO)

22

by @jamilaumarjanafty

*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Na*
 
*AISHA ALTO*
*JAMILA UMAR(Janafty)*

*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*

*Sanyi flusher!* 
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. 
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*

*Tightening set na hade mace ta  dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.

*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*

*Muna da gimbiyar zabuwa  da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.

  *BABI NA ASHIRIN DA BIYU*

Sai da Farida taci uban kukanta ta gode Allah, sannan ta share hawayenta ta miƙe jiki a sanyaye ta shiga toilet tayo wanka ta fito ko mai bata tsaya shafawa ba ta zira doguwar rigar atamfa a jikinta ta zauna a bakin gado ta zabga tagumi ta tsurawa guri guda idanu tana saƙe saƙe a zuciyarta.

Bayan sallar Isha'i Tahir ya shigo gidan, tana jin motsin shigowarsa ta miƙe a sanyaye ta ɗauki hijabinta ta fice ta nufi ɗakinsa, yana ƙoƙarin shiga toilet ta shigo, kallo ɗaya yayi mata kawai ya ɗauke kansa gefe ya buɗe ƙofar toilet ɗin zai shige abinsa, da sauri ta isa gabansa ta riƙo hannunsa ƙwallah na taruwa a cikin idanunta ta marairaice gwanin tausayi tace "Don Allah don sonka da Annabin rahama kayi haƙuri kazo muje ɗakin Mufeeda...Akwai maganar sa nakeso nayi daku ne dukkanku...Don girman Allah Abban Basma kar kace a'a..." Ta faɗa da magiya ƙwallah na gangarowa daga cikin idanunta suna zubowa kan fuskarta, tsam yayi kawai ya tsura mata ido yana kallonta kamar ba zai je ba, can sai ya janye hannunsa a nata ya raɓa ta gefenta ya nufi ƙofa, da sauri tabi bayansa suka fice suka nufi ɗakin Mufeeda.

Suna shiga suka iske su Innaro da Iya dasu Basma da Bassam a ɗakin tare da Mufeedan suna hira, a hankali ta taka ta shiga tsakiyar ɗakin ta tsaya agaban Tahir daya tsaya ya zuba mata ido yana kallonta yayinda gaba ɗaya su Iya da Innaro dasu Basma suma suka zuba mata ido suna kallonta, a hankali ta durƙusa a gaban Tahir ta zube gwiwoyinta a ƙasa hawaye na zubo mata ta duƙar da kai cikin rawar murya tace "Don Allah don Annabi don girman Allah...Kayi haƙuri ka yafe min na tuba..Ka yafe min duka laifin dana aikata, bazan sake ba, na yarda nayi kuskure kuma zan gyara halayena..." Ta faɗa tare da fashewa da kuka, a hankali yace "Na yafe miki...Allah ya yafe mana baki ɗaya.." Wani sanyin daɗi taji ya ziyarci zuciyarta har sai da ta saki ƙaramin murmushi ta juya tana share hawayen fuskarta ta matsa gaban Mufeeda dake zaune ta duƙar da kanta tana wasa da farcenta, a hankali Farida ta riƙo hannunta tana kallon cikin idanunta take faɗin "Nasan nayi miki abubuwa da dama waɗanda bazasu lissafu ba Mufeeda..amma karki dubi munin abunda nayi miki ki dubi girman alkhairina agareki ki yafe min kuskurena..nasan na cutar dake sakacina ya jefaki cikin wani yanayi, na cuci rayuwarki...Kuka ya hanata ƙarasawa. Da sauri Mufeeda ta faɗa jikinta itama ta fashe da kuka tana faɗin "Bakiyi min komai ba Momy..kuma duk abunda ya faru dani daga Allah ne dama dole sai ya faru dani ban isa na kauce masa ba, kuma na ɗauki hakan a matsayin ƙaddarata, don haka ki daina cewa na yafe miki bakiyi min komai ba, nice ma zan roƙeki yafiya...Don Allah ki yafe min, kuma duk abunda kika yi min wanda na sani da wanda ma ban sani ba duka na yafe miki..." Ta faɗa tana ƙara ƙanƙame Faridan a jikinta, ƙara rungumeta Faridan tayi itama suna sharɓan kuka, Tahir dai na tsaye yana kallonsu jikinsa duk yayi sanyi, a hankali Farida ta janye Mufeeda a jikinta ta durƙusa agaban Iya itama ta roƙeta ta yafe mata sannan ta durƙusa agaban Innaro itama ta yafe mata sannan Basma da Bassam suma duk suka yafe mata. Nan take taji ta fayau zuciyarta tayi mata wasai taji kanta kamar an sauke mata wasu tulin kaya.

Haka a ɓangaren Tahir yaji daɗin abunda Faridan tayi sosai a ransa har hakan ya nuna a fuskarsa kuma yana fatan Allah yasa hakan ya zama gaskiya har a zuciyarta tayi tuban ba tuban muzuru ba.

Miƙewa tayi a hankali ta ƙarasa inda gadon jariran yake inda suke ciki a kwance luf abinsu ta tsaya tana murmushi ƙwallah na taruwa a cikin idanunta ta buɗe ta ɗauko macen ta riƙe sannan ta ɗauki namijin shima ta haɗasu ta rungume a jikinta tana jijjigasu kafin kuma ta cirosu daga jikinta ta tsura musu ido tana kallonsu har bata san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba, ƙarasa tayi gaban Tahir da fara'a a fuskarta tana faɗin "Abban Basma zoka gani, wallahi yaran nan tamkar Basma da Bassam lokacin dana haifesu suna jarirai.." Ta faɗa tana ƙarasawa gabansa, yana dariya ya karɓi namijin a hannunta yana kallonsa yace "Wallahi haka nace nima.." Innaro tace "Nima dai haka nace.."
Tahir yana murmushi yace "Ai kamarsu da 'yan uwansu ce ta fito sosai."  Ya faɗa yana miƙa mata yaron. Karɓarsa tayi ta miƙa masa macen tana faɗin "Yanzu da wane suna za'a dinga kiransu kenan..?" Ta faɗa tana kallonsa, yana dariya yace "Mufeeda wane suna za'a dinga ce musu..?" Ƙara sunkuyar da kanta ƙasa tayi cike da kunya tana faɗin "Duk abunda kuka zaɓa yayi Momy.." Ta faɗa tana murmushi. Farida tace "To shikenan, namijin zamu dinga kiransa da Ayman macen kuma mu ce mata Airah.." Da murna Basma tace "Yauwa Momy...Wallahi sunan yayi mana daɗi sosai..kuma ya dace dasu..Allah ya raya mana ƙannen mu.." Da Ameen duk suka amsa, kafin daga nan suka shiga hirar yanda taron suna da bikin tariyar zata kasance, kowa ka gani fuskarsa cike da fara'a da farin ciki take, har ta su Basma da Bassam ma walwalarsu ta ƙaru a wannan daren, sai farin ciki da annashuwa suke.

Sun daɗe sosai a ɗakin suna hira har ƙarfe 10:30pm kafin Tahir da Farida sukama su Innaro da Iya da ita kanta Mufeedan data fara barci sallama suka fice tare dasu Basma da Bassam kowa ya shige ɗakinsa bayan sun musu sallama suma, suka nufi bedroom ɗin Tahir.

Suna shiga ciki ta janyosa jikinta ta rungumeshi ta baya ta zagaya hannayenta a saman cikinsa tana shafo ƙirjinsa a hankali cike da wani irin salo, juyo da ita yayi gabansa ya tsura mata idonsa, kasa jurar irin kallon da yake mata tayi ta zame hannunta ta faɗa jikinsa ta ƙanƙamesa ta fashe da kuka mai tsuma rai da zuciya tana ƙara bashi haƙuri.

A hankali ya fara shafa bayanta alamar lallashi yana hura mata iskar bakinsa a cikin kunnenta cike da wani irin salo mai tafiyar da ruhi haɗe da zuciya mai ƙara azalzala wutar ƙauna, ƙara shigewa jikinsa tayi ta lafe tana karɓar saƙonsa, a hankali ya fara tafiya da ita zuwa gurin gadon dake ɗakin tana jikinsa a narke tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa mai sanyaya zuciya, a haka suka isa gaban gadon, cike da shauki ya ɗagata cak ya ɗorata a saman gadon ya kwantar da ita flat, sannan ya hau kai shima bayan ya zare rigar shadda dake jikinsa yayi saura daga shi sai dogon wandon kayan.

Wani irin shauki da tsantsar soyayyar mijinta Farida taji tana ƙara kamata, tana daga kwancen tana kallonsa ya hayo saman gadon ya fara ƙoƙarin zare mata rigar jikinta, wani irin daɗi da farin ciki mara misaltuwa Farida taji sun kamata lokaci ɗaya daɗi ya baibayeta ta ɗago ta faɗa jikinsa tana ji a ranta yau zata gwada masa tsantsar ƙauna wacce bata taɓa nuna masa ba, zata nuna masa tsabtatacciyar ƙauna mara iyaka wacce babu algus a cikinta, zata sa yayi alfahari da ita ta tsaya a ransa ya kasa gogeta a zuciyarsa. Cike da salo ta jawo makunnin wuta ta kashe wutar ɗakin, ɗakin yayi duhu kaɗan ta miƙe ta sauka daga kan gadon ta cire rigar da kanta yayi saura daga ita sai pant da bra suma a hankali ta zaresu ta koma saman gadon ta haye jikin Tahir dake zaune mamaki ya gama cikasa ya zuba mata ido kawai yana kallonta, ganin irin kallon da yake mata mai cike da mamaki yasa ta ƙara zagewa ta jawosa jikinta ta haye saman cinyarsa a hankali ta fara shafo fuskarsa zuwa leɓensa da wani irin salo kafin ta ɗago haɓarsa tana kallon cikin ƙwayar idanunsa ta haɗa bakinsa da nata, wani irin lumshe idanu Tahir yayi cike da jin daɗi ya ƙara matso da ita jikinsa sosai ya kamo tattausan harshenta ya fara mata wani irin tsotsa mai tayar da hankali dasa mutum mantar dashi kansa waye. 

Sake zagewa Farida tayi sosai ta kamo harshensa ta shiga aika masa da wani lafiyayyen kiss mai kashe jiki da zuciya, Tana yi tana shafar sumar kansa tana tura yatsunta ciki tana masa wani irin salo kamar tafiyar tsutsa, a haka ta sauka har kan gadon bayansa tana shafa bayan tana masa tafiyar tsutsa kamar tana masa susa, idan ta ja har tsakiyar bayansa sai ya gantsare ta dawo da hannunta sama tana shafo ƙeyarsa, in banda sauke numfashi da gurnani babu abunda Tahir ke yi, hakan ya ƙara mata ƙwarin gwiwa ta zage sosai ta dage ta shiga nuna masa tsantsar ƙauna mai cike da nuna tattali da tsantsar so mai tsayawa a zuciya.

Duk wani salo mai kashe zuciya da saka rai cikin tsantsar buƙatuwa, sai da Farida tayi amfani dasu gurin kashe jikin Tahir ta mantar dashi kowa da komai a wannan dare, ta zage ta nuna masa cikakkiyar kulawa da tattali.

Wani al'ajabi da mamakin Farida ne ya kama Tahir, sagale ya tsaya kawai yana kallonta a ransa yana tambayar kansa dama kenan ta iya komai take tsaya masa kamar gunki ta barsa yayi kiɗinsa yayi rawarsa? Ko ta nuna masa bata son komai da yake mata ita ta gaji bata iya ɗaukar lalurarsa? Lallai Farida yau ta bashi matuƙar mamaki, kuma yaji kimarta da darajarta sun fara dawowa a zuciyarsa.

Sosai Farida ta zage ta kafa tarihi mai tsayawa a zuciyar Tahir a wannan dare, tayi duk abunda tasan zai faranta ransa ya manta da komai da kowa sai ita. A ɓangaren Tahir kuwa shima tsayawa yayi tsam ya nuna mata tsantsar kulawa mai dasa farin ciki mara gushewa da walwala mai matuƙar tasiri a zuciyar duk wasu ma'aurata masu so da ƙaunar junansu.


Washegari da sassafe Farida ta tashi bayan sunyi wanka da Asuba sunyi sallah Tahir ya koma barci ta fice ta nufi ɗakin Mufeeda, lokacin ko tashi Mufeedan bata yi ba tana ta sharar barci abinta, sai Innaro dake zaune akan darduma tana lazumi Iya kuma na kichen zata dafa ruwan wanka, bayan sun gaisa da Innaro ne ta fice taje ta haɗo ruwan zafi a babban robar wanka, Innaro tace ta bari za suyi musu wankan taje ta kula da mijinta, amma Farida tace A'a su bari ita zata wanke 'ya'yanta tas. Haka kuwa akayi ta ɗauko jariran a cikin gadonsu ta fara yiwa Ayman sannan ta yiwa Airah itama, ta shiryasu tsab cikin lafiyayyun kayan sanyinsu masu kyau da tsada, Innaro na zaune tana kallonta gwanin sha'awa. Sai data gama musu sannan ta fesa musu turare mai sanyin ƙamshi ta sakasu a cikin shawul ta miƙawa Innaro su sannan ta miƙe ta ɗauke robar ta kai Toilet d'in Mufeeda ta zubar da ruwan ciki, sannan ta sake haɗawa Mufeeda ruwan wankan itama ta fito ta tasheta, ta cire kayanta suka shiga toilet. Farida Ita ta taimakawa Mufeeda tayi mata wankan jego tsab ta gasata sosai Mufeedan sai sunkuyar da kai take tana jin kunya amma ita Farida ko a jikinta ta zage ta gyarata tas ta rufa mata babban tawul suka fito..Suna fitowa ta zaunar da ita a bakin gado ta ɗauko mai ta bata ta shafa kafin ta buɗe akwatinta ta ciro mata wata atamfa riga da zani ta ajiye mata, ta koma ta ɗauko humra da kulacca da Innaro tazo mata dasu ta bata ta shasshafa a jikinta sannan ta saka kayan ta zauna ita kuma Farida ta fita. Bata jima da fita ba ta dawo ɗauke da babban kofi da kayan tea a hannunta, Mufeeda dai sai binta da kallo kawai take tana jin tsananin farin ciki a ranta, Farida kuwa tana jin bala'in kishin Mufeeda a ranta amma tana dannewa kada a gane, a haka ta haɗa mata tea mai kauri ta miƙa mata ta tura mata bread da filet ɗin soyayyen kwai ta tasata gaba sai da taci tayi dam zufa sai keto mata take, haɗa kayan Farida tayi ta fitar dasu ta kai kichen sannan ta dawo ta haɗa kayan da Mufeedan ta cire da waɗanda ta cirewa jariran ta fita dasu can bayan gidan ta wankesu tsab ta shanya sannan ta dawo lokacin ƙarfe 8:20am tace Mufeedan ta koma ta kwanta ta huta bari taje su gama haɗa breakfast da Iya, Innaro ta amsa tana sa mata albarka ta fita a ɗakin ta nufi kichen. 


Lallai Farida ta sauya sosai kuma duk wanda ya santa a ranar ya ganta dole zai gane hakan, Iya ma sai kallonta take suna aiki, tare suka gama haɗa komai suka jera a dinning table kafin ta nufi bedroom, tana shiga ta samu Tahir ya tashi yana Toilet yana wanka. Tuɓe kayan jikinta tayi itama ta shige toilet d'in don suyi wankan tare.

Mintuna talatin suka ɗauka a toilet d'in sannan suka fito ɗaure da tawul a jikinsu suna rungume da juna suna dariya, ita ta shafa masa mai ta shiryashi tsab sannan shima ya tayata ta shirya ta feshesu da turarensa mai daɗi da sanyaya zuciya ta ɗauko hularsa zanna bukar ta kafa masa yayi kyau sosai tana kallonsa tana jin wani kishi na taso mata tayi saurin kawar dashi ta riƙo hannunsa tana murzawa a nata cikin kwantar da murya ta fara faɗin "Abban Basma ya kamata fa a siyo kayayyakin da Mufeeda zata saka tunda tare za'a haɗa da taron suna da fitar biki..." Ta faɗa tana sumbatar tsakiyar tafin hannunsa, lumshe idonsa yayi ya kamota jikinsa yana faɗin "To shikenan, zan turo miki kuɗi ta account ɗinki sai ku sayi abunda ya dace.." Ya faɗa yana sakar mata kiss a goshinta, tana murmushi ta kama hannunsa suka fice daga ɗakin suka sauka ƙasa.

Sai da suka shiga ɗakin Mufeeda ya dubasu ita da yara suna ta barci suka gaisa da Innaro da Iya dake shirya Naila kafin suka fice bayan Farida ta ɗauki Naila tace su Innaro su fito Dinning suci abinci, suna fitowa daga ɗakin suka samu Basma da Bassam sun fito daga ɗakinsu wanda da alama sun shiga su gaishesu ne basu samesu ba, da murna suka nufesu suka faɗa jikinsu, Tahir ya ɗago Basma daga jikinsa yana murmushi yake faɗin "Karki kayar da Daddy mana..ko bakisan kin girma bane..?" Ya faɗa yana jan kumatunta, turo baki tayi ta duƙa ta gaisheshi ya amsa cikin sakin fuska tare da shafa kanta, sannan ta juya ta gaishe da Farida dake kallonsu tana murmushin jin daɗin gyara rayuwarta da tayi, shima Bassam ya gaishesu kafin Tahir ya kama hannunsu yace suje Dinning su karya, da sauri Basma ta zame hannunta tana faɗin "Zanje na ga ƙannena da Aunty Mufeey tunkunna Daddy.." Ta faɗa tare da ƙoƙarin rugawa da gudu, saurin kamota Farida tayi tana harararta tace "To barci suke yi..baza kije ki tashesu ba.." Ta faɗa tana nufar dinning, ba don Basma taso ba tabi bayanta tana turo baki, Tahir dai na kallonsu yana murmushi bai ce komai ba.

Sai da suka gama karyawa sannan Farida ta rakashi harabar gidan ya shiga mota Garzali yaja har suka fice tana ɗaga masa hannu kafin ta koma cikin gida ta shiga bedroom ɗinsa ta gyarashi tsab ta fesa room freshener mai ƙamshi ta saka turaren wuta mai daɗi ta janyo ƙofar ɗakin ta fice..tana saukowa taji alert ya shigo wayarta tana dubawa taga transfern kuɗi ne masu yawa Tahir yayo mata tana murmushi ta nufi ɗakin Mufeeda tace Innaro ta shirya zasu fita kasuwa.

Haka kuwa akayi ita da Innaro suka je kasuwa ta narkowa Mufeeda siyayya sosai ita da jariranta ta haɗo musu kaya masu kyau da tsada, a nan kasuwar ta samu haɗaɗɗen shagon ɗinki ta bada kayan Mufeeda ta zaɓar mata ɗinkuna masu kyau da ɗaukar hankali, bayan ta biya kuɗin ya faɗa mata ranar da zata zo karɓa suka dawo gida.

Duk waɗannan abubuwan da Farida take yi kawai tana daurewa ne don tayi alƙawarin ta gyara halayenta, bazata ƙara yin abunda tasan zai sa wani yaga baƙinta ba balle mijinta da iyayenta da 'ya'yanta su tsaneta su dinga jin haushinta ba, saboda haka ma duk wasu ƙawayen banza tayi watsi dasu ta daina bi ta kansu, yanzu ta gyara rayuwarta zata tsaya ta kula da mijinta da 'ya'yanta.


Bayan kwana biyu da haihuwa Goggo Abu tazo duba Mufeeda da yaran taji daɗin yanda ta ga Farida ta koma ta saki jikinta tana ta kula da Mufeeda da yaranta nan ta tarasu tayi musu nasiha sosai mai ratsa jiki da zuciya. 


*BAYAN SATI ƊAYA...*


Ana gobe taron suna da yamma Farida ta ɗauki Mufeeda suka tafi cikin gari ta kaita wani haɗaɗɗen Saloon inda take zuwa aka tsantsara mata ƙunshi da kitso ta biya kuɗin suka dawo gida. Suna zuwa suka tarda Ashe dasu Muda da Laila sun zo, nan Ashe tayi ta yaba kyaun da Mufeedan tayi, ita dai Farida sai dai tayi dariyar yaƙe kawai tana ƙoƙarin danne abun data ji yana taso mata.

Washegari tunda sassafe Zahra matar Ishaq da 'ya'yanta suka zo. Nan suka haɗu dasu Innaro da Iya da Farida da Ashe suka shiga aiki baji ba gani, don ba wani taro za'ayi sosai ba, iya yasu yasu ne kawai suka cika gidan.
Farida da kanta ta kira mai kwalliya tazo har gida ta tsantsarawa Mufeeda kwalliyar data ƙara fito da ita tayi kyau sosai, ta ɗauko mata wani haɗaɗɗen leshi blue mai adon stones cikin waɗanda aka ɗinko mata ta bata ta saka tayi cacas a ciki, nan kyaun Mufeeda ya ƙara fitowa sosai ita da kanta Farida sai da ta kalleta ta ƙara kallonta don gani take kamar ba Mufeedan data sani bace a gabanta, Farida da kanta tayi mata lafiyayyen ɗaurin ɗankwalin daya sake fito da kyawun fuskarta tayi fayau abinta sai ɗaukar ido take tana ƙyalli. Haka jariran suma expensive kaya aka saka musu haɗaɗɗu masu kyau da tsada sai ƙamshi suke suna walwali abinsu, Basma da Bassam ma da Naila sunyi gayu abinsu sun sha kyau suna rungume da ƙannensu Ayman da Airah sun hana kowa ɗaukarsu sai dai ka gansu a hannayensu duk inda sukai dasu Naila na nan nane dasu itama.

Taro yayi taro an gama lafiya an tashi lafiya, sai dare Ishaq yazo ya ɗauki Zahra da 'ya'yansa bayan Farida ta haɗa musu kayan suna cike da leda ta rakasu har gurin mota sukayi sallama ta koma cikin gida, don yau duk a gajiye take ko hirar dare da suka saba yi a ɗakin Mufeeda bazata tsaya yau ayi da ita ba, wanka kawai zatayi ta haye gado kafin kuma uban gayyar shima ya dawo.


Washegari Ashe dasu Muda da Laila suka koma Ɗanbatta suma, nan Innaro da Farida da Iya suka cigaba da kula da Mufeeda da yaranta, Basma da Bassam kuwa indai suna gida kullum suna nan liƙe da ƙannensu haka Naila sai tasa rigima itama sai ta ɗaukesu.

Wannan kulawar da Farida ta gani kowa na ba Mufeeda shiya ƙara saka mata kwaɗayin son taga ta sake haihuwa itama, don taga duk wata kulawar Tahir da tattalinshi ya ɗorasu duka ne akan Mufeeda da 'ya'yanta.

Ranar da Mufeeda tayi arba'in a ranar Innaro tace bazata ƙara kwana a Kaduna ba, itama Ɗanbatta zata koma, haka kuwa akayi Tahir da Farida suka haɗa mata sha tara ta arziki da kaya niki niki Garzali ya maidata.


Nanny(me reno) Free book ne amma ga waɗanda ba za su iya jira ba akwai completed documemt 1k ne ku tura ta wannan acct ɗin 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK ko tuntuɓar waɗannam lambobin ***
***.

*Janafty*
*Aisha Alto...*