JODAH

25

by @sadisakhna


 

 

______👑 *JODA* 👑_____ 

 

              

 

Na  

 

*Sadi-sakhna* 

 

Ƴar mutan Jama'are 

 

 

THE TRIO OF TALES  

(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)  

 

@sadisakhna on Arewapen 

@SAKHNA03 On Wattpad 

*** on Whatsapp 

 

 

LITTAFI NA 1 

 

 

👑*Warƙa ta (25)*👑 

 

 

Murmushi nakeyi,idona yana kan Rubutun danake a jikin allo,amma hankalina kuma yana kan shafamin gashin tsuntsu da Hammar yake a bayana,kasa jurewa nayi hakan yasa na juya ina kallonsa nima ina dariya. 

 

"Miye haka Hammar dan Allah ka barni na ƙarisa mana, ina kayi alƙawarin daga na gama wannan zaka cewa Baba guru ka warke ko?" 

 

"Inace ke jaruma ce ai bakyajin cakulkuli....ahah sai kin iya Jefar da takobin hannuna tukunna idan muna gwaji" 

 

"Ahah bamuyi haka dakai ba,kace daga na jefar da mutummutuminnan a cikin rabin sa'a to na gama koyan faɗan kare kai. Sai gashi na iya jefar dashi a cikin daƙiƙa sha biyar ma,dan haka ni wlh bazan yarda ba,wayo kawai kakemin"  

 

Na ƙarisa maganar ina zuba shagwaba wanda nasan a duk lokacin danayi yakan rikitashi,sakin baki yayi yana kallona,ban ankara ba naji yajawoni jikinsa ya matseni gamm. Wannan baƙon yanayin na shiga,wanda zuwa yanzu na fara sabawa dashi,kallon cikin ido mukeyi ban ankara ba sai jin muryar Addah rahila nayi akaina. 

 

"Uhm uhm Masoya kuyi haƙuri amma zan katse muku hanzari" 

 

Tayi maganar tana murmushi tareda ƙarisowa inda muke,tana goye da Jaririnta wanda yafara wayo yanata bacci. 

 

 

Duburburcewa nayi na tashi tsaye daga jikinsa ina kakkaɗe ƙasar dake jikina cikin wayancewa,abinda na kuladashi kuma yabani mamaki shine yanda Addah rahila ko a jikinta da yanda takalli muka kasance, haka nan shima uban gayyar yana kishingiɗe yana kallona fuskarsa ɗauke da murmushi,hankalinsa kwance ya gaisheda Addah rahila,itama ta amsa cikin fara'ah.  Nayi matuƙar mamakinsu su dukka biyun,to kodai bata kalli abinda mukayi bane,amma ita ai ba makahuwa bace ta gani. Na kula tun ranar data kalli ya sumbaceni lokacin daya rakoni da daddare ta nuna razanarta,amma washagari dayacemin yana son yagana da ita na haɗasu. Tun daga wannan haɗuwar komai suka tattauna oho banida masaniya,to daga ranar bata ɗaga hankalinta ko kaɗan idan ta ganni a tareda shi. To kodai biyanta yayi kai,amma Addah Rahilah batayi kama da irin waɗannan mutanennan ba. 

 

"Kayi haƙuri Hammar zan ɗan ari mutuniyar taka ummu hajar na ƙiranta,na kula kwannannan ko kaɗan baka barmana ita ka ƙwaceta dukka" 

 

"Ahah ni na isa Addah Rahilah,gata nan dama yanzu zamu tashi mungama bitar karatu ne" 

 

"To shikenan anata ƙoƙari,kizo muje idan kingama kaɗe kaɗen ana jiranki,ummu hajar nason magana dake tazo nemanki bakyanan shine tace nayi ƙiranki. Kuma da alama na gaggawane" 

 

Harna fara bin bayanta naji muryarsa. 

 

"Uhmmm Joda nace ba........." 

 

Waigawa nayi na kalli har ya tashi ya taho inda nake,kallon idona yakeyi da wannan kaifin wanda yake yankar zuciyata a kwananann dashi. 

 

"Shine zaki tafi babu ko sallama" 

 

Yayi maganar cikin wani salo mai kashe jiki,lumshe idona nayi kafin nace. 

 

"Wanne sallama zanyi maka bayan ko ban dawo ba zan kalleka ka fara zagaye cikin makarantar nan nemana idan an jima" 

 

Ƴar dariya yayi dan yasan haka halinsa yake kwanakinnan. 

 

"Ya zanyi ne bana gajiya da kallonki ne,da fari kizamemin magani,amma yanzu na gano rayuwata ta ta'allaƙa akai tayanda bana iyawa saidashi. Kije ki dawo kiji wani zance" 

 

"Wanne iri ka shirya faɗamin daga ina kake kuma waye kai?" 

 

"Ehh dukka haddashi,sannan da sanarwa Guru almahdi cewar na warke ko kin manta" 

 

"Ina kuwa zan manta,ina nan ina sane dama zuba maka ido nayi naga shin zaka faɗamin ko kuwa tunda kace idan lokaci yayi zan sani" 

 

"Najidai yanzu yimin sallama na anan" 

 

Yafaɗa yana nunamin gefen kuncinsa inda ya lotsa,tun yana bani mamaki har ya far a dainawa,idan aka cemin zai iya irin wannan abubuwan bazan taba yarda ba,yanda yake tsare fuska amma ni yayi tamin abu tamkar bashi ba. 

 

Saurin manna masa sumbatar nayi a wajen dayace sannan nayi saurin barin wajen kada yasake tsayar dani. Tunani kala kala ne a cikin raina. Kafin nayi ƙaramin murmushi. Hammar kenan ina mamakin yanda kake rena tunanina,amma babu komai a je a hakan tunda shi ka biɗa. 

 

Banyi sansaninmu ba saina wuce kai tsaye inda ummu hajar take,a wajen marasa lafiya na sameta,tayata nayi ta ƙarisa abinda take kafin nabi bayanta xuwa turakarta na wanda take ganawa da marasa lafiya. 

 

"Wai watanninnan ina kike shiga ne ba'a ganinki,sai anyi ta nemanki tukunna?" 

 

"Kiyi haƙuri ina wani uzurine shiyasa,amma zan gama nan kusa Insha'allahu" 

 

"To ba wannan ba takarda ta taho daga fada cewar anayi miki ƙiran gaggawa,jikin gimbiya Asmah ya rikice,sunso tahowa da ita to bazata iya zuwa ba dole saidai kije" 

 

"To tunda har an aiko takarda kam ai kamata yayi ke kije ummu hajar,tunda ni baiwa ce kuma dokane bama fita daga cikin Jami'a" 

 

"Nima zanso naje ɗin saboda babbar damace da kowa keso,to amma sunanki suka ambata a jiki cewa ke suke so kije ba kowa ba,kuma na gaggawane gacan keken doki yana jiranki,hatta Akwatinki na bada taimakon gaggawa addah Rahilah ta haɗomiki saboda karki bata lokaci" 

 

Jimm nayi ina tunani a raina,bazaiyiwu nace ahah ba,to amma tafiya ta ban faɗawa Hammar ba shima babbar matsalace wanda nasan koda na faɗamasa bazai taba amincewa ba idan yaji cewar cikin gidan sarautane kuma akwai yaƙinin zamu haɗu da Yerima kabeer. Kawai barina je tunda na gaggawane har zanje na dawo,nasan zayyi fushi amma na lokacine idan na bashi haƙuri zai haƙura. 

 

Da wannan tunanin na hau keken dokin dayazo ɗaukata muka bar cikin gidan sarautar,na bar masoyinnawa da dakon ganina da daddare domin ya fallasamin sirrin zuciyarsa,kuma yacika min alƙawarin daya ɗauka na bani ƴan ci na,kasancewar an fara shirye shiryen fara jarrabawarsu a watan gobe. Na zabi zuwa badan kar su ummu hajar suji haushi ba,badan inada sha'awar taimakon Gimbiya Asmah ba sai yaƙinin ganin mahaifiyata,wanda bana mantawa lokacin da Dogarai suka kamata naji ance gidan sarauta za'a kaita,to wannan babbar dama ce dazanyi amfani da ita wajen dubata. 

 

Tunda muka fita daga cikin makarantar nake kalle kalle,wani hawayene daya zubomin na yi saurin ɗaukewa da hannuna,babu abinda nake tunawa sai biyo hanyar danayi shekara shida da suka wuce lokacin inajina tamkar jaririya wacce a lokacin ta buɗe idonta,batasan wacece ita ba kokuma ina zata shiga. Bayan hakan abubuwa da dama sun faru,har kullum ina godewa baba yakub duk da cewar yarabani da mahaifiyata amma kuma yayi min silar samun abubuwa da dama wanda kuɗi ko dukiya bazasu taba siyansa ba. Tafiya muke ina kallon sauye sauyen da gurare da dama suka samu har muka shiga cikin gari muka kama hanyar Masarautar Daular Songhay. 

 

Baki na wangame ina kallon katafaren ƙawataccen ƙofar shiga cikin masarautar. Girmansa yakai iya girma tamkar giwayene zasu wuce ta wajen,anyi masa Zane kala kala harda zinare,wanda ya ƙara ƙwatashi dakuma bashi gwarjini mai amsa amo. Dogarai ne da dakaru suke kai kawo a bakin masarautar suna tare dukkan wanda zai shiga koya fita,sai ya bada bayani gamsashshe kafin a bashi damar wucewa,muma da namu keken dokin yazo saida yayi magana dasu kafin suka ɗaga mana hannu muka wuce. Nidai yi nayi tamkar na mamuce,wannan wayon danake ganin inada shi duk nemansa nayi na rasa dana fito cikin duniya. 

 

Wani babban gini na hango a tsakiyar cikin gidan sarautar,mai tsayi da faɗi,tun daga nesa zaga jiyo gizonsa ya cika maka idanuwa. Dama haka gidan sarautar yake,gaskiya dole su dunga taƙama suna nuna zasu iya taka kowa. 

 

Wata hanyar muka nufa ba inda babban ginin yake ba,saidai shiɗinma babbane sosai,duk inda muka ce bayine suke ta kai kawo,sai rarraba ido nake ko zangano mahaifiyata a cikinsu,amma ko mai kama da ita bangani ba,koda dana ciki ma nasan zayyi wuya na ganta,kasancewar kayansu dukka iri ɗayane mata da maza. 

 

A haka har muka ƙariso Ginin da muka nufo ɗin,wasu bayine amma kayanxu na nuna su manyane suka iso inda muke,babu yabo babu fallasa sukayimin iso zuwa wani sashe dayafi ko ina ado da cika ido a wajen. Suna gaba nidai ina binsu har muka shiga ciki. Da Sunkia madina muka haɗa ido,hakanne yasa nayi saurin zubewa a gabanta cikin girmamawa kaman yanda kowanne bawa yakeyi,amsawa tayi kafin tace. 

 

"Sannunki da hanya mun tasoki kina wani abun ko? Zanso kaiki masauƙi ki huta kici abinci,amma kiyi haƙuri babu halin hakan domin bamuda lokaci. Marar lafiyar tana cikin mawuyacin hali." 

 

"Ahah karki damu ranki ya daɗe ai tafiyar bamai wahalarwa bace zan iya dubata babu gajiya" 

 

"To shikenan ki taso mu shiga ciki ki fara aiki" 

 

Duk da tana ƙoƙarin wajen ganin ta mutuntani saboda ganin su suke nema a wajena,amma a cikin muryarta ina jin kaman yazama dolene na aiwatar da aikin banida wani zabi. Haka suke halinsu ne haka,ji suke tamkar an haifemu ne domin muyi bauta a garesu. 

 

Tun kafin mu ƙarisa shiga nake jiyo sautin numfashinta mai ƙarfi yana tashi. Akwatin dayake hannuna na ajiye a gefe kafin na isa inda take na tsugunna ina kare mata kallo. Ta ƙara haske tayi fayau da alamun jini ya zuba a jikinta sosai. Idanuwanta na buɗe nagansu fari sol,hakama tafin hannunta da fatar bakinta alamar jikinta yafara shiga hatsari na rashin jini. 

 

Kallon baiwar dake gefenta nayi,da alama baiwarta ce inaga. 

 

"Idan bazaki damu ba ina buƙatar ruwan ɗumi Da  gishiri a ciki bamai yawa ba" 

 

Batayi musu ba ta tashi ta fita waje Zuwa dashi. Kafin ta kawo ɗin  nayi amfani da wannan lokacin ina dudduba jikinta. Bugun jijiyar ta na hannu baya yi sosai alamar zuciyarta tayi rauni,amma kuma babu alamar hauhawa na gudun jininta,saima nakeji kamar yayi ƙasa fiyeda na mutum mai lafiya. 

 

Daddana cikin nayi ya dunƙule a waje guda baya motsi sosai duk tabashin danayi,hakan yana nuna akwai matsala kenan. 

 

Tare suka shigo itada ungozamar dake dubata,wanda nasan taxone domin taga mai zanyi wanda ita ta gagara yi. 

 

Hannuna na saka na wanke sosai a ruwan kafin na buɗe cinyoyinta,ƙunzugu na kalla wanda akayi mata da alama na zubar jini ne. Cirewa nayi na ajiye a gefe,ɗauke komai nayi daga raina na wanke wajen,ƙalubalen aikinmu kenan ya gaji haka,ina kallon hawaye yana fita daga idonta,da alama tana sane da dukkan abinda yake faruwa da ita wannan karon,saidai tsananin azaba da yanda jikinta yayi laushi bazata iya yin komai akai ba. 

 

Hannu nasaka har cikin mahaifarta,babu abinda yasami wajen kawai zubar jinin da tayi a farkone ya saka jikinta yin laushi ta gagara turo ƴar dakanta,shima kansa bakin wajen rashin karfin jikinta yasa ya gagara taimaka mata wajen turo abinda yake cikinnata,kuma da alama akwai bayan gida a cikin hanjinta shima ta gagara fiddashi. 

 

Wai akwai aiki babba na faɗa a raina. Goge gumin daya keto min nayi kafin na kalli ungozamar dake gefena. 

 

"Akwai aiki babba saidai idan aka dace babu wata matsala Insha'allahu,yanzu dai ina buƙatar aska mai kaifi sosai,a sakata a wuta tayi ɗan zafi kafin nan a sakata a cikin ruwan zafi ta tafasasu tareda wannan zaren dazan baki sai a kawomin su a cikin kaskon daga an cire daga kan wuta,sannan ina buƙatar mutane guda uku zan musu wani gwaji son samu maza" 

 

Wani irin kallo take bina dashi,tanaso ta tambayeni mai zanyi da waɗannan abubuwan amma kuma saita fasa,ta amsa da to kawai ta fita. 

 

Bayin da suke gefena na kalla suma na cemusu. 

 

"Kuyi mata wanka da ruwan ɗumi ku sanya gishiri kaɗan da kuma wannan ruwan,na faɗa ina miƙa musu ruwan khal. Sannan ku saka mata iya zani a jikinta sannan ku kwantarta akan gadon kafinnazo" 

 

Da to suka amsamin daga nan na miƙe na fita a ɗakin,har wani jiri nakeji saboda yunwar da tayimin kamun kazar kuku. 

 

Da Sunkia madina na haɗu da wata kuma wacce itama da alama Matar sarkince don tasha kayan alatu. 

 

Maganar dasukeyi suka tsaya suna kallona domin suji mai nake buƙata,durƙusawa nayi cikin girmamawa kafin nace. 

 

"Inason ganawa dake ranki ya daɗe,ko kuma zan iya magana babu matsala" 

 

"Ehh karki damu kiyi maganarki wannan mahaifiyarta ce Saurayina Abidah ta iso yanzunnan daga Daularsu,munyi tunanin sai gobe zata iso ashe tana hanya yau,yanzu take cewa zata shiga ta dubata nace ta dakata tukunna ki gama aikinki" 

 

"Na kalli jikinnata, tayi zubar jini sosai wanda ya janyo jikinta ya sake kuma yayi laushi,tsokar da suke turo jariri na kunkuminta sunyi rauni bazasu iya hakan dakansu ba dole sai an taimaka mata,sannan abinda yake cikinta shima yana cikin haɗari,dan haka yana buƙatar a fitar dashi cikin gaggawa idan ana son ceto ransa." 

 

"Uhmm yanzu tana cikin wannan halin amma ban kalleta a wajen duba marasa lafiya ba zagaye da manyan Masu magani ana ƙoƙarin shawo kan rayuwarta?  Sai wannan kaɗai" 

 

Kallonta nayi naga yanda take bina da kallo marar daraja,banyi ƙasa a gwiwa ba na gaisheta,amma a kalma ɗaya kawai ta amsamin. 

 

"Nayi tattaki na ɗauko doguwar tafiya nazo domin naga ƴata,saina tarar wai kaf ƙasar a rasa wanda zai dubata sai an ɗauko baiwa daga wani waje,wannan raini ga jinin sarauta kamar Asmah har yaushe,gaskiya kin bani mamaki Madinah,nayi zaton yarda da amanar dake tsakaninmu ya wuce haka....... 

 

 

 

 

Sadi-sakhna ce ✍🏼 

 

Comment  

Like  

Share  

Follow