Episode 1
*_๐ป๐๐๐๐๐ผ๐ ๐ฟ๐๐๐๐...๐ป_*
*_Rabi'a wakili_*
*_ุจูุณูู ู ุงูููููู ุงูุฑููุญูู ููฐูู ุงูุฑููุญููู _*
*_Book 1_*
*_Episode 1_*
_______________________
Kowane ษan adam yana ratsa sararin duniya ne ษauke da wani tsari na daban wanda Allah Ya tsara mana a rayuwa. Wannan tafiyar ba ta da wata fuska ta zahiri, kuma ba ta da siffa ko launi da za a iya kallo da idanu muddin mutum yana raye, sai dai nauyinta da zafinta suna sauka ne kai tsaye a kan zukatan da ke ษauke da ita. Akwai lokutan da walwala da daษi ke bayyana a fili tamkar farin wata, akwai kuma lokutan ฦalubale masu ษaci da ke girgiza jiki da firgita tunani, har ya kai ga mutum ya ringa gani a ransa tamkar dukan kofofin mafita da hanyoyin samun sauฦi sun riga sun datse, an bar shi shi kaษai tsakanin tsananin fargaba da fita tsammani. To sai dai, a daidai lokacin da hasken rayuwa ya dusashe, sa'ad da dukan kewayen mutum ya turnu da baฦar inuwa ta tsananin rudani, makami mafi ฦarfi da ke share fagen samun mafita shi ne natsuwa ta dindindin gami da jajircewa ta gaskiya. Kowa ya sani, Zaman jiran dadi, sai mai babban bargo.Haka kuma, duniyar nan ta zama tamkar igiyar ruwa, tana juyawa da kowa yadda ta ga dama, ba ta taษa tsayawa a guri guda ba. Saboda haka, ikon tsayawa tsayin daka a lokacin da wannan igiyar ruwan ke kwasar mutum zuwa ga gaษar da bai sani ba, wani babban matsayi ne da kwarjini na daban wanda ba kowa ke iya kaiwa gare shi ba. Mutumin da ya siffatu da wannan juriya, ya riga ya buwayi dukan wata barazana da kowace irin maฦarkashiya da ke tunkaro shi daga kowane sashe na rayuwa. Jajircewa kuwa ita ce danyen ฦarfin da ke tursasa wa mutum ci gaba da takawa, tana tilasta wa ฦafafunsa ci gaba da takawa a ฦasa ko da gangar jikinsa ta gaza ษaukar nauyin kanta saboda tsananin gajiya da wahala. A cikin tsarin tafiyar duniya, fuskantar matsaloli ko kaษaitawa a cikin damuwa ba ฦasฦanci ba ne, kuma ba yana nufin an ฦare ba ne; wata koyoce ta musamman, wani darasi ne mai tsada da ke gina mutum, yake ฦara masa kaifin basira domin ya shirya shi da dukan dambarar da zai fuskanta a gobe. Wannan rayuwar ba ta taba tafiya daidai da burinmu ko yadda muke tsara ta a cikin zukatanmu ba. Idan igiyar ruwan ฦaddara ta taso da ฦarfi, tana juyawa ne kawai a kan sahihin tsarin da Mahalicci Ya riga Ya ฦaddamar tun kafin halittar komai, domin a ฦarshe kowa ya gane cewa matsalolin da ke zuwa ba su da manufar ruguza mu ko share mu daga doron ฦasa, illa gyara mu da za su yi, su fito da ainihin juriya da ฦarfin da ke ษoye a cikinmu. Duk wanda ya fahimci wannan ma'ana ta sirri, ba ya fargabar tsayawar al'amura, kuma ba ya tsoron shiga cikin sabon rikici ko wata turkaturka ta rayuwa, domin ya san cewa tafiyar duniya ba ta taba kayar da wanda ya iya dakatawa ya bar wa Allah ikonsa ba. Haka kuma, mutumin da ya karษi dukan abin da ya zo masa da zuciya ษaya gami da gamsuwa ta ciki, ya sanya juriya a matsayin garkuwarsa ta yaฦi, sannan ya dogara ga ALLAH, lallai ne zai riski nasarar da aka riga aka rubuta masa, zai kuma taka da ฦafafunsa a kan daukakar da aka yi masa alkawari ko da dukan hanyoyin da za su kai shi gurin a halin yanzu sun Lulluษe da baฦar inuwa ta duhu mai ban tsoro. Domin a ฦarshe, rayuwa gaba ษayanta, arziฦi, matsaloli, da daukaka, duka suna naษe ne a cikin babban shirin nan na ฦaddara, wata doguwar hanya ce da kowa ke bi yana takawa daki-daki cikin duhun dare, ba tare da ya san wace irin dambarawa ko jarrabawa ce ke jifansa a gaba ba, sai dai kawai amincewa da juriya da kuma dogara ga ALLAH, shi ne hasken da ke haska masa kowane taku.
________________
Kano state Nigeria.
Yammace saฦaliyan ana gab da magrib, wani mutum na hango, bai cika kiษa ba, Sauri yake ta zubawa kamar wanda zai tashi sama, babbar rigar da ke jikin shi wacce ta sha ruwa sai tashi da sauka yake, kamar wanda zaiyi tsuntsuwa ya fire sama, tafiya yake baya ko kallo inda yake saka ฦafa, kamar yadda baisan inda yake takawa ba, haka zuciyar shi ta kasance tana chan wani wajen daban. Burin shi kawai ya koma gida, ko ya samu sarari na daga abinda ya taru yai masa yawa.
Tun da ya doso farkon layin anguwar ake binsa da kallo, kallon da ke mishi inkiya da gagarumin matsala, eh kam dole ya ambaci haka da matsala mana, dan babu rana na ALLAH da zata zo ta wuce bai samun irin waษan nan idanun a kansa ba, wanda ba yau farau ba, yana kuma da babban tabbacin ba ฦarshe bah kenan, matuฦar yan kokawan gidan sa suna nan, ai shikenan.
A maimakon yanayin sa ya chanza, amma ina babu alamun haka tattare da shi, inda sabo ya saba, dai dai da kwayar zarra hakan bai taษa ci masa tuwo a kwarya ba, idan sun kashe kansu maฦabarta har yau har gobe kai har wani shekara bata cika ba, toh akan mi zai na dinga wahalar da rayuwar sa a kansu, su bar sa da abinda yake damun sa mana.
"Mmmtwwwsss" ya ja doguwar tsuka dai dai ฦofar wani ษan matsakaicin gida da hayaniya ke tashi daga ciki babu ฦyaukyautawa, wanda sautinsa yake tashi ana ji har ฦofar gida da maฦota.
Shiga ciki yayi, Inda ya tarar da su a hargitse, sai faman yaษawa junansu magana da son maida martani a zafafe cikin fusata dan a kular da abokin faษan. Hakan ba sabon abu ba ne cikin rayuwar gidan ba, domin ga wanda bai san su ba sai ya yi tunanin sun haษa tsatson ฦดan dambe ko kuma maguzawa, ta yanda ba sa raina ruwan shuka, kamar jira suke yi a ce kule suce as.
ฦauke kai ya yi tare da jan doguwar tsaki da nufin barin wajen. Babu shiri babu tsammani ya ji sauฦan bokiti a bisa goshinsa, take ya cije leษen sa tare da dafe goshinsa da tafukan hannayensa saboda azabar zafin da ya ziyarci har cikin ฦoฦon kansa, nan take malolo makure sa a wuya.
Shiru ya mamaye wajen tamkar an yi ruwa an ษauke, duk wannan hayaniyar ta gushe tamkar yadda ruwa da sabulu suke gusar da ษauda. Ba komai ya haddasa hakan bah illa ganin kwaษar da suka kwaษa, watsar da makaman yaฦin da suka yi niyyar tadawa suka yi yayin da kowa ya sha jinin jikinsa.
Da sauri ya ciro hannun sa akan goshin dan tabbatar wa shin da gaske ษin sun raunata sa? Cikin sa'a ba ciwo ba kuma jini, a ษoye ya sauke ajiyar zuciya da hamdala ganin ba su zudda masa da jini a banza da wofi ba, dan ba yi da hanyar kuษin magani balle a ษallo masa wata jinyar.
ฦara ษaure fuskarsa ya yi waje guda tamkar magribar ษinya, ya na cin magani haษi da bin su da kallon ษaya bayan ษaya, Ji ya yi wani sabuwan baฦin ciki ya ฦara shigewa kai tsaye har cikin ฦasan zuciyarsa, dan takaicin ganin yadda suka nuna rashin damuwa sai ma kallon da suke bin sa dashi kamar da shi za su ci gaba da dambarwan, nan take malolon sake linkuwa fiye da wanda yake ciki, a yanzu hakan kuwa ya taimaka wajen ฦara tunzira shi, ga takaicin su da takaicin ya dawo bai samu abin da ya fita nema ba, abin sai ya haษu ya haษe masa goma da ashirin. Hakan ya ฦara taimakawa wajen tafasar da zuciyar dake kwance cikin ฦirjinsa.
A fusace ya soma cewa "Uban wa ya halbo ni? Wallahi idan kuma ba haka Allah sai na lahira yafi ku jin daษi, a waje mutum bai huta ba, a ce cikin gidansa ma ba zai huta ba? Duk kun ฦarar da ni dan masifarku kamar wanda Maye ya yi wa ajiya. Na ce uban waye ya halbo Ni?" Ya ฦare maganar yana mazurai cikin maษaukakin ษacin ran da ya bayyana har a cikin kalmominsa.
Duk tsam sukayi suna binsa da kallo, kamar sunga wani sabuwar halitta, ko wani majigi. ko ma ace kamar waษan da basu gane yaren da yake yi ba ma bare su fahimci inda ya dosa.
manyan mata ne su uku da yan mata uku, chan ฦarshen gidan wata matashiya ce zaune a ฦofan madafa sai dai ta juya musu baya, duk wannan masifar da suke ko ษagowa ta kalli halin da suke ciki batayi ba, bare ta ce wani abu, idan ba ka lura ba, ba za kace akwai mutum a wajen ba, dan gaba ษaya yanayin matashiyar ya nuna bata ma san halin da suke ciki ba. "Ooh ga ษan iska na magana ai dole ku maida ni tataccen haihuwar ฦasar gada! Dan....."
Cikin sauri mama ta tare shi jin zai fara sakin ashariya tace "haba mana mallam kasan dai mutum ษaya zaiyi wannan aiki ba wai duk mutanen da suke a wajen nan ba koh? bare kuma kazo kana wa mutane kwakwazo, da son tarawa mutane jama'a cikin gida?, Kai ma kasan ba aikin kowa bane sai ta yar gaban goshin ka, dan haka ka juye a kanta ba wai waษan da basu san hawa da sauka ba".
Wata muguwar kallo ya wurga mata wanda yake cike da takaici da ษacin rai mai tsanani, ba mama da yake watsa wa kallon ba har su Umma duk sun sha jinin jikin su suka tsime waje ษaya, sanin kansu ne kwaruru ba sa'an wake bane, banda ALLAH yasa gwiwa ta faษi ฦas wanwar da wane mutum naji mutuwa, Inda a lokacin da yake amsa sunan sa ne, da wata magana ake ba wannan ba, a fagen rashin mutunci baya ya basa ba gaba bah, duk wani nau'ikan rashin mutunci da suke fama dashi a ฦarฦashin ฦafar sa suke, dan kuwa kam sai sun jira sa.
"Nace uban waye ta hal ban? Wan nan itace ta ฦarshe ba zan kuma magana ba, amma zan yanke hukunci ga wanda yayi bai faษa ba, dan nasan ko wace, walau yayi ma mutum daษi ko akasin haka". Ya faษa a tsawace har jijiyoyin wuyansa suna tashi.
Binsu da kallo ya shiga yi kafin ya gyada kai yana ฦara tabbatar da cewa eh kam lailai ya cika ษan iska haihuwar ฦasar gada, yo to inba ษan iska ba waye zai ta ษaษatu a rasa mai tanka mai? Nan da nan ransa ya ฦara ษaci, fiye da wanda ya shigo dashi gidan, Fiye da wanda suka ฦara masa.
"wa.." da sauri umma ta katse shi dan tasan shi tasan halin shi sai dai ma su ba wasu labari, dan ba mutunci ne dashi ba, yanzu yana iya mata duk abinda ya ga dama gaban kishiyoyi, "kayi haฦuri mallam nice! hakan ta faru cikin rashin...
"Isassa, shafaffa da mai, hamshaฦiya, wallahi ALLAH ni nasani, tunani na bai tafi a banza ba dan nasan kaf gidan nan kece zaki aikata min haka, san nan tsabaragen rainin da kikayi min ina tambaya sai kallo na kike da fiฦiฦin idanun ki Kamar kinga mahaukaci sabon kamu"
Nifa ba da gangan na jefe ka ba, bare ka taso ni gaba da maganganu kamar wacce ta burma maka wuฦa a ciki, alhalin ษan bokiti ne fah ya same ka a ka, naga kuma bai kumbura ko zub da jini bah! Ka daiyi haฦuri Mallam ba kai nayi niyyan halba ba sai matar ka zuhura, amma Wallahi ko yanzu ษin ma ba sha tayi ba, ALLAH sai nayi abinda nayi niyya".
Nan fa ta shammaci kowa ta wurga wa Inna lariya, cikin Sa'a kuwa ya sauka kan goshin ta, dake lariyar ฦarfe ce Kuma ta ษan ษalle hakan ya bada daman kartan mama a goshi kaษan.
"Kan bala'in nan......har ni zaki zubda wa jini? Lailai Rashida kin ษebo abinda yafi ฦarfin ki, ya kuma fi ฦarfin dangin ki". Tana kaiwa nan tahau dube duben abinda zata maida raddi itama.
"Ke awaaa....? Tsaf umma ta haษiye Maganar da tayi niyyar furtawa, sakamakon ganin mama ta dunfaro ta wuฦa kai tsaye.
tabbass ta tsure jinin jikin ta duk sun dawo kan kumba, sai dai gefe na zuciyar ta tana gaya mata kar ta gudu, idan ta gudu ai sai mama taga lagwan ta.
ฦara gyara tsaiwa tayi tana jiran tazo ษin taga iya gudun ruwan ta. Saidai kafin mama ta ฦaraso gare ta Samha da Hanifah sun riฦe ta kam wanda hakan yaja mata dakatawar dole.
"Ku sake Ni, wallahi ni ko ita cikin gidan nan, har ni zata zubda wa jini?"
"Ke Hanifah ku sake ta! Ke kuma idan kin fasa chaka mata wukar baki haihu ba, na bar muku fili, ku cigaba amma a bakin auren ku, ni Muhammad na gama magana".
Shiru ya mamaye ilahirin gidan kaman anyi ruwa an ษauke, wanda har Abba ya bar wajen basu samun zarafin cewa uffan bah.
Shi kuwa yana gama faษin haka ya bar su nan tsaye ba tare da ya dube ko wanne su ba.
ษaukar buta yayi ya nufi hanyar makewayi. Anan ya lura da ita, daman duk ษinsu bai jituwa da ita dan bata bashi abinda yake so, wato kuษi!, shikuma mutum ne da idan kana bashi to fah zakuyi mutumci rana ษaya ka tsallake bakai haka ba, shikenan ka shiga sahun waษan da basu da amfani, shi yasa yaran duk basa basa wani girma, duk kuwa da cewa shi ya haife su. bayan su suna da yayu guda uku da suke a gidan ma'auri "sannu da zuwa Abba! Ina yini?" Ta miฦa masa gaisuwa cikin girmamawa,. ko kallo bata ishe shi ba, Ya shige banษaki, sai da ya fito san nan ya dube ta yace "gwara ki chanza mugun halin nan naki ki waye ki zama kamar sauran ฦดan uwanki,ba wai ki zauna kina jiran sai an miki ba! bani zaki taimaka ba sai kanki, shawara nike baki dan ki amfani kanki da ษan ki" yana ฦare faษin haka ya bar wajen.
Har Abba yayi alwalla yazo zai fita a gidan Basu samu zarafin cewa komai ba, dan maganar da yayi ya zame masu kamar gubar da ke ฦona jinin jikin ya hana Mutum moruwa haka suka kasance a tsai a nan kaman wasu mutum mutumi.
"masifar da kuke nima ya tsaya kanku! idan ku ka jiwa juna ciwo biyar na baza tayi kuka ba, idan kun so ku kashe kanku". Cewar Abba da ke shirin fita daga gidan.
Ganin fitar sa yasa duk suka watsar da makaman yaฦin su Kamar basu ne suka so tada wata babbar husuma a cikin gidan ba.
Sai dai ba'a hana ษan sabo da abu, nan fa suka koma kan wannan matashiyar dake a ฦarshen gidan dan duk maganar da Abba ya yaษa mata a kunnin su, nan fa suka shiga sukar ta da aibanta mata yaro, Kamar sun manta da ฦaddara tana kan kowa.
bata ษago ba bare ta nuna tasan sunayi, sai cigaba da kaษa miya da tayi. Wannan halin nata na nuna rashin damuwa na ษaฦanta musu zuciya, shi yasa basu cika bi ta kanta ba sai ta yaron ta wanda gaba ษaya bata ragi, tanan ne kuma mutum zai gane tana da baki da tsiwa. Sai dai duk da irin soyayyar da take wa Maher hakan bai hana ta tsayu tsayin daka wajen ba shi ingantacciyar tarbiyya da uwa ta gari take baiwa yaranta ba.
"Su inna an daiyi sallah, san nan dan Allah ku barta ta huta, ai ba kanta farau ba kuma ba ฦarau ba! ฦaddara ai tana kan kowa Haba mana" cewar Samha, ษaya daga cikin yan matan nan uku.
Doguwar tsuka umma taja haษi da faษin "Kece bakin ta, ita bata iya magana ba ne? Toh ahir ษinki! Kar ki kuma ana mata magana kina sa baki,nasha kwaษan ki bakya ji! Amma..." Ta ฦare maganar da jijjiga kai.
"Sa'a ki ka ci bakya a kusa dani da na buge maki baki gobe baza ki kuma ana ma wata magana ki saka baki bah" Cewar Mama..........โ๐ป
Toh jama'a wannan karan ina muka kawo kan mu ne haka?๐ค
***
Shere fisabilillah
***