Episode 2
🗻INUWAR DUTSE....🗻
_Rabi'a wakili_
Ep 02
Bismillahi Rahmanir Rahim.
★...
♡♡♡ ♡♡♡
__________
ꨄꨄꨄ
"O'o'o a gaiyar wa zaki taɓa min ƴa? tab da anyi tashin tashina a gidan nan! Bar ganin Mallam ya wani kafa doka Wallahi take shi zanyi, sai mi toh tunda nasan ba Ni ɗaya zan fita bah, bana kuma so ina wa yarinya ta magana wasu na saka baki, dan ku ɗin ma ba so kuke ba, dan haka kowa yaji da lalurar da ta dame shi banda shishigi, bama ka gama da taka matsalar ba kana shiga wani, ɗan daurawa kai abinda Allah bai ɗaura muku ba?".
"ALLAH sarki! ALLAH ya baki haƙuri, Daman daga ƙin gaskiya sai ɓata, ALLAH ya kyauta" ta ƙare maganar da miƙewa ta ɗauki buta dan alwalla. Sai ya rage da umma sai mama da suke ta antaya wa junan su kallon tsana. sauran yaran kam duk sun shige ciki. Ganin haka yasa suma ɗaura alwalla suka shige inda aka bar wannan matashiyar a wajen. Ganin duk sun bar wajen yasa ta sauke ajiyar zuciya ta ɗaura alwalla ta shiga wani ɗaƙi daban, kyakkyawa ce ajin ƙarshe fara fet masha ALLAH, tana da ƙira mai kyau da jan hankali.
Tana idar da salla ta fito dan cigaba da aikin da take daman bata gama ba. Shimfiɗa tabarmu tayi a tsakar gidan da yasha siminti ga yasha shara, ɗauko tuwo da miya tayi ta aje su anan. Shima na Abba ta aza masa bisa tabarmar da yake nashi. Har zuwa lokacin cikin su Umma babu wanda ya leƙo.
Komawa chan ƙarshen gidan tayi kusa da madafa ta zauna, tana ɗan danna wayarta da ta kasance yar shafa, sai dai ƙarama ce.
"Aysha!?" Matashiyar da take zaune ta ɗago cikin nutsuwar data riga tabi mata jiki da jini a hankali, haɗi da watsa mata manyan fararen dara daran idanun ta da suka kasance kamar mai mai suna walƙi. Ɗauke kai tayi ta maida ga abinda take. Cikin rashin damuwa yusrah ta furta "idan su umma sun fito kice musu na fita sauri nike bazan tsaya shiga wajen su ba" ɗagowa tayi ta duɓe ta a karo na biyu wanda sai yanzu ta shiga binta da kallo, sauke ajiyar zuciya tayi ganin kayan da suke jikin ta da ɗan sauƙi akan waɗan da ita karan kanta ke sawa a baya. Cikin sanyin murya ta furta "idan kinje karki daɗe, a matsayin ki na ƴa mace bai kamaci a ce kina waje a wannan lokacin ba, ki kula".
bata ko gama rufe baki ba umma ta chaɓe da faɗin "Allahu Akbar inji mai kiran sallah, iyeeee tubabba kewa wata wa'azi! Ikon Allah! Wai kin manta lokacin da kikayi naki ne, uban wa ya sani? Inace sai randa sakamako ya baiyana? Dan haka ki ƙyaleta ta sakata ta wala a gidansu, tana kuma tare da addu'ar uwa, dan ni ba irin uwarki bace da ta yasar dake ta gudu ta bar mana ke ciwon ba, bugu da ƙari in Sha Allah ƴata gata nan, gani nan bari nan kazan mayu, baza ta aikata irin naki ba". umma ta ƙare maganar cikin fusata.
inna da ta fito dan taji abinda ke faruwa ta furta "sakamako kuwa da guzirin É—an gaba da fatiha!!! dan an buga an buga an rasa yadda za'ayi da shi, shi yasa ya wanzu a yanzu yake rayuwa, idan ba dan haka ba baza mu san anyi ba" .
Da sauri ta rintse idanun ta da lokaci ɗaya suka kaɗa sukai jawur dan jin furucin inna, ji tayi har tsakar kanta kaman an kwaɗa mata guduma, danne zuciya tayi kawai ta miƙe tsaye ta nufi hanyar ɗakin da take rayuwa da yaronta, tasan zaman ta a wajen zasu tunzira ta ne ta yi abinda ba daidai ba, da hakan ya faru gwara ta bar musu wajen.
har ta kai ƙofa taji inna tana cigaba da faɗin "zamani ya chanza, budurwa zata aje yaro wanda ba'a san tushen sa ba, dan rashin ta ido idan akayi magana tace ta fusata akan ɗan...."
"yaro na ba shege bane" tana faÉ—in haka ta shige abinta tana jin zuciyar ta na tafarfasa bata juran a dinga aibanta mata Maheer a kunnin ta.
A ƙule da son ƙara ƙular da Aysha tace "Kin wa uwaki,bani ba, toh idan ba shegen bane, ki fito da uban shi mana..." Nan suka ci gaba da maganganun su na zagar mata yaro wanda duk mi suke faɗi kaf a kunnen tah, daga karshe ma earpiece ta maƙala a kunnen ta inda ta kure ƙara tana sauraran kira'a.
A chan waje kuwa kallon tsaf Yusrah tabi su da shi kafin ta nufi kofa da niyar barin gidan, har ta kama labule ta tsinkayi muryan mahaifiyar ta tana faÉ—in "ke yanzu duk rashin mutumci da yarinyan nan tayi mana baza kice komai bah sai dai ma kisa kai zaki fita?"
Juyowa tayi a hankali kamar wacce wuyar ta ke mata ciwo cikin cika ta furta "bani da ta cewa sai dai duk mi ya faru ku kuka fara, dan haka nayi nan" Tana gama faÉ—in haka ta fita daga gidan ba tare da jiran jin amsar umma bah.
Kafin dayan su ta kai ga cewa komoi sai ga Hanifah ta fito tana wani tashin kamshi wanda har shiga kai yake, ta haÉ—e cikin wata material fitted. Sai wani ya mutsa fuska take, yarinyar inna kenan cikin halin mahaifiyarta ba abinda ta manta bata É—auka ba, har taso ta fita a wasu wajajen daman ance Magaji mafiyi.
Ba tare da ta dubi ko wanne daga cikin iyayen su ba ta sai kai ta bar gidan ko mahaifiyarta bata sallama ba, a yadda ta nuna kamar bata san da wanzuwar su wajen ba, suma É—in cikin rashin damuwa suka É—auke kai.
Bangaren Aysha kuwa tunda ta saka earpiece bata yarda ta cire bah sai chan da ta daidaici lokacin shigowar Abba ta cire abin kunnin dan tasan yana shigowa ita zai hau kwalawa kira.
Ilai kuwa ba'a ɗauki mintuna biyu ba sai ga tashin muryan Abba yana kwala kiran Aysha ba ƙauƙautawa. Cikin nutsuwar da ta bi mata jiki ta miƙe a hankali ta fita.
Zaune suke tsakar gida suna cin abinci iya iyayen kawai sai Abba.
Duƙe takai gaban shi haɗi da faɗin " sannu da dawowa Abba, gani". Sai da ya gama bin ta da kallon tsaf yace "dan rainin da ya shiga tsakanin mu kina ji ina kiran ki kikai min banza dan tsabaragen samun waje! Toh nagaji da halin nan taki da ba'a cin miriyarki sai dai ke kici, na gaji dan na lura baƙin cikin taimaka min da zaki yi ki keyi, dan haka nima nan gaba kamar yadda kike datse idanun ki kike baɗe su da toka, nima haka zan koma, in har bakin cikin zaki ci gaba da min, kin san Allah sai kin dinga biyan haya na ɗakin da kike zaune da ɗanki, kamar yadda baki tausaya min ba nima haka, ganan sauran ƴan uwanki duk sun fita nema dan su taimaka min amma keeee ɗin nan hayya ban dai ce komai ba, amma kuɗin haya kam zaki fara biyan shi inhar baki chanza hali ba Allah kuwa" da sauri ta ɗago da kai ta dube shi jin abinda yake faɗi, nan take ta saki wata uwar murmushi wacce ta tsaya iya labban ta. Sai dai bata ce komai ba, sai shi ne ya buƙaci da ta tashi ta wuce. Tun kafin ta gama barin wajen mama tace "Allah yasa ba asarar yawun bakin ka kayi ba Mallam, amma sai naga yadda ta natsu kamar zata ɗauka maganar ka, barin ma taji ance zata fara biyan haya"
Inna dake gefe tace "Aikin kawai, sai ku dinga abu kamar baku san wace ita da taurin kan tsiya ba! Ai baza ta yi bane in da dai dan kanta tayi niyya toh ba makawa ko da kuwa zamuyi gunduwagunduwa da sassan jikin ta ne sai tayi......." Muƙut ta haɗe abinda yayi saura bata furta bah, dan ganin irin mugun kallon da Abba ke watsa mata. Sai da ya gama binta da mugun kallo yace.
"Duk taurin kanta ai bata fi ƙarfi na ba! Anya ma ba kece ke hure mata kunni bah? Dan gaskiya na fara zargin ku, amma ku cigaba Allah ya kawo ranar da zan kama ku, da hannu dumu dumu a ciki".
" Haba mana Mallam ba zai yiwu ka tara mu kai ta sakar mana magana tun ɗazun muna shanye wa ba fah, san nan a dai na daura mana laifin da ba mu mukayi ba, daga ƙarshe idan haka kake tunani haka din ne" Cewar mama.
Karab kuwa inna ta chaɓe da faɗin "toh nima da baki na baza'a hana ni yin magana ba yauwa" ƙin tanka masu yayi dan idan ya biye su rikicin zai koma babba ne shi kuma bai shirya wa haka bah, cigaba da cin abincin sa yayi gefe kuma yana sauraron Radio.
Koda Aysha ta koma ɗaki watsar da maganan Abba tayi dan tasan ba abu bane mai yiwa ba, sai dai ita ta karɓa daga gare su, sai dai bata fatan wan nan ranar dan Abba uba ne gare ta. Taɓe baki tayi ta samu gefen gado takai zaune.
Ji tayi ɗakin gaba ɗaya yayi mata faɗi dan rabon da ta kwana ita ɗaya tun bayan haihuwar maher da tayi. Tare take rayuwa dashi a ɗaki har tsawon Shekaru huɗu da rabi, shi yasa soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi ya shiga tsakanin su, hakan yasa baya yarda da kowa idan kacire Abba dake dawo masa da alawa, sai yaya Abdul.
Haƙura tayi ta danne zuciyarta dan kuwa inda maher yake tamkar yana wajen ta ne. dan yana wajen babbar yayan su Anty Ramlah, ɗazun da tazo da rana ta wuce dashi duk kuwa da baiso ba. Ɗauke tunanin haka tayi ta samu waje ta kwanta abinta har bacci yayi nasarar kwasanta.
Ihu da kukan yaron da ya karaɗe ilahirin gidan shi ya fiddo da mutanen da ke rayuwa a ciki, kuka yaron yake kamar wanda ake yanka namar jikin sa, a gigice Abba ya fito daga ɗakin shi jin kukan jikan shi da Allah ya daura masa son sa fiye da sauran jikokin nasa, bai jira jin komai ba ya hau sababi, "ai sai da nace kar a kai yaron nan ko ina amma sabida taurin kanta sai da ta ɗauka tun da su mutum bai isa dasu ba! Ai kaima gashi ka samu rabon ka an taso ka da daren nan" ya kare Maganar da kallon uncle Isma'il da ke tsaye riƙe da yaro a hannun sa wanda sai kuka yake, Cikin rashin damuwa Uncle Isma'il ya saki murmushi haɗi da gaisar da Abba.
Abba bai amsa ba sai cewa da yayi "Bani shi nan" yayi maganar yana miƙa hannu, fir mahir ya ƙi yadda da ke akwai duhu baiga fuskar Abba ba yasa yaƙi, sai da Abba ya furta "haba aboki nine fah" jin muryan Abba daf dashi yasa ya faɗa jikin shi da sauri haɗi da sauke wata babbar ajiyar zuciya kamar wani babban mutum, Abba kuma bubbuga bayan sa ya shiga yi a hankali har kukan nasa ya lafa. Sai ɗan ajiyar zuciya da ya ke saukewa a hankali.
LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
ALƘAWARIN SARAUTA
Jidderh Galadima
SARƘAR DUHU
Oum Fadeel
ALEENAH ALEEM
Aid Walee
INUWAR DUTSE
Rabi'a wakili
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Via
9119359211
Moniepoint
Rabi'at Sani Adamu
Sai katura shedar biyanka anan👇
***