Episode 3
🗻INUWAR DUTSE....🗻
_Rabi'a wakili_
Ep 03
Bismillahi Rahmanir Rahim.
★...
♡♡♡ ♡♡♡
_____________________
ꨄꨄꨄ
Aysha da dake a ɗaki har bacci ya fara ɗaukar ta, kamar daga sama taji kukan maher, ba shiri ta miƙe zaune tunanin ko dan ta sa a rai ne shi yasa take jiyo kukan sa, sai dai ta tabbata ba mafarki bane jin har ta farka tana jin kukan sa, ga muryan su Abba da uncle Isma'il tana ji, har ta tashi zata fita sai kuma ta fasa, baza ta iya zuwa wajen su da sunan zata ɗauki maher ba, tana da kawaici sosai a kansa duk kuwa da irin son da take masa,fasawa tayi ta koma ta zauna, tana dai ta jin su har dai maher yayi shiru a san nan ne ta ji wucewar uncle Isma'il.
Yana fita Abba ya ɗaura da faɗin, "toh sai ku wuce kuje ku kwanta koh?, banda bin kwaf mi na fitowa bayan uwar da ta haife shi ma tana ji amma taƙi fitowa sai ku yan niman suna". Babu wacce tace uffan ta koma ɗakin ta, ganin wucewar su yasa ya shiga kwala kiran Aysha kamar ba dare bah. Kafin ta fito, sai ga shigowar Hanifah ita da samha, a ɗage suka ɗaga masa hannu har zasu shige ciki a kausashe,?ya daka masu tsawa da ya haifar masu da tsayuwar dole, da matsanancin mamaki fiye da tunani sam basu yi tunanin haka daga gare sa ba, yaushe rabon da Abba ya ɗaga musu murya, yaushe rabon Abba ya yi musu haka a matsayin uba? Sun manta tun kafin sukai haka amma yau shi yake daka musu tsawa a matsayin muryan uba, ba su kaɗai bah har Aysha dake a baya sai da mamakin haka ya daskarar da ita.
Jiki a sanyaye haɗi da tsoron da ya yi musu shigar ɗaya, suka juyo gare sa, sai dai abinda ya daure masu kai fuskar nan tashi na nan a sake ba wata damuwa, sauke ajiyar zuciya sukai ba su kaɗai ba har su umma da suke hange ta window, "icce kuka gani da zaku zo ku wuce sa?" Yayi maganar kamar yadda ya saba a kullum, "san nan nawa kuka samo?" Ba tare da sun amsa masa ba suka buɗe jaka zasu fiddo da abinda suka samo, nan kam murmushi mai faɗi da yalwa ya cika masa fuska, har ya tara hannu zai karɓa umma ta riga shi, ta amshe duka tana binsa da kallon banza da kallon mutum mara amfani.
"Wlh Mallam bazan baka kudin nan ba, baka san ci da shan mu ba, sai dai mu mu nema mu baka? Toh ba zan bayar ba,?cefane za'a yi dashi idan Allah ya kaimu, kai ma ka amfana, amma ba zan baka ko biyar ba ka kaima gidan chacha da baka taɓa cin moriyar shi ba yauwa, ka dai jira idan ka samu kuɗin kanka sai kaje kai tayi ba dai da kuɗin yaran mu....." Hauren da ya kai mata shi ya katse ta ba shiri, ganin ya dumfaro ta a zafafe ysa ta wurga ɗakin ta, da Allah ya taimaka a buɗe ta barshi, tana shiga ta datse da key. Bubbuga ƙofar ya hau yi kamar zai ƙalle ƙofar saboda tsananin bugu.
"Dan Allah Abba ka daina dare ne fa, Mutane zasu shaida halin da muke ciki fah" cewar Samha.
a fusace Abba ya furta "idan sun sani sai me akwai abinda basu sani bane daga cikin Rayuwar gidan nan bane? tunda kun maida kanku yan terere" ya ƙare Maganar da buga kofar da ƙafa da ƙarfi, a dai dai nan maher da ke hannun sa ya tsaga ihu dan bugun ya firgita shi.
ALLAH ya jarabce shi da son maher hakan yasa lokaci ɗaya ba shiri ya natsu ya hau buga bayan sa alamun lallashi. Har sai da yayi shiru san nan ya cigaba da buga kofar da zuba duk tijarar daya ga dama. Itama daga ciki tana maida masa da martani. "Dan Allah Abba kayi haƙuri ga wannan in Sha Allah idan Allah ya kaimu sai na cika maka sauran" nutsuwa kuwa yayi tsaf, hannu har rawa yake wajen karɓan kuɗin, bata jira cewar shi ba ta tara hannu zata amshi maher ya hana, ganin haka yasa ta shige ciki daman Hanifah ta dade da shige tun kafin su fara tijarar su.
Da murna sosai Abba ya chusa kuÉ—aÉ—en a aljihun rigar sa haÉ—i da kwala kiran sunan Aysha. Da sauri tasa hannu ta É—auke hawayen fuskarta na tausayin halin da suke ciki. Fitowa da ga inda take ta isa inda yake.
Cikin sanyin murya kalau ta furta"Abba gani" "na ganki mana! Kin kuma kyauta, kin ma kanki, dan wulaƙanci kina jin yaron nan na kuka kuma kin san ke yake biɗa kin masa banza, dake baki damu dashi ba idan ma abin cutarwa ne sai dai ya cutar da shi kenan dan baki son sa? Kin san baki buƙatar shi mi yasa kika samo cikin sa?".
Ita dai shiru bata ce komai ba, dan bata da abin faÉ—i, lamarin Abba ba'a iya masa, yanzu da ace ta fito sai ya shuka mata rashin mutumcin da kaf anguwar sai anji, gashi duk gudun da tayi bata tsira ba.
Cigaba Abba yayi da faɗin "toh Ni Inason sa yafi min ke so dari da ƙari, dan baki da wani amfani gare ni". magana yake amma maher sai faman kiciniyar a sauke shi yake haɗi da ɗaɗɗaga hannayen sa a dole yaga mahaifiyar sa. Cikin takaici Abba ya dungure masa kai, ba tare da ya kuma cewa komai ba, ya dungurar mata da shi ya shige ɗakin sa.
Yana jin sa a jikin Aysha ya lafe luff, haÉ—i da sauke ajiyar zuciya, shafa bayan sa tayi san nan ta shige É—akin ta dashi.
Tana shiga ta kwantar dashi bisa gado har ya bare baki zai fara mata kuka fuska ba wasa tace "Allah ya baka Sa'a kamun kuka sai na maida kai inda ka fito, tunda kai baka san kara ba, baka da yarda kamar wanda za'a je a siyar" dariya ya kyalkyace dashi dake yaron akwai sa da wayau sosai. Kwanciya tayi itama a gadon tana lakace masa pointed noise da y gada a wajen ta, dariya ya kuma yi gefen kumatun sa na dama suna loɓawa, faɗawa yayi jikin ta. Yana son cigaba dayi mata rigima, "kayi! Zan wurgar da kai ne a wajen ummo ta cinye ka" ɗif yayi babu wani jimawa bacci ya ɗauke sa daman Bacci yake ji barin ma gashi yasha kuka.
Gyara masa kwanciya tayi ta shiga binsa da kallo, lokaci ɗaya tausayin yaron na ƙara shigarta a rai, da tsoro mai tsanani, tasan nan gaba idan ya girma zai tambaye ta ina baban sa, bata fatan wannan ranar, gudun haka kuwa, matsayi biyu a zata taka a rayuwar sa, wato ta zame masa uwa da uba.
Shafa sumar kansa data kwanta yayi luf tayi a hankali kafin ta zuba masa ido, sak da sak yake kama da ita har hasken fata ba abinda ya baro nata da bai É—auka ba, sauke ajiyar zuciya tayi haÉ—i da manna masa sumba a goshi tayi musu addu'ar bacci ta shafe masu jiki dashi.
LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
ALƘAWARIN SARAUTA
Jidderh Galadima
SARƘAR DUHU
Oum Fadeel
ALEENAH ALEEM
Aid Walee
INUWAR DUTSE
Rabi'a wakili
₦500
Via
9119359211
Moniepoint
Rabi'at Sani Adamu
Sai katura shedar biyanka anan👇
***