INUWAR DUTSE.......

Episode 4

by @rabearhwakili

INUWAR DUTSE.


Rabi'a wakili


Epi 04


Bismillahi Rahmanir Rahim.


___________________


https://www.arewapen.com/book?id=69582540cab84f8707da2483



          Washegari bayan ta kammala aikin da zatayi ta shirya maher cikin sabon uniform ɗinsa na makaranta, basket din sa da ta haɗa masa abin break ta ɗauka, san nan ta ɗauke shi suka nufi ɗakin iyayen.

     Duk ɗakin da suka shiga basa wani jimawa suke fitowa, su kuma iyayen ba wanda ke wa Maheer magana, shima Maheer ɗin bai nuna yasan da zaman su ba, duk da karamin yaro ne amma yana da halin fuskewa kamar wani babban, wanda yan gidan suke ganin halin Aysha ya kwasa.

      Dakin Abba ta shiga inda ta same sa zaune yana sauraren Radio,  ganin Maher yasa ya washe baki sosai yana miƙa masa hannu, kafaɗa maher ya noƙe alamun baya zuwa. 

     "Toh zo ga shi" yayi maganar yana nuna masa biscuit. Nan ɗin ma maƙe kafaɗa yayi wan nan karan har da daure fuska, "kai ka sani daman halin uwarka gata nan kake da, dan haka ku kuka sani, zaku ma ku kai shi idan kaya ne" ita dai bata ce komai ba sai gaisar dashi da tayi, jin ya amsa ba yabo ba fallasa yasa ta sallame sa suka fito bayan ya bawa maher biscuit. 

      Bayan sun fito daga gidan tafiya ba mai tsayi ba ya kawo su titi, dake basu da wani nisa, ba jimawa ta samu abin hawa suka tafi makarantar su maher. A dai dai gate din makarantar mai napep din ya tsaya, bayan ta fito ta biyasa kuɗin sa, ta ɗauki maher da basket  nasa suka nufi ciki, sai da suka gaisa da Baba mai gadi ta karasa.

    Makarantar kuɗi ce sai dai mai ɗan ƙalilan kuɗi irin namu na ƴaƴan mallam Shehu, suna daf da shiga kofar class din Maher ya juyo ta yadda zai ga fuskarta da kyau, cikin muryan sa ta yara ya furta "Mamy!?" Ya faɗa haɗi da langwabar da kai. 

       haɗe fuska tayi waje ɗaya dan kar ya kawo mata wargi kafin tace "ya akayi ne chuchu narh?" 

    ɗan jim yayi sannan yace "Mamy, ba zanje school gobe b..." Hararan da ta zuba masa da manyan idanun ta shi ya katse shi yayi shiru da bakin sa

      "da mi akayi zaka ce baza ka school gobe ba? Ko kana da abinda zakai ne?" Tura dan ƙaramin bakin sa yayi kaɗan bai kuma cewa komai ba, wai shi nan  yayi fushi.

      ba tace dashi komai ba har sai da suka kawo ajin sa san nan ta sauke shi haɗi da faɗin "wash Allah narh" tayi maganar tana kama hannun da ta ruƙo shi dashi, ganin haka yasa maher kyalkyacewa da dariya ganin yadda take da fuska, itama dan murmushi ta saki mai laushi, haɗi da zuba masa daradaran idanun ta masu kaifi, tana jin wata sabuwar soyayyar yaron da tausayin sa na ƙara shigarta, har bata san sanda kwalla cikar mata a ido ba, sai chan ta ankara, cikin fuskewa ta ɗauke su da hannu, haɗi sa furta "chuchu narh! Ba Mamy ka kake wa dariya bah?shikenan" kwaɓe fuska yayi lokaci ɗaya yace "na dai na" "yauwa! Toh muje na kai ka wajen zaman ka kar nayi latti" "Mamy zan biki".

     "In da ka aike ni zaka koh?  Karatun kuma ka bar ma waye? Wuce muje! Kace kai baka da yarda ko kaɗan, gwara ka chanza tun wuri" shi dai maher shiru bai ce komai ba har ta kama hannun sa suka shiga class nasa, gaisawa da malamar sa tayi san nan ta miƙa shi har wajen zaman sa ta fito, wata napep ta samu ta koma gida, sai da ta ɗan taɓa bacci sannan ta tashi ta shirya dan zata ɗan fita.

      Ko bayan da ta gama shiri kulle kofar ta tayi tana jefa key cikin jaka.

        A ƙofa tayi kiciɓis da Yusrah, duban ta tayi tace "sai ina haka?" "Zani gidan Radio amma in Sha Allah ba jimawa zanyi bah" "yau kuma AY? Inace kin ce ba ki son wajen" "ba aiki zanyi ba, ya ta kira na ne wanda ni ban san kiran ta mi bace kinga kuma ai bai kamata naƙi zuwa bah! Na tafi" ta ƙare maganar tare da ficewa dan idan ta biye Yusrah sai su shekara a wajen. 

       Napep ta samu ya kai ta har ƙofan gate na gidan rediyon bayan ta sallame shi ta shige ciki ba ta zarce ko ina ba sai cikin reception, dake an San da zuwan ta nan aka bata izinin shiga wajen Oga kai tsaye. 

        Dai dai ƙofan ta danna door bell daga ciki dattijon mutuminya amsa da "shigo" jin muryan sa yasa ta tura ƙofar a hankali ta shiga ciki. 

       Mutumin da ya ke zaune a kujera ya saki murmushi haɗi da faɗin "bara na tashi na biki kujerar ai kece Oga AY! Sannu da zuwa" ba wani sakewa a fuskar ta ta amsa ma sa da "ina yini sir" zuwa yanzu ya gama karantan ta tsaf sai hakan bai dame sa ba ya amsa da "lafiya qlau! Zauna mana" ya ƙare maganar yana nuna mata kujerar dake gayaye da table ɗin. 

     Ba musu ta zauna haɗi da maida hankali a kan sa jin ya fara magana "kiyi haƙuri d taso ki da nayi, da kuma takura dan tabbas nasan na takura miki amma kiyi haƙuri" bai bata daman magana ba ya cigaba da cewa "kamar kullum dai yau ma da ƙoƙon bara nike tafe gare ki da ki karɓi tayin da mukayi miki na zama ɗaya daga cikin ma'aikatan wannan gidan rediyon, tabbas irin ku ake buƙata a waje duba da irin jajircewar ki" numfasawa yayi kafin ya cigaba da cewa "idan albashin ne bai yi ma ki ba sai ki yanke iya yadda ki ke so, ni kuma in Sha Allah zan duba na ga ni" ya ƙare maganar yana duban fuskar ta da addu'ar Allah yasa ta amince dan gidan rediyon sa yayi ƙasa, lokacin da Aysha take nan kuwa t taimaka sosai wajen saka gidan rediyon a jerin lissafi.

      Ba tare da dogon tunani ba tace "sir kayi haƙuri, in da kafin yanzu ne da na karɓa" haɗe fuska yayi tamau haɗi da faɗin "kamar ya kenan?"   "Na samu wani aikin ne" sai da ya danne fushin sa sannan ya ce "shikenan bazan hana ki aikin ki ba! Am ma dan Allah ki duba ki gani" miƙewa tayi kan ƙafafun ta haɗi da faɗin "Nagode" ta fice daga office din zuwa waje zuciyar ta na ta ma ta saƙe saƙ

     Shi kuwa da cizon ɗan yatsa ta barshi, yasan ta akwai ta da taurin kai ba lailai ta karɓi tayin sa ba.

        

        Tana nan tsaye bakin titi tana jiran abin hawa har ta fidda rai da samu haka yasa ta yanke shawarar ta ɗan taka zuwa gaba ko Allah yasa ta samu.

       Tafiya ke yi cikin nutsuwar da ya bi mata jiki kamar bata son taka ƙasa. 

       Wata baƙa wulik ɗin mota ta shararo a guje kamar zai tashi sama dan titin express ne. 

Har motan ta gitta ta sai ga motan tana yo wa baya a hankali, dai dai saitin ta ya ja ya tsaya, haɗi da buɗe ƙofar motan. 

       Ko kafin ta gama buɗe motan Aysha da ta cika tayi fam, haɗi da jinjina rashin mutumci na mai motan, danne zuciya tayi ta ja ƙafar ta a hankali ta fara taku da niyan barin wajen b tare da ta waiga dan taga wane wannan ba.

      Kyakkyawan budurwa ce yar fara wacce baza ta wuci sa'ar su Aysha ba, fuskar ta ɗauke da kyakkyawar murmushi ta shiga taka wa Aysha baya, da yake  ba wani sauri ta ke ba nan ta cimmata haɗi da faɗin "Sister?" Chak taja ta tsaya bata ƙara ko taku ba, haka da wannan matashiyar ta gani ne ya bata ikon taka wa zuwa gaban ta har sannan murmushi na fuskar ta. 

    Kamar mai ciwon wuya ta daga kanta a hankali dan taga waye dan sam bata gano mai muryar ba. Idanun ta bai dira ko ina ba sai a fuskar wan nan matashiyar, kallo ɗaya tayi mata ta ɗauke kai ɗan sam bata waye ta ba, kai tana iya cewa ma bata san ta bah.

      Sai dai gudun kar tayi rashin mutumci yasa tace "sannu" wannan matashiyar kuwa kuwa ta amsa mata da "ina yini! Ya baby?" 

      Babu shiri ta ɗago tana duban ta d mamakin jin maganar ta na ƙarshe. 

     Wan nan matashiyar kuwa bata jira cewar Aysha ba ta cigaba da faɗin.

     "Na san ba lailai ki waye ni ba, amma idan nayi miki bayani kila ki tuna! Sunana Fadila, shekarun baya da suka wuce mun taɓa haɗuwa dake a Federal university of Adamawa! Sanadin baby naki da yike ta kuka ga shi lokacin kina da exams har an fara shiga hall, ganin kukan baby yayi yawa yasa kika fasa shiga kika juya da niyan barin wajen, sai dai security da ke wajen suka dakatar dake tare da tambayar ki exams ɗin fa? Ki ka ce kin fasa! Hakan yasa suka taimaka maki suka karɓi babyn suka kira ɗaya daga cikin student dake zaune a wajen wanda  ba kowa bace face ni, suka ce na taimaka na taya ki rikon yaron zaki rubuta jarabawa, idan baki manta ba har ku ka gama kika fito inda kika same ni a nan wajen security ɗin" 

      Eh tabbas ta tuna wan nan ranar sai dai fuskarta ne ya ɓata mata dan a ranar ma ba wai tayi mata kallon tsaf bane dan Maheer ya gama ruɗa ta. 

      "Allah sarki! Sannu" cewar Aysha fuskar nan ba sakewa.

"Alhamdulillah daman fata na ki gane ni, dan Allah Anty Muje na rage miki hanya" 

      A karo na uku Aysha ta ɗago ta kalle ta jin ta ƙaƙaba mata sunan da bata san inda ta samo shi ba, dube ta babba da ita tana wani kiran ta da Anty. Kamar zata yi mata magana sai kuma ta fasa.

      "Dan Allah Anty kar ki ce a'a" 

Dan murmushi kawai tayi wanda sai ka dube ta da kyau za ka gane haka. 

     "Nagode" Aysha ta furta haɗi da nufan wajen motan, ganin haka yasa Fadila take mata baya nan suka shiga suka bar wajen, tafiyar tasu ta kasance shiru, sai da Fadila ta katse shiru ta hanyar faɗin "Anty wai nikam ina baby na ya ke, yanzu dai nasan ya zama saurayi?"  

      "Yana makaranta" "ma sha ALLAH! Nikam ban san sunan baby na bah"

     Allah ya gani zuwa yanzu duk ta fara gajiya da surutan nan nata am ma mutumin da ya riƙe maka ɗa da amana a bayan idanun ka ai babban masoyin ka ne. 

        "Sunan sa Muhammad Maheer" 

   "Wow ma sha ALLAH! ALLAH ya raya a kan sunnah" 

     Da Amin Aysha ta amsa cikin zuciya ita Kuma Fadila ta zarce da bata labarin neman ta da tayi tsawon wannan lokacin. Aysha kam bata ce komai ba nata ji ne kawai. Cikin rashin damuwa Fadila ta cigaba da zuba mata surutu bata ko tsayawa.

       "Ya ALLAH na manta na tambaye ki in da muka nufa afwan pls" amsawa tayi da ba komai haɗi da faɗa mata pack zata. 

      Suna isa, da murmushi ɗauke a fuskar Aysha tace"nagode sosai ALLAH ya saka da alkhairi" "haba dai ba komai wallahi". 

       Balle murfin ƙofan Aysha tayi kafin ta gama fita Fadila ta riga ta. Ita dai duk tunanin ta daga nan Fadila wuce wa zata yi. 

      Kaman tasan abinda Aysha take tunani tace "ta ya za'ayi na wuce bayan kuma nice na kawo ki? Ai wasa neh" 

       Ba tare da ta tanka mata ba ta fiddo da wayarta ta latsa wata number bugu biyu aka daga. ba tare da jiran cewar sa ba ta furta "ina a first gate"

       


Share fisabilillah 

***