INUWAR DUTSE.......

Episode 5

by @rabearhwakili

🗻INUWAR DUTSE....🗻


_Rabi'a wakili_

 

Ep 05


Bismillahi Rahmanir Rahim.


_________________


            INUWAR DUTSE....




_Rabi'a wakili_




Ep 05




Bismillahi Rahmanir Rahim.




_________________




           Da sauri tasa hannu ta toshe baki, kwarai ta gigita da jin bautun da suke, "mi yasa wasu mutanen basu da imani ne? Mi yasa wasu mutanen basa tsoron Allah?" Zuciyarta ta shiga yana yin tambaya. 


   motsin da taji na alamar za'a fito, bata san sanda wani kuzari shigar ta ba, ta miƙe da sauri ta bar wajen bata ko kallon inda take jefa ƙafafu.


     Babu inda ta zarce sai bakin titi, abin hawa ta samu ta koma gida zuciyarta na lugujen daka, tayi zurfi sosai cikin tunanin da ta faɗa wanda tayi iya yinta na ganin ta yakice haka a zuciyar ta hakan bai samu bah. 


     Wayarta da ya shiga ruri shi yayi nasarar dawo da ita duniyar mu ta mutane. Sauke numfashi mai kauri tayi kafin takai hannu ta ɗauki wayar da take daf da katse wa. Lokaci ɗaya ƙirjinta ya buga fiye da wanda yake dazu, zare manyan idanun ta masu girma tayi dan tabbatar da da wanda yake kira din. Eh kam idanun ta basu yi mata karya ba yaya Abdul ne, tana cikin sakawa da kwancewa wani kiran ƙara shigowa, sai da ta daidaita kanta sosai sannan ta dauka cikin nutsuwa. Kafin tace komi ya katse ta cikin karaji, duk da ta razana amma bata nuna haka ko a fuska bah, ta amsa masa da "toh" tana katse wayar tun kafin ya katse.tunani ta shiga yaushe ya dawo? Tunanin ta katsewa yayi jin napep ya tsaya, sauke numfashi tayi a hankali haɗi da fitowa bayan ta sallame sa. Jiki a sanyaye ta nufi layin su, nan da nan ta kawo gida daman basu da wani nisa da titi.


     Bakin ta dauke da sallama ta shiga cikin gidan inda ta tadda su Hanifah, Yusrah, Samha, suna aiki, su umma kuma na cikin ɗaki da alamu dai bacci suke.


        Dake duk ɗin su tafi shiri da Samha yasa ta dube ta murya chan ƙasa tace "lafiya kuwa yau naga gidan shiru?" "Dakin dake a farkon gidan Samha ta kalla kafin tace "yaya ne ya dawo fah, Kuma ya tambayi inda kike, toh Allah yasa lokacin Abba na nan yace kin tafi kai maher makaranta" .


     Boyayyiyar ajiyar zuciya ta boye da nufin barin wajen chak taja ta tsaya, haɗi da tattare fuska gu ɗaya. Sakamakon jin muryan Yusrah tana faɗin "sannu da fitowa yaya".


        Kyakkyawan matashin  dake tsaye a ƙofa hannayen sa harɗe a ƙirji fuskan nan tamau ba wasa, ya furta "daga Ina kike?" Duk da ta ɗan razana amma ta ɓoye, duk bin ƙwaf na mutum ba zai gano halin da take ciki bah. 


       A hankali ta juyo sai dai bata yarda ta dubi fuskar sa bah, murya chan ciki ta amsa masa da cewa "na kai maher school ne" ido kawai ya zuba mata yana son ya gano iya gaskiyar ta, kasa gano komai yayi  ya ɗauke duban sa daga gare ta, yana wurga mata wata tambayar "daga nan kika nufi ina?" Sai da ta gama binsa da kallon kasan ido sannan ta amsa masa da cewa "babu ko ina an dai samu matsalar go-slow ne" Ta kare maganar a gundire. 


    Ba tare da ya kara bi ta kanta ba ya wuce abinsa daman fita zaiyi. 


         ganin fitar sa yasa duk suka sauke ajiyar zuciya idan ka cire Aysha da tayi kaman abin bai dame ta ba nan kuwa kam, Allah kadai yasan fargaban da ta shiga, ta san sa ba mutum bane mai wasa, yanzu sai yace zai yi musu duka karamin aikin sa kenan, shi yasa kaf cikin yayun su sunfi tsoron sa da shi da Anty Ramlah. Sai dai nashi yafi tasiri cikin zuciyar su. 


        Sai da suka tabbatar yayi nisa da gidan suka hau gulman sa, Aysha kuwa saɗaf saɗaf ta shige ɗakin ta dan abinda ya dame ta ya dame ta. 


       Zubewa tayi bisa gado, ta shiga aikin sakawa da kwancewa akan batun da taji na waɗan nan mutanen, ta ɗauki tsawon lokaci sosai a haka ganin zata ɓatawa kanta lokaci yasa ta yi yaƙin yakice haka a zuciyar ta shima da ƙyar. Tana kwance anan bacci yayi awon gaba da ita.


     Chan tsakar gida kam su Yusrah har sun kammala aikin da suke daman ba wani aiki bane mai yawa,  hakan yasa gidan yayi tsit ya natsu kamar ba mutane, sai yay kamar ba gidan da ake kwasan yan kallo cikin ta bah. Duk sanadin dawowan yaya Abdul dan har iyayen nasu shakka shakkan sa suke duk bala'i basa yi idan yana gari. 


        Tun daga zaure Goggo take ta doka sallama ba ji ba gani kamar wacce zata tashi gidan. Sallaman nata shi ya fiddo dasu umma wanda daman duk sun daɗe da tashi kawai dai fitowar ne basu yi bah. 


       Ba wani sakin fuska suka amsa mata sallaman bayan ta shigo shima ciki ciki wanda ba lailai bane ace taji bah. Tana shiga safna bin bayanta, sai Abbu. Basu kai ga yi masu sannu da zuwa bah sai ga Anne ta danno kai, sai wani yatsine fuska take haɗi da bin ko wacce da kallon uku sauran kwata.


       Ganin ta da rana tsakar nan ya basu mamaki, ba wanda yasan da dawowarta a nan kusa ma bare ace wai gata gaban su a yanzu din. Nan take kuwa duk suka sha jinin jikin su suna kuma tattare fuska waje ɗaya. 


       Kafin su dawo dai-dai daga bazata da suka faɗa suka tsinkayi muryan Anne cikin ƙwaƙwazo "tunda nikam bani da darajar da zakuyi min sannu da zuwa ni ina yi muku sannu! Allah yasa ya faranta muku ko akasin haka zama daram dam dam eheee, sai dai duk wacce taga baza ta zauna dani bah ga ƙofa nan a hankaɗe ta fita ba takura" ɗan jim tayi haɗi da binsu da kallo kafin ta cigaba da faɗin "watam an zata a chan zan dauwama har kun mimiƙe kafafu kuna ta shan sha'anin ku! An mance da sabgata daman na san ba son zama na kuke ba, toh ba kuma yadda zakuyi dani, gani nan bari yauwa" ta ƙare maganar da turo ɗankwali gaban goshi. 


       Shiru gidan ya ɗauka kamar anyi ruwa an ɗauke babu wacce tace mata komai dan sun san duk hayaƙin kai ta fisu. tun da yafendo ta fara magana maman safna (Goggo) take ta gwaɗa kai da yatsine fuska, jin ta kai aya tai saurin chaɓewa da. "A toh Anne naga kaman ba dawowar ki ne kawai ba'a so bah har da tamu! Yo harda mu mana duk sallmar da mukai ta dokawa babu wanda ya amsa bare muci arzikin ai mana sannu da zuwa, Allah na tuba ba haka aka so ba! Kai jama'a....." 


       "Suwaiba!"Abbu yai kiran sunan maman safna (goggo) a dake ba wasa, wanda tun sanda ta fara magana yake ta wurga mata wani mugun kallo amma inaaaa bata san yanayi ba, tayi nisa bata jin kira burin ta dai ta guma masu gumamma. 


     Maƙut ta haɗe sauran tijarar da tayi niyyar direwa, Abbu ba abokin wargin ta bane baya ɗaukan irin abubuwan mutanen gidan. 


       "Wuce ciki" Abbu ya furta hakan ba tare da ya kuma kallon maman safna bah. Ai kafin ya rufe baki sum sum ta shige ciki tana jin zuciyar na mata tuƙuƙin takaici. 


      "Dan Allah kiyi haƙuri Anne! ki samu ki huta kinga ma ga tafiyar da muka shawo, idan kin huta sai a zauna ayi magana". Dan kallon shi tayi kamar zata ce wani abin kuma ta fasa itama din dai hanyar ɗakin ta ta nufa tana jin babu daɗi, itafa ba iya haka taso abin ya tsaya ba! Toh taya za'a yi ba zai tsaya a haka bah tunda ba Abba bane daman shine bai gani ya ƙyale barin ma yaji ance da yafendo ake koda kuwa itace bata da gaskiya bayanta zai bi suyi ta raba abin faɗe a anguwa, shi kuma Abbu sanyi hali yike da,sam ba'a jin muryansa cikin hayaniyar gidan.


       Ganin ta shige shima ya nufi hanyar ɗakin sa, har ya shige ya barsu umma  tsaye nan, sai daga baya ko wacce ta shige ciki. 


     Ɓangaren yan matan gidan kuwa duk suna jin diramar da akayi, fitowa ne kurum basu yi ba amma dai sun leƙa ta taga. 


      Safna kam ƙin bin goggo tayi ta zarce ɗakin da yake mallakin Aysha a yanzu, tura ƙofan tayi cikin Sa'a ƙofar ta buɗe tasa kai ciki, ganin ta tayi kwance bisa gado tana bacci.


     Gaɗa kai tayi haɗi da faɗin "oooh ni safna! Amma toh bara dai na tausaya miki kiyi baccin ba dan halin ki bah" ta ƙare maganar da ɗaukar frame dake ɗauke da hoton maheer akai wanda yake kaman a zahiri kyakkyawan fuskar sa ɗauke da murmushi. kai hannu tayi a hankali ta shafa fuskar maheer dake cikin frame haɗi da sake murmushi. Firgigit ta ɗago a tsorace murmushin dake kan fuskarta suna disashewa, gefe zuciyar ta na lugujen daka,waigawa baya tayi dan ganin wanda ya kwace hoton daga hannun tah, dan tasan tabbas Aysha bacci take.