Episode 6
INUWAR DUTSE.
Rabi'a wakili
Ep 06
Writer's connect pens
Bismillahi Rahmanir Rahim.
_______________
juyowa tayi ta kalli Safna kamar wacce akayi wa dole ta furta "yaushe a gari".
"Allah ya shirya min ke AY! Ba wani jimawa, dawowar mu kenan na wuto nan! Sai dai fah da babban baƙuwa muke tafe, watam Anne"
da sauri Aysha ta zaro manyan fararen idanun ta har bata san sanda bakin ta ya furta "tabbb".
"Ke dai bari ai dazun ma kaɗan ya rage ba'ayi ba, ALLAH dai ya taimaka Abbu yana nan shi ya hana ya lallaɓa ta amma duk da haka akwai zama na sani".
taɓe baki Aysha tayi kawai, cikin zuciyar ta tana jinjina fitinar kakan tasu, gefe guda na zuciyar ta na shiga fargaba.
Tashi safna tayi ba tare da jiran cewar Aysha ba ta nufi mirror ta gyara fuskar haɗi da yin rolling gyalen da ke kanta ta nufi hanyar fita.
Duk abinda take da ido kawai Aysha ke binta har ta isa ƙofa.
"AY bara naje na ɗauko Maher nasan lokacin tashin su yayi"
"yaya Abdul na nan kin san zai ɗauko shi" Aysha ta furta cikin sanyin murya.
Kamar ƙyaftawan ido sai ga safna gaban Aysha murya har zuga yake wajen faɗin "wani yaya Abdul ɗin! Yaushe ya kuma dawo?" Ta jefa wa Aysha tambayar a haɗe.
Kaɗan ya rage dariya bai kufce mata ba ganin yadda safna duk ta ruɗe lokaci ɗaya, amma ta gimtse kayanta dan bata cikin yanayin tace "shima yau ɗin ya dawo". Sai da safna ta gama yi mata kallon tsaf sannan tace. "Amma ke muguwa ce AY shine baki gaya min bah kika barni na taho? Ba komai nasan zama na dake yar rainin wayau kawai"
"Tunda daman kin gaya min kina hanyar tasowa yau ai dole"
"Naji ban kira na gaya miki ba amma ke mi zai hana ki kira ki gaya Min?"
Sai da Aysha ta mula dan kanta Sannan ta furta "abinda ya riƙe ki".
Har safna ta buɗe baki zata yi magana sai ga sallmar yaya Abdul, tsaf ta haɗiye maganar ta ta chanza akalar maganar zuwa amsa masa, tashi tayi ta fita zuwa ƙofa, cikin girmamawa ta gaisar da shi cikin kamewan sa ya amsa mata haɗi da miƙa mata maheer da yake ta faman binta da kallo kaman bai santa ko gane ta bah. Tana karɓan sa ta juya ciki dan bata so ko inuwa su haɗa.
"Idan ka gama gaisawa da kanwar ubanka kazo Inason ganin ka, shanyayye kawai"
cewar Goggo dake tsaye daga ƙofa haɗi da watsa masa mugun kallo.
Sauke kai ƙasa yayi haɗi da shafo kansa zuwa ƙeya kafin ya nufi ɗakin mahaifiyar tasu, zaune ya tadda ta tana kaɗa ƙafa da gani ƙiris take jira ta watso da abinda ke zuciyar ta.
Nisa kaɗan da ita ya kai zaune "sannu da dawowa Goggo! Ya hanya? Na ma shigo ɗazun na tadda kina sallah, sai na koma da niyyar idan kin idar na dawo". Tun da yaya Abdul ya fara magana ta shiga binsa da mugun kallo kaman idanun ta zasu zube ƙas.
Sai da ta ɗauki tsawon mintina kafin tace "kaga ba wannan na tambaye ka bah! Shin ban hanaka shiga safgar wanchan yarinyar da ita da shegen ɗanta bah? Toh uban mi ya kai ka harda jigilar ɗauko yaro daga makaran...." Rintse ido yayi da ƙarfi yana haɗiye abinda yayi masa tsaye a maƙoshi.
Har ga Allah baya son yaji ana shegenta maheer ji yake har cikin makwallaton zuciyarsa ba zai jure sauraran sautin muryan mahaifiyarsa na shegen ta maheer bah yasa cikin nutsuwar da ya tattaro ya katse ta ta hanyar faɗin "Goggo dan Allah kiyi haƙuri tabbass nasan nayi kuskure zan kiyaye, amma dai Goggo itama kanwa take gare ni kaman yadda safna dasu Hanifah suke....
Ƙatuwar hararan da Goggo ta sakar masa shi ya tilas ta masa yin shiru ba tare da ya kai aya bah.
"Sannu uba na, ai tuna min zakayi tunda ni na manta". ta faɗa a zafafe duk da ƙoƙarin dannewar da take.
"A'a Goggo ba haka bane kawai dai gani nayi itama nauyi nane tunda itama ƙanwa ce gare ni Kuma sai naga...." Sai kuma yai shiru ya kasa ƙara sawa dan ba lailai ta fahimce sa bah.
"Ina jinka uba na ya kayi shiru, kai ƙarshen maganar taka mana"
"Wai daman am daman sai naga idan akayi haka kaman an nuna banbanci ne tsakanin su bayan du....." "Eh kam wuyan ka ya isa yanka! yo ta isa yanka mana tunda gashi ka zaunar dani kana gaya min magana uhm?" Shi dai shiru bai ce komai bah.
Jin shirun nasa yasa ta cigaba da faɗan, inda take shiga ba tanan take fita bah, sai da tayi ma'ishi sannan ta haƙura haɗi da faɗin "tashi ka bacewa gani na". Har zuwa lokacin yaya Abdul bai ce bah, sai sanda yake ƙoƙarin tashi ya ƙara bata haƙuri sannan ya fito.
Jin motsin fitowar sa yasa umma saurin matsawa daga jikin ƙofan Goggo, sai dai da kaga yanayin ta farat ɗaya zaka ga alamun rashin gaskiya tattare da ita duba da yadda ta shiga kame kame.
Ɗauke kai yaya Abdul yayi kaman bai ranfo ta bah ya gaishe ta, tun kafin ya dire tai karaf ta amshe da "lafiya qlau ya gajiyar hanyar, ɗazun aka ce ka shigo sai da na farka Hanifah ke faɗa min".
"Eh anyi haka, fatan na same ku lafiya?"
"Alhamdulillah Wallahi sai ɗan abinda ba'a rasawa na yau da kullum".
"Ehem ehem ehem!"
Gyaran Muryar da Goggo tayi daga ƙofan ta shi ya sa suka waiga baki ɗaya suna duban ta.
"Ba fita zakayi bane yayan su?". Cewar Goggo, tana binsa da kallo. "Eh Goggo! Na tafi"
"Shikenan a dawo lafiya" amsawa yayi da Amin Ya fice, umma dake tsaye wajen taɓe baki tayi a fakaice kafin itama ta shige nata ganin Goggo ma ta shige.
Mama dake hangar su ta window kwashewa tayi da dariya haɗi da faɗin "shishigin banza dana hofi! Kaɗan kika gani indai munafuncin da zakiyi kenan Rashida, hmmm mtswww" ta ƙare maganar da jan doguwar tsuka, har takai zaune tai zumbur ta miƙe kamar wacce ta tuna wani abu, da sauri har tana shirin kai wa ƙasa amma bata damuba burin ta dai ta isa inda take son zuwa. Kamar ƙyaftawan ido sai ga mama gaban ɗakin Goggo kamar wacce bata son aji muryan ta chan ƙasa ta shiga rangaɗa sallama.
Sai da aka ɗauki mintuna biyu masu kyau kafin Goggo ta amsa, jin amsar ta yasa mama sauke ajiyar zuciya tana ƙara bin gidan da kallo, ganin har zuwa lokacin babu wanda ya fito daga mutanen gidan, tana cikin tunanin, Goggo ta leƙo ba wani sakewa tattare da ita ta dubi mama duban fisha ta ɗauke kai haɗi da faɗin "ko Lafiya?"
"Ita ta kawo haka, daman nazo ne na ƙara maku sannu da hanya" tayi maganar kamar ba ita bah.
"Mun gode gajiya kuma tabi jiki" tana faɗin haka ta koma ciki abinta ta bar mama nan da baki sake.
Duk da abinda da Goggo tayi mata ya zafe ta amma ta shanye, dake tana niman fuska daga gun Goggo.
Barin wajen tayi zuciya duk a kutace, gudun kar wani ya fito ya ganta a ƙofan Goggo.
Tun daga zaure babu abinda zaka fara juyowa a gidan sai kukan Maheer! Hakan da Abba yaji ne yasa ya ƙarasa ciki da sarsarfa
"Subhanallah wai Aysha bata a gidan ne ta bar yaron mutane yana ta tsala ihu da farar mangaribar nan?! Ke Safna shiga ki dubo abinda ke damun shi".
"ba ya jin daɗi ne Abba, jikin nasa yayi ɗau kamar wuta yanzu ma ruwan sanyi nazo ɗiba a turara masa jikin ko ya ɗan lafa"
"Muje naga! Kun kira Yayanku kun sanar masa kuwa?''
"Eh toh...."
Maganar ta katsewa yayi ganin Aysha ta fito duk a susuce hannun ta ɗauke da Maheer da a yanzu kukan nasa baya wani fita sakamakon ƙarfin sa yayi ƙasa.
"Ke kuma da kika fito da shi ina zaki kai shi ga sanyin magriba! Ai gwara cikin akan waje"
Muryan ta a dishe tace "zan kai shi asibiti ne yaya Abdul na jiran mu a bakin titi".
"Kawo shi nan" karɓan shi yayi ya saɓa sa kafaɗa jin yadda jikin sa ke ta rawar sanyi duk da uban kayan sanyin da ta lafta ma sa.
Hanyar ƙofa ya nufa ganin haka yasa Aysha take masa baya, bayan ta kuma Safna.
Cikin matan gidan kuwa ko leƙe basu leƙo su ba duk irin uban kukan da Maheer yai ta zabgawa.
Suna isa bakin titi sai ga yaya Abdul ya iso wajen a cikin napep, nan duk suka shiga da maneji suka nufi hanyar asibiti.
"Yaya Golden care za'a kaisa a nan muke da File.
Ai tun kafin yaya Abdul ya samu zarafin cewa komai Safna ta riga sa wajen furta Golden mi? Kin kuwa san inda kike faɗi kuwa?"
"Ai duk asibiti asibiti ne a kaita inda tace kun san kowa da asibitin da yafi gane ma...."
"Asibitin da Aysha take magana fah Abba wallahi na masu kuɗi ne Asalin Masu kuɗi kuwa, kuma turawa suke aiki a asibitin...."
"Ungo naki nan....." Abba y ware dukkan hannun sa biyar a kan Aysha kafin ya zarce da faɗin. "Ke yaushe kika zama haka ne halan? Toh Ni na iya riƙe talauci nah, idan har ke kin gagara riƙe taki! Taimakon ki fa za'ayi shine har kike da bakin zaɓan asibiti koh? Toh bismillahi"
"Abba rabu da ita! Inda muka ga dama nan zamu kai shi! Kai Mallam kaimu general" cewar yaya Abdul.
"Dan ALLAH ku fahimce ni! A chan muke da File kuma sun san da zuwan mu ma yanzu haka"
Shiru napep ɗin ya dauka kaman anyi ruwa an ɗauke jin zancen ta na ƙarshe.....
"Mallam samu waje ka sauke ni! Kai kuma Abdul sai ka kaita asibitin dan ba za'a je da ni wajen da nasan ban kai ba"
"A'a Abba ka bari mu tafi gaba ɗaya! Tunda tace nan ɗin mu kaishi ɗin in sha ALLAH baza ta gagara ba! Mallam mai adedeta ka kaimu golden care"
"Toh shikenan Amma ficika ban magani daman yau ɗin nan haka na tashi"
Daga nan Cikin su Babu wanda ya kara cewa komai dan kuwa Aysha ta gama sakar masu d jijiyar jiki.
Tun daga tsarin ginin zaka tabbatar da masu shiga cikin ta sai waɗan da suka ci suka tada kai a nera! Maƙut Abba ya haɗiye yawu mai kauri yana kara bin ginin da kallo da yake a tsare.
"Abdul zaka iya da wannan asibitin kuwa? Ka duba ka gani fa kaman a ƙasar waje! Ko dai mu juya mu koma inda muka fi wayau Tun kafin wani ya kama mu"
"Ba zata gagara ba Abba in Sha Allah" "toh shikenan! ALLAH ya rufa asiri"
Duk da Amin suka amsa suna shiga cikin gate din da yake abin kallo.
Kamar jira kuwa tun daga gate wasu turawa biyu suka fito tarban su, ɗayar nurse din ce ta karbi Maheer suka Shige ciki ba tare da wani bincike ba! Sai ma girman da ake ta basu ko ta ko ina.
Abba, yaya Abdul, Safna, bin Aysha suka koma yi kaman raƙumi da akala har suka shiga asalin cikin asibitin inda aka wuce da Maheer dan ayi treating nashi da gaggawa.
Ba Abba kawai ba bar safna da yaya Abdul bin asibitin da kallo suka shiga yi suna ƙara jinjina wannan lamarin ko wanne da tambayoyi taff cikin zuciya da basu da mai basu amsa sai Aysha.
Shiru Asibitin baka jin motsi da hayaniyar komai! Kai baka ce akwai mutanen da suke rayuwa a ciki ba.
Suna zaune a ta dakin da aka kwantar da Maheer sai ga doctor da nurses din nan biyu sun fito ko wacce fuska a sake bisa ga nasarar da sukayi a aikin nasu.
Ganin fitowar su yasa suka mike suna jiran su ji daga gare su duk kuwa da murmushin fuskar su ya wadatar da samun amsar su.
Cikin mutuntawa wannan doctor din ya ƙarasa wajen su! Cikin girmamawan da ya ba su Abba mamaki ya shiga gaida Aysha dasu, kafin ya zarce da faɗin "congratulations Madam! He's not in danger now! He's safe" wata wawiyar ajiyar zuciya ta sauke Cikin harshen turanci mai lafiya tace "ba buƙatar ƙara mishi jini kenan?"
"mun ƙara masa! we got it from some one"
Wani mugun kallon da ta shiga binsa dashi ne yasa ya kama kanshi! Kafin daga ƙarshe ya wuce nasa office din.
"Bismillah Abba mu shiga"
Wannan karan kallon da suke bin ta dashi ya tashi a na mamaki ya koma tsoro...... Baku nan su kam tuni suka mutu mus.
Ya subhanallah! fadar Irin tsaruwar dakin bata lokaci ne, ƙarasawa wajen Maheer dake a kwance samɓal fuskar nan tashi tayi fayau.
"Cikin tausayawa Abba yace Allah ya ƙara sauƙi takwarana"
Duk amsawa sukai da Amin. Kafin Aysha ta faki idanun kowa ta wuce office din doctor Kai tsaye.
Sai da tayi knocking kafin ta tura kofar ta shige zuciya duk a jagule da masifar da ke hidima da zuciyar ta.
Ba tare da jiran komai ba murya babu wasa ta shiga fadin "so nawa zan gaya maka da ka daina ɗorawa Maheer jinin kowa? Kayi na farko kuma kayi na ƙarshe Ko da bakin wasa karda ka ƙara min irin wannan, kar da ka kara banaso,idan kuma ba haka ba i gonna report you! Just give a trial and see! Rub........"
Tsaf sauran maganar bakin ta makele mata a baki sakamakon jin kamshin tulare daf da ita, da tunda ta shigo take jinsa amma bata maida hankali ba dan masifa ya rufe mata idanu, ba kuma abinda ya ƙara kiɗimar da ita sai jin tsayuwar mutum a bayan ta ga lokaci ɗaya wutar office din ya ɗauke gaba ɗaya ga ya haɗa da dare sai office din yayi dilum......"
A hankali ya zagayo gaban ta, ganin haka yasa ta shiga taku da baya a hankali shima ɗin yana binta bata ankara ba har ta mannu da bango.
Ganin haka yasa wannan mutumin da Rashin haske ya hana na gano fuskarsa ya tokare hannun sa daya a bango wanda hakan ya bada katanga mai kyau tsakanin ba tare da kwakwaran space ba, amma duk da haka jikin su bai haɗu bah.
Cikin dakiya da nuna jarumta duk kuwa da ta tsorata amma baza ta taɓa barin raunin ta ya baiyana bah.
Cikin tsiwar da ta bi mata jinin jiki tace "waye ne kai! Ka matsa min na wuce......"
Ɗallan ƙananun pink lips nata yayi wanda hakan ya katse maganar ta ta.
Cikin amo da sanyi Muryar sa da kan saka ruhi natsuwa sai dai tana da kauri amma ba chan bah Ya furta.......
LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
ALƘAWARIN SARAUTA
Jidderh Galadima
SARƘAR DUHU
Oum Fadeel
ALEENAH ALEEM
Aid Walee
INUWAR DUTSE
Rabi'a wakili
KUKAN ZUCI
Matar Dear
Share fisabilillah
***