INUWAR DUTSE.......

Episode 7

by @rabearhwakili

INUWAR DUTSE.


Rabi'a wakili

 

Ep 07


Bismillahi Rahmanir Rahim.


_________________


         "Kina buƙatar ƙarin haske kenan! Uhmm?"

Ji tayi ƙirjinta ya buga fiye da ɗazu jin sautin muryan sa a kunnin ta, ga saukar numfashin sa da take ji a bayan wuyar ta..... 

      Ranƙafowa yayi sosai yayi mata rumfa da faffadan ƙirjin sa inda numfashin sa da nata suka sarƙafe guri ɗaya, jin bazata iya juran musayar numfashin su ba yasa ta kame numfashin ta tsaf...

     Taɓe lips nashi yayi kafin ya shiga raɗa mata magana cikin kunni kamar wanda yake gudun wani ya ji sa "uhmm! Naji kina cewa Maheer bayi da alaƙa da kowa ko.......? Dan dakatawa yayi yana kai hannu bisa goshin sa ya murza kaɗan dan jin yadda kan ke ɗan sara masa sakamakon maganar nan da yayi.. dan gani yake ai ba ƙaramin surutu ya zuba ba saboda miskilancin irin nasa..... Daurewa yayi ya cigaba da faɗin "dan an kara masa jinin dake gauraye da jinin jikin ki ki ke wa mutane ihu a kai da nuna kaman kin fi kowa iko a kan...... Cikin tafasar zuciya da ke taso mata a kuma tsiwace tace.....

    "Yes dole na gwada iko a kansa dan yaro nawa ne! Duk abinda nayi a kawo idanu kawai a zuba min, duk Wanda kuma yaga ba zai iya ba dan ALLAH dan ALLAH, ya ɗauke idanunsa daga gare ni, Dan babu wanda yake da iko dashi sama ni! Ni kadai nan...... Idan kuma akwai me shi na gansa gaba nah idan ya isa"

     Tana kaiwa nan ta ratsa ta gefen sa ta wuce tana ɗan buge sa, dan ta cigaba gaba da tsayuwa a gabansa tabbass zai sa ta aikata abinda batai niyya ba....... sai dai ko taku biyu batai ba ya finciko hannayen ta inda ta dawo baya gaba dayan ta dan abin yazo mata a matuƙar bazata, hakan yasa kaɗan ya rage bata faɗa kan faffaɗan ƙirjin sa ba, banda yayi saurin ja baya kaɗan....... Ita kuma tai ƙoƙarin tsayuwa kan ƙafafun ta...... Kallon ido cikin ido suka shiga yi wa juna dan idanun su ya sarƙafe guri ɗaya an kuma rasa wanda zaiyi juriyar ɗauke tashi........ Da ga karshe shi ya ɗauke tashi ya shiga bin jikin ta da kallo duk kuwa da ba sosai yake ganin ta ba dan rashin haske......

      Jin idanu suna yawo a kanta yasa jikin ta ya ɗauki kyarma abubuwan da suka shude suna tariyo kansu cikin idanun ta, hawayen da take ta rikewa tun ɗazun nan suka ɓalle mata, inda tayi saurin kai hannu ta ɗauke su...... Haɗi da faɗin "Aliyu....?" A tsawace........ 

      Wata makirin murmushi ya saki wanda taji sautin fitar sa cikin kunnin ta....... "Ka matsa min na wuce nace" 

      Ta faɗa a dake dan kuwa zuwa yanzu jaruntar ta duk sunyi nasu hanyar dakiya ce kurum....... A maimakon ya matsa kamar yadda ta buƙata sai ma ƙara kare ko ina da yayi........ Cikin izza gami da miskilanci ya ɗan motsa kananun pink lips nashi, Kamar wanda zaiyi magana sai Kuma ya gimtse, sai can ya buɗe baki zaiyi magana kenan aka buɗo ƙofar haɗi da kunna wutar office din in da haske ya baiyana tarrr.....

     Nan fa ko ina ya washe da hakse ido na ganin ido sai dai ba wannan mutumin da ya rutsa ta.....

      Wata nurse ce ta shigo hannun ta riƙe da file report!. 

     Ganin Aysha a zaune akan cushion yasa matar ta shiga bata haƙuri dan batayi tunanin Akwai mutum a ciki ba tunda tasan doctor yana waje hasali ma shi ya aiko ta. 

     Aysha Kam da kanta ke duƙe tana sauraran bugun zuciyar ta, ba tare da ta amsa mata ba ta tashi ta fice daga office din tana nufan ɗakin da aka kwantar da Maheer. 

    Sai da ta kawo ƙofan shiga ta tsaya ta kara saita kanta! Har ta kama handle zata buɗe sai kuma ta dakata sakamakon jin yadda jikin ta ke tashin kamshin wannan mayen tularen..... 

  Cikin karyayyen murya da tashin hankali ya gama baiyanu tattare dashi tace 

      "Nikam yau na boni! Ya zanyi?"

 "Weldone Madam"

Cewar Wannan nurse din hannun ta riƙe da waya da wata paper. 

   Ba tare da ta kalle ta ba ta Gada mata kai kawai dan Allah kaɗai yasan halin da take ciki a yanzu. 

    "Sorry Madam daman kinyi mantuwa ne" 

Cikin rashin maida hankali ta karbi wayar da papern dan gaba ɗayan hankalin ta yayi kaura daga gangan jiki...

      Hannu ta kai tayi kundunbalan buɗe ƙofar ta shige ganin tsayuwar nurse din a wajen

   Sai dai fah fuskar nan tata a ɗaure take tamau dan a yau ɗin nan a AY take jin kanta ba Aysha bah.

   Ido yaya Abdul ya zuba mata baya ko kyaftawa, shima tashi fuskar a ɗaure take kaman zatayi aman wuta, ba komai yaja haka ba sai jin tularen da yake tashi a jikin ta ba shi ke jikin ta ɗazun bah. 

     Nan fa kishin yan maza ya motsa daman shima ba sauƙi. 

    Ba zato ba tsammani taji saukar muryan yaya Abdul a cikin dodon kunnin ta kai tsaye..

     A maimakon ta amsa masa sai ta shiga bin dakin da kallo a fakaice ko zata ga Abba ya cece ta, sai dai babu shi babu Safna. 

     Da yake zuciya tana kusa nan ya dunfaro ta a fusace yana jin zuciyar sa tana tafarfasa. 

    Bai jira komai ba ya ware dukkan yatsun sa biyar zai daura a fuskar Aysha da ta daskare ta kasa ko motsi tana jiran taji saukar mari.....

      Jin shiru yasa ta ɗago a hankali dan taga abinda ya hanasa....

     Nan ta ga hannun sa riƙe cikin hannu wani da sauri ta waiga dan taga waye wanda ya cece ta nan...

     Doctor ne riƙe da hannun sa ƙam! A kausashe cikin muryar gargaɗi yace "kar ka fara! Wannan ba hurumin ka bane, don't cross your limit" ya ƙare Maganar da yarfar da hannunsa ya na duban Aysha yace "kiyi haƙuri ma'am"  wata muguwar kallo ta shiga binsa dashi kafin ta furta "who there you...." 

    "Kiyi haƙuri madam kawai gani nayi abinda zaiyi ba dai dai bane" 

     Shiru tayi bata ce dashi komai dan ta rasa abin fade kamar yadda ya Abdul ya rasa ta cewa daga karshe ma dakin ya baro a fusace da kudirin sai yaga uban da ya tsaya mata...... Dan shi kam tunda suka shigo golden care sai yaga kaman an wani sauya ta....... Dan tattali da girman da yaga ake ta bata........ Shi kuwa ba zai so hakan ta faru ba........... (Toh jama'a ni kuwa nace anyaaaa kuwa..... Yaya Abdul hmmmmm🤔 baki na dai da goro) 

     Cikin girmamawa wannan doctor din ya kara bata haƙuri ya fice yana jin zuciyar sa fess, dan ko banza shike da Nasara. Inda suka barta cikin ƙaulani

     Ganin tsayuwar ba zai haifar da mai ido gare ta ba yasa ta shige toilet ta ɗauro alwalla ta zo ta gabatar da sallar i'sha'i da aka idar tuntuni..


     9:pm Abba da Abbu ne gaban Anne tana yi musu ƙorafin abinda ba'ayi ba,su kuma sune bata baki da fadin za'a gyara har sun tashi zasu fita ta katse su suka koma suka zauna.

     "Kunga har zan mance ko? Ai gwara da ALLAH yasa na tuna...! Kaga waɗan nan guzumyen da kuka tara min cikin gida babu aure toh wannan karan na gaji da ganin su! Sabida haka bana son yaran nan su kaimin wata biyar cikin gida, bazan iya zama dasu ba kar wata rana takaicin su ya kashe muku ni a barku da maraici, dan gudun haka a aurar dasu kawai!kar ka ga da na gansu ɗazun na zata iyayen ne, a'a toh ba ruwa na, ganan bikin da muka je yara ne ƙanana da basu kai su ba, waɗan nan ban san mi suke jira ba duk sun gansame suna haɗa kai da iyayen su, dan haka ayi musu magana shekaru 24 ba wai Shekara ɗaya bane ehe"

       Ta ƙare maganar da karkaɗe kafafu idanun ta na kan su Abba. "Za'ayi musu magana ai ko nan da wata ɗaya kika ce haka za'ayi se idan yaso sai a siyan masu tabarmu su je dasu matsayin gado da katifa". 

       "A'a baza'a yi haka bah, ko uwayen su ai sa saya masu, hakan ne ma yasa na bada lokaci mai tsawo har haka! Kai baza kayi magana bane?" Anne ta ƙare maganar tana maida duban ta ga Abbu da tunda ya zauna baice komai bah. 

     Sunkuyar da kai ƙasa yayi haɗi da faɗin "ayi haƙuri Anne in Sha Allah yadda yaya yace haka za'ayi, sai ayi masu maganar". Iya abinda Abbu ya furta kenan yaja bakin sa ya tsuke.

     "Ai shikenan ku tashi kuje Allah ya tashe mu Lafiya" amsa wa sukai da Amin bayan sun sallame ta suka fito sai dai tsakar gidan ba kowa, ba kaman jiya da suka yi zaman waje bah. 

     Nan din ma sallaman juna sukayi sannan suka rabu da zummar zuwa safiya sai su zanta akan batun da Anne tazo dashi......


       Danƙararre Kuma hadaddiyar mantion, mai lafiya da ɗaukar hankalin mai kallo, ba ƙaramin kuka kudade suka yi a gidan ba duba da komai na ciki na musamman ne........ Part part dake Cikin gidan sunyi biyar ko wanne da tazar nisa tsakanin su da juna kai kace ko gida daban daban ne....... Kuma duk komi nasu ɗaya Sai guda ɗaya da ke da nisa da sauransu hudun nashi tsarin dabam take dan tayi wa sauran fintinkau duk da su ma ɗin sun ƙeru........


        Daga daga cikinsu part din na shiga..... Wata hamshaƙiyar mata ce zaune hakimce akan 1 seater da ta kusa mamaye shi, dan kam matar tabarakallah akwai kiɓa....... Gefen ta Daddy ne da ya zauna yayi shiru kamar mai nazarin wani abin.

         "Amma Alhaji abinda yaron nan yake yi yana kyautatawa kuwa? Ka duba ka gani......."

     "Ki natsu mana Hajiya! Ai ya kusa shigowar hannu! Wannan na ɗaya daga cikin abin da yasa nace Maleeka ta dawo Nigeria dan ayi ta ta ƙare kawai! Wallahi ALLAH wannan karan ko yana so ko baya so sai na aura masa Maleeka, dan ba zaiyu ya maishe mu marasa amfani ba, kinga Kuma idan na aura masa Maleeka ita zata kankaro mana mutumcin mu na iyaye gare sa ko da kuwa ba ya......." Maƙut ya haɗiye sauran maganar sakamakon jin shigowar mota! A tunanin sa ko shine hakan yasa ya leƙa ta window! Nan kuwa idanun sa sukai masa kyakkyawan gani dan kam ba shi bane, kakan sa ne, da baban sa sai matan sa, da wasu yan mata uku a shekaru zasu yi 24, gefe kuwa wata kyakkyawar farar mata ce, sa wani namiji gefen ta. Ko wannen su ka gani fuskar sa cike take da walwala.

     Nan take yaji zufa tana tsantsafo masa ko ta ko ina, duk kuwa da AC da ke aiki a falon, hular kansa ya ciro ya hau fifita da ita, ko ys samu rangwame na daga zafin da yake ji har chan ƙasar bargon sa. 

     "Alhaji wai lafiya kuwa naga duk ka bi ka kiɗime lokaci ɗaya kaman wanda aka sarrafa da remote?" 

      "Shikenan Hajiya wallahi ta ƙare sai kuma abinda muka gani" 

    "Kaman ya ta ƙare? Ban gane abinda kake nufi bah"

     "Modɗibo ne da Alhaji Ahmad da sauran iyalan s......"

     A mugun zabure ta miƙe a kiɗime dan tafi Daddy shiga halin ruɗu..

     "Har da Hajiya shuwa kenan aka zo?" 

"Kowa ma! Amma Aliyu akwai dan iska da rashin mutunci da tijara! Kawai ba zato ba tsammani sai dai kawai muga mutane daga sama babu sanarwa?"

      "Yan......" 

     Mommy, Daddy zan je na ga gari cewar wata matashiyar budurwa bata da wani kaurin kirki kaman ka hura ta ta faɗi....... Tana da matsakaicin kyau sannan bata cika tsayi ba......... A shekaru kam zatayi 27.......... A kallon farko zaka fahimci idanun ta a buɗe suke ........ Maleeka kenan matashiyar budurwa mai zamani sanye take cikin shirin English wear inda ta Kawo hular nan mai malfa amma na gayu ta kafa a kai inda kitson da tayi na ƙari ya sauka ta kasar hular........

     Cikin rashin damuwa da shigar da ke jikin ta suka amsa mata da a dawo lafiya. Ta fice daga falon..... Su kuma suka cigaba da zancen nasu dan gani suke kamar anci amanar su.......


***