Episode 8
INUWAR DUTSE.
Ep 08
"Amma Alhaji why not mu kira moon muji daga gare ta" "idan mu kayi kiran nata yanzu ai zasu gane mun san da zuwan su! Dan haka ba sai an kira ba mu zuba ido kawai dan muga iya gudun ruwan su, sannan kar mu leƙa su mu nanu kamar basu san da zuwan nasu ba period" "gaskiya Kam Alhaji, kasan ta kan tsiya, duk lokacin da suka ga daman gaya mana sai mu leƙa su, kaga nima an kawo min sauƙin da yanzu ina chan kitchen ina wahala"
Nan dai suka cigaba da zancen su kamar sun mance da wanzuwar wasu baki a gidan.
***********
A chan ɓangaren da aka sauke su Baffa, modɗibo ne zaune bisa kujera ya kasance kyakkyawar farin bafulatani duk da tsufa ya baiyana jikin sa hakan bai ɓoye kyawu da haibar da ALLAH yayi masa bah.
Zaune yake shiru ya zuba ma waje ɗaya ido yana kafe hoton dake a bangon dakin da kallo, hannu yakai ya ɗauke kwallar da yaji ya cikar masa a kurmin ido yana sakin wani murmushi mai ciwo yana jin zuciyar sa tana zogi da tafarfasa.
Baffa da ya shigo dakin tuntuni ganin halin da moddibo ke ciki ne yasa ya ƙarasa wajen frame photo din ya dauke shi daga wajen. ya furta "Babu abinda ya gagari ALLAH! Bai manta da lamuran mu....." Dakatawa yayi yana doson Inda modɗibo yake ya kai zaune gefen sa yana riko fararen hannayen sa cikin fulfulbe ya cigaba da maganar sa "kayi dauriya ni shaida ne modɗibo! Amma ka ƙara bisa ga da, ina ji ajiki na komai ya kusa zuwa ƙarshe, hakkin jini ba zai taba barin ko waye bah" shiru modɗibo yayi ba tare da yace komai ba. shi ba Mutum bane mai yawan magana ba, idan anji maganar sa kuwa shi da Aliyu ne. "Bara naje na kwanta modɗibo ALLAH ya tashe mu lafiya" bai jira cewar sa ba ya miƙe zai tafi sanin a wannan lokacin ba amsa zai samu daga gare sa ba. "Ka maida hoton inda yake" "amma modɗibo...." "Bana son musu kayi yadda na buƙata" "ALLAH ya huci zuciyar ka Allah guburo" tattausar murmushi ya saki jin abinda Baffa yace, shima kuma yayi ne dan zuciyar sa tayi sanyi. "Mutanen gidan nan fatan suna lafiya? Kun shiga kun duba su kuwa?" Cewar modɗibo "Eh duk mun shiga! har da Moon kafin su wuce sai da muka shiga duka, suna kuma gaishe ka, sun zo zuwa ɗazun nan, Ni nace su bari zuwa da safiya! Amma ita Hajiya Turai bata na" "ma sha ALLAH haka ake so, shi gogan bai shigo ba kenan?" Murmushi Baffa ya saki yace "wane ni na shiga tsakanin ku modɗibo! Kila dai wata sabgar ta riƙe sa dan......" Cak ya dakata da maganar sa sakamakon ganin Inuwar mutum a ta bayan window. "What! Mutum kuma?" Ya faɗa cikin subutar harshe, wanda hakan yaja hankalin modɗibo ya maida duban sa ga window ɗin wanda sai a sannan wannan ɗin yake barin Wajen.
Da sarsarfa Baffa ya fita dan ganin ko waye amma bai hangi kowa ba sai gilmawar mutum da ya gani. Nan ya nufa kai tsaye, da yake wajen akwai karancin haske. Baiyi aune ba yaji saukar abi mai matukar zafi ya ziyarci kwanyan kansa, wata azababbiyar ihu ya saki inda gaba ɗaya gidan yayi amsa kuwa.
Zubewa yayi wanwar a ƙasa numfashin sa suka tsaya cak. jini ya cigaba da malala a ƙasa.
Shi kuwa wannan da yake cikin shigar badda sahu, ganin halin da Baffa ya shiga ne yasa ya wurgar da karfen dake hannun sa, Kamar ƙyaftawan ido ya kama fence ya gudu.
Gaba ɗaya ihun da Baffa ya saki kaf illahirin gidan sai da ya amsa, nan da nan kowa ya fito har da ma'aikatan gidan, da modɗibo, hankali tashe, aka shiga dube dube dan tabbass muryar Baffa suka jiyo.
"Hajiya tashi! Ba lafiya" cewar Daddy a kiɗime zufa sai karyo masa yake ko ta ko ina duk da fanka da ac dake aiki a dakin amma hakan bai hanasa jiƙewa sharkaf da zufa ba kaman wanda ya watsawa kansa ruwa.
"Wai Alhaji lfy kuwa! Waye ba lafiya?" Shiru babu amsa, sai dana sanin da ya koma na tashin ta da yayi. "Lfy fah! Koma abinki" kallon nazarta ta shiga binsa dashi, ta buɗe baki zata yi magana kenan taji kaman hayaniyar mutane. Zumbur ta miƙe ta nufi window tana yaye labule.
"Ya subhanallah! Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" ta faɗa da ƙarfin haɗi da dafe hannu a ƙirji tana jin zuciyarta na gudu, nan da nan bugun zuciyar ta ya sauya. Sakamakon ganin an dauki Baffa kaman matatce ga jini ya jike farar jallabiyar jikin sa. Ji tayi tsakiyar kanta tana jujjuya mata yana harmutsewa, hannu takai ta fizge hular kanta, ta shiga ya mutsa kanta Kamar wata sabuwar kamu a hauka. Haɗi da kurma ihun da ya dakatar dasu modɗibo daga shiga mota..
Ita kuwa Mommy Nan idanun ta suka shiga rufe wa a hankali kafin ta fadi nan sumammiya.
"Ke ke lafiyar ki kuwa? Mi yake faruwa dan Allah ki rufa mun asiri, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, lahaula shikenan.....zulaihat zulaihat dan ALLAH ki taimaka ki tashi"
Ya faɗa yana girgiza ta amma ina bata ko motsi.
A zabure ya mike jiki na rawa ya shiga zagaye dakin kafin yayi aune yaji bugun ƙofa wanda hakan ya ƙara harmutsa ya'yan cikin sa. Sai da aka ƙara buga ƙofan san nan ne yayi kundunbalan nufan ƙofa jiki na rawa ya buɗe yana rumtse idanun sa.
"Sir!!!! Is there anything that happens he...." Bai kai ga ƙarasawa ba idanun sa ya sauka akan Mommy dake kwance bata ko nunfashi.
Daddy da ganin ɗaya daga cikin security na gidan ne yasa ya shiga sauke nunfashi a ɓoye. Cikin dakiya yace "give help to carry her to the hospital" "Ok sir" nan aka kwashi Mommy aka fitar da ita, suna dai dai ƙofan falon Maleeka na kutso kai ciki.
"What is happening Daddy? What happened to my mom" Cewar Maleeka tana bin Daddy da kallo irin kallon tuhumar nan.
"Karki damu she is scary that why! Don't worry dear, let quickly take her to hospital" yana kaiwa nan suka ci-gaba da tafiya har suka fita aka saka ta mota suka bar gidan a guje kamar waɗan da zasu tashi gari. Daman su modɗibo tuni sun wuce da Baffa zuwa hospital na Golden care.
***********
AY industries...... Fitatce Kuma shahararren Company wanda gaba ɗaya duniya tasan da zaman ta, na wannan matashi mai ji da kyau,ilimi, wayewa, dukiya, miskilanci. Yaro da kuɗi abokin tafiyar manya, dan kimanin shekaru 35 a duniya.... Sosai Company ya tsaru tsayawa fallasa tsaruwar s bata baki ne..... Shiru Company ya ɗauka baka jin motsi da hayaniyar komai, dan Company ɗin yana a bayan gari ne sai dai tun daga farkon layin akwai street light wanda ya haskaka ko ina.
Sai dai wutar ma'aikatan a kashe suke, banda office ɗaya da ke dauke da haske amma ba sosai ba
Zaune yake ya juyawa ƙofa baya doguwar sunan kansa da yasha manyan kitso guda biyu jelar ta sauko har gadon bayansa, kunnin sa kuwa da magnet sakale a gefe ɗaya dayan kunnin kuma babu. A hankali ya shiga jiyo da turning chair da yake kai ya juyo gaba ɗayan sa haɗi da kai hannu sa da dake dauke da glove kan fuskar sa ya yaye abinda ya ma fuskar sa shamaki da bayyanuwa...... Ya subhanallah kyakyawa kuma hadadde halitta mai cike da kwarjini da haiba, ƙyakyawan fuskar sa fara fet ɗauke take da manyan dara daran idanun da suke sheƙi gasu farare fet kamar madara, inda bolls din suka kasance brown, ga Kuma zarozaron gashin ido. wanda hakan ya ƙara fidda kyawu da shape nasu.... Eye brown din sa kam kamar su haɗe sai dai gefen dama na eye brown nasa a tsage take, hancin nan nasa ya kasance pointed, ga kananun pink lips nasa da suke kaman ya zizara jan baki. Ga fuskar nan zagaye take da saje irin na matasa masu ji da lokaci da kuɗi, yasha gyara sai kyalli da ɗaukar idanun mai kallo yake.
Mutum ne mai faffaɗan ƙirji. Ya subhanallah, wuyar sa kuwa ɗauke take da chain kamar yadda hannun sa dake dauke da gargasa yake ɗauke da Chain da gani ba sai an faɗa ba kasan yaci kuɗi.... Cikin sautin muryan sa mai cike da kwarjini da amo da kauri amma ba chan din nan ba kamar wanda akayi wa dole ya furta "done" yana ɗan sakin makirin murmushin da bai wuci pink lips nasa ba ya kai hannu ya cire glove din yana sakawa a dust been.