Episode 9
INUWAR DUTSE.
EP 9
Tsaye ya miƙe kan ƙafafun sa Cikin tafiyar nan nasa mai cike da izza ya Isa ƙofa, kama handle din yayi ya buɗe ya fita daga office din inda ya tadda ɗaya daga cikin security shi yana jiran sa daga ƙofan. Komai bai ce da shi ba, ya wuce abinsa, excort nasa yana take masa baya. Ba tare da ɓata lokaci ba aka buɗe masa back seat ya shige, inda excort ɗin ya shiga ya tada motar suka bar ma'aikatan. Sai da suka hau titi sannan ne Ameer ke tambayar sa inda suka yi. "Boss! Ina zamu, Gida ko hospital?" Sai da ya ɗauki tsawon mintuna biyu kafin ya amsa a gajarce yace "gida" jin haka da Ameer yayi ne yasa ya shiga duban AY ta front Glass.
Ba abinda AY yaƙi jini irin kallo, aikam baiyi ƙasa a gwiwa ba yayi kicin kicin haɗe ƙyakyawan fuskar sa guri ɗaya. Ganin haka yasa Ameer ɗauke idanun sa daga kansa.
Koda suka isa gida Sanin duk suna asibiti, yasa ya shige kai tsaye zuwa nasa part din da ya fi na kowa haduwa. Koda ya shiga bai zauna ba ya watso ruwa ya fito ya ɗauki system ya cigaba da aikin sa cikin kwarewa.
***********
Tun bayan da aka kai Baffa asibiti likitoci ke kansa suna ƙoƙarin cetan rayuwar sa dan jinin dake zuba a kansa ya gagara tsayawa.
Ana shiga da Baffa sai ga su Daddy sun iso Inda aka mika Mommy ɗakin dake kusa da na Baffa. A kallo ɗaya kayi wa family zaka fahimci suna cikin tashin hankali marar misaltuwa, a wannan karan har shi Daddy ya shiga tension sai dai kasar zuciyar sa ba haka take bah. Suna zaune a nan jigum jigum sai ga doctor din ya fito yana tunkarar su modɗibo.
"Doctor ya jikin nasa?" Cewar modɗibo yana zuba masa idanu da jiran jin abinda zai ce.
"Jiki Alhamdulillah! Mun samu jinin ya tsaya, yanzu dai yana bacci sakamakon allurar da mukayi masa" zuba masa ido kawai modɗibo yayi kafin ya ɗauke yana gaɗa kansa. Sai can yace "ya jikin ita zulaihat ɗin". Saurin tarar maganar Daddy yayi da faɗin "ai jikin da sauƙi daman tana irin haka, da zarar anyi mata wata allurar shi kenan! Yanzu haka ma nasan zuwa da safe zamu samu sallama" murmushin manya modɗibo y saki kafin yace "ma sha ALLAH haka ake so! Jeka abinka doctor, ALLAH ya ƙara masu sauƙi" amsawa yayi da Amin yana komawa chan ɗayar kujerar da Maleeka ke kai sai wani cin magani take yi.
"Daddy what this people are doing here? And when did they came without any noticed" "calm down Dear, let us get back home I will explain....." "Nooo Dad you tell me now" ta faɗa a ɗan ƙule dan a duniyar ALLAH nan ba abinda ta tsana da kin jini kaman dangin AY dan a nata wautar su ma basa son ta barin ma shi modɗibo. Taɓe baki Daddy yayi kafin yace "amm Baffa ne ba lafiya! Ban kuma san baida lafiya ba sai da muka zo, U kno they're taking us for granted". Shiru tayi tana jujjuya maganar Daddy cikin rai lokaci ɗaya kuma tsanar su yana ƙara chakar mata zuciya. Cikin iyayi ta furta "buh Daddy we support to stop them from all this, like doing things without our knowledge"
"Daugther kenan! Wannan aikin sai ke, ai shi yasa I'm eager na ga kin mallaki Aliyu, amma dowowar su ba zai bar komai ya tafi mana dai dai ba, hasali ma yana iya zama silar rashin mallakar AY a rayuwar ki" zaro yan madaidaitan idanun ta tayi haɗi da miƙewa a zabure cikin ɗaga murya tace "what????". Aikam karaf sai a kunnin modɗibo da yafendo (matar Baffa) dake zaune shiru ga kuma dare, waje yayi tsit hakan ya sa muryar ta yin amsa kuwa. "Mi haka wai? Zauna mana daɗi na dake gaggawa, ko so kike ki jawo hankalin wanchan tsohon gare mu". Hannu ta kai ta shafi goshin ta haɗi da furzar da huci da baki tace "na zauna fah kece! Impossible......" Waige waige Daddy ya shiga a kiɗime gudun kar da modɗibo yaji sai dai ganin hankalinsa sa ma gaba ɗaya baya wajen ya ya sauke ajiyar zuciya kafin ya miƙe tsaye ya kama hannun Maleeka suka bar Wajen zuwa bayan wani window.
"Ke fa watarana sai ki dinga misbehaving kamar mara wayau" a ɗan tsawace kamar mai magana da tsaranta Maleeka tace "excuse me Please! Whatever you will say i fucking doesn't care! I don't know or how you will do buh don't let everything escape from I......" Dakatawa tayi tana duban Daddy cikin raunin da ya ziyarce ta a lokaci ɗaya ta faɗa jikin sa, ta cigaba da faɗin "i really Loves him! And the loves of him to me I kno it's destiny! you loves me Right? Then show the Love through giving me the person a loves More than everything in this world, pls Daddy" ta ƙare maganar tana duban Daddy.
Hannu daddy yasa ya maida Ita jikin sa, ya shiga bubbuga bayanta alamun lallashi sai da ya tabbatar da ta samu natsuwa ya ɗago ta yace "in Sha Allah i will try my all best to give you what you want! I will use my power on him.... But definitely if this people are still with us, we are getting nothing from what we want! Sai dai karki cire tsammani, your Dad is here for you okay?"
"Gaɗa kai tayi da murmushi ɗauke da fuskar ta ba tare da tace komai ba. "Bara na koma sai kin zo" nan ɗin ma bata ce dashi komai ba, shima bai jira cewar ta ba ya bar wajen.
Koda ya koma ya tadda su modɗibo sun bar wajen, sosai ya yi farin ciki da haka, shima bai zauna nan ba ya Shige ɗakin da aka kwantar da mommy.
***********
Washegari
Abba ne shirye cikin shirin fita, sai dai kayan da ya saka da gani Wani waje mai muhimmanci zaije duba da irin ɗaukar idanun da take ga yasha guga, takalman ƙafar sa suma sun sha folish, tularen yan duri ya ɗauke ya bi jikinsa da ita, yana ƙara duban kansa..... Karan kansa yasan ba karamin ƙure a daka yayi ba "ALLAH sarki shatu, duk mugun halin ta dai a kwai kyauta, tunda har take dinka min kaya" ya faɗa yana ƙara bin kayan da kallo.
"Abba ka fito kai ake jira mai napep ya iso" cewar Safna daga ƙofa. Yana jin haka ya fito sai wani tashin kamshi yake.
Su umma dake tsakar gidan ai sake sukai da baki suna kallon Abba cike da mamaki, sai Anne itama ta fito cikin tata shigar alfarma. Nan fa mamakin nasu ya dadu fiye da da suka shiga binsu da kallon al'ajab. Dan kuwa kansu ya gama ɗaurewa. Cikin rashin damuwa da kallon nasu Abba ya maida duban sa ga safna yace "ke Safna kin tuna ki ɗauko masu kaya?" "Eh Abba na ɗauka har na kai napep yaya Abdul ma yana waje yana jira" "toh muje! Anne bismillah, kar mu makara" "yanzu kuwa! Toh jama'a da alkhairi! Mukam sai kun ganmu" cewar Anne tana washe haƙora da son ƙular dasu. Babu yadda suka iya suka sallame su, su kuma su Abba suka fice daga gidan. Inda suka bar safna a ƙarshe.
"Safna Safna! Zo nan" Goggo ta shiga kiran Safna chan kasa gudun kar su Anne suji. Ba musu kuwa ta je kiran da Goggo ke mata a maimakon su tsaya tsakar gidan sai ta jata zuwa ɗaki. "Ina zaku je ne, da kuka ci wanka haka babu labari! Kema ana son a koya maki munafunci Koh?" "A'a fah Goggo! Zamu dubiyan jikin Maheer ne! Toh Anne da Abba da Abbu kaman akwai inda zasu ne" "aiyoo in ce! To tashi kije! ALLAH ya kiyaye" amsawa Safna tayi da Amin da murmushi kan fuskar ta, dan karyar da tayi..... Babu inda su Abba zasu je banda golden care duba jikin Maheer, toh shi ne Abba yace kowa yaci wanka sosai dan asibitin masu kuɗi ne, jin haka da Anne tayi ne yasa itama ta fidda Kayan kasar akwati Kamar waɗan da zasu ganin gommna. Ba ta tsaya bin ta kowa ba ta fice daga gidan tana fita kuwa sai ga Anty Ramlah da Anty Ameerah suna isowa ko wanne hannunta rike da basket.
"Toh toh ku shiga dan babu lokacin batawa" dake napep biyu ne nan ya kwashe su suka bar layin. Mama dake leken su! nan ta saka ma fitar nan tasu alamar tambaya. Gada kai tayi tana komawa ciki da tunani barkatai a cikin zuciya da bata da mai bata amsar su sai su Abba. A dai dai gate na asibitin a ka sauke su, nan suka sauka suna dosan ciki, sai dai basu samu wucewa kai tsaye ba sai da suka bi dukkan wasu procedure na Asibitin.
Anne Kam ba baki sai ido, bakin ya mutu mus an kasa furta ko mai, cikin zuciya kam dankare take da tambayoyi. Haka ma ya kasance bangaren su Anty Ramlah, dan kam dole suyi mamaki, Asibitin da ke da mugun tsada mi alakar Aysha da Asibitin.
Shiru dai babu wanda ya furta komai, suna daf da shiga corridor da zai Sada su da reception sai ga wata musulmar mota ya doso kai cikin asibitin. "Garin daɗi na nesa! Allahu Akbar kai Abdul kalli motar chan ka gani, dankari" "Abba idan kana dube dube fah Akwai cctv ko ta ko ina zaka iya zama suspect" Kai ka sanshi! Ni ALLAH na tuba, Anne sai naga kaman Abdul ya koma ɗan baƙin ciki, kiga fah tun jiya ya chanza hali gashi yau ma da kyar na tasa keyar sa muka taho kema shaida" "toh Ni banda ma ka faɗa ai ban san yana yi ba kaga kuwa yayi aikin banza koh?" "Hakane kam" da wannan zancen har suka shiga sai dai ganin mutane yasa duk suka ɗinke baki.
Direct ɗakin da aka kwantar da Aysha suka nufa inda suka tadda ta zaune a kan kujerar da yake kusa da dakin da aka kwantar Maheer. "Ikon ALLAH mi kuma kika fito dauka a waje da kika baro yaro shi ɗaya a daki?" Cewar Abba yana bankama Aysha harara. Ɗago da dara daran idanun ta tayi tana duban su. Cikin sanyin Muryar ta tace "sannun ku da zuwa" ta zarce da miƙa masu gaisuwa. duk amsawa sukai da tambayar ta mai jiki banda yaya Abdul da bai ko dube ta ba. "Mi yasa kike waje ne mama nah?" Cewar Abbu yana duban ta da tausayawa, dan guntun murmushi ta saki kafin ta amsa da "yana bacci ne Abbu, shine na dan fito" "ayyyo ALLAH ya ƙara sauƙi! Amma ai ya falka ko?" "Eh Abbu ya falka cikin dare jikin kuma Alhamdulillah" "madalla haka ake son ji Allah ya kara sauƙi". Duk da Amin suka amsa suna zama a kan kujera.
Suna a zaune Abba da Abbu suna hira sai Safna da Anty Ameerah da Aysha dake dan saka masu baki a hirar tasu. Sai Anty Ramlah da Anne da suke tasu sama sama, yaya Abdul kam ja gefe yayi ya fita batun kowa.
"Allahu Akbar! Ramlah duba kiga! Ma sha ALLAH kin ga wasu kaman wankan injin?" Anne ta faɗa tana taba Anty Ramlah da ta waiga ta gani... Ba musu kuwa ta waiga idanun ta suna fadawa a kan kyakkyawar farar fuskar Anty moon. Gaɗa Kai ta shiga yi dan tabbass Anty moon kyakkyawar mata ce, ga wata budurwa da ke kama da ita sak har kamanin ya ɓaci sai wata a gefen ta na hagu.
yan matan dai baza su wuce 24 years bah, bayan ta wani matashi ne shima kyakkyawa ma sha ALLAH sai dai waya ne ƙare a kunnin. Ganin suna dunfaro inda inda suke yasa Anty moon ɗauke ido tana cewa "Anne ki bar kallon su haka mana kin san irin Mutanen nan idan ka cika kallon su sai su aza zargi a kan ka" "kuma haka ne! Ai Ni sai yanzu na ƙara jinjina ma Abban ku da ya kawo shawarar kowa ya saka kaya masu kyau, fisabilillah yanzu ɗin da wujiga wujiga muka zo nan din ya kike tunanin za'a kalle mu?" "Anne kiyi shiru gasu sun kusa isowa fah"
Ɗif ta ɗinke bakin ta, ta shiga binsu da kallon gefen ido ji take kaman ta tashi ta kamo su........
"What????" Cewar fadeelah da idanun ta suke a kan Aysha da bata san da isowar wasu wajen bah..... "Ke lafiyar ki kuwa fadeelah?" Cewar Anty moon tana kallon ta. "Rabu da Ita Anty ina ga yan kanta ne suka motsa" cewar Intisar. "Ke dalla ware! Anty wallahi Kamar Mammy Maheer, wacce nake baku labarin ta ɗin nan ne fah" ta ƙare maganar cikin zumuɗi... Da yake Anty ta san Aysha a bakin fadeelah tun ba yanzu ba yasa tace "ina take halan? ALLAH yayi yau dai zanga Mommarh na ido da ido" "wai wacce wannan ɗin ne, ta ishe mutane ne wai?" cewar Hamma Aslam wato wannan matashin dake a bayan su Anty amma yanzu ya dawo ta gefen su..... "Toh nima Hamma Aslam ban san ta ba fah" cewar Intisar. Bata ko tsaya tayi yi musu bayani ba ta kwasa da ɗan sauri ta doshi inda Aysha take fuskar ta ɗauke da murmushi.
Ba zato ba tsammani Aysha taji an faɗo mata jiki, a kuma dai dai nan wani sanyayyen tulare kame wajen da kamshi mai saka nutsuwa..... Intisar da itama ta kwasa a guje zata gun Aysha dakatawa tayi cak sakamakon jin sanyayyun tularen AY....
"Auuuch" Aysha ta faɗa tana ɗan ya mutse fuska kamar wacce zata fashe da kuka...... Su kuma Anne Abba Abbu su yaya Abdul da sauran duk sake da baki sukai suna kallon ikon ALLAH barin ma Anne da ta Fara Ganin su......
Dagowa fadeelah tayi tana sakin siririn dariya haɗi da faɗin "sorry Anty! Ai daga nesa na hango ki nace kai wannan kece, ina Maheer?" Dan hararan ta tayi kaɗan Kafin ta ɗauke kai tana maida shi gefe nan idanun ta ya faɗa a na Hamma Aslam...... Dan zare manyan idanun ta tayi kaɗan haɗi da sakin guntun murmushi....... "Hajiya AY" Hamma Aslam ya faɗa bayan ya karo so wajen fuskar sa ɗauke da murmushi mai faɗi....... " A kuma dai dai wannan lokacin! Mayen tularen AY ya cika wajen wanda hakan yaja hankalin su Abba duka suna Maida duban su gare sa....... A kuma dai dai nan ƙirjin Anty Ramlah bugawa tare da na Aysha da jin kamshin tularen AY da ganin Anty moon ya haifar mata..... Ita kuwa fadeelah nan da nan ta natsu kaman ba ita bah....