Episode 10
INUWAR DUTSE.
Ep 10
Jin idanu ya dawo kan sa, yasa ya ƙara ɗinke fuska tamau, p-cap dake a kansa ya ƙara jawowa ya rufe masa rabin fuska, inda jelar kitson da ke kansa suka sauka gadon bayan sa. Sai da ya zo gaf da su suka ɗauke ido a kan sa jin kwarjinin sa ya cika masu idanu...... Anne Kam ƙasar zuciyar ta gulmarsa ta shiga yi akan kitson dake kansa...... "Aliyu??" Anty ta ambaci sunansa, lumshe manyan idanun sa yayi ba tare da ya amsa ba ya cigaba da tafiyar sa, sai da yaje gaf su Abba ya miƙa masu hannu sukai musabaha ya ƙara gaba ba tare da ba yaya Abdul hannu bah sai wani mugun kallon da ya watsawa Hamma Aslam a fakaice. Sum sum Hamma Aslam ya bar wajen.... Abba Kam riƙe hannum sa yayi ya shiga murza wa dan har zuwa wannan lokacin yana jin tautausar hannun AY a nasa. Sai washe hakori y shiga yi..
Ganin wucewar sa yasa a kusan tare Aysha da fadeelah suka sauke ajiyar zuciya sai dai na Aysha ya kasance ɓoye. Anty moon ce ta katse shirun da wajen ya dauka ta hanyar miƙa masu gaisuwa, inda suka amsawa cikin kulawa, barin ma Anne.... "Ke fadeelah da mugun son jiki kike! Da ALLAH daga min Mommarh nah" cewar Anty moon. Dariya ta saki tana ɗaga Aysha haɗi da faɗin "ALLAH Anty yaya ne ya ruɗa mu! Kiga Intisar fah har yanzu ita bata dawo normal bah" kwashewa sukai da dariya kaman hadin baki ita da Intisar sai Safna. "Ki dage ya jiki kinga sai kiyi masa bayani yadda ya kamata" "sorry Anty" fadeelah da Intisar suka faɗa suna zarcewa da gaisar da dasu Anty Ramlah da Anty Ameerah, suma da murmushi ɗauke da fuskar su suka amsa masu cikin kulawa. Aysha da kanta ke ƙasa tun bayan da ta sunkuyar bata ƙara ɗagowa ba, tana sauraren bugun zuciyar ta gefe kuwa tana jin nauyin kallon fuskar Anty moon. Da kyar ta ɗaure sai dai bata ɗago ba tana a Yadda take tace "Ina yini Anty?" Anty moon dake ta lura da ita ta saki murmushi da jinjina halin ta dan a ɗan Kasancewar nan tasu ta gane Aysha miskila ce. Watsar da tunanin komai tayi ta amsa da "Alhamdulillah! Ina Maheer?" Shiru bata amsa ba sai Anty Ramlah ce ta amsa da faɗin "ai wannan kanwa taki Kunya ke gare ta! Maheer kuma yana cikin babu Lafiya" "subhanallah! Mi ke damun sa" cewar Anty "ai tun jiya aka kwantar damu! Amma jikin yanzu Alhamdulillah yana ciki ma ai yana ta shan bacci" "ALLAH ya sawwake zamu iya shiga mu duba sa?" "Ikon ALLAH! Ai ku tafi kanku tsaye Wallahi an zama ɗaya ai, barin ma ai ita mahaifiyar tasa ta sanku, kuma kun santa don haka ku shiga kanku tsaye" Cewar Anne. "Toh mun gode Hajiya mama" cewar Anty Moon ita Kuwa Anne baki har kunne jin ance mata Hajiya. Duk kwasa sukai suka shiga ciki sai dai su Abba Basu shiga ba haka ma Aysha. "Kedai Aysha Allah ya yaye miki wannan hali taki! Kowa ya tashi dan ya duba jikin yaro amma banda ke! Allah ya kyauta ya yaye miki" cewar Abba. Bata ko ɗago ta kallesa ba dan abinda take ji yana mata yawo a ƙirji ya fi gaban wasa.
Basu wani dade ba sai ga Anty da su fadeelah sun fito tare da Anty Ramlah da Anty Ameerah inda aka bar Anne kawaii a ɗakin. "Mun gode ALLAH ya bada lada ALLAH yayi albarka" cewar Abbu" Amin ya ALLAH mun gode Baba! Zamu karasa ciki in Sha Allah zamu dawo zuwa anjima" "madallah a gaisar da masu jiki muna nan shigowa dai in Sha Allah! Ramlah da Ameerah ku bita kuje ku dubo marar lafiyar tasu" amsawa sukai da toh, suka bi su Anty dan duba masu jiki.
"Aysha wai ina kika samo waɗan nan mutanen ne? Anya ba kya ɓoye mana wani abu da ya kamata ace mun sani?" Cewar Abbu yana duban ta. Shiru babu amsa dan bata san amsar da zata basa ba.... "Dake nike magana fah Aysha! Ina kika San family Aliyu Bashir Sardauna?" Abbu ya kara wurga mata wata tambayar a karo na biyu. "Mi kake faɗa ne haka? Wani familyn Aliyu? Ba dai shahararren dan kasuwan nan bah?" Cewar Abba yana kallon Abbu da jiran karin haske. "Eh yaya familyn Aliyu Bashir Sardauna kenan" jin hakan yasa Abba samun waje ya zauna yana kallon Aysha Irin kallon tuhumar nan, rasa abin fade da yayi ne yasa ya tsuke bakin sa yayi shiru ba wai dan babu bane a'a sun yi masa nauyi.
Sai chan yace "Ni tsoro kike bani Aysha! Ni kar Muna zaune watara ki sayar da mu dan kam ke din nan abin a kiyaye ne! Ka barta wannan mai mugun zurfin cikin ba fadi zatai ba, Idan kuma ka matsa ta tara maka mutane a nan yauwa" "shikenan yaya yadda kace din haka za'ayi idan mun koma gida sai a yi a chan". Haka dai suka tsaida magana suna a haka saiga su Anty Ramlah sun dawo sai dai wannan karan basu zauna a waje ba suka koma ciki, da yake dakin yana da fadi sosai, ga shi kuma Maheer ne kawai ke ɗakin wanda har zuwa sannan bacci yake ta faman sha.
**********
Jikin Mommy yayi sauƙi sosai daman tsoro ne ya Shige ta. Dan har an basu sallama. Sai da suka gama kwasan komi nasu ne suka shiga dakin da Baffa yake da Maleeka da ke ta faman zunburo baki gaba. Sai dai jin kamshin tularen AY a ɗakin yasa ta natsu kamar wata na ALLAH ta shiga gaida modɗibo da yafendo d tambayar mai jiki. Banda ganin AY a wajen da baza ta gaisar da ko wasu mutane bah. Nan ta shiga satar kallon sa sai dai ganin fuskar nan tasa kadaran kadahan ya sa bata karasa gare sa bah. "Toh modɗibo ALLAH ya kara sauƙi bara mu lallaɓa mu koma gida sai in na dawo zuwa anjina" amsa masa modɗibo yayi, shi kuwa Daddy ya kama hannun Maleeka suka fice daga ɗakin. Intisar da fadeelah dake laɓe a wajen kuwa ganin tafiyar su Daddy ne yasa suka fito daga moɓuyar su suka nufi wajen Aysha.
"Modɗibo ya maganar binciken da ake yi ya kamata zuwa yanzu ace an gano bakin zaren amma shiru ba wani labari" cewar Anty. "Haka na so amma gashi nan shi ya dakatar da binciken wanda ban san dalilin sa nayin haka ba" modɗibo yayi maganar yana nuna AY dake ta fama da waya.
"Toh ALLAH yasa haka shi yafi alkhairi" "amin Ya ALLAH" suna cigaba da wata zancen jifa jifa yafendo tana saka masu baki. Suna a haka sai ga sallamar su Intisar bayansu kuma Aysha. "Ikon ALLAH yanzu Mommarh nah sai da kika taso bayan kin baro yaro babu lafiya?" Cikin sanyin murya ta amsa da "Anty Ramlah suna nan" Kafin ta zarce da gaishe su cikin karfin hali dan tunda ta shigo take Jin kaifaffun idanu a kanta daurewa kawai tayi, tayi abinda ya kawo ta. "Moon wace wannan ɗin kodai surukarki ce" a kusan tare AY da AY suka daga kai suna duban sa kafin kuma su ɗauke a tare AY yana maida nashi kan AY da ta shiga wasa da yatsun hannayen ta tana jin zuciyarta tana bugu. Motsa pink lips nasa yayi kaman wanda zai saki murmushi sai kuma ya gimtse kayar sa. Yana jiran jin amsar d Anty zata bada.
"A'a fah! Ita ce mahaifiyar yaron da muka shiga dubawa Kafin mu shigo nan" murmushin manya modɗibo y saki, Idan ya dubi AY ya maida duban sa ga Aysha. Wanda hakan yaso ɗaure wa su yafendo kai. Sai chan da sauran murmushi kan fuskar sa yace "ALLAH ya raya Muhammad Maheer" a 360 Aysha ta ɗago gaba ɗayan ta tana duban modɗibo da tunanin inda ya san full name nasa. Wata kaukauran yawu ta haɗiye tana maida kanta ƙasa. Shi Kuwa AY a Wannan karan kasa ɓoye murmushin sa yayi yana cigaba da satar kallon ta, shi kuwa modɗibo na Nazarin sa. "ALLAH ya ƙara sauki" Aysha ta faɗa tana miƙewa da niyyar tafiya. Ganin haka sai yafendo da Anty dasu fadeelah suka tashi danyi mata rakiya daga nan yafendo ta duba jikin Maheer. "Ku zo nan" Cewar AY sai dai idanunsa yana kan wayar sa, ƙululu cikin su ya shiga halin ƙugi jiki a sanyaye suka dawo su Anty moon Kuma suka fice, sai ɗakin ya koma daga modɗibo sai Baffa dake bacci har zuwa lokacin sai su fadeelah da ya dakatar.
Ba tare da ya dube su ba yace "kan ku yana mosti ko? Zan baku last warning kar ku ƙara fadawa mutum haka a jiki.... Live my site" jiki na rawa sosai suka fice daga ɗakin.
Modɗibo kam murmushin manya ya saki kafin ya ce "waye suka danne halan dan in anga kayi magana To tabbass abin yana da matuƙar muhimmanci" manyan idanun sa ya zuba kan modɗibo kafin ya ɗauke yana tashi ya bar dakin gaba ɗaya "gulmamme ai zaka magantu ne" modɗibo ya faɗa da dariyar dauke a fuskar sa.