HASASHEN SOYAYYA

HS 3

by @legendspen

HASASHEN SOY
_Imagination of love_


_Page 03_


~~~~~ Unguwar Nyan'ya 

"Kaga Abdulwahab ka tsaya muyi magana a nutse ta fahimta."

Bhatool dake zaune cikin ɗakinsh bayan tagama yi mai shara da mopping, hardasu turaren huta ta saka masa. 

Kallonta yayi yasan dole akwai abinda take buƙata kuma babbane tunda ta kai ga yi masa shara harda mopping sannan kayansa da'aka kawo daga wanki ta jera mai a cikin sif.

Mama na kallonta tana yi ta ce mata. "Fati mai kuma ake buƙata!."

"Haba Mama shikenan ni bazanyi abu dan Allah ba."

"To ai Fati ansan halinki ne?."

"Ni ba abinda nake buƙata kuma idan akwai abinda nake buƙata ai munfi kusa wajen ɗan-uwanah."

Shiru Mama ta yi, dan tasan dai dole akwai abinda take ɓukata hakan yasa yanzu dataji tanayiwa Abdul daɗin baki yasa tayi murmushi.

"Yaya kaci abincin kona daƙƙo maka ruwa ne?."

"A.a barshi kawai ki faɗi abinda zaki faɗa."

"Yaya kaga wallahi ina wannan ƙawartawa Suhaima?."

"Suhaima!." Ya maimaita sannan kuma ya ce: "Ni ban santa ba gaskiyya."

"Baka gane ta ba, wacce muke makaranta tare to bikinta za'ayi nan da sati biyu, wani mai kuɗine yazo zaiyi wuff da ita, shi ne ankon nata da kuɗin kwalliya da komai da komai zai kai dubu ɗari."

"Dubu ɗari Bhatool?."

"Eyh Yaya!, wai nace yama sunan buduruwarnan taka, ai ranan mun hadu da ita har ƙasa na tsugunna na gaisheta, tana da mutunci sosai gaskiya kayi dance."

Dariya ce ta kwace masa amma ya riƙeta.

"Bhatool yaushe kika bani atamfofi na siyomiki, kikace bikin ƙawayenki za'ayi."

Marairaice fuska tayi sannan ta ce: "Yaya kasanni da farin jini."

Haɗe rai yayi sannan ya ce: "Farin jinin nake ne yasa har yanzu baki da tsayayyen saurayin dazai aureki."

"Haba wannan ai gori ne, kuma Allah bai manta dani ba, wallahi natashi kawo mijina duk sai kunyi mamaki, ni yanzu kabani kuɗinnan na wuce." Ta ƙarashe maganar cikin asalin yanayinta da take mai magana dashi na isa da izzah.

"Bazasu samu ba."

Miƙewa tsaye tayi sannan ta ce: "Wallahi sai kabiyani sharar da mopping ɗin danayi maka."

"Aibani nasaki ba."

Tsaki taja sannan ta fice zuwa dakinta, mayafi ta ɗauka da jaka ta fice. 

Mama tana faɗin: "Ina za ki?."

"Police station."

"Bhatool wallahi karki fita."

Dawowa tayi ta ajiye jakar da mayafin nata takwanta akan gado.


~~~~~Washe gari

Tun 7:30 tagama shirinta, fitowa tayi Mama da Abdulwahab na falon tahucesu tana shirin ficewa.

"Ina za ki?."

"Makaranta."

Ta faɗa a dakile.

"Bazaki karya ba."

Mama ta tambayeta, shikuma Abdulwahab ya ce:

"Kuɗin makarantar fa."

"Naƙoshi. Zanje a ƙafa."

Duka tabasu amsa a haɗa tare da ficewa, bakin titi ta nufa tasami napep tahau, bama makarantar ta nufa ba Gidan Yaya Karima ta nufa dake unguwar. Red bricks.

Itama gidan nata babbane amma bai kai ko rabin nasu Senate ba, amma suna thesame line ne, su Yaya karima sune gida na biyu, a ɓarin hannun hago, sukuma su Senate suna gida na biyar a ɓarin hannun dama.

Yana zaune man kujera a parking space yaji zuciyarshi tafara bugu da sauri da sauri, bugun yana ƙaruwa akai-akai, runtse idonsa yayi saikuma yaji kamar Abinda yakeso na tunkaro dashi.

Da sauri ya sauka daga kan kujerar ya nufi gate, hannu yasa ya buɗe ƙaramar ƙofar jikin gate ɗin ya fito. 

Dai-dai lokacin da ita kuma ta tsaya ƙofar gate ɗin gidan Yaya Karima.

Kallonta yake kamar wata sabuwar hallita yanajin bugun zuciyarshi yana daidaita sannan shi kanshi yanajin shi very full, kamar yagama cika cikakken mutum.

Ƙofar gate ɗin aka buɗe mata tashige ba tare da tasan da tsayuwarshi a wajen ba.

Kasa komawa ciki yayi yasamu waje ya tsaya yanabin ƙofar data shiga da kallo, itakam tana shiga cikin gidan main falo ɗinta tafara faɗin.

"Anty! Anty!!."

Yaya karima dake cikin ɗaki ta fito tana faɗin.

"Inna'illahi lafiya?."

Tsayawa tayi turus ganin Bhatool, ita kam Bhatool naganinta ta kwanta a ƙasa tare da fara birgema tana faɗin.

"Anty Abba yace karku barni nayi kukan maraici, karku barni nayi kukan rashinshi. Amma kun rantse sai nayi."

Barrister Bashir ne yafito yana faɗin.

"Autar Abba, me ya faru kuma me akayi miki?."

Kukan ta cigaba tana faɗin.

"Sunkasa riƙe amanar da akabasu, sunkasa cika alƙawarin da suka ɗauka."

Kallon Karima yayi yana tambayarta me sukayi mata, girgiza mai kai tai alamun bata sani ba.

"Kiyi haƙuri kidaina kukan-nan haka, kar yaranki sufito suganki haka."

Tashi tayi tare da fara goge hawayen nata.

"Yawwa, yanzu faɗamana abinda ya faru?."

Goge hawayen tafarayi sannan tace:

"Kafin Abba yarasu saida yabasu amanata ita da yaron can, sannan yace nayimusu biyayya sabida haka nayarda nabarmasa girman, amma su sunkasa riƙe amanar sunbarni sai garari da shan wahala nake:

Kallonta sukayi baki ɗaya, Yaya Karima kuwa ta ƙufula hae wuya jitake kamar takamata tafara dukanta har sai taga banta numfashi.

"Me kuma sukayi miki?."

"Yaron canne nace yabani kuɗi nayi ankon bikin Suhaima amma yaƙi."

"Ubanki ke da Suhaiman."

Yaya Karima ta faɗa a fusace sannan taɗora da ce wa:

"Ke rayuwarki baki da aiki sai anko da biki, a haka rayuwarki zata ƙare, Bhatool kinayiwa kanki faɗa?."

"Kiyi shiru Karima, ai lokaci ne idan tayi aure bayi zata yi ba."

"To yanzu waye zai aureta a haka, tasawa ranta masifar girman kai, bata kulakowa sai yawon biki biki, duk kayanta anko ne baki ɗaya."

"Kiyi shiru dai na faɗa miki."

Barrister Bashir ya faɗa, yana maida hankalinsa kan Bhatool.

"Ki daina kuka Bhatool ai hardani Abba yabawa amanarki, dan haka idansu sunƙi riƙe amanar ni kizo zanriƙe, nawane kuɗin ankon?."

Goge hawayenta tayi sannan ta ce:

"Shi ankon 65 thousand saikuma kuɗin ɗinki da make-up."

"Bhatool wallahi sainaci ubanki, kuma karki ƙara zuwarmun gida."

Yaya Karima ta faɗa a fusace tare da tashi tabarmusu wajen, tasan kome zata faɗa Bashir sai yabata kuɗin nan.

"Shikenan bari nakawo miki zaikijeki siye ankon, Allah yasanya Alheri."




~~~~~

"Meyasa zaka bawa yarinyarnan kuɗin-nan, kullum ita bazatayi hankali ba? Yar waye ita da zata dinga yin irin waƴanan anko ɗin?."

"ita ɗin ƙanwar matar barrister Bashir ce, ko laifine idan tayi?."

"Bazaka gane ba, tunda Abdulwahab ya hanta kuɗinan yakamata kaima ka hanata, last zuwan danayi gida atamfofi guda biyar yakawo mata, waita bashi ƙyallen kuma duka na ankon bikin ƙawayenta ne, sannan yanzu tazo tana maganar bikin wata Suhaima, yarinyar da anan Makarantar da suke suka haɗo."

"Inaso kigane komai lokaci ne, yanzu nanda wani ɗan lokaci bazatayi ba."

Shiru Yaya Karima tayi amma itadai tagaji da wanan halin na Bhatool, zama yayi kusa da ita tare da dafamata kafaɗa.

"Kiyi haƙuri kuma ku cigaba dayimata addu'a."

"Shikenan Allah ubangiji ya shiryata."

"Amin ya Allah, sannan dan Allah banaso kinuna mata ɓancin rai kinji.", Ya ƙarashe maganar kamar mai naiman alfarma.

Tashi ta yi tadawo falon tasame Bhatool data zauna ɗai-ɗai tana faman danna waya.

"Bazaki makarantar bane?.", ɗagowa tayi ta kalleta sannan ta ce.

"Hutawa zanyi yau nagaji da wahalal makarantar nan."

"Bhatool muyi magana dake mana, idan kinada time?."

"To Yaya inajinki." Ta faɗa tana kashe wayar alamun tabata hankalinta baki ɗaya.

"Bhatool kinsanfa kin girma, sannan ƴan-uwan Baba sunsa ido akanki, meneyasa bazaki nutsu kifitar da miji ba kiyi aure."

Kallonta Bhatool tayi sosai cikin yanayin nutsuwa sannan tace: "Yaya wai idan mijinan baizo ba, ni zanjanyo shi ne?."

Kallonta Yaya Karima tayi ido cikin ido sannan ta ce: "Kinaso kicemun duk cikin samarinki babu wanda kikeso?."

"Gaskiya ni bakowann irin namiji zan aura ba."

"Wane iri kikeso?."

Gyara zama Bhatool ta yi kamar wacce zatayi karatu ko dogon jawabi sannan ta ce: "Yaya inason namiji wanda zai bani ƴancina, wanda zaibani soyayya, yabani damar da zanyi duk wani abu da name buƙata."

Dariya Yaya Karima ta yi sannan ta ce: "Bhatool kina *Hasashen soyayya* a rayuwarki, kina tunanin akwai sakaran mijin da zai ɗauki duk wani shirmenki ne?."

"Kamar ya ina *Hasashen soyayya*, *Yaya nasan Mace bata canja Namiji, yana canjawa ne sabida yana sonta* to nima zannemi maisona wanda zai canja."

"To Allah yabaki sa'a akan wanan Hasashen soyayyar

Ku yi following ɗina, ku dinga yi min comment shine ƙwarin zai ƙaramin ƙwarin gwiwa.