GUMBAR DUTSE

G_D - 23

by @khadeejacandy

◦•●◉✿ GUMBAR DUTSE ✿◉●•◦

𝗕𝗬 𝗞𝗛𝗔𝗗𝗘𝗘𝗝𝗔 𝗖𝗔𝗡𝗗𝗬 ✍️

Turaren wuta kike nema? Ko kuma na jiki? Humra kike nufi ko kambasa spray? Ke na tuna turaren set kike so? Ko kuma dai ke zaki zaba da kanki? Au oil perfume wai? Ke ni kamshin turaren ya rikita ni, bana fahimta wane kuke so daga ciki, iyakar abun da zan iya shaida shi ne, kamshi mai kwantar da zuciya da sanyaya ruhi, ya kwantar da hankali. Ya Salam🤦🏻‍♀️kina son kamshi baki nemi yar fillo Collections ba? To me kika yi? 😳 Haba ai da sauranki shiyasa na ji dan tsami tsami🫢

Tana da turaruka kala kala, iri iri, masu kamshi da tashin kai, ga sauki ga mutuntuka, karku bari wannan damar ta wuce ku, chat her ***

𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 2️⃣4️⃣

Yana isa bangarensu kira ya shigo wayarsa, sai da ya duba sannan ya amsa ya kara wayar a kunnennsa yana kokari shiga falon.

"Eh har na karya"

"Okay, tohm zuwa yamma kamar 4 haka ko 5 zai maka akwai wata da zaka je gidansu ku gaisa, amman wane time zai fi maka? Na fi son ka tafi da rana saboda ka ganta da kyau ta ganka"

"4 after na yi sallah la'asar zan tafi"

"Tohm, Allah ya kai mu zan maka text din address dinta, idan ka je sai na kirata"

"Okay"

Ya amsa tare da sauke wayar.

"Ka ga yarinyar ta gyara ko'ina amman taki yarda ta hau sama ta gyara dakunan balle naka, na yi na yi da ita ta ki"

Gwaggo ta fada, Jawad ya kalleta kamar yadda take zaune tana kallonsa, da kai yayi mata alama da ta hau stairs din, sai ta lake kafada ta girgiza masa kai alamar ba zata hau.

"Ko tsoron hawa kike?"

Gwaggo ta tambaya take ta daga kai da sauri.

"Ai dole ki koya idan ba haka ba, ba zaki iya share dakunan ba"

Jawad ya fara taka stairs din few steps ya juyo.

"Ki cire wannan tufafi ki saka wasu"

Ya fada ne saboda dazun ya ga lokacin da take shafe ruwan hannunta a jiki kayanta da ta fito kitchen din Hajja Yelwa. Ta ware hannayenta ta masa alamar babu, sai ya tuna be zo da ita da komai a gidan, juyawa yayi ya cigaba ya tafiyar ya shiga dakinsa.

"Ni saboda ciwon kafafuwa ne bana hawa amman ba tsoro ba ne, ko yanzu sai idan bata kama ba, ki gwada hawan kadan ki gani"

Batula ta yi kasa da kanta fuskar kamar zata yi kuka, bata taba hawa gidan sama ba, ko ganinsa ba bata taba yi ba sai a nan, idan ta kalla ma jiri dibanta yake ina ga idan ta hau, ta bata rai sosai alamar bata son hawan.

"Ke"

Ta dago ta kalli stairs din.

"karbi"

Ya fada yana saukowa stairs din rike da abun da bata san miye ba sai da ya karaso. Ta mike tsaye ta isa gabansa ta daga kai tana kallonsa domin iyakar tsayinta kafadarsa idan zata kalleshi sai ta daga kai.

"Ki shiga dakin ki yi wanka"

Ta san sauran labarin, dan haka ta karba da hannu biyu ta warware black T-shirt din sai talkami suka fado, da alama rigar ya saka ya nade sabin talkamin da suke cikin leda, manya ne sosai na maza masu tsada irin talkamin da ake sakawa a cikin gida ayi yawo da su.

Ta rike rigar ta mayar masa da talkamin tana girgiza masa kai. Baya son dagon zance if not da zai iya fada mata cewar wasu talkamin zai mata.

"Ai da kin karba kin saka a haka, gaba ba sai a siya miki na girmanki ba"

Batula ta juya ta kalli Gwaggo dake maganar a zatonta Batula bata son saka talkamin ne saboda talkamin maza ne kuma sun mata girma. Ta daga kafarta ta girgiza hannunta ta sauke, babu abin rubutu balle ta fada musu abun da take son fada. Jawad be amsa ba ya juya koma dakinsa ya barta da su rike a hannu.

"Kawo nan, ai ba zai karba ba, kin yi arziki ma da ya dauko miki ya kawo"

Ta karasa ta mikawa Gwaggo.

"Da kin daure a haka kin saka, ni ma tun jiya na lura kamar baki zo da talkami ba, haka kike ta yawo, tufafi ma baki zo da shi ba ko?"

Ta daga kai, Gwaggo ta ce

"Kin ga inda kika alwala din nan, akwai gurin wanka da sabulu da soso ai kin gani ko?"

Ta daga kai.

"Toh nan zaki yi wa kanki, idan kika fita falon nan kika zagaya ta nan baya zaki ga Fanfo akwai bokiti a gurin ma sai ki wanke wannan kayan da kika cire, nan dakin dake kusa da kitchen din idan kika shiga zaki ga man wanke tufafi akan enginin wanke kaya, sai ki dauko ki wanke kayanki, ba lallai kin iya amfani da engine din ba ai da sai ki wanke kayan, ni kaina sati sati ake zuwa a dauki kayana a wanke"

Batula ta kalli kofar dake kusa da kofar Kitchen ta maida idonta kan tv, Gwaggo ta yi awa daya zaune a gurin sannan ta tashi

"Zan shiga ciki na yi bachi, na fara jin bachi idan kika lokacin Sallah yayi ki tashe ni kin ji ko"

Batula ta daga kai, tana kallon Gwaggo dake tafiyar tsofa har ta shige dakinta, minti daya Batula kara zaune ba ta zabura ta nufi dakin da Gwaggo ta fada mata ta kama karfen kofar ta murda ta tura, sai da ta fara lekawa sannan ta shiga, ta kalle ko'ina na ma'ajiyar sannan ta dauki man wankin da Gwaggo ta fada mata, ta shinshina ta bude ta zuba a hannunta ta murza ta ga yayi kumfa sannan ta fito ta janyo kofar ta rufe.

Rigar da Jawad ya bata ta dauka ta fice daga falon tana ta sauri kar a ganta, ta bi bayanin Gwaggo ta zagaya ta dayan side din sai gata a garden dake cike da itatuwa kala kala, hankalinta yana gurin abun da ya kawo ta, dan haka ta karasa ta sauri gurin fanfan ta dauki bokiti ta bude ruwa ta zuba ta jefa rigar ta zuba sabulun ta fara wankewa, jin take kamar ba zata iya saka kayan maza ba domin abu ne da bata taba ba, balle kuma shi da bata sani ba, hankalinta be kwanta da ta saka rigarba har sai ta wanke, shi ma sakawan dan babu yadda zata yi ne, if not ba zata saka ba.

JAWAD POV.

Zaune yake kan wata kyakkyawar kujera dake kusa da jikin Window dakinsa, hannunsa rike da wayarsa. Jin ruwa na zuba ya saka shi juyawa a kalli ya kall Garden din dake kasa gefen windows din da suke duka dakunan gidan suna facing dinsa.

Batula ya hango gaba fanfo, ya dauke kai ya cigaba da taba wayarsa, kamar ance dago ka gani, ya sake juyowa ya kalli gurin rigar da ya bata ya hango ta daga tana shinshina daidai inda hammatansa yake tana sake maidawa a ruwan ta wanke, ya tattara girarsa yana kallonta da mamaki, faduwa rigar ta yi ko kuma kyamarsa take? Ya kai hancinsa ya shinshina hammatansa na dama da hagu babu abun da ke fita sai kamshi, kuma ma ai rigar daya bata a cikin wankakun tufafinsa take ba wai wanda ya saka ba ce, ya kai tsaye yana kallon, ya dan tabe baki, shi ma ai ba son bata rigar yake ba, kawai saboda baya son tsayawa tambayar kanensa ne abun da zai ya fi karfinsa, and be son kananan maganganu, lura da abun da ya faru jiya, gashi kuma baya son ya sauko ya sake ganinta da wannan tufafi da take sanye da su tun jiya ne.

Key dinsa ya dauka ya zira wayarsa aljihu ya dauki turare ya kara fesawa a jikinsa sannan ya fice. Tun da ya shiga motarsa ya dauki hanya be tsaya ko'ina ba sai gidansu Momy wato Hajiya Binta aminiyar mahaifiyarsa kuma mahaifiyar abokinsa Ariz. A harabar gidan yayi farkin ya fito ya shiga ciki gidan.

"Maraba Maraba da ɗa abun alfahari, lale marhabun"

Yayi murmushi ya zauna kan shinfidar carpet din da take zaune a balcony.

"Momy ya gidan?"

"Gida lafiya kalau Jawad ya naku gidan"

"Lafiya kalau"

Ya amsa.

"Momy Ariz fa"

"Ariz be shigo gidan ba yau, tun jiya da ya leko mu da rana be dawo ba, kasan shi ya girmi gida, kiri kiri a tare a gidansa kamar wani mai aure"

Murmushi yayi ya ciro wayarsa aljihu yana lasawa.

"Kai ba mata shi ma ba mata kun taru kun zama, ko da yake kai ka kusa barinsa tun da an samo maka mata"

Ya kalleta amman be ce komai ba.

"Akwai wata yarinya yar gidan Alhaji Sule wammako ita ake son ka je ka gani ko Allah zai saka a dace, kamin ma a yi mata magana sai da Sa'adatu ta kira ta fada min mun yi bincike a a kanta mu dai ba mu ga wata matsala ba, kuma yarinyar tana da mutunci da tarbiya sosai"

Be yi mamakin jin haka daga Momy ba, domin ya san Adda Sa'adatu bata aiwatar da komai sai ta nemi shawarar Momy ko kuma ta sanar da ita, a cikin mutanen da suka dauka iyaye Adda Sa'adatu bata aikata abu ba da izinin Momy ba

"Ita ce zan je na gani anjima?"

"Eh ita ce, yarinya ce mai kyau, ta yi karatu bana ta gama masters"

Ya kara wayar a kunne.

"Ariz ina kake? Na zo gida baka nan"

"Daman idan zaka nemi ai na gidanmu zaka je ba, gidana zaka zo ko kuma ka kira ka ji inda nake"

"Toh yanzu me nake yi?"

"Waya san maka, ni dai yanxu ina asibiti wani abun ne?"

"Na so duba ginin nan ne, kuma ina son magana kai"

"Zamu iya maganar a waya?"

"I will text you"

Ya kashe kiran. Kadan suna taba hira da Momy yana dan amsa mata dan dole kamin yayi mata sallama ya mike tsaye.

"Tohm a gaida gida, ka dai kula ina yawan fada maka ka rike addu'a da kyau"

Ya daga kai.

"Kuma idan zaka je gurin yarinyar karka tafi hannu sake, ka yi yar siya ka je mata da ita, na san can inda ka fito flower ku ke fadawa toh nan kam akwai banbanci, kar kuma ka tafi da Ariz, kai kadai ya wadatar ka ganta ku gaisa"

Yayi murmushi.

"Na gode, a wuni lafiya Momy"

"Tohm Allah ya maka albarka ya baka mata ta gari, ya tsareka ya hada kanku kai da yar'uwarka"

A ransa ya amsa da Ameen ya nufi motarsa ya bude zai shiga ta kira shi.

"Jawad, jira bari na saka a dauko maka ruwan zamzam"

Ya saki murfin motar ya dawo inda take zaune, jikarta ta kwallawa kira ta zo da gudu.

"Ya Jawad ina wuni"

Ya daga mata, daman gidan ba bakonsa ba ne, mutanen gidan sun san halinsa, be zama lallai idan aka gaishe shi ya amsa da baki ba sai da kai.

"Dauko ruwan zamzam din nan da yake ɗaki, babbar jakar zaki dauko"

"Tohm"

Ta tashi, babu jimawa ta dawo rike da katon kwalin mai dauke da 5L

"Je ki saka masa a mota"

Yarinyar ta dauki kwalin daker ta nufi motarsa.

"Kullum da safe ka karya da shi, tun daga Saudi na saka aka siyo min su Alhaji Junaidu da zai dawo domin kai kadai kawai, suna magani da yawo ka rika sha idan ya kare ka fada min, kuma dan Allah ka sha kasan ana zagaye da makiya ta ko'ina, wasu ma a boye suke"

"Na gode Sosai Momy, zan sha"

"Tohm Allah ya maka albarka"

"Ameen"

Ya amsa wannan karon. Sannan ya koma motarsa yaja ya fice gidan, Hajiya Binta na daga cikin mutanen da Jawad yake so kuma yake son ziyarta, wannan tafiyar ma bata Ariz din ba ne shi kadai har da Momy domin ya kwana biyu saka ta a ido ba. Gashi ta fada masa abun da yake son ya tambayi Ariz wato da me zai je idan zai tafi gidansu yarinyar. Super market ya shiga ya siyo abubuwan da ya san za su dacewa as gift, sannan ya dawo gida. A mota ya bar kayan ya shiga cikin gida.

A bangarensu yayi parking amman be shiga ba sai da ya kira daya daga cikin kanensa ta zo.

"Shiga ki gyara min dakina"

"Tohm Yaya"

Ta amsa da mamaki, a ganinta ai an kawo mai aiki me zai saka su aiki a bangaren yanzu, sai dai bata isa ta musa ko ta tambaya ba, dan haka ta shiga ta dauki mapper da abun shara ta shiga ta gyara dakin saf ta saka turaren wuta na yar fullo collection. Falo ya kishingida yana latsa wayarsa har ta gama ta fito, sai kuma yayi mata umarni data dauko masa ruwan zamzam a mota, ta fita da dauko ta kai masa dakinsa sannan ya mike tsaye ya nufi stairs.

Be bar gidan ba, ba sai 30:30 bayan Hajja Yelwa ta cika masa cikinsa, a hanya yayi sallah la'asar sannan ya kama hanyar gidansu yarinyar da Adda ta turo masa adireshin gidansu ta wayarsa.

BATULA POV.

"Ki hau har can"

Batula wacce ko rabin stairs din bata yi ba ta juyo ta sauka jikinta na rawa idonta cike da kwalla tana rike da karfen stairs ta sauko a hankali zuciyarta na buga da karfi.

"Kin ga ko, da kin daure zaki iya hawa, idan baki sake jiki ba, yaushe zaki iya gyara can din"

Ta sauke kanta kasa cike da damuwa, abubuwa da yawa da bata san su ba, bata iya amfani da su ba, ta zo ta tarar da su a nan rayuwar karkara da birni ba daya ba, birnin ma irin masu rufin asiri.

"Amman kin iya girki ko?"

Batula ta daga kai, ta iya irin na su na kauye domin ita take girkawa lokacin da suke gidan Malam Salisu Na-Malam.

"Da sauki, wani lokacin sai ki rika girka mana ai, shi ne amfanin mai taya aikin gida, shi ma hawan da sannu zaki iya, zauna ki yi kallonki, idan karfe 2 ta yi ki tafi can bangaren ki karbo abinci"

Batula ta zauna tana rike da gefen dankwalinta, ranta a jagule irin na wanda be shirya karbar da sabon rayuwar da dake fuskanshi ba, Gwaggo kuma ta juya ta nufi hanyar dakinta. Duk iri son kallon Batula bata manta da agogo ba, tana ganin karfe biyu ta yi sai ta tashi fice zuwa bangaren Hajja Yelwa. Kofar falon a bude take dan haka bata wahala ba gurin shiga ciki, sai dai yadda zata janyo hankalin mutanen falon zuwa abin da ya kawo ta ne aiki a gurinta, ba dan kuma ba su ganta ba sai dan babu wanda yace mata uffan sai kallonta suke.

"Ke waya baki rigar nan?"

Husaina ta tambaya tana cire safar makarantarsu. Batula ta juya ta nuna kofa, bi ma'ana Jawad. Husaina ta bude baki ba dan logon kamfanin da Jawad yake aiki da su dake leke a jiki ba, da ba zata yarda rigar yayarta ba ce.

"Amman dai be ganki ba kika dauka ko?"

Ta girgiza kai.

"Ya sani?"

Wannan karon Hajiya ce ta tambaya da kanta tana maida kofar dakin dake kasa ta rufe, Batula ta daga mata kai, sai ta tsaya tana kallon tufafin dake jikin Batula, zane ne na Atamfar roba, da dankwalinsa iri daya sai rigar da ke jikinta wanda ta kasance T shirt black color da farin logo. Hajja Yelwa ta tsaya tana kallonta da mamaki sannan ta sauke ajiyar zuciya.

"Me kika nema?"

Batula ta mata alamar abinci.

"Ok, bari Husaina ta kai muku abinci ke bari na aike ki ki siyo min kati kin ji?"

Ta daga kai cikin rashin gamsuwa, ai bata gama fahimtar gidan ba ma balle wata waje. Sai da ta saka Husaina ta dauki abincin ta nufi bangarensu Jawad, sannan ta haura sama, Batula dai tana tsaye a falon jiran Hajja Yelwa, madadin ita sai Hannatu ta sauko rike da 1k sabuwa, da farin veil, kudin ta fara bawa Batula.

“Ungo, ki fita gida gaba daya, ki fita gate sai ki yi dama, ki yi ta tafi, zaki ga shago ki siyo min kati, karki dawo sai kin gane gurin kin siyo min kinji"

Ta daga kai, ta karba ta juya.

"Karki tafi bangarenku ki tafi a haka yanzu yanzu ki dawo"

Ta amsa da kai, sai ta mika mata wani karamin mayafi da yake hannunta, tafiya da karamin mayafi ba wani sabon abu ba ne a gurinta domin tana fita haka a kauyensu, ta inda kawai zai zame mata sabon abu saboda a nan ita bakuwa ce, dan haka ta da fita harabar gidan sai ta kwance dankwalin kanta ta yafa ya sauko mata, sannan ta kara da gyalen ta nufi kofa a yanayin dake nuna damuwa karara a fuskarta, mai gadin gidan be ce mata komai ba yana kallonta har ta fice.

Ta yi minti biyar da barin Batula dakin Hajja Yelwa ta fito.

"Allah yasa kar ya hadu da ita ya hana ko ya dawo da ita, na ga fitarsa dai ban ko tafiyar mai jimawa ce ko aa ba"

"Ameen"

Suka amsa.

"Wato wani makirci ne aka kulla tsakaninsu, shiyasa aka kawota a gidan ta zo saka mana ido, ta dauki rahoto, shi ne jar da daukar rigarsa ya bata ta saka, amman ku be taba dauka ya bakiku ba, yan'ubancin yake nunawa kiri kiri, baki batun da shi ba kullum yake zs

ma ba, amman ita zata iya daukar rahoton komai ta fada, Allah kadai ya sani ko kurmarce a gaske ko karya"

Ta kashe ido tana jin ranta yana baci sosai.

'idan kun san wata baku san wata ba, dan kauye ai ba zai fi ɗan birni wayo ba, balle wacce da ace Allah ya bani haihuwa da wuri da yanzu na yi jika da ita, amman mu zuba zuwa...'

Ta fada a ranta tana bin kofar falon.