G_D - 25
◦•●◉✿ GUMBAR DUTSE ✿◉●•◦
𝗕𝗬 𝗞𝗛𝗔𝗗𝗘𝗘𝗝𝗔 𝗖𝗔𝗡𝗗𝗬 ✍️
Turaren wuta kike nema? Ko kuma na jiki? Humra kike nufi ko kambasa spray? Ke na tuna turaren set kike so? Ko kuma dai ke zaki zaba da kanki? Au oil perfume wai? Ke ni kamshin turaren ya rikita ni, bana fahimta wane kuke so daga ciki, iyakar abun da zan iya shaida shi ne, kamshi mai kwantar da zuciya da sanyaya ruhi, ya kwantar da hankali. Ya Salam🤦🏻♀️kina son kamshi baki nemi yar fillo Collections ba? To me kika yi? 😳 Haba ai da sauranki shiyasa na ji dan tsami tsami🫢
Tana da turaruka kala kala, iri iri, masu kamshi da tashin kai, ga sauki ga mutuntuka, karku bari wannan damar ta wuce ku, chat her ***
𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 2️⃣5️⃣
Hajja Yelwa ta sake kallon yaranta.
"Idan aka samu wata matsala, ko kuma ya dawo bata dawo ba, ko ya dawo da ita kar wanda yayi magana, ni zan amsa masa"
Ta juya kenan suka ji parking din mota a harabar gidan, Hajja Yelwa ta juyo da sauri, Firdausi dake kusa da windows ta daga curtains din ta laka waje.
"Ariz ne, shi kadai"
Hajja Yelwa ta sauke numfashi, hankalinta zai fi tashi ne idan Jawad ne, amman Ariz ba shi da zafin rai da rashin yarda kamar abokinsa.
Ya shigo da sallama, Hajja Yelwa ta amsa masa baki har kunne.
"Oyoyo yaushe rabon ɗana da gidan nan"
"Wlh Hajiya kwana biyu aiki ya min yau, yau ina samun free time na gudo gida"
"Aiko dai ka kyauta lalle lalle marhabun, kuma ka zo a daidai yanzu nan aka sauke girki, ga dinning nan sai abun da ka bar mana"
Ya tsaya dan daman dinning din ya nufa kai tsaye
"Shikenan ni an maida ni acici"
Duk suka saka dariya, Firdausi ta fara gaisheshi sannan sauran ma, ya amsa yana murmushi.
"Ina Ayla"
"Ayla ai aba zama take ba kasan, yau suna can gobe suna nan"
Ya karasa dinning din ya zauna.
"Bari na shiga kamin ka gama cin abincin"
"Okay Hajiya"
Ta juya sai kuma ta juyo.
"Na manta cake na nan a fridge idan zaka ci sai ka dumama ko ka saka su dumana maka"
"Kayan Zafi sai Jawad, ni dai bar ni da abinci, na ci na ji cikina yayi nauyi"
Hajja Yelwa ta yi dariya sannan ta haura sama, Ariz kuma ta bude abincin ya fara zubawa kansa. Sallah ta yi ta sake saukowa, wannan karon ta tarar da Ariz zaune a daya daga cikin set din kujeru falon, Firdausi na zaune kusa da shi tana cin chips, kamin Hajiya ta karaso ta zauna ta watsa mata harara, irin na yaron da yayi ba daidai ba, Firdausi ta matsa gefe ta rage dariyar da take.
"Har ka gama cin abincin?"
"Tun dazun, su Hannatu da hassana sun fita wai za su siyo wani abun basa son doya da miyan da kika yi"
Hajja Yelwa ta tabe baki tana murmushi.
"Iskanci kala kala yaran nan suke min a gida, suna da kudin kashewa shiyasa"
Ta zauna, sai ta dauko masa wata hirar ya rika mata da yake Ariz gwanin son zancen ne, a cikin hirar ta fi karkata kan Jawad tana dan tambayarsa wasu abubuwan da bata sani ba, game da shi saboda ta san Jawad be da abokin sirri sai Ariz, Ariz din ya kan amsa mata wanda yake ganin normal ne babu laifi ta sani wanda kuma ya san sirri ne mai karfi a tsakaninsu sai ya shashanntar da tambayar, sun kusa awa biyu suna hira ita da shi, can ba a rasa ba ne Firdausi ke jefo bakinta, domin duk abun da ya shafi yayan na su Jawad ba son shiga suke ba, saboda halinsa ba ita kadai na har sauran yan'uwanta haka suke, shi ba a yi masa abun da gwaninta ko burgewa, kuma zaka iya shiga a lamarinsa ka yi tsumu tsumu ya kunyata ka.
Wayar Ariz din ce da ta yi ringing ya katse amsar da yake bawa Hajja na filin siyar da motocin da Jawad zai bude ba da jimawa ba.
"Hello Adda"
"Albishinka"
Adda Sa'adatu ta amsa daga dayan bangaren cikin yanayin da ke nuna tana cikin farinciki.
"Goro fari kal"
"Jawad ya samu mata"
"Samun mata ai ba shi ba ne abun murna sai ya amince, na san halin kayana"
"Ai mantawa na yi ban fada maka ba, ranar Hakim ya kone ya zo gidan nan, har yake ce mim shi be son mace marar class yafi son wanda zata ce sai dai shi ya zo gidansu ba wai ta zo gidana su gaisa ba, tohm wata ce fa na samo masa mai ji da kanta kamar shi, daman yau muka yi da shi zai je ya ganta kuma ya je, yanzu nan ya bugo min waya yace ta amsa"
Ariz ya kyalkyale da dariya.
"Shegen yaro, wato Jawad ko a cikin yan iska yana sahun gaba, kai da aka kawo ma mata har gidan yayarka ku fahimci juna ka ce wai baka so sai wanda zaka je da kanka"
Adda ta yi dariya.
"Kasan halin Kanen nawa duk inda mutum ya biyo, shi sai ya karya yace ba haka yake so ba, yanzu da ni nake tura shi gurin yan mata kuma cewa zai yi sai dai su zo gidana"
"Jawad ai murdaden mutum ne, mai wuyar sha'ani ga kafiya, amman dai Alhamdulillah tun da an samu abun da aka so"
"Eh Alhamdulillah kam, yanzu sai mu bar su su fahimci juna, idan tafiyar ta yi sai iyaye su shiga ciki"
"Tohm Allah ya tabbatar da alheri"
"Ameen, bari na kira Momy ban fada mata ba daman ta gurinta muka samu yarinyar"
"Okay tohm"
Ya sauke wayar yana murmushi, Hajja Yelwa ma da murmushin take ta ce.
"Albishir ne akai maka ko?"
A ganinsa zancen Jawad ya samu wanda yake so ba wani abu ba ne kuma daman dole kowa zai sani, dan haka ya fadawa Hajja Yelwa.
"Eh Adda ce, da Momyna sun samo masa mata kuma yace ta masa, da can fa ita Adda gidanta take kawo yarinyar su gaida, tohm shekaranjiya da Hakim ya kone, yaje gidan yake fada mata shi be son haka, to yanxu dai yaje ya ga yarinyar a gidansu kuma yace ta masa"
Hajja Yelwa ta dora yatsanta a hanci ta rangada guda, zuciyarta kuma na tafarfasa kamar zata kone tsabar bakinciki, amman ta kasa nuna hakan yadda take gudar sai ka rantse ta fi kowa farinciki.
"Alhamdulillah Allah, Alhamdulillah Allah na gode maka, kai amman Daughter ta kyauta kai wannan abun dole na yi sadaka, kai My Son ya samu mata? Kaiiii Alhamdulillah, ah ni zan yi ma Daddynmu wannan albishir din, Allah ya tabbatar da alheri"
Ariz yayi murmushi ya mike tsaye.
"Bari ni ma na tafi na yi ma Gwaggo albishir, daman ban shiga can bangaren ba na zo da yunwa na ce bari na fara cika cikina"
"Ah ahh lallai tafi kam wannan ai abun murna ne, ashe ita kuma daughter yaronta konewa yayi, Subhanallahi ban sani ba, bata fada min, shi kuma ɗan nawa kasan ba son magana yake ba"
"Eh wallahi amman dai da sauki"
Ya kalli Firdausi.
"Sis"
"Bye"
Ta daga amsa hannu sannan ya fice. Yana fita fuskar Hajja Yelwa ta sauya daga murmushi da far'a zuwa bakinciki da bacin rai.
"Wato can aka zagaya ita da aminiyar uwarta aka sama masa mata, saboda ni gani banza a gida, ni da ɗan mijina wata kawar uwa ta fini iko da shi"
"To wai ita Adda kishi take da ke ko me?"
Firdausi ta tambaya.
"Shi ne mana, idan ba shi ba ni ban isa na samo masa mata ba? Duk wani abun da ya shafi Jawad wannan bakar Sa'adatu sai ta shiga ta yi kankanba ta nuna shi ne dan'uwanta, amman idan ya shafi nawa yaran babu ruwanta bata shiga, yanzu kin ji ɗanta ya kone bata fada min, albishir ma sai Ariz aka kira aka yi ma saboda ya fini a gurinta, ina nan ina yakin yadda za'ayi na samu masa mata ta bangaren ashe sun haka kai da wacan makirar Hajiya Binta an samo masa wata, uwarta ta yi kishi da ni ta mutu, an bar kakar dan ta hana ni jindadin zaman gidan nan hakan be musu ba, yanzu kuma ita da kanta take kishi da ni"
"Ai wallahi duk laifin Daddy ne da ya hana wacan bakar tsohuwar komawa kauye, wanda kike zaune dan ita ta mutu to zaman ne zaki yi?"
Hajja Yelwa ta kashe ido ranta na kuna.
"Tashi ki dauko min wayata"
"Hajja dan Allah karki kirata, ki yi banza da ita, yadda ta nuna baki da muhimmanci ke ma ki nuna mata"
"Ba maganar zan mata ba, dauko min dai"
Firdausi ta tashi tana ta mita ta haura stairs din ta dauko wayar ta fito ta kawowa Hajja Yelwa. Sai da number Adda Sa'adatu ta amsa sannan Hajiya ta kara a kunne cike da far'a.
"Assalamu Alaikum Daughter"
Adda ta amsa mata cikin yanayin da ke nuna bata son jin muryarta.
"Hajiya an wuni lafiya"
"Laifi kalau daughter ya gida ya yaran"
"Lafiya kalau"
"Ashe mijina konewa yayi baki fada min ba? Yanzu nake ji nace bari na kira kamin na zo"
"Aa ba sai kin zo na Hajiya, ba wani sosai ba ne tiriri ne ya shafe shi, amman dai ya ji sauki na"
"Kin tabbata? Ko dai na zo na duba kayana kin san ba a wasa da miji"
"Aa da sauki Hajiya, ai da sosai ne da zan fada muku"
"Toh Alhamdulillah Allah ya tsare gaba, na ga mai aiki ai an samowa my son na ce kin kyauta zata rage masa wasu abubuwa kuma Gwaggo sai ta samu abokiyar hira"
"Eh haka ne"
Adda ta amsa mata a takaice.
"Amman na ce bata zo da tufafi ne ko mantasu aka yi a gidanki? Da safe nan sai rigar Jawad ta saka shi kuma ba magana yake ba kin san halin ɗan nawa, shiyasa na ce bari na tambaya idan babu sai mu duba mata wasu a nan, tun da ba zai yiyu ace tufafinsa take ta sakawa ba"
Adda ta dan yi shiru kamin ta amsa.
"Eh an manta kayan ne can"
"Tohm za mu duba mata wasu a nan, tun da be dace tana saka tufafin maza ba suna sharing, kuma tana matsayin mai aiki ka saka kayan ɗan masu gida kuma, zan duba mata wasu a nan"
"Ba sai kin duba ba Hajiya, zan saka a duba mata a shago a dinka mata, na gode sai anjima"
"Tohm a gaishe da yaran"
Kamin Hajiya ta sauke wayar har Adda ta katse kiran. Firdausi da haushi ya isheta ta ce.
"Hajiya miyasa zaki damu da rashin zuwanta da tufafi haba dan Allah"
"Ke yarinya ce ba ki san komai ba"
"Gashi nan har yanzu bata dawo ba, an fi awa daya fa kusan awa biyu yanzu"
Tun kan aje ayar zancen Hajiya ta karba da.
"Allah yass ta bata"
"Toh idan ta bata me zaki cewa Ya Jawad?"
"Dan Allah ki bar ni na ji da bakinciki nemawa Jawad mata, karki kara min wani"
Ta mike tsaye wanda hakan yayi daidai da shigowar Hannatu Harira da kanenta falon rike da ledodin takeaway.
ARIZ POV.
Gwaggo kamar ta tashi ta yi rawa don murna da farinciki, babu abun da take ganin ya rage mata ta gani a yanzu kamar auren Jawad da yayansa.
"Alhamdulillah mun gode Allah, Allah ya tabbatar da alheri, idan kuma babu alheri a ciki Allah ka kawa masa wata"
"Ameen"
Ariz ya amsa yan kara bajewa kan kujera.
"Yanzu can ka fito gidan Sa'ade?"
"Aa ina falon Hajiya ta kira ni"
"Au kana gidan ma ashe?"
"Eh tun dazun na zo, na zo da yunwa ne na sauka can na fara cin abinci sai muka tsaya hira, kin san Hajiya da son mutane bata son ka tafi idan ka shiga"
Gwaggo ta yi murmushin manya.
"Tana dai sonku ku, ni nan ai bata shigowa sai idan wani abu ya samu"
"Saboda ba ku jituwa ne Gwaggo kin san kin ke da Adda ba ku son matsawa kusa da Hajiya, amman Hajiya bata da matsala gaskiya"
Gwaggo ta sake yin murmushi.
"Ta shi ka dauko min plate zan ci abinci, tun dazun kuiyar tashi nake ji, jikin nawa yau sai a hankali, ga yarinyar da na aika bata dawo ba, kirata ka ce ta turo min Batulla ta zo ita ma ta ci abinci"
Ariz ya tashi ya nufi Kitchen din ya dauko mata plate ya kawo.
"Wacece Batula Gwaggo"
"Sabuwar mai aiki ce da Jawad ya kawo, daga gidan Sa'ade shekaranjiya, ita ce take kama nana abubuwa yanzu kuma ina jindadin zamanta a nan kurma ce kuma marainiya babu ruwanta"
"Ashe na kwana biyu ban zo gidan nan ba, yar aiki aka kawo ban da labari"
"Eh shekaranjiya ne ai kwananta daya, zata rika kula da can da nan din ma, tun dazun na ce taje karbo abinci bata dawo ba sai Husaina aka bawa ta kawo abincin, wata kila ta saka ta wani aikin nan, kuma ba ma lallai ta bata abinci ta ci ba, ta zo nan ta ci abincinta"
Ya ciro wayarsa ya kamo number Hajja Yelwa yana fadin.
"Gwaggo Hajiya ba zata hanata abincin ba, ko kare aka kawo ai sai ya koshi da abincin Hajiya balle mutum"
Ya kira layin ta, sai ta amsa masa da far'a.
"Hajiya wai Gwaggo ta ce ki turo mai aikin nan tana nemanta"
"Oh yar kurma, ai tun dazun ta fita da zo karbar abincin na ga hankalinta kan kallo sai na ce yara su kaiwa Gwaggo ita kuma ta zauna ta yi kallonta sannan ta tafi"
"Okay"
Ya kashe wayar sannan ta fadawa Gwaggo abun da Hajiya ta ce.
"Bata dawo ba, amman leka min ɗakin nan ka gani ko tana ciki nan kadai take shiga sai can baya gurin fanfo"
Ariz ya tashi ya shiga dakin ya duba har bandaki be ga kowa ba ya fito ya zagaya baya inda Fanfon be ga kowa ba, ya dawo falon.
"Bata nan baki aike ta ba?"
"Aa iyaka ci da ita bangaren Hajiya, kaje can ka sake dubowa dai"
Ya juya ya fice zuwa bangaren a falon ya samu kanen Jawad suna cin abincin da suka siyo, ya tambaya kowa yace be ganta ba, ya juya ya koma bangaren Gwaggo ya sanar mata.
"Ni wannan abun ya ban mamaki ko ruwa ta fada? Duba min nan ka gani"
Ta nuna inda swimming pool din yake, Ariz ya isa gurin ya daga curtains ya bude glass door din ya leka be ga kowa ba.
"Gwaggo bata nan ba"
Suna haka suka ji tsayawar motar Jawad, ya dauki minti biyar a mota sannan ya shigo falon yana sanya da shadda kansa da hulla sai kamshi yake zubawa. Ko zama be yi ba Gwaggo ta fada masa bata ga Batula ba cikin yanayin damuwa.
"Jawad, Batulla ta bata na aikata bangaren Hajiya karbo abinci Husaina ta kawo min abinci, ita kuma yanzu ba a ganta ba, kuma an duba ko'ina bata nan, Hajiya tace bata bangarenta"
"Wannan yaron yaje ya dubo miki ita"
Ya nuna Ariz.
"Wannan yaron ya fi karfin ka aike shi Wallahi"
Jawad yayi murmushi yana zaunawa, daman idan yana son tsokana ba shi da abokin yinta sai Ariz.
"Ba fa wasa ake ba, Wallahi ba a ganta ba, ni dai bangaren Hajiya Yelwa kawai na aikata"
Gwaggo ta nanata har da rantsuwa, sai a lokacin Jawad ya dauki maganar serious, ya mike tsaye wayarsa na vibration, Adda Sa'adatu ce ke kiransa.
"Hello"
Yana samawa ta hau fada.
"Hello Jawad yarinyar ni na manta ma bata zo da tufafi ba, zan aiko mata ko kala biyar ne, amman dan Allah ka daina bata kayanka tana sakawa ina ita ina tufafinka, su ma bakar tsiya ce da shegen kwadayi za a zo birni ga na banza a saka in ba haka ba ai sai a aiko yaro da kayansa mana, dan Allah karka sake bata tufafinka, yarinya tana aiki a gidanku kuma ace ta saka rigarka ai kaskanci ne, ko tufafi zaka bada ka bawa wani mai daraja mana ba yar aiki ba, yar aikin ma wanda idan ta saka sai kowa ya gani, wani lokacin sai ka yi ta abu kamar ba kai ba, haba mana"
Be ko tsaya tambayar waya fada mata ta saka rigarsa ba ya daba mata wata maganar data bata mata rai.
"Saka rigata da ta yi shi ne matsalarki?"
"Eh be dace ba"
"To ki kwantar da hankalinki, gobe ma wata rigar zan bata ta saka"
Ya fada cike da izza, A take zuciyar Adda Sa'adatu ta hau, daman can ita ba gwanar hakuri ba ce.
"Idan baka bata ba, baka haihu ba, kayan da zan aiko mata ma na fasa ka bata kayanta ta yi ta sakawa har abada, bari na hadu da ita kuma yarinyar ko wanda ta kawo ta dan ubanta, komai ka hada da bakauye sai ya nuna maka halinsa..."
Bata kai karshe ba Jawad ya kashe wayarsa ya maida aljihu ya fita falon ransa na burbushin baci, sun fito harabar gidan shi da Ariz da nufin nufar bangaren Hajja Yelwa.