21
Chapter 21
Yau ma kamar ko yaushe bayan gama da gidan Alhaji Badamasi ta tsaida napep ta hau suka nufi gida, suna isa ta sauka tare da basa kuɗinsa kana ta yi ciki. Sai dai me? Ganin dandazun jama'ar gidan a waje sai kaiwa da kawowa a ke kowa na tofa albarkacin bakinsa ga fuskar kowa ba daɗi, a hankali ta tako har gaban Ammie da har da ita cikinsu ta ce.
"Ammie me ya faru na ganku kun yi cirko–cirko haka a nan lafiya dai?" Ammie dai bata ce komai ba sai ma gauran numfashi da ta sauke tare da miƙa mata yar farar takardar da ke hannunta, dalilin da ya sanya jikinta ƙara yin sanyi, jiki a saɓule ta saka hannu ta amshi takardar ta buɗe, cikin rashin fahimta ta ɗago ta kalli Ammie da fadin. "Notice kuma?" Na waye."
Maman Sadiq ta taɓe baki. "Wai mu a ka kawowa saboda rashin ganin daraja ya saida gida ba'a faɗa mana ba a ka bar mu cikin duhu sai yanzu da masu gida suka buƙaci waje a ka wani tura mana da takarda ba mu san hawa ba ba mu san sauka ba, lokaci guda daga sama a zo a na wani fadin wai mu tashi mu bar wuri za'a rusa waje a yi sabon gini, saboda rashin mutunci shekara da shekaru muna cikin gida rana tsaka a wani zo mana da sabon zanci kuma ma dan renin hankali wai sati biyu suka bada kowa ya tattara ya tashi ya bar gida."
"Tofa! Wata sabuwa, to su haka a ke ne lokaci guda rana tsaka su tashe mutane?" Yo ko a shariya ma wata shida a ke baiwa mutum ya shirya ya nemi wuri kafin ya tashi ba haka bakatatan ba su ce sun bada sati biyu a tashi." Maman Khadija ta daura da "Kema kya faɗa saboda renin hankali mana yau mu ke zaune cikin gidan da za su nemi su rena mana wayo, ina suka ga a na haka yo ko gidan haya ka isa ka samu cikin ƙanƙanin lokaci haka yanzu da gidaje ke wahalar samu shi ne za'a wani aiko mana da saƙon takarda. Shima uban gayyan Alhaji Lauwali ya san bai da gaskiya shi ya sa ya ƙi zuwa ai ya aika mana da mutanen nan, yanzu da a ce kuɗin hayan sa ne ya dinga mana sintiri kenan da ɗiban albarka amma da ya ke ya san tsiyar da ya shuka ko wutsiyar sa wa ya gani?"
Haka suka ta maida magana kan abin da a ka yi masu ba'a kyauta ba kuma ba'a masu adalci ba, Ammie dai ta kasa magana tunanin inda za su koma kawai ta ke idan har a ka fidda su daga wannan gida, da tsayuwar ta gundireta ma ciki ta koma tana tabka da warwara yayin da Nazli ta mara mata baya.
"Ammie kin yi shiru tun ɗazu ba ki ce komai ba." "Me kuwa zan ce yar nan aikin gama ya gama, yanzu jira mu ke mu zuba ido mu ji yadda za ta kaya gobe da su Ali za su je wurin shi Alhaji Lauwali a ji daga bakin sa idan ma barin gidan ne ya kama sai ya san yadda zai yi da mu, idan ma a ka kafe sai an bar gidan sai a ƙara mana lokaci kan wanda suka bada har zuwa ranar da za mu samu wuri mu tare, amma bakatatan haka a zo a wani ce mu bar gida kamar wasu awakai maras galihu ina suke son mu koma? Idan ta kama ko kuɗin ne a basu su ƙara mana lokaci."
========
Washe gari kamar yadda suka tsara mazan gidan suka yi tattaki suka je har gida suka sami Alhaji Lauwali da maganar, amma sai ya nuna masu ai shi tuni suka gama da su ya saida gida dan haka yanzu sai abin da suka faɗa ko tsara gida ba a hannunsa ya ya ke ba dan haka ba shi da isa ko ikon saka baki cikin lamarin. Sun yi ciniki ya riga da ya saida masu gida ya kuma karɓi kuɗinsa dan haka ba shi da hurimin tsuka masu baki cikin lamarin da bai shafe sa ba dan haka su yi abin da a ka umarce su da shi kawai ko kuma su ƙarata da su, ruwansu su bar gida ko kar su bari ƙarshe ya ƙara da jadda masu kar su sake zuwan masa gida su same shi da wannan maganar dan yanzu babu wata alaƙa da ta haɗa dama gida ne yanzu kuma babu shi.
Sabon takaici kasa magana suka yi suka bar wurinsa sai dai fa kowa zuciyarsa na masa zafi ji suke kamar su hadar masa su yi masa dukan tsiya amma babu dama haka suka bar wajen zuciyar kowa a shunkushe, dama waye bai san Alhaji Lauwali da son kuɗin tsiya kamar dan shi ya zo duniya.
Gidan ba ma na sa bane na marayun Allah ta'allah, y'ay'an wansa da Allah ya yi ma rasuwa a ka ɗanka masa gidan gadon yara a hannunsa duba da shi ne kaɗai gwallin gwal ɗan uwa a garesa, a ka ɗanka masa gidan yara suka koma ƙarƙashin sa da zama.
Tun farko ya so ya saida gidan ya ci kuɗin amma Malam Haruna aboki ga marigayi ya yi ruwa ya yi tsaki dan hana faruwar hakan, a cewarsa yara har yanzu ƙananu basu gama mallakan hankalinsu ba dan haka ba abin da za'a saida cikin gadon su ya salwantar a banza idan lokacin faruwan hakan ya yi za'a san abin yi.
Hakan da ya yi ba ƙaramin baƙata ran Alhaji lauwali ya yi ba dan ya so a barshi ya saida gidan dan wani buri na shi na son zuciya, amma duk da hakan bai daddara ba sai da ya saida gidan nan da sunan yaran zai wa hidmar makaranta da su bayan ya karɓi kuɗin hayan ƴan gidan gabaki ɗaya na shekara ya saida gida ba tare da sanin kowa ba. Ya karɓi kuɗi ya cinye gashi yanzu ƴan gida sun buƙaci waje, saboda kunya da tsoro ma ya kasa zuwa ya faɗa masu sai su da kansu mutanen da suka ɓukaci waje za su fara aiki suka je har gida dan isar da saƙon su bayan bada tsawun wata shida da suka bada amma ɗan tahalikkin nan ya kasa zuwa ya sanar da kowa sai yanzu da suka zo dan kansu.
Maimakon ya bada hakuri da amsan laifinsa sai ya tsaya yi mu su borin kunya wai ba shi da yadda zai yi, haka dukkanin su suka koma rai a ɓace da kuma takaicin abin da ya yi, ba abin su titse shi ya fidda sauran kudin hayan na su da ya rage na watanni biyar yanzu sai a yi tashin tashina dan ba fidda kuɗin zai yi ba.
Da dare bayan sallar isha'i suna zaune kan tabarma Nazli ta ce. "Ammie yanzu ya zamu yi da batun gidan nan tun da zuwa gidan Alhaji Lauwalin ma bai yi rana ba sai ma tarin takaici da ya ƙara." Ammie ta numfasa "Hmmm!! ido za mu zuba mu ga ko Allah zai dubi zuciyoyinsu su ƙara mana lokaci kan wanda suka bada har sanda Allah zai nufa." "Allah ya sa Ammie, amma zai yi wuya a ce za'a samu gida cikin sati biyu nan da suka anbata, yanzu fa gidaje na mugun wahalar samu ba lallai ka samu wanda zai yi daidai da ra'ayinka ba cikin ƙanƙanin lokaci haka ba." "To mu dai gamu nan dai mun miƙa lamarin mu ga Allah in sha Allah zai zaɓa mana mafi Alkairi a ciki." "In sha Allah." Ta furta kan laɓɓanta.
–––––––
Gaba ɗaya kwanaki da suka biyo baya basa cikin nustuwa, kowa ya miƙe yana neman gida ba don sun so ba sai dan matsin lamba da a ka saka masu kowa ya bazama nema. Sai dai fa har yanzu shiru ta ɓangaren su Ammie, sun yi shige da ficen amma har yanzu shiru babu kaykkyawan sakamako musamman da ya zama macece abun ba sauke.
gabaki ɗaya gidajen da suke samu ba su yi daidai da ra'ayinsu wanda suka yi kuma sun fi ƙarfin su. Gari ya yi masu zafi ga lokaci na tafiya dan har an cinye kwanaki goma amma shiru ba labari.