Chapter 8
by @oumfatayat
*FARAUTAR MUTUNCI*
Na’ima Sulaiman Daƙayyawa (Oum Fatayat)
Page: 9
Yadda yaga Mrts.Raju ɗin ya masa ne abun ya ɗaure masa kai, rungumo shi yaga ya yi yana dariya ya kama hannunsa gyam, sanna ya fara magana da harshen turanci.
“A gaskiya Mahmud munyi matuƙar farinciki, yadda a sanadiyar ka ne Larabawan nan suka ga ya kamata mu haɗa hannun jari da su, wannan Nasara ba wai ta mu bace mu kaɗai nasara ce a tsakanin Ƙasashe Uku India Nigeria da kuma Lebanon.
A bisa irin namijin ƙoƙarin da kayi ne, muka ga ya kamata a ce na naɗa ka maitaimakin M.D na wanna Kamfani, wanda ɗana Ajay zai zama M.D, sai dai harkokin za su zauna a ƙarƙashin kulawar ka ne tunda shi kaga saurayi ne har yanzu, kuma bai gama karatuba yana London, amma da zarar ya kammala, zai dinga kawo muku ziyara a kai a kai, za mu sa lokaci da za ayi bikin karrama ka, acikin taro da bainar jama’a nagode, na gode bisa ƙoƙarinka ga Kamfani da kuma taimakona”.
Gasaƙe Mahmud ya yi yana kallon Mrst. Raju, ya kuma kasa cewa komai,duk da dai ya san shi ne ya yi ta faɗi tashi ganin Larabawan sun amince da haɗakar kasuwancin nasu sai dai bai taɓa tunanin wannan matsayin a lokacin yanzu ba, lallai Allah shi ne mai iko a kan komai, cikin farin ciki suka yi sallama da ogan nasa ya fito ya tafi gida.
Kamar kullum haka ya sameta, ta gama shirya musu komai ta tsuke cikin riga da wando iya guiwa ta raba gashin kanta a biyu ko wanna ɓari ta riƙe shi da ribbon, cikin murna da ɗokin yake faɗa mata abun alkaharin da ya same su, nan Nuri ta ja da baya tayi sujudu shukur, dariya Mohmud ɗin yake mata, haba Hajiyan Sujjada, ya da haka ba hijabi ba ɗankwali dariya ta yi kana ta ce wallahi fa na manta kwatakwata, tsabar farin ciki da murna.
Rungumota ya yi, kana ya ce Duk abubuwan nan da suka faru Nuri ke ce sila, don kece wacce a kullum kike sani cikin nutsuwar da ban san lokacin da nake gudanar da komai a cikin tsari , gaskiya, da kuma riƙon amana ba, don a koda yaushe burina na ciyar da ku da halak bana so haram ya shiga cikinku ko kaɗan Nuri, shiru ya yi sai can ya ci gaba da cewa, sai dai zuciyata a wasu lokutan takan kasa nutsuwa sai naji kamar wani abu yana gab da faruwa kuma abun kamar marar da…
Rufe masa baki Nurin ta yi, nan da nan ta sa shi ya manta duk wani abun da ya zo zuciyarsa na wasuwasi da ƙyar suka iya mai da kansu ɗaki, don gaba ɗaya Nuri tasa Mahmud ɗin ya shiga duniyar da yake mantawa duk wani abu marar amfani.
5:30 daidai Mahmud ya je ya ɗakko Al’tab a makarnta, kwanar da zai sha ya shigo layinsu ya gana Nana da Yaya Usman a cikin adaidaita suma suna dosar gidan nasa, gaban sane ya faɗi domin kuwa yasan lallai ba bu wata soyaya tsakaninsa da Yaya Usman. Shi ne ɗan fari a wajen Hajjo matansa biyu yana da yara 9.
Hajjo ‘yayanta 5 Maza huɗu mace ɗaya Usman ,Nura da Sani sai ‘yar autarsu Nana, wadda sai da Hajjo ta manta da batun haihuwa kana ta same ta a ƙarshe, sai kuma Mahmud shine cikon na 5 ɗin wanda Hajjon ta dage take sa shi a lissafin shima ɗanta ne, na cikinta haihuwarsa ce kawai bata yiba.
A daidai lokacin da Mahmud ya karyo kwana su kuma har sun ƙaraso baki gate ɗin gidan, har Nana za ta fara buga ƙofar sai suka hango motar Mahmud ɗin na zuwa, tsayawa suka don jiran isowarsa, yana zuwa horn ya yi Dakiɗo mai ga di ya buɗe masa ƙofa ya shiga, biyo shi suka yi abaya, ka fin a ce ya yi parking motor Yaya Usman ya sha gabansa, da sauri Mahmud ɗin ya ja birki, ji ka ke ƙiiiit.
“Ah, lallai Mamuda wuyanka ya yi ƙwari, saboda kana da wanna akwalar motar taka, da wanna ruɓaɓen gidan shine kake ƙoƙarin bige ni, to wallahi aniyar ka ta biki, kuma in sha Allah sai ka rigani Mutuwa”.
Nana ce ta zun ɓura bakin fitsara, “Haba Yaya, ya za ka masa fatan mutuwa yanzu tun ban aure shi ba”.
Tsaki Mahmud ɗin ya ja tsabar takaici, don shi ba abunda zai iya ce musu, don kwatakwata shi baya buƙatar tashin hankali a yanzu, don zuciyarsa cike take da farinci, da kuma godiya ga Allah.
Miƙawa Usman hannu ya yi don su gaisa, wani kallo da Usman ɗin ya watso masa na ya sa Mahmud ɗin girgiza kai.
“Ba gaisuwa ce ta kawo muba, dama Hajjo ce tace tana son ganinka ta kira ka, ta kira ka amma baka ɗaga ba, ba wani abu bane dama cewa ta yi Nana za ta dawo gidanka da zama don ku samu ku daidaita kanku, tunda ta ga kai ka ɗauki abun da wasa”.
Daidaita kai kamar yaya,wai wacce ma Nana ake magana?. In ji Mahmud
“Laha’ilaha’illahu Mahammada Rasulullahi, lallai Hajjo ɗan riƙo bai mata rana ba, ke Nana wuce muje don banga wajen zanamki a gidan nan ba”.
Bubbuga ƙafa Nana ta farayi ta zunɓoro baki gaba, duk da dai tana da kyanta daidai misali, sai dai Hajjo ta riga da ta shagwaɓata mutuƙa gaya bata ganin kan kowa da gashi, sai Mahmud da take bala’in so tun bata san ma mainene son ba, kuma kallo ɗaya ya ke mata take fahimtar inda ya dosa tund can ma. Ganin kallon da Mahamud ya watso mata ne yasa ta kama kanta ta bi bayaan Usman ɗin suka fice.
Sai dai duk abunda ke faruwa akan idon Nuriyya, hawaye ne suke zuba wani na bin wani a kumatunta, shi kuwa Al’tab ya ɓuya a bayan Babansa leƙo su Baba Usman da Aunty Nana kawai yake yi har suka fice.
Da sauri Nuriyya ta goge hawayen da yake idonta, don bata son Mahmud ya san kuka ta ke, ilemun kuwa yana zuwa abunda ya fara tambaya kenan, “Nuri ba dai wanan abun da su Yaya Usman suka yi ne ke damunki ba, ai ya kamata a ce idan da sabo kin saba, kuma matuƙar ina raye ba wani wanda zai zo ya miki ba daidai ba, ke ɗin rayiwata ce”.
Murmushi Nurin ta saki ta matso jikinsa ta yi lakur kamar mage, Al’tab ma haka ya mamuƙo cikinsu, rungumesu Mahmud ɗin ya yi yana mai ƙara godema Allah da ya azurtashi da mata kamar Nuriyya
*Gidan Hajjo*
“Dama ai Hajjo na sha faɗa miki tun yaron nan yana ƙarami wallahi bazai miki rana ba, amma fur ki ka ƙi yadda, yanzu ga shinan babu wacce zai zubawa ƙasa a ido sai ke, to da wannan abu ma za ki ƙaru da shi, yaron da Uwarsa ma ta gudu ta barshi, danginta kuma basu damu da shi ba”.
Hajjo kuwa huci take faman yi kamar tsohuwar kububuwa, ta furzar da wani irin nunfashi kamar ta kai sara bata samuba.
“Dan Allah Usman yi min shiru ka barni da abunda ke damu na, kuma wallahi nasan ba laifinsa ba ne, na riga da nasan makircin yarinyar nan da Uwarta ai ba Allah a ransu, sun ɗauka Mamudan ba shi da uwar da zata nema masa karya tambaya, to wallahi inan da raina ban mutu ba”.
Nanace ta amshe zan cen da cewa
“Wallahi Hajjo don ma baki ga yadda Yaya Mahmod ya mana ba, korar kare fa, saboda yar gwal ɗin tasa karta juyo mu, kuma wallahi in bai aure ni ba ina ga mutuwa zanyi”.
“Ki ma mutu mana, yar shegiya ke ana minki fafutuka sam bakya gani, to ki k…….
بقلم أم فتيات 👧👧👧✍🏼….