Page 33/34
💫MARYAMA💫
EPISODE 33/34
BY
UMMU FADEELA
Ƙanƙame ta Jabeer ya yi jikinsa na rawa tamkar ana kaɗa masa gangi a lokacin da ya samu nutsuwa, kafun a hankali ya faɗa gefenta jikinsa gaba ɗaya yana saki kamar ana zare masa laka,a hankali ganinshi da jinshi ya fara ɗaukewa kafun wani lokaci da bai iya tantancewa ba duhu ya mamaye ganinshi gaba ɗaya idanunshi suka rufe kana numfashinshi ya ɗauke cakkk ya tafi doguwar suma.....a nata ɓangaren itama Maryama tuni ta sume tun ba'aje ko'ina ba dan Hamman nata bai zo mata da salon wasa ba,plus yadda abin ya zo mata a bazata hakan ya haddasa mata ɗaukewar numfashi na wucin gadi...
(Wannan shi ake ƙira haihuwar guzuma, ɗa kwance uwa kwance,..ina jin dai ba iya Maryama zaku gasa ba team JAY harda oga kwata kwata🙆).....
A hankali ya fara buɗe idanunshi da suka mashi nauyi matuƙa sakamakon iskar asubahi da ta fara busoshi .A kan ta ya sauƙe jajayen idanun nashi kana ya na sauƙe wasu irin tagwayen ajiyar zuciya a jejjere kamar wanda ya yi tseren doki,Duk da baya iya ganinta saboda duhun da ke a ɗakin.Ta ke abubuwan da suka faru suka fara dawo masa cikin ƙwanyarsa dalla dallah tamkar a lokacin suke faruwa,hannunshi ya sa akan waist nata ya janyota zuwa jikinshi ya matse ta gam yana jin kuka na taho masa amma ya kasa yin kukan sai ajiyar zuciya kawai,...Har lokacin Maryama bata dawo hankalinta ba tana cikin suma.
Kamar wanda aka mintsina jabeer ya tashi tuna cewa tun wani ihu da tayi cikin dare bai ƙara jin motsinta ba,laluɓen wayarshi ya fara jiki na rawa,da ƙyar ya tsinto ta a acan gefe ya kunna light ya dallare fuskar Maryama da shi, kwance take ba alamun numfashi tattare da ita,fuskarta ta kumbura ta yi jajur hakama idanunta sun haye suntum duk da a rufe suke,wanda hakan ke alamta irin kukan da ta sha,ga wasu busassun hawaye layi bibbiyu kwance saman fuskar.
Dam dam darandam...haka kirjin Jabeer ke bugawa tamkar haɗuwar ƙarfe da ƙarfe,a rikice ya fara girgizata da iya ƙarfinshi ya na ambaton sunanta, "Pretty! pretty!!Maryamaaa!!! wani irin wawan tsalle ya yi ya dira daga gadon,ya manta da rashin karfin da ke tattare dashi ganin ba alamar numfashi a tare da ita. A tamanin ya fita palo ya ɗau ledar pure water guda ɗaya da wani gudun ya koma ɗakin yana tsinke bakin ledar da haƙwaranshi.Tamkar bakin pampo haka Jabeer ya hau bulbula mata ruwan saman fuskarta har zuwa kirjinta ba tare da ya damu da yadda ya ke jiƙa gadon ba...still ya yi a wajen zuciyar shi na bugawa da karfi karfi ganin ya juye mata ruwan amma bata farfaɗo ba,karasa hawa saman gadon ya yi ya tallabi kanta ya ɗaura bisa cinyarsa yana jijjigata da iya karfinsa...ba abin da ya ke fita a bakinshi sai ƙiran sunanta ba ƙaƙƙautawa, amma ko gezau, Maryama ba ta yi ba.Iya ruɗewa Jabeer ya ruɗe idanunshi sun kaɗa sunyi jajur da su...
Kamar daga sama yaji tana sauƙe wani irin ajiyar zuciyar da ya sashi kuma tallafo kanta ya matse a kirjinsa kamar mai tsoron kar a ƙwace masa ita ya ce, "Pretty pretty buɗe idanunki ki ganni, ni ne,hamma jay na ki ne,dan Allah ki buɗe idanunki ki ganni", ya faɗa yana ƙara matse ta gam gam.
Sama-sama kamar a cikin iska Maryama ta ke jiyo muryar Jabeer,yayinda take ta kokawa da numfashinta wanda ya yi nisan zango.....Wani irin fizga ta yi da ƙarfi ta sa ki marayan kuka mai karya zuciyar mai sauraro.
"Alhamdulullah" Jabeer ya furta kana ya lumshe idanunsa yana shafa bayanta a hankali alamar rarrashi...duk yadda ta so ta zame kanta daga jikinsa kasawa ta yi dan ji take kamar an É—aÉ—É—aureta ne da igiya ga jikinta da ya É—au zafi zau tamkar wuta ko hannunta bata iya motsawa, a gefe É—aya kuma wani irin tsanar Jabeer ne da kuma tsoronshi suka ma ta dirar mikiya lokaci É—aya...
Ganin lokaci na tafiya ne ya sa Jabeer sassauta riƙon da ya mata yana zame ta bisa gadon, ƙara Maryama ta saki mai ƙarfin gaske sai dai bai fita da ƙarfin ba saboda dishewar da muryarta ya yi.
"Sorry Pretty, I don't mean to hurt you, sorry please, I don't really know what came over me."Ko kallon inda ya ke bata yi ba har ya gaji da sambatunshi ya fita cikin rashin sanin abun yi...zagaye tsakar gidan Jabeer ya fara tamkar soja yana tunanin mai ya kamata ya mata, a gefe ɗaya kuma wani irin farin ciki ne fal ranshi, ji ya ke tamkar ya tsaga zuciyar shi ya jefata ciki kana ya ɗinke cifff abinsa Duk yadda yake tsammanin abin, it beyond his expectation kamar yadda ta bashi wannan precious gift ɗin da bazai taɓa mantawa dashi ba, dole shima ya samo something special da bazata manta dashi ba ya bata as pride gift.
Murmushi mai kyau ya yi yana shafa kai ya ce, "... kitchen ya faÉ—a daga karshe jin zai rasa sallar asubahi, stove nasu ya kunna ya hawar da ruwan zafi,..babban flask ya janyo da nufin idan ruwan ya yi ya juye ciki, sai ya jishi cike da ruwa.
A bocket ya juye ruwan flask ɗin ya surka ya shiga toilet na dashi bayan ya ɗauko wani boxer da towel a ɗakin...Bayan wani lokaci kadan ya fito sanye da wankakken gajeren wandonshi da towel rufe a kafaɗunshi,ruwan da ya hawar sai zaɓalɓala yake hakan ya sa shi juyewa da dan sauri sauri,wani irin tsalle Jabeer ya yi yana yarda tukunyar gefe haɗi da fara yarfe hannu kamar ƙaramin yaro sakamakon taɓa shi da ruwan ya yi lokacin juyewa,yana cigaba da yarfe hannun ya kuma ɗaga tukunyar ya cika da ruwa ya mayar bisa stove ɗin,tamkar soja haka jabeer ke tsaye kan ruwan har shima ya tafasa ya juye cikin bocket ɗin ya surka sannan ya mayar ɗaki.
Lokacin da ya koma É—akin Maryama ta ci kuka har ta galabaita ga muryar dama ta dishe.
Ranƙwafowa ya yi kanta cikin sanyin murya ya ce, "Sweet wife!"
Wani irin bugawa kirjina ya yi jin muryarshi dab da kunnena,da gaske wani tsoron hamma Jay ne ya dirar min dare É—aya.
"Pretty ki tashi kiyi wanka na haɗa maki ruwa kar time na salla ya wuce,"pretty"ya ƙara faɗa yana shafa kumburarriyar fuskata.
Ko motsi banyi ba, ba dan banji shiba sai dan yadda na ke jin ko ina na jikina a ɗaure.Ganin ta na ɓata lokaci ya sa Jabeer ya sunkuce ta ita da bedsheet ɗin kamar yar baby ya fara takawa zuwa waje.ƙanƙameshi gam Maryama ta yi tana fashewa da wani kukan dan yadda ta ke ji kamar zata mutu.
Bai tsaya ko ina ba dai banɗaki ya fara ƙoƙarin sauƙeta,sai dai a nan ake yinta,duk yadda Jabeer ya so ta tsaya da ƙafafunta abin ya faskara sai rawa da jikinta ke yi idanunta na tsiyayar da hawaye,.sosai yanayinta ya bashi tsoro dan haka cikin sanyin murya ya ce, "Pretty ina ke maki ciwo,?baki da lafiya ne?"tamkar zai yi kuka ya ke maganar.amma ko uffan maryama ta kasa faɗa ba don bata da abin faɗa ba sai dan yanayin da ta ke a ciki.
Saman ɗan dakalin da aka yi musamman dan wanka ya ajiyeta yana yaye bedsheet ɗin zaro ido Jabeer ya yi zuciyar shi na bugawa ganin bedsheet ɗin ya yi kaca-kaca da jini kai kace kaza aka yanka. Naɗe wa yayi da sauri gami da ajiyewa gefe ya fara mata wankan ganin da gaske bazata iya ba,...da ace ina da iko bazan barshi ya taɓa ni ba, amma inda nake ko yatsata na motsa ciwo ya ke min.
Ina ji ina gani hamma Jay ya wanke ni tas ya kuma ɗaukata kamar baby ya maida ni ɗaki haɗi da kwantar da ni saman kujera ya rufe ni da towel nashi. ɗakin ya koma ya ɗan goggoge saman gadon inda ya yi staining sannan ya canja bedsheet ya fitar min doguwar riga ya dawo palon, kimtsani ya yi ya kuma ɗaukata again zuwa saman gadon ya kwantar da ni haɗi da lulluɓa min wani lallausan duvet...kafun Jabeer ya gama hada hadan har gari ya fara haske,dan haka ya shimfida abin sallah kawai a gida ya zura jallabiya ya gabatar da sallah,sosai ya gabatar da addu'oin godiya ga Allah, sannan ya koma toilet ya haɗa ruwa ya wanke bessheet ɗin da ya baci tas ya shanya saman igiyar dake tsakar gidan.
Da sauri sauri ya gama ya koma ɗakin. Zuwa lokacin jikin Maryama ya gama ɗumewa da zazzaɓi sai rawar sanyi ta ke yi haƙwaranta suna bugun juna, "Subhanallah, pretty!meke damunki? Pretty baki da lafiya ne? ko mu tafi asibiti? Gaba ɗaya Jabeer ya rikice ya zama wani abin tausayi shima jikinsa ba ƙarfi mazantaka ya ke nunawa kawai amma shima da zai samu dama kwanciya zai yi.
Hannu ya sa saman wuyarta da sauri ya É—aga jin yadda ya yi wani zafi kamar wuta.shidai Jabeer kanshi ya É—aure ya rasa abin da ya kamata ya yi,gaba É—aya komai ya tsaya mashi,waya kamata ya tambaya, "Innarmu" zuciyar shi ta bashi amsa ba tare da tsayawa dogon nazari ba ya É—au wayarshi ya fara dialling layin Innarmu ringing biyu ta É—aga cikin sallama. Amsa sallamar ya yi yana faÉ—in, "Barka da asuba Innarmu, ya muka tashi?"
"Lafiya Alhmdllh" cewar innarmu.
"Jabeer, ya kuke? Lafiya dai ka ƙirani yanzun nan? ko dai akwai abin da kuke bukata ne Fati ta kawo muku..."
Inna ta ƙara faɗa jin jabeer baice mata komai ba kuma ga katin shi yana tafiya,. A ɓangarenshi kuma samun kansa ya yi yanzun da jin nauyin Innarmu abin da bai taɓa yi ba.
"Kana tare da ni kuwa jabeer? Ko dai baka jina ne?"
Shafa kai ya yi yana jin wani irin kunya na lulluɓeshi amma baida mafitar da ya wuce sanar mata ɗin gashi kuma ya kasa hakan.