MARYAMA

Page 35

by @ummufadeela01

💫MARYAMA💫

EPISODE/35

      By

   UMMU FADEELA.



***



Babana kana tare da ni kuwa?".
cewar Innarmu jin Jabeer ya yi shiru bai ce komai ba. "kana jina?" ta kuma tambaya.

Da ƙyar Jabeer ya yi ƙundunbalar cewa, "am ehm dama Innarmu dama ita ce",

"Jabeer ƙalau kake kuwa mai ke faruwa na tambayeka amma ka cika ni da In'ina"

"Innarmu ita ce bata da lafiya tun jiya kuma yau ko tsayawa bata iya yi, plsss Innarmu kizo ki ganta dan Allah" ya ƙare maganar da ɗan karaya a muryarshi.

"Subhanalla! mai ya sameta haka?" Inna ta kuma jefo mishi tambayar da ya kuma rikita shi.

Haka kawai fa Innarmu haka kawai ta kasa tashi da kanta ba abin da ya sameta.

"To sai kuje asibiti ai, ni mai zan zo in maku a gida?" cewar Inna tana yanke kiran.

Wani irin murmushi yana bayyana saman fuskarta, ba tun yanzu ba tasan itace mutum na farko da Jabeer ke fara tunkara da damuwarshi tun yana yaro, kuma wannan shine tarbiyar da ta bashi na cewa duk abin da ya sameka ko ya shige maka duhu ka fara tuntuɓar iyayenka kamun wasu suji, kuma Alhmdllh Jabeer ya ɗau wannan tarbiyar sai dai batai zaton har a irin wannan al'amarin zai iya sanar mata ba, dan sarai ta fahimci abin da ya faru, and she's happy da Allah ya nuna musu wannan lokacin murmushi ta kuma yi har haƙwaranta na bayyana.

"Ah'ah na shiga uku ni jikar mutum huɗu, wai ba magana nake miki bane Dijah amma kin min shiru kamar wata shashasha".cewar Daada da ta ajiye kayan da take ta aijin naɗewa tun bayan da Innarmu ta amsa ƙira ta zuba mata idanu.

"Ayya kiyi haƙuri Daada ban jiki bane ba".

"Yo ina zaki ji ni dama gaba É—aya kin ruÉ—e kin firgice, me ya samu takwarar nawa na ji kina ambaton sunan asibiti da safiyar nan?" ta tambaye ta tun bata dire maganar ba.

Murmushi ta kuma yi. a'a ba maganar murmushi bane Dijah faɗa min abin da ke faruwa, kar dai ace rashin haƙurin yaran zamanin ya nuna ya turmushe mana ƴa ba tare da ya dubi ƙanƙantar ta ba?" murmushi Inna ta kuma yi ta sinne kai ƙasa, ita tana rasa gane kan daada, komai ya zo bakin ta faɗa take tana manta cewar ita surkarta ce kodan su ɗin yan uwane?

A firgice ta É—ago kanta tana zare ido sakamakon wani irin salatin da Daada ta rabka, haÉ—i da kiran sunan" lami, lami"

Har tana tuntuɓe Inna lami ta shigo ɗakin tana tambayar "lafiya Daada"?

"Inafa lafiya ƴannan, Jabeeru dai ya cika tantirin mara kunya lamba ɗaya, Ina faɗa miki lamba ɗaya na bugawa a jarida shafin farko yanzu inba rashin kunya ba bazai jira mu koma ba tukunna ya ida rashin kunyar tashi. Yau ni naga jaraba da farar safiyar nan? amma ko zuwa ganin ɗaki bamuyi ba ace yaron nan ya turmushe yar mutane daren jiya kuma tsabar rashin ta ido yanzu ya ƙira uwar wai yar bata da lafiya? tir wannan zamani da ya yara basa girmama ƙimar mata, mu a lokacinmu basai yarinya tayi shekaru uku a ɗaki ba tare da mijin ya riƙe ko dan yatsanta ba, amma jiba ki gani daga kai mashi yar kwana biyu har ya haiƙe mata."faɗa daada keyi ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba.

"Yanzu ni abin da ban gane anan ba daada shine, laifine dan Jabeer ya haÉ—a shimfiÉ—a da matarsa? Ina ce takanas kika taso daga nijar dan shaida É—aurin aurensu amma kin zo kina ta bambamin faÉ—a dan kawai ya aikata abin da yake na halal. kinata wani haÉ—a zamaninku da ake da karancin wayewa da wannan zamanin" cewar Inna lami da maganganun daada ya tunzurata.

"To dama nasan ba kirki ne dake ba ai lami, yanzu sai ki iya kawo min duka, wuce muje muga mai ya aikata mata, wataƙila ma ciwo dan banzan ya ji mata ya kuma kasa gasata."

"Kin wuce ne ko sai na ɗauke ki a ka?".inji daada ganin inna lami na tsaye ƙiƙam. Daada ya za'ayi mu wani je gid....."

Wani kallon da innarmu ta watsa mata ne yasa ta yin shiru ba dan ta so ba, "kuje kawai lami wataÆ™ila akwai abin da zaki taimaka mata dashi ga can abin karinsu da Fati zata kai idan anjima dama ki É—auka" 

Ba don taso ba ta yafa mayafi haÉ—i da bin bayan daada wacce har tayi nisa tana ta sababi, ita a ganinta wannan sirrinsu ne bai kamata wani ya sani ba.

Turus daada ta tsaya a tsakar gidan tana ƙarewa babban zanin gadon dake shanye tsakar gidan yana ta ɗigar ruwa kallo juyowa tayi haɗi da kallon inna lami da ta ja tunga ta tsaya itama tace, "Lami kin gani ko?" munafuƙin har ya wanke zanin gado"

Murmushi kawai Inna lami tayi tana bawa zuciyarta tabbacin dole fa daada tana bukatar uzuri dan shekaru sun ja, dan ma dai akwai karfin jiki.

                   ************

Zama Jabeer ya yi bakin gadon haÉ—i da dafe kanshi cike da rashin sanin abun yi lokacin da Innarmu ta yanke wayar, ya daÉ—e a haka ba tare da yasan what next ba.

"Ya Allah" ya furta ya dafe kanshi dake sara mashi gami da juya kanta jin wani irin hucin zazzaɓin da take fitarwa ga kukan da take amma baya fita.

Kanta ya tallafo zuwa kan cinyarshi ya kwantar gami da fara shafa dogon gashinta zuwa saman kumburarriyar fuskarta, "Sorry pretty" kawai Jabeer ke faɗa idanunshi sun kaɗa jajur dasu....a wannan yanayin ne kuma ya fara jiyo magana kamar daada a tsakar gida,bai gama tantancewa ba yajiyo sallamar inna lami a bakin ƙofar ɗakin.

A hankali ya sauƙe kan Maryama da yai mata matashi da cinyarshi zuwa kan pillow sannan ya miƙe yana gyara mata kwanciya,haɗi da shafa kyakkyawar fuskarta da ta kumbura tayi haske fayau.Sannan ya fita.

"Haan ya kika tsaya daga waje baki shiga ba?gidan baƙonki ne ko dai shi jabeerun ne ya kafa allon sanarwar kar wanda ya shiga mishi ɗaki".?

"Eh musamman ma idan wanda ya zo ɗin ban gaiyyace shi ba."Cewar Jabeer da ya ji maganar da daada take yi lokacin da ya ke fitowa.Risinar da kai ya yi ƙasa ya ce, "Barka da zuwa Inna"

 Da murmushi Inna lami ta ce, "yauwa barka ka dai ango,ya É—iyata É—in Innarku ta ce bata ji daÉ—i ba".

Yana shafa kanshi ba tare da ya ce komai ba, daada da ta É—aure fuska tamau ta ce, "kaga ja'iri mara kunya zaka bamu hanya ne ko yaya?."

ÆŠan matsawa yayi fuuu ta shige É—akin ba tare da ta kalleshi ba,É—an dariya kaÉ—an Inna Lami tayi tana kallon Jabeer da still kanshi ke kasa ta ce, "Daada yanzu sai an haÉ—a mata da uzuri,dariyan yayi shima yana gyaÉ—a kai da faÉ—in "haka ne kam".

Sosai sukayi mamakin halin da suka tadda Maryama da zuwa lokacin jijinta ya ƙara yin tsami dan rashin amfani da ruwan zafin da basu yi ba tun asuba ɗin, "dama nasan za'ayi haka,inba rashin imani irin ma alhassan da dijah ba ina Jabeer lutete dashi ƙiran samudawa ina maryama da take yar firit da ita? ai kowa yasan daman cutar ta kawai za'ayi to gashin nan dai tun ba'aje ko ina ba kun fara gani".

Daada kenan ke ta sababi ganin Maryama sai maƙyarƙyata take tamkar an jiƙa kyanwa.shigowar Inna Lami ya sata yin shiru.

Ruwan zafi Innan ta haɗa daidai zaman mutum cikin baho sannan ta kama Maryama da dambe da komai ta tsoma ta ciki, ihu ta ke yi tana ƙanƙameta,duk da ta fahimci irin azabar da take ci hakan bai sa ta barta ba don shine gatan da zata mata.a hankali ta fara jin ruwan yana mata daɗi har da lumshe idanu ganin haka inna lami ta fita ta barta a bayin....

..........................*******...........................

                       GOMBE

Tsabar doƙi Khadija kasa bacci tayi a ranar sai juyi kawai take a kan gado,ƙiran sallar farko a kunnenta dan haka ta tashi ta fito a hankali ta kama handle ɗin kofar ta buɗe without making any sound,sauƙa ta fara yi daga stairs ɗin cikin sanɗa dan kar Mommy ta jiyota,saura baifi steps uku ba ta gama sauƙa taja ta tsaya tana turo baki gaba gami da kama bakin rigar baccinta tana wasa dashi.

Mommy ce zaune downstairs idanunta sanye da glasses tana operating laptop dake gabanta...ɗan sauke madubin idon kaɗan tayi zuwa ƙasa tana kallon Khadija da taƙi gaba taƙi baya.Hannu Mommy ta sa ta yafitota haɗi da nuna mata gefenta, da sauri ta gama sauƙowa tazo ta zauna gefenta ɗin tana mata side hug "morning Mommy".

"Morning dear, ina zakije yanzun nan ko Salla ba'ayi ba?".

"Mommy zan jiƙa rice ɗin da zan wa yaya girki dashi ne, kin san fa ya ce morning flight zai bi, and ba wani nisa tsakanin port da nan" ta kare maganar cike da shagwaba, shafa kanta Mommy ta yi ta ce, " God bless you dear, je ki jiƙa but be fast kar jam'in salla ya wuce ki."

"Thank you my momm" ta faÉ—a tana bawa mommy peck a hannu ta shige kitchen É—in da É—an gudunta. Iya tsaruwa wannan kitchen É—in ya tsaru, babu ce kawai babu a cikinta, store É—in dake manna cikin kitchen É—in ta shiga bayan ta dauki mazubi mai É—an girma kaÉ—an,farar shinkafa ta É—iba kofi biyu ta fito ta kunna tap ta zuba ruwa akan shinkafar sannan ta ajiye a gefe ta fita.

Lokacin da ta fito babu mom a palon ta haura sama, dan haka itama hayewa ta yi ta shige ɗakinta direct toilet ta shiga ta ɗauro alwala babban hijab har kasa ta ɗaura saman riga da wandon baccinta ta gabatar da rak'atal fajr, tana zaune bisa pray mat ɗin da qur'an a hannunta har aka tada sallar asubahi, da ta kammala yau ko azkar batayi ba ta yaye hijab din gami da linke shi ta ajiye saman bedside drawer. Gashinta ta naɗe cikin hula sannan ta sauƙo kasa, babu kowa palon har yanzu kuma gari da ɗan duhu dulum dulum,kitchen ɗin ta koma ta janyo apron ta ɗaura akan pyjamas nata ta fara aiki.Ruwa ta jona a kettle sannan Shinkafar ta duba ganin ya mata yadda ta ke so ta wanke shi ya fita tas ta juye cikin blender haɗi da markaɗa shi yayi luƙui,wasu glass bowl babba da ƙarami ta ɗauko ta juye a cikin babban ta ajiye blender ɗin cikin sink.

Babban cokalin miya ta ɗauka ta debi markaɗaɗɗen shinkafar ludayi daya da kaɗan ta zuba cikin karamin bowl ɗin sannan ta koma kan kettle nata da zuwa lokacin ruwan ciki ya tafasa kashewa tayi ta ɗaga ta zuba tafasashshen ruwan akan ƙulli ludayi daya da kaɗan ɗin da ta zubawa karamin bowl ɗin, take ya haɗe ya zama tamkar kunu,juyashi ta dinga yi har yayi sanyi ƙalau da yake sauri take yi,bayan yayi sanyi ta hadesu da sauran ɗanyen ƙullin ta juyasu suka hade jikinsu sannan ta zuba yeast daidai ta zuba baking powder shima daidai da ƙullin ta kana sugar (according to your taste) sai gishiri ɗan kaɗan.,ta juyasu sosai ta rufe da babban marfi ta barshi a wajen.

Gaban frizer taje ta buɗe ta fara tunanin da mai zata haɗa miyar kifi ne ko gajeren ƙashi or peppe chicken.murmushi tayi har babban wushiryarta na bayyan tuna irin amincin dake tsakanin yayan nata da kaza,thou SINASIR da jajjagen danyen kifi yafi daɗi amma bari tai masa peppe chicken ɗin kawai.

Wata dakwalar kazar gidan gona ta ɓanɓaro kasancewar ta dasƙare, cikin ruwa ta jefa ta barshi ya yi melting ta koma kan kayan miya ta jajjaga attaruhu da tattasai mai ɗan yawa kana ta dau plate ta daura curry powder da maggi thyme garlic and ginger powder tumeric soysource da sauran kayan spices da take bukata gyara kazar tayi bayan tayi melting ta yayyanka su into peaces sannan ta wanke ta zuba kayan kamshi da albasa ta ɗaura kan gas wani albasar tayiwa yankan slice mai ɗan yawa shima ta ajiye gefe, da sauri sauri take aikin.fry pan ta fitar ta ɗaura bisa gas, wata tukunyar ta kuma zubawa ruwa haɗi da mint leaf ginger cinnamon da sauran kayan shayi ta daura a gefe, sannan ta koma kan ƙullinta da zuwa lokacin ya taso yayi kyau, fry pan ta ɗaura saman gas shima ta shafa mai ta fara suyan sinasir ɗin ta, take gidan ya baɗe da kamshin abubuwa kala kala, cikin ƙanƙanin lokaci ta gama soyawa ta zuba cikin food warmer mai dan karen kyau shima tea ɗin dake ta tashin ƙamshi ta juye a tea flask da sauri sauri ta soya kazar ta ta haɗa peppe chicken that look so mouth watering kasancewar ya samu kala mai kyau. shima ta juye a warmer duka ta fitar ta jere saman dining, sai a lokacin cooks na gidan suka shigo dan fara aikin breakfast.

A gurguje ta faɗa wanka ganin karfe takwas ya wuce,tsawon minti talatin ta kwashe tana dirzar jikinta sannan ta fito tana goge jikinnata mai ɗan karen sulɓi da towel, duk da kasancewarta baƙa, amma tana da glowing skin,da shike ita ma'abociyar kamshi ce nan ta fara bulbilawa kanta turare kala kala daga na jiki na hammata, na bayan kunne, na gashi ko ina khadija tana da turarenshi na mussamman, sai da ta gama sannan ta fara shafa haɗaɗɗen manta wanda shima ke cike da ƙamshi,
(Ƴar uwa ki kasance mai yawan amfani da turare, domin mace mai ƙamshi darajarta da ƙimarta daban yake.)

Kasancewarta ba ma'abociyar kwalliya ba a take ta gama shirinta cikin wani tsadadden abaya ash colour ta yane kanta da mayafin abayar sannan ta ƙara feshe jikinta da wani turaren ta ɗauki jakarta ƙirar channel ta rataya ta sanya wasu takalma sau ciki suma na kamfanin channel ɗin ta zari wayarta ta kama hanyar fita tana duba agogon dake tsintsiyar hannunta,zaro ido tayi ganin lokaci ya tafi ashe bata ankara ba.

Da sauri har tana tuntuɓe ta faɗa ɗakin mommy, amma bata sameta ba, dan haka ta fita tana zumburo baki ta nufi side na abbu.still tayi a wajen tana lumshe idanu riƙe da hannun ƙofa bayan ta shiga ɓangaren abbu ɗin sakamakon ƙamshin turaren da ta shaƙa cikin hancinta ..