Page 36
💫MARYAMA💫
BY
UMMU FADEELA
Page 36
Turo baki tayi gaba ganin duk sun zuba mata idanu, "ya kika tsaya a can mamana ki ƙaraso mana" cewar abbu da ya bar hirar da suke ya juyo ɗauke da murmushi.
Takowa take yi cikin palon cike da yauƙi irin na yan mata masu ji da lokacinsu idanunta ƙyam a kanshi, "Ya Allah!karfa inyi abin kunya"cewar Khadija dake dab da isowa.
A ƙasa ta zauna kusa da ƙafar Mommy bayan ta cire takalman ƙafarta. "Good morning Abbu." cewarta, "Yaya muka tashi Mamana?hope all is well?"
Ƙara risinar da kai Khadija tayi cike da girmamawa tace, "Alhmdllh, Abbu"
"Masha Allah" tsohon mai cike da ƙima da haiba ya faɗa yana maida kallonshi kan Sadeeq dake ta aikin danna wayarshi.A kallo ɗaya zaka fahimci tsananin kamar da Sadeeq ke yi da Abbu, a wajenshi ya ɗauko baƙar fata da tsawo kamar daren layya,😜yayinda ya ɗauko yanayin zubin hallitar fuskar Mommynsu.hakan yasa shi zama kyakkyawan gaske haɗe da kuɗi da gyaran jiki da kuma hutu.
"Bakiga yayanki bane duk É—okin da kika kwana kina yi É—in sannan ki kasa gaishe shi?". cewar Mommy tana shafa kan Khadija da ta kwantar saman kafarta.ÆŠagowa Sadeeq yayi suka haÉ—a ido murmushi ya mata haÉ—e da É—age gira guda É—aya,amma sai ta turo baki gaba idonta na cika da kwallah ta ce,duk abin da suke iyayen nasu na lure da su, É—an mirmushi kawai Abbu yayi yana É—auke kai.
"Mommy ba shi ne ba" kamar jiran ta furta hakan take ta fashe da kuka mai cike da shagwaɓa.
"Ya salam!wai yaushe zaki girma ne Khadija,you're no longer a baby fa"
"Mommy ina shi ne ya yi tahowarsa kuma bayan nace maki zanje in É—aukoshi a airport É—in,maimakon ki hanasa tahowa sai na gama shiryawa."
Gefe abbu ya yi da kai yana ƙunshe dariyarsa,yayinda Sadeeq ya zaro ido jin abin da ta faɗa,mommy kuwa kanta ta cigaba da shafawa a hankali ta ce, "Ohhh sorry,kinganshi nan haka muka ganshi da sassafen nan kamar wanda aka jeho ko bala ma bai jira ya je ba,inajin ma taxi ya shiga,amma na miƙi alƙawarin ke zaki kaishi idan ya zo tafiya ohk?maza jeki ki gaida shi".
Da rarrafe Khadija ta iso wajenshi kasancewar ba bu nisa tsakaninsu,ɗan gefe kaɗan da shi ta zauna tana langaɓar da kai gefe haɗe da tunzuro baki gaba ta ce, "Sannu da zuwa yaya,shi ne tun asuba ina kitchen dan haɗa maka breakfast da kafi so kai kuma kaƙi jirana in zo in ɗauko ka ko?wai ma wani irin flight ka bi ne haka da sassafen nan?ko dai private ne?".
Ajiye wayar shi Sadeeq ya yi haɗi da riƙe kumatu yana ta kallon bakinta dake ta zayyano bayani ba tsayawa,ajiyar zuciya ya sauƙe jin ta yi shiru ya ce, "Kin gama tambayoyin naki duka?" gyaɗa mashi kai tayi,gami da kafe shi da kyawawan idanunta, "are you sure?" ya kuma tambayarta. "ehh mana yaya".
"Ohk,to ina kwana"
Da sauri ta rufe idanunta da hannayenta duka biyu tana dariya...Murmushi ya yi ya ce, "Mom kamar ji nayi kince yarinyar nan ta zo ta gaishe ni, amma maimakon gaisuwa sai ta buge da tambayata kamar sabuwar yar jarida".
Duk dariya suka sanya Abbu yana miƙewa ya shige bedroom nashi.
"Kai dai yaya na manta ne fa," cewar Khadija still hannunta saman fuskarta..."Yauwa MAN kaji ai ta manta ne" cewar mommy da murmushi saman face nata.
"Murmushi ya yi shima yana shafa beard nashi, "Yaya ina kwana to, ka kawo min tsarabata?" khadija ta faÉ—a bayan ta buÉ—e fuskarta, tun bai amsa mata ba ta cigaba da cewa na shirya maka wani abu mai daÉ—i yaya ta so muje kaci,".
"Hmmm,ji ta kamar wani girki ta iya yen yen yen sai anje aji ba wani abin kirki".
Hannunshi ta kamo haɗi da miƙewa ta fara janshi wai ya tashi, sai dai ko motsa shi ta kasa yi wajen.
"Da gaske fa yaya ya yi daɗi ka tambayi mommy ma kaji,kafun mommy ta basu amsa Abbu ya fito daga bedroom hannunshi ɗauke da wasu tarin takardu ya ƙaraso palon yana zama a kujerar da take tashi ce shi kaɗai ke zama kanta,ganin haka ne ya sa khadija sakin hannun Sadeeq.
"MAN Idan kayi karin kumallo ina bukatan ganinka,"tsungunar da kai Sadeeq ya yi haɗi da cewa, "Insha Allah".kana ya miƙenya bi bayan Khadija da har ta iso ƙofa jin abin da Abbu ya faɗa.Da ƙayataccen murmushi iyayen suka bi ƴaƴan nasu, kafun Abbu ya ce, "Ya kamata zuwa yanzu yaron nan ya fara wani motsi fa,gimbiya"
"Nima abin da ke raina kenan yallaɓai,tunda ta kusa ƙare makarantarta kawai a fara shiri kar abubuwa su zo su kacame mana gashi abu ne tuwo na maina," dariya mai ɗan tsayi Abbu ya yi sannan ya ce, "Ina jinjinawa uwar amarya kana uwar ango," cike da barkwanci ya faɗa yana ɗaga mata hannu alamar jinjinawa, itama dariyar ta sanya ta ce, "ahto gaskiya ne ai, gwara in aura masa abin da na raina da hannuna tunda dai naga sun haɗa kansu, akan ya ɗauko min yaran yanzun nan da suke raba mace da ɗanta tunma basu shigo ba".
(To,na shigenge.Mommy ya da haka?.kar dai kisa Maryaman mu ta sake reshe ta kasa kamo ganye).
"Hakane kam gimbiyata Allah ya tabbatar mana da alheri, yanzu muje a bani breakfast kar yunwa ya min illah....A jere suke sauƙowa daga stairs ɗin cike da tsohuwar soyayya har suka shigo dining area ɗin,Khadija dake serving Sadeeq sai surutu take zuba mishi kamar zabiya ta janyowa Abbu kujera ɗaya zuwa baya, sannan ta janyowa mommy ma nata,plate din da ta zuba sinasir guda uku ta turawa sadeeq gabanshi sannan ta ɗau wani bowl mai shape na heart ta zuba peppe chicken da ke ta zabga kamshi ta ajiye masa haɗi da black tea da ya sha kayan kamshi.
"Tanks" ya faÉ—a kasa kasa yana jan kamshin abincin.
"Abbu kai ma in sa maka wannan ɗin?". "Mamana abin na rowa ne kenan".rufe fuskarta tayi ta ce, "a'a fa abbu shi ɗinma dan yana so ne". "to samin guda ɗaya inji.ɗaya ta sanya mishi hadi da p chicken ɗin ta janyo wani plate ta zuba mishi ainahin breafast da cooks sukayi ta haɗa ta ajiye gabanshi, haka ta sawa mommy ma sannan ta zuba nata ɗan kaɗan tamkar na ƴar baby ta zauna,Sadeeq da ke ta aikawa cikinsa haƙƙinsa dalilin daɗin da abincin yai masa ya ce, "Bani soft drink". da sauri ta kuma tashi ta janyo orange juice da tasan yana so ta zuba nishi a dogon glass cup ta miƙa mishi sannan ta fara cin nata a hankali kamar ba ta so...da kanshi ya janyo kular sinasir ɗin ya fara zuba wani bayan ya gama cin wanda aka zuba mishi.
Mommy ne ta yi dariya ta ce, "Ta nan ka fi ƙarfi ai, a dafa kaci har da ƙari, amma ka kasa kawo mai girka maka na din din din,"
Sosa kanshi ya fara kamar munafuki ya ce, "Mom dama fa zan faÉ—a maku cewa na kusa yin aure, kusan dukkansu uku a tare suka É—ago yayinda murmushi ke bayyana saman fuskar su, saidai take murmushin ya fara fading sakamakon jin abin da ya cigaba da faÉ—a.
"Mom sunantan MARYAMA, bafulatanar Adamawa ce sai kin ganta Mommy kyakkyawa da ita...Wani irin tari ne ya turnuƙe khadija ta ke ta fara tarin har idanunta na ƙwalalowa waje sakamakon tsokar kaza mai cike da yaji da ta sa a bakinta.
"Subhanallah! sannu khadija, cewar mommy da ta taso da sauri bayan tayi namijin ƙoƙarin tashi daga shock ɗin da Sadeeq ya bata.bayanta ta fara bubbugawa a hankali tana shafawa,hannu na rawa Sadeeq ya tsiyaya ruwa a cup ya kai bakinta, ba tare da musu ba ta ƙarɓa ta sha ƙaɗan ta zauna tana ta maida numfashi sama sama duk sannu suƙa ringa mata tana ɗaga musu hannu gami da gyaɗa kai...
*************--------------------***************
BAYAN KWANA BAKWAI.
Zuwa lokacin Maryama ta samu lafiya ta dawo normal, sai dai har lokacin tsoron Jay ta ke yi babu kusanci ko kaɗan a tsakaninsu. Bayan ya aikata abin da ya aikata ne kuma dan su sami kusanci su zama abu ɗaya. Dosai hakan ke affecting nashi, a cikin kwana bakwai ɗinnan har ya fara fita a kamanninshi dan wani irin ramewa yake kamar ba angon sati ɗaya ba, irin annurin nan da ake gani a fuskar sabbin angwaye sam babu a wajen Jabeer, shi ya ke gaba ɗaya aikace aikacen gidan kamar shara da wanke toilet da kuma mopping girki dai har yanzu innarmu ke turo musu ta ce sai sun samu kamar wata ɗaya, amma a zahiri tausayin jabeer ta ke yi dan tasan bashi da kuɗin yin cefane kullum, dabararta shine nan da cikar watan ya fara ɗaukan albashi,tunda ya fara zuwa wajen aikin da ya samu na koyarwa, idan ya dawo kuma gidan ba daɗi haka yake tafiya wajen aikinshi na da inda suke buga gadaje, gaba ɗaya jabeer ya sauya a take rashin nutsuwar zuciyarshi ta bayyana akan fuskarshi, ita kuwa bata da aiki saidai tayi wanka da sallah sai kuma ɓuya, duk sanda ta ji motsin shigowarshi gida duk abin da ta ke yi sai ta bari ta gudu ta ɓuya a bedroom nata,dan tuni ta yiwa ƙofar wani dabara yanda take iya rufeshi yaƙi buɗuwa ta waje...a ɓangaren wayarta kuwa kusan kullum sai ta tuna Sadeeq,amma da zaran ta ɗaga wayar zata ƙirashi sai ta ga kamar Jabeer na tsaye a kanta haka zuciyarta zaita bugawa ba shiri take mayar da wayar maɓuyarta.
Yauma kamar kullum misalin karfe biyu na rana ya dawo gidan daga makaranta duk ya yi gaje gaje da chalk lamarinka da sabon shiga ga wasu takardu a hannunshi ga uban yunwar da ya kwaso haɗi da ƙishirwa da ranar da ake ƙwalawa ya haddasa mashi, randar dake tsakar gidan ya buɗe ya kwankwaɗi ruwa sosai sannan ya sa kai cikin palon bakinshi ɗauke da sallama ba bu kowa palon sai kular Inna dake tabbatar masa na abincin rana ne, ajiye tarkacen dake hannunsa ya yi akan one seater ya shiga bedroom ɗin da yau Maryama ta manta bata rufe ba kwance ya sameta saman gado ta yi ɗai ɗai abinta tana ta sharar baccinta peacefully, ya daɗe tsaye kanta yana ƙare mata kallo kafun ya fito a hankali dan kar ya tada ita, abincin dake palon tuwo da miyar ɗanyar kubewa ya ɗiba a plate ya zauna ya fara ci, yana tunanin mai zai sayawa Pretty ta ci,dan yasan bazata ci tuwo ba sai dai ta zauna da yunwa,...kasancewar ya yi sallar azahar a makaranta, wanka kawai ya shige bayan ya gama cin abincin ya fita da kwanukan,...Bai wani jima a bayin ba ya fito ya shafa mai sama sama ya fesa turare, duk abin da ya ke yi a hankali yake yi dan kar ta tashi, wani three quater ya sanya ba tare da yabi ta kan riga ba ya hau gadon haɗi da janyota jikinshi ya lumshe ido yana sauƙe nannauyar ajiyar zuciya,cikin bacci na jini jikin mutum ga mayataccen kamshinshi da ko a cikin mitum ɗari zan bambance nashi da ya cika min ƙofofin hanci.
Mutsu mutsun tashi na fara amma ya hanani damar hakan sai ma wani irin iska da hura min cikin kunne murya can kasa kasa ya ce, "bacci plssss".
Rikicewa na ƙara yi jin yanda yayi maganar da wani salo a muryarshi, buɗe baki nayi zan yi ihu dan gaba ɗaya baccin ya gudu sai luguden tsoro da ƙirjina ke yi, amma kamar yasan abin da zanyi ya yi saurin rufe bakina da tafin hannunshi, ya kuma ce wa, " Shhhhhit Bacci" shiru na yi ina zare ido ƙirjina na dukan tara tara.
A maimakon baccin da hamma jay ya furta sai na ji ya canza hanya,dan kuwa ɗan yatsanshi ɗaya ya ɗaura saman lebena bayan ya sake min baki ya fara zagaye lips ɗin a hankali da yatsarshi,a hankali na yake zagayewa idanunshi a lumshe, cikin lokaci kaɗan jikina ya fara amsan saƙonshi, da ga haka wasan ya sauya salo....
................
Siyama kwanaki takwas ta kwashe tana jinya a asibiti,an mata treatment sosai ciki harda haƙorin roba da ta nemi a sanya mata a inda haƙorinta ya fita, yanzu ma da take zaune gaban dressing morror ɗinta, takaici ne fal ranta sakamakon haƙorin da ta wangale baki take kallo a mirror ɗin . (Lallai za ki san ko ni waye Maryama,wato kinyi aurenki kinacan kina farin ciki a gidan ki ko?tabbas kin taro match) siyama dake kallon kanta a mirror ta faɗa kamar mahaukaciya...