KARFE DÜKKA KARFE NE

BABI NA SHA BAKWAI

by @maidambu41

KARFE DUKKA KARFE NE...!!!
{Zanen ƙaddarar Falilah}
BABI NA SHA BAKWAI

🌸 Assalamu Alaikum Yan'uwa Mata.

Kowace mace tana son ta ga kitchen ɗinta cikin tsari da kyau, tare da kayan zamani masu inganci. Amma abin da kan hana mutane shi ne tara kuɗin saye lokaci guda.

Shin tara kuɗin saye ne ke miki wahala?
Ko kuma idan kin tara sai wasu buƙatu su sa ki kashe su?

Ki kwantar da hankalinki, domin MA KITCHEN ta zo da mafita.

Mun buɗe Adashen Kayan Kitchen domin ki mallaki kayan da kike buri cikin sauƙi, ba tare da wahalar tara kuɗi lokaci guda ba.

✨ Abubuwan da za ki samu:
✅ Kayan kitchen na zamani masu inganci.
✅ Farashi mai sauƙi.
✅ Adashe mai sauƙi da kwanciyar hankali.
✅ Ana kai kaya zuwa duk inda kike.
✅ Biyan kuɗi a hankali cikin sauƙi.

Za a fara nan ba da jimawa ba, In shaa Allah.

📞 WhatsApp/Call: ***

📲 Shiga WhatsApp Group ɗinmu domin samun cikakken bayani da fara rajista:
***

🌹 Arha ta fi bashi, adashe kuma ta fi bashi kwanciyar hankali. Ki yi rajista tun da wuri, ki mallaki kitchen ɗin mafarkinki cikin sauƙi.

MA KITCHEN – Muna tare da ke har ki cika kitchen ɗinki da kayan da kike buri. 💚


A hankali nayi ta kallonshi kamar na sanshi, amma na manta inda na sanshi. “Barka!” Na tsinci kaina da gaishe shi Ina me dauke idanuna akanshi. “Mss liman barka dai yasu Twins?” Muryanshi ta dake ni sama da kome a rayuwata nasan muryan me yasa na kasa sanın waye a gabana, mikewa yayı tare da takowa gabana. Ya tsaya baya kadan nayi ya ce min. “Ni ne Barista Khalid Yobe da fatan kin ji labarin na samu Ya Man.” Ji nayi kofofin hancina sun toshe bakidaya naji ya bani wani kawo min wata irin iska mara dadi. Turo kofar office din aka yi abokiyar aikina ce Aunty Bisi.
“Barista nan ka shigo?” Jinjina mata kai yayı ya nufe ta, yana barın gabana na sake wata irin ajiyar zuciya kamar zan yi kuka why? Waye shi? Me yasa naji haka?

     Wadanan tambayiyon na kasa bawa kaina amsa, nayi na wuce kan tablet dina na zauna, na kasa hasala kome dole nayi ta kallon kofar office dina, har zuwa wani lokaci da aka buga kofar na bada izinin a shigo, murmushin kan fuskata ce ta kara fadada, Hamma Jamal, mikewa nayi tare da cewa. “Barka da zuwa Hamma Jamal.” Murmushi yayi tare da niman wuri ya zauna yana murmushi,  frij din office din na dauko mishi ruwa da cake na Leda da nake ajiyewa nace mishi.

     “Kayi hakuri ba wani Abu sai wannan.” Kafe ni yayi da idanunsa, ya gyara zamanshi yana murmushi. “Wannan man na gode sosai!” Ruwan ya sha, sannan ya ce min. “Na biya ta gidan na ga twins sun girma yaushe zaki kawo su yola?  Hajiya tana kewarsu.” Murmushi nayi
Mishi tare da cewa, “in sha Allah zan kawo su a sallah.” “Masha Allah!” Ya furta yana kallon office din. “Anan Ahmad ya rayu ko?” Gyada mishi kai nayi, ina jin kewarshi sosai, “Ayshatou ko zaki bani damar zama har abada?” Ya tambaye ni yana me kura min ido, jikina ne ya dauki rawa nace mishi. “Hamma Jamal kai fa Yayan Ahmadi ne!” “Muslunci bata hana ba, ba wai Ina bayan abinda kike da shi ba ne, Ina son aurenki ne.”  Shiru nayi kaina a sunkuye har ya gama maganarshi ban ce uffan ba, yana gama abinda ya kawo shi ya ajiye min mint na dollars ya saka kai ya fita a office din, tunda ya fita kuka ya kwace min, me yasa Ahmadi ya tafi ya bar ni. Da iya wannan kyautar na fahimci ba kudin da nake tarawa Yaran ne matsalar shi ba, amma taya zan kara tura kaina gidansu Ahmadi bayan ban sha ta dadi ba a baya, Ya Allah ka kawo min dauki.  Ina cikin wannan halin Bisi ta shigo ta ga ina kuka.

    “Mrs lamido!” Kallonta nayi da idanuna wanda suka yi jajjur,  na ce mata, “Sorry bari na duba miki!” Na mike ta dawo da ni tare da fadin. “No zauna kawai magana nake son dake!” Zama nayi Ina share idanuna. “Kin san dai ke ba Yarinya ba ce? Sannan kowa yana alfahari da aikinki, amma kin san me? Idanun mutane yana kanki, Musamman da aka san ke matar later Ahmad lamido ce, ban ce ki kasa tsayar da hankalinki, a yanzu ban San iya mazan da suke son mallakarki a cikin maaikanta nan ba, balle kuma mu kai ga waje, so zaki ga mutane Kala Kala amma idan da hali ki tsayar da mutum daya kada magana ya fara yawo a kanki. A lokacin da Ahmad yake raye kusan nice abokiyar hiransa.” Tana gama fadar haka ta mike tare da barın dakin,  tana fita ta bar min dakin na ji kamar na fashe da kuka Ahmad ya tafi ya barni da fita.

    Lokacin da na fita daga maaikanta, na nufi gida, da yake kai ni ake a dauko ni, sai da na isa gida ya ce min. “Hajiya baki lura da wata mota tana bin bayan mun ba ne?” Girgiza kai nayi ina shigewa çıkın gidan nan, Hamma Jamal na gani a gidan, da shi da Ya Bana suna ta hira sai Hajja Mama da take gefensu, “sannunku da gida.” Ahmadi ya taso da rarrafenshi da sauri na dauke shi ina rungume shi. “Ahmadina!” Na furta ina wuce parlor, na nufi dakin na ajiye shi na fara cire kayana sannan na bashi nono ya sha, shigowar Hajja Mama da batul yasa na cire Ahmadi na karbeta ina bata tare da shafa kanta. “Uwata maganin kukana. Sannu damo sarkin hakuri.” Na shafa kanta Ina kallon Hajja Mama.
  
 “Wan mijinki ya zo dağa yobe, ki sani babu wnada ya kai ki sanın dangin Ahmadi idan da zai dawo duniya sau dubu Wallahi ba ni zabin da ya wuce shi, wancan watan ma wani yaje gidan tun bayan da kika haihu maza ke zarya akan ki,  Falilah ki sani a yanzu ya kamata ki huta, dük mazan da suke safa da marwa akanki muyum daya ne zai iya rike Yaranki ba tare da ya damu da wani Abu ba,  amma zan barki ke da kanki ko nimo a cikin mazan da suke tare da ke, ina ta gayawa Allah matsalarki, dük da mazan da suke zagaye dake dukkansu alkhairi yake tatattare da su, amma ni nafi son ki samu Wanda zai rike yaranki da ke kanki.”

   Gyada Kai nayi, ina kallon Yarana, bayan fitarta na zurfaffa kaina da tunani, kamar nayi kuka, haka nayi shiru. Kiran sallah ya saka na mike na kira Jamila Yarinyar da take min renon Yaran, ta fita da suna shiga nayi wanka tare da alwala na gabatar da sallah, bayan na idar na gyara jikina na fito parlorn Ya Bana ne kawai, zama nayi muka kara gaisawa, shine baki fito kun gaisa da Jamal ba?falilah wanan bakin halin fa?” “Bai gaya maka ya same ni an office ba ne?”  Shiru yayı yana kallon yadda nake magana hankalina yana kan waya, “and so!” “Ni bana raayinsa, ni ba Matar gado ba ce da zaa ce don kani ya aure ni, sai lallai wa ya aure ni? Tsakani da Allah Hajja Mama a ina aka taba haka? Ya tafi ya nime wata mace ba dai ni ba, matarshi bata da mutunci maybe don na Mariah ya fito ne amma ni ba gado ba ce da zaa ce kowa sai ya kasa ni a rabonsa.”

    Zai kara magana Hajja Mama ta ce mishi, “Gaskiya ta gaya maka fa, ai ko musulunci bai hana ba alada zata shiga lamarin!” “Amma Hajja shi wanda kuke so ya samu zama a ranta ne?” Murmushi tayı ta ce mishi, “ina da yakinin ya samu kuma zai cigaba da haka.” Ganin yadda Hajja ta bi bayana ya fara fushi karshe bai kwana a gidan ba,

    Washe gari ya Kama jumaa, tunda na isa ake meeting har sai lokacin sallah muka fito aka gabatar da sallah tare da cin abinci, ni ba zan iya cin abinci team ba, office na koma. Ina zama aka turo kofar, Ya Nafi’u.

     “Kin San tun dazun nake jiranki?” Murmushi nayi ina fadin.”Daddy kai ne dağa sama haka?” Shigowa yayi na tura mishi abincin, sannan na mike na fara dauko mishi kayan ruwa na ajiye mishi. “Ya aikin?” “Alhamdulillahi” na fada mishi Ina kallon yadda yake cin abincin. “Yunwa kake ji ne haka?” “Aa dük abinda zaki bani ai yana da daraja da kima ko bakya son Naci ne?” Ya tsame hannunsa, girgiza kai nayi ina fadin. “Ko daya daddy!”
          “Ok!” 
Ya cigaba da cin abincin yana d’ago kai ya kalle ni lokaci zuwa lokaci, “barista Khalid ya same ni da maganarki Falilah ya samu Ya Man ya ce sai dai ya tuntube ki, to ya sake zuwa ta hannuna. Ga wan Ahmad shima ya zo. Kına da lokaci tında har yanzu baki yaye Yaranki ba, ki nutsu akan abinda zai dawwamar da rayuwar ki a gidan aurenki, kada ki bi son zuciya.”

         “Na bawa Hamma Jamal hakuri ta hannun Yaya Bana, shi kuma barışta yazo har nan amma bai ce min kome ba!”
“Ok ki cigaba da kame kanki, kaddaranki Allah yana sane da ke.”
“Ya jikin Maam?”
Murmushin karfi hali yayı min ya ce min, “Da sauki.” 
“Allah ya bata lafiya!” Na fada ina janye idanuna akanshi saboda wnai irin Abu da nake hangowa a cikin idanunsa a kaina, “Falilah baki da matsala ko?” Murmushi nayi mishi na ce .”Ba matsala Daddy!” “Ok” ya fada yana mikewa zai wanke hannunsa, ban dakin office din na nuna kishiya shiga ya wanke hannun, sannan ya fito, yana göğe hannunsa da tissue,  “Zan tafi Yan matan Ya Man!” Murmushi nayi na biyo shi muka cigaba da tafiya yana ja na da wasa Ina murmushi har muka İsa inda motar da ta kawo shi take, kallona yayı yana fadi. “Wurin ki Jamal ya zo I think gashi can!” Na juya ina kallonshi shima ya fito daga motar, ban san me yasa yake da kwarin gwiwa haka, yana zuwa ya mikawa Ya Nafi’u hannu. “Ka shigo Abuja kenan?” Murmushi ya Nafi’u ya mishi yana fadin. “Na zo ganin auta ce.” “Ok nima gani na zo naji da bakinta me take nufi da ni?” Dauke kai nayi na ce mishi, “ban shirya aurenka ba, bana da raayin aurenka!” Sannan na juya ina kallon Ya Nafi’u da idanunsa suke cike da salama tare da aminci me yawa ya Lumshe idanunsa da suke wani oil ya bude a kaina, ya ce min. “Auta ba a gayawa mutum haka kai tsaye.”
“Daddy taya zan auri Ahmadi na koma na auri Dan uwansa? Daddy Ahmadi naso ba wani cikin kaddaran gidansu ba, idan don Yaran ne ko yau ha yaye su zai iya dauka kayanshi.”

     A hankali Jamal ya juya tare da cewa. “Ba zan mallake ki ta karfi ba, amma ina gaya miki gaskiya.”
“Kayi hakuri matar ka zata iya yin fiye da abinda Maria tayı, matanku zasu iya kome akan kishi, ga Hajiyarku har abada bata sona, kuma ba zata taba sona ba, so kayi hakuri ni yanzu bana son abinda zai hana ni barci.”
“Idan babu matata zaki zauna da ni?”
“Mafi girman kuskuren da zaka aikata ka sake matarka saboda ni, ni dai ban da raayin auren wani çıkınku.”
   Na fada Ina dauke kai na kamar ban San yadda ya shiga mamaki ba, bude mota Ya Nafi’u yayı ya ce min, “ki koma ciki, Akwai sako na bawa masinjanki ya baki” na juya tare da barınsu a wurin, lokacin da na isa office ban San da mutum a ciki ba, sai da na shiga naji muryanshi a bayana.
“Yana da kyau ki tsayar da daya çıkın maza ukun da muka fara zarya akanki? Domin ba zan iya jure bin mace kamar wani mara aji ba.”

    Wani irin juyawa nayi ina kallonshi, duk wannan Maganar da yake bai d’ago kai ba, domin wata rigar hook ya saka, wannan rigar ya Tuna min shekarun da na fasa motar mr Aljani……….
*Wannan satin muna da biki ga mai gidana da bai da lafiya zaku min uzuri don Allah*