Hs 5
by @legendspen
*HASASHEN SOYAYYA💅*
_Imagination of love_
_Page 05_
"Dum Dum" yaji bugun zuciyarshi na ƙaruwa da sauri-sauri, hannu yasa ya dafe ƙirji tare da rufe ido.
Da sauri Anas ya ce: "Senate are you okay?."
Bai kai ga bashi amsa ba Muryar Momi tayi sallama suka shigo cikin falon Batool na biye da ita.
Da sauri ya mike yana kallon ta yayin da yaji bugun zuciyarsa ya samu nutsu, wani sanyayyen murmushi ne ya kufce masa.
Momi ta dubi Bhatool da take tsaye ta ce. " Daughter ki zauna mana."
Murmushi ta mata tana zama a k'asa.
" Ah haba ki zauna a sama mana k'asan akwai sanyi ai."
Tashi tayi tana zama a kan kujera mai zaman mutum uku dan shine kusa da ita.
Anas ya dube inda yake yaga ita yake kallo, taba shi yayi ya buge masa hannu, murya k'asa k'asa kamar wanda ya buya baya son a gan shi ya furta. " Anas leave me Abeg!."
Momi na fadin. " Ina zuwa."
Gurin su ta iso tana kallon shi cike da so da kauna, kafin ta ce. " Son kaje ku gaisa."
Girgiza kai yayi. " Ina tsoro gaskiya."
" Har yaushe tsoron zai tsaya? Anas ka raka shi."
" Ok Momi." Ya kama hannu Senate yaja zuwa tsakiyar falon.
Tana zaune ta aro nutsuwar dole ta sawa kanta, jin kamar tsayuwar mutane yasa ta dago kanta a hankali ta zuba masa sexy eyes dinta, ji tayi kamar ta taba ganin fuskar nan a wani guri.
Da sauri ya janye idanunsa daga gareta yana matse hannu da karfi, Anas na sakar mata murmushi.
" Sannu fa."
" Yawwa ina wunin ku."
" lafiya, ya gida?."
" Alhamdulillah."
Zama suka yi a kujera mai facing nata, duk motsin da zata yi akan idanunsa, sai ta jita duk a takure, can Anas ya katsai shurun da fadin.
" Ya sunanki Sis?."
" Bhatool."
"Wow" ya fada a ransa yana lumshe ido kafin ya bude ya zuba mata, karaf suka had'a ido, wani kwarjini ta gani a tattare dashi hakan yasa ta sunkuyar da kai.
" Wani school kike ne?."
" YSU." Ta fad'a a dakile dan ta fara gajiya da tambayar.
" Ya ban sanki ba a school din? Wani department?."
" ENT."
" Ok bana daukar ku shiyasa, iya yan Anatomy nake dauka."
" Ayya."
" Ni baki sanni bane?."
Daga kai tayi ta gan shi ta girgiza kai alamu bata gane shi ba.
Hararansa Senate yayi jin yana zakewa dayawa, dariya kawai yayi bai sake cewa komai ba.
Momi ta fito hannunta rike da leda fari.
" Daughter kinyi shuru, ga yayunki bakwa hira dasu."
Sunkuyar da kai kawai tayi tana wasa da yatsun hannunta tana murmushi da iyakacinsa fuska.
Mika mata ledan Momi tayi ta karba tana mikewa ta ajiye bowl din hannunta ta ce. " Mun gode sai anjima." Ta juya zata fita.
Da sauri Senate ya dubi Momi kamar zai yi kuka yana girgiza mata kai, ya mike da wuri yana kallonta har ta fita a falon, zuciyarsa ce ta harba da karfi yasa hannun yana dafewa, Momi tayi saurin isa gurin shi.
" Ka ajiye tsoron nan ka fuskanci soyayyarka, if not you'll loose her."
" A.a Momi, ki ce ta dawo."
~~~~~Bayan ta fito daga gidan ne ta shiga gidan Yaya Karima tana mita.
" Yaya Karima ni fa bana son takura, haba."
Fitowa Yaya Karima tayi daga d'aki.
" Yanzu kuma me aka miki?."
" Tun dazu kawai jiran sak'o, ta kawo da wuri shine ta ajiye ni ta tafi ciki, tabarni da yaronta mai surutu, amma Yaya naga wani kyakkyawa fa."
Zama Yaya Karima tayi tana ganin yanda take wani lumshe ido tana juyawa.
" Ke!! Kina lafiya kuwa?."
" Hmm Yaya kenan bazaki gane ba, guy din ya hadu over, sai dai har na tafi ko magana bai yi ba, sai na gefensa da yake over sabi ya dame ni da surutu."
Zuba mata ido kawai Yaya Karima tayi tana ganinta.
" Yaya ina miki magana ma kin mantar dani! Uhm to nikam nama tafi zanje na siya anko, dan yanzu ko bazaku min ba Uncle zai min." Ta dauki jakarta ta fice daga gidan.
A waje takira wayar Suhaima tasa taturamata ankon dan so take taje kasuwa da kanta.
Ta dade tsaye a bakin titin amma ba machine, dan dama unguwar ba machine ake samu ba saboda yayi nisa da gari.
Tana tsaye wata baƙar mota ta tsaya a gabanta, sauke glass ɗin motar akayi, Anas ne da kuma Senate, ɗan haɗe rai tayi kafin Anas ɗin yayi magana.
" Ah Bhatool ina zuwa haka?."
" Bayan tasha zanje."
" Ok shiga mu kai ki ko?."
" Dama kun bari ai zan samu machine."
Bata rai Senate yayi yana mintsinin Anas.
" Ah ah baza ' ayi haka ba, shiga muje."
Madadin ta shiga ta gurin Anas sai ta zagaya ta shiga ta bayan Senate, wani sanyi yaji ya mamaye shi lokacin da ta shiga, sanan yaji bugun zuciyarshi yadaidaita tsaf. jan mota yayi suka nufi hanyar bayan tasha.
" Yau ba makaranta ne?."
" Bazan je bane, yau zan huta." Ta fada a dakile dan haushin Anas ta fara ji.
Bakin Senate na rawa ya furta. " Kahh-rage music É—inn.. nan."
' Dama yana magana kenan? Na dauka ai kurma ne.' tafaÉ—a aranta afili kuma murmushi kawai tayi domin muryarshi kaÉ—ai abunso ce.
Daganan babu wanda yaƙara cewa komai harsuka isa bayan tasha.
Anas ne yace: " A ina za ki sauk'a?."
" A shagon Alhaji Mala."
" Ok." Yayi parking kusa da shagon, ta bud'e ƙofa tayi tafice Senate ne yabi bayanta ya fita, da mamaki Ansa ya fito yana kallon Senate.
" Senate where?."
ÆŠame fuska yayi yana kallon Anas É—in, nufan shagon tayi yana biye da ita Anas ma ya mara musu baya.
Ankon Suhaima tanuna hoton,Nan aka ciro mata su guda uku.
" Nawa ne?."
" Ya kama 76k."
Bud'e jakarta tayi da niyar bada kudin Senate ya miƙa ATM dinsa da sauri, bin hannunsa da ido tayi.
Cire kudinsu suka yi suka mata package nashi a leda, ya dauka mata, murmushi ta sakar masa tare da fadin. " Thanks."
" You're welcome."
' Dai-dai ne, ai kuwa shagon takalma zamu wuce da gyelle idan yaso har da jaka ni ai gaba takaini gobarar titi.' Ta fada a ranta a fili kuwa sai murmushi take masa.
Bud'e baya yayi ya saka mata, Anas da ya zama dan kallo ya ce. " Saura ina?."
" Ina ta baku wahala fa da kun barshi ma kun tafi sabida daganan inaso naje wani shago ne." Ta karashe tana dan sosa kai.
" Don't take it some bother."
Anas ɗin yasake faɗa, shidai Senate sai binta abaya amma baya cewa ko ƙala.
" Thanks." TafaÉ—a. Kafin ta nufi shagon Alhaji Nuhu Tata suna biye da ita, duk da yana tsoro amma hakan bai hana binta ba sai dai baya bari su hada ido.
" Veils nakeso da shoes and handbag."
" Wani colours?."
Juyawa tayi ta kalle shi. " Please key din motar zan dauko kayan."
Mikawa Anas yayi bai yi magana ba kuma kansa a sunkuye, fita Anas yayi dan dauko kayan, yayin da shi kuma ya isa kusa da ita dan ganin wani yana mata magana hakan kuma ba karamin taba zuciyarsa yayi ba.
Ganin ya tsaya kusa da ita ne yasa ta kalle shi.
Y'an matan shagon sai ganinsa suke dan duk inda Senate ya shiga abun kallo ne, namiji iya namiji ga kyau ga hali ga k'asaita uwa uba farin jini.
Dawowa Anas yayi yana bata kayan, cirowa tayi tana kallon colour kafin ta kalli pink din jaka da takalmi ta ce a kawo, haka ma taga maroon da brown, gyalle kuma ta dauki shentili baki da brown.
Lissafa kudin kayan suka yi aka ce. " 64k."
Nan ma kafin ta ciro kudi Senate ya bada ATM an cire.
Tsaya kallon shi tayi a ranta tana fadin. ' Akwai Capacity ba laifi, shima kila Abba ya basa amanar nawa ne, amma shi sai yanzu ya bayyana.'
Hada kayan suka yi daya daga cikin yaran shagon ya dauko musu, fita suka yi suna jerawa tana ta danne-dannen waya, aka saka kayan a baya.
" Nagode sosai fa Allah ya biya."
Kallam da ya fara shiga zuciyarsa kenan ya zauna.
" Bansan ina zaku yi ba na katsai muku tafiya."
" Don't worry, yanzu ke ina za kiyi?."
" Gida zan tafi."
" Ok shiga mu kai ki."
Shiga tayi kafin suma suka shiga.
" Wani unguwa?."
" Nyan'ya."
Hanyar suka nufa tana musu kwatance har suka isa.
Fitowa tayi tana bud'e bayan ta fito da kayanta, Senate ya fito yana jin zuciyarsa na harbawa tamkar abun da yake buk'ata yana nisa da shi.
Jin an zuba mata ido yasa ta ce. " Nagode sosai sai anjima."
" Uhmm yaushe za ki dawo gidan Barrister?."
" Bani da lokaci kawai duk sanda naji inason zuwa nake."
" Ok sai anjima."
" Nagode." Da haka ta shige ciki.
" Senate shiga muje."
" A nan zan zauna."
" Lover boy, muje gobe ma zaka ganta ai."
Numfashi ya sauke kafin ya shigo motar.
~~~~~~ Tana shiga Main falon ta tarar da Abdulwahab da Mama suna zaune.
" Rayuwa dadi, dadi! Rayuwa dadi! Wayyo dadi! Wayyo dadi! I'm so happy! I'm so happy, dama haka rayuwa take idan wani yakika wani zai sonka, y'an uwana sun kasa rike amanar da Abbana ya basu yayin da wasu bare suke rike amanar hannun biyu."
" Ke! Waya baki kudi kika siya kayakin nan."
" Mama kenan! Kyautata wacce ba'a tsammani tana zuwa daga masoyi ne wanda yassan soyayya kuma ya damu da mai son shi."
" Tambayar ki fa ake?."
" Abdulwahab ka min shuru a nan, wait tukun ni sa'arka ce ma."
" Lallai yau Bhatool ta samu duniya."
" Ai da kaki bani kudin Allah ya turo wanda ya bani." Ta fada a asalin yanayinta na isa da izza.
" To waye ya baki?." Cewar Mama tana zuba mata ido.
" Mijin Yaya Karima da kuma wani Kyakkyawan saurayi."
" Waye ne shi din?."
" Bazaku gane ba." Daga haka ta tattare kayakinta ta nufi daki. " Ni yanzu ba mutumiyar banza bace da kudina a aljuhu.....
it's free book, all I want is follow my page, and discuss about the book, pls.
Na gode