Hs 6
by @legendspen
*HASASHEN SOYAYYA💅*
_Imagination of love_
_Page 06_
" Bazaku gane ba." Daga haka ta tattare kayakinta ta nufi daki. " Ni yanzu ba mutumiyar banza bace da kudina a aljuhu."
" Abdul yarinyar nan fa sai an dakatar da ita, rawan kanta ya fara yawa."
" Hmmm Mama yanzu kana magana zata kwanta ta fara burgima tana fadin ita sam ba'a kyauta mata, daga karshe ma ta ce amanar da abbana ya baku baku rike ba."
" Haka za'a zuba mata ido?."
" Mama zata daina fa, komai lokaci ne." Ya daura da fadin. " Sai dai wani abun da yake burgeni da ita bata kula maza bare har ta bari a bata mata suna, iya iskanci ta dai a gida ne da kuma gurin kawayenta, sai Yaya Karima kuma."
" To! Allah ya shiryar da ita."
" Ameen."
Akan gado ta zuba kayan tana video din su, WhatsApp group nasu na iya yen Team nasu ta shiga tayi posting tana caption da *bayan ni sai wacce? Saura dinki kawai ya rage min guys*
Nan da nan Amrah ta gani.
" Kina wuta ina binki da fetur, yarinyar nan akwai capacity ba laifi."
Jannah da itama yanzu ta hau online tagani, voice ta danna da wuri.
" This gurl Wallahi kina bamu a jikinmu, da nayi calculation over a 150k fa."
" Dey play yara, remain dinki shi ma zai kai 50 ko?." Ta tura tana danna musu emojin dariya.
Suhaima ta danna Video call, nan kowa ta shiga aka fara hira, sai hura mata kai suke chan da hiran nasu yayi nisa ne ta furta.
" Ina zamu kai dinki ne? Coz inaso a cire ni sosai a samu a fitar da shape kamar zasu fito a kayan."
" Ke!!! Ki bari kawai gobe a school muyi maganar." Cewar Suhaima tana kashe kiran.
"Dama naje wajen É—inki, sunbiya kudin. Kokuma karson zuciyata yayi yawa."
Tafada a ranta bayan sun kashe wayar.Cilli tayi da wayar ta nufi toilet.
~~~~~~~~~~ Red Bricks
Yana kwance a kan gadonsa ya rungumi filo idanunsa a rufe, yayin da Anas ke zaune kusa da shi yana fama magana.
" Senate yanzu ko maganar kirki ka gagara yiwa yarinyar nan, haka za'a yi soyayyar."
Mantar dashi yayi ya sake rungume filon a kirjinsa yana lumshe ido.
" Senate are you okay kuwa?."
" Anas barni, ka hanani kallonta me kyau sai damuna kake."
" Wait a ina kake kallonta?, don't tell me that you're imagining her?."
Bar masa kan gadon yayi ya dawo kan kujera dake tsakin ya dunkulu a ciki yana rufe ido, dariya Anas ya saka yana kallon shi tare da ficewa daga dakin.
Momi da fitowarta daga kitchen ta kalle shi ta ce. " Are you okay? Laughing for?."
" Momi Senate mana! He's gone crazy, wai fa imagination nata yake tun da muka dawo."
" To why not yaje ya same ta."
" Momi yanzu zai fara I'm scared." Ya karashe yana kwaikwayon yanda Senate yake.
Dariya kawai Momi tayi ta nufi dakin nasa, Anas kuma ya tafi gida dan dare yayi.
~~~~~~~Washe gari
Tun 7:35 ta gama shirinta dan zuwa makaranta, fitowa tayi hannunta rike da wayanta ta rataya handbag dinta.
Wajen daining ta nufa tana kallon su kafin taja kujera ta zauna.
" Mama ina kwana?."
" Lafiya! har kin shirya?."
Gyada mata kai tayi.
" Kai baka iya gaisuwa bane? Ko baka san akwai manya a nan ba?."
" Bhatool da alamu daga jiya zuwa yau akwai kwayar da kike hambuda ko?."
" Bana son raini irin naku na yaran zamani, yanzu kai Abdulwahab zaka dubi cikin idona ka fadamin zancen banzan nan tsabar raini da fitsara."
" Yau din kuma Fati? Da alamu bakya buk'atar komai a gurin shi ko?."
Mama tafaɗa ganin yanda ta zaƙe sai rufe ido take wai ita babba. Tashi ma tayi ta dauko wayarta da jakarta ta fice bata kula su ba, murmushi kawai Abdulwahab yayi Mama ta bita da addu'a.
Tana fita ta samu machine ta hau, boss stop ya kaita ta bashi kudinta kafin ta hau wani machine zuwa Makaranta.
Direct gurin garden ta isa ta zauna akan resting bench, wayanta ya fara ruri ta dauka.
" Rich kid ban ganki ba."
" Ina resting bench." TafaÉ—a tare da kashe wayar.
Isowa gurin ta su Amrah sukayi suna fadin.
" Sai da ke yar kuna bakin wake, tamu ba irin tasu bane."
Dariya suka kwashe da shi kafin ko wacce ta samu guri ta zauna sannan Suhaima na fadin.
" I can't believe wai har kin gama siyan komai na auren, remain dinki fa."
Gyara zama tayi tana kallon su daya bayan daya.
" Ba abun surprise bane fa, kudi ne zai yi magana."
Shigowa haraban Makarantar yayi tare da yin parking ya nufi gurin garden, bugun zuciyarsa ne ta fara sauyawa ta soma bugu da sauri sauri a hankali ya furta. "Bata shiga ajin ba kenan."
Inda ya saba zama ya zauna yana ciro wayansa ya soma dannawa.
" Ni fa yanzu bani da damuwar komai, yau kuma sai 2-4 muke da shi, so ina gamawa zan ware gida kawai, dan wannan yaron sai ya bani kudin dinki ban isa ba bazan kashe kudina ba kuma."
Dariya suka yi Jannah na cewa." Kina son kudinsa kuma kina ce masa yaro Bhatool ke fa sai shiriyar Allah."
" To ai Yaron ne tun da kam na girme shi, a kudi ne kawai ya girme ni, kuma idan bai bani kudin nan ba yau sai Hizba."
Taba ta Amrah ta soma, buge hannunta tayi. " What dalla kina mintsini na."
" Dalla ke baki iya gulma ba, ga can Guy din nan fa yau ma ya sake zuwa."
Idan ta nuna musu suka kallo Jannah na dariya k'asa-k'asa. " I think guy din nan yana son daya daga cikin mu ne."
" Idan ma daya daga cikin ku yake so ai is not forbidden ko?."
Shiru ita dai Bhatool ta yi tana zuba masa ido ko giftawa bata yi Jannah na dariya da fadin.
" Wata fa ta fola."
" No ba falawa nayi ba fadawa nayi gaba daya."
Murmushi ya yi yana gyara zaman shi tare da kiran Salman.
" How far?."
" I'm waiting for you fa." Sanyayyar muryansa ya daki dodan kunnen ta.
Tashi tayi tsaye ta kalle su. " Guy din nan ya kamata yau na tambaye shi me yake zuwa yi."
" Bhatool dawo ki zauna ko kin manta school ne? Kowa kan iya zuwa yayi harkan gaban shi, mu da kullum muke zama a nan an taba yi mana magana ne, let him."
" Maybe ta fada love ne."
Jannah tafaɗa tana dariya ƙasa ƙasa. "Jannah daily talk naki kenan Love."
Cigaba da hiran su suka yi amma hankalinta ya dawo kansa, duk ta gagara nutsuwa kawai so take taje taji dalilin bibiyar ta din da yake, dan ta fara ganewa bibiyarta yakeh.
"Ke ban iya barin bala'i yayi sleep ba, ko barni naje."
Bata jira amsarsu ba tatashi. Jiyayi zuciyar ta buga da wani mugun ƙarfi, da sauri ya juyo idanunsa suka faɗa cikin nata.
"Hey."
Tafaɗa tana zama, jikinshi ne yafara rawa ƙafafunshi na ƙakaɗawa, amma ya ƙureta da idanu.
"Senate!!." tafaɗa sakamakon jiya taji ankira shi da haka, wani sanyi yaji acikin zuciyarshi gaba ɗaya a rayuwarshi baitaɓa jin wani yakira sunanshi dai-dai ba kamar haka ba.
"Yeyes." YafaÉ—a tare da sauke ajiyar zuciya kamar yau yafara magana a rayuwarshi.
"Kaine kenan, anan school É—in make?."
Girgiza kai yayi alamun "A'ah", sai a lokacin ta tuna cewar baya magana.
"Ko Anas kake jira?."
"A'ah, Eh." YafaÉ—a duka da sauri, murmushi tayi sanan tace.
"Okay nagode faa."
"Dame?." yafaÉ—a yana kallonta ciki da mamakin yanda yakejin shi complete kaman yasamu duk abinda yakeso a rayuwa.
"Jiya mana ko kamanta?."
"A'ah wanan baby komai."
"Tom zantafi." Tafaɗa tare da tashi ta koma cikin ƙawayenta. Dai dai lokacin da Salman yazauna yana faɗin.
"So my man is now fall in love."
Girgiza kai Senate yayi sanan yace "No."
Karfe goma cif ya tashi ya bar Makarantar.
Juyawa tayi dan ganin ko yana nan taga wayam, numfashi ta sauke kafin ta ce. " Muje capteria."