ALWASHI 2

43

by @rufaidaumar

ALWASHI 

   68


Fareed ya kai duba ga Areef a sadda suka fito don bai wa Mama Kubra wuri su yi hira da mijinta. 

"Allah Sarki, matarnan ta ban tausayi sosai. Ashe ba ta da cikakkiyar lafiyar ƙafa ma. Allah kaɗai ya san wahalar da suka sha a baya kafin haɗuwa da danginsu tunda na ji Daddy Adam ya ce kamar ita ma ba ta san inda za ta same su ba, ba ta taɓa zuwa Maiduguri ba."

"Uhm, hakane. Abin da ya fi tsaya min a rai yanzu, gani nayi ba ta huce ba, ba ta yafe min ba. Sannan ina son sanin labarin Sameera, babu wanda na ji ya ambace ta." 

"Lokaci ya yi da zamu tambaya, ka lura, Kowa ya san cewa Laila ka aura ba Sameera ba idan ka ɗauke mutanenmu na can Katsina da suke ganin sunayen biyu duka na Sameerar ce. Don haka ya dace ka tambaya."

Areef ya yi shiru sai dai ya gamsu da abin da Fareed din ya ce. Sun jima sosai kafin Fareed ya ce ya dace su tafi tunda jirgin ƙarfe takwas na dare zasu bi zuwa Kano. Mama dai ba za ta gaji da waya da Mijinta ba. Idan ma wani abu ne suka yanke shawarar bai wa Daddy Adam lambar Mama din. 

Da wannan suka koma ciki da sallama. 

Mama ta ɗan katse zancen da take yi ta amsa sallamarsu, yanayin fuskarta ya sa su kallon juna. Gaba ɗaya ta sauya ba kamar murmushinta na farko ba da ya fi kama da na yaƙe. Wannan karon murmushi ne na zallar ƙauna da farin ciki. 

   "Na barku da zaman jira ko?"

Areef ya yi murmushi har ransa ya ji sanyi. 

A gefenta kuwa amsawa Daddy Adam take cewa eh su Areef ne suka shigo. Ko me ya ce, sai ta yi murmushi kawai. Can kuma ta ce. 

"Zai bani lambar wayarka ai."

Kamar ba zasu yi sallama ba, haka ta miƙawa Areef wayar. Koda ya amsa, Daddy Adam godiya da sa albarka yake masa, ya ƙara da neman alfarmar a ba Mama lambar don su dinga gaisawa ta waya. 

"In sha Allahu Daddy. Za'a yi hakan." 

Amsar da Areef ya ba sa kenan. Da wannan suka yi sallama, a take kuma ya karɓi wayar Mama ya sakamata lambar Daddy Adam ya miƙa mata. Ta karɓa da murmushi. 

"Nagode ƙwarai Areef, nagode nagode. Baki ba zai iya misalta irin farin cikin da ka saka ni ciki ba. Har a yanzu ji nake tamkar mafarki nake yi da zan farka kowane lokaci. Allah ya yi maku albarka, komai da ya faru kuma ina mai tabbatar maka ya wuce Areef. Na yafemaka, ina kuma roƙonka don Allah ka gyara tsarin rayuwarka. Ka ƙara sanya Allah a ranka. Duniyar nan ko ba ta ƙare da kai ba, za ka tafi ka bar ta dole. Zina babu abin da take haifarwa sai tarin nadama. Allah ya ƙara shiryamana ku, ya zaunar da ku lafiya da iyalinka. Ita kuma Sameera Allah ya jaddada rahma gareta, ya sa aljanna ce makomarta."

A razane suka dubi Mama, hankali a tashe da kuma rawar murya Areef ya ce. 

"Mama, Sameera ta rasu?"

Ta ɗan yi cak tana kallonsa, bai san cewa Sameera ta rasu ba ko kuwa dai tsabar yanda nasihar ta shige sa ne? Laila ba ta sanar da shi mutuwar ƴar uwarta ba? Kan Mama ya yi mugun ƙullewa. Ta nisa ta ce. 

"Sameera ta rasu mana har ta kusan cika shekara biyu da rasuwa. Ba ku sani ba?"

Ta faɗi tana rarraba idanu tsakaninsa da Fareed din wanda shi kansa ya yi turus. Areef dafe kai ya yi yana ambaton 'Innalillahi.' har zuwa ƙarshenta. Idanunsa suka kaɗa, ƙirjinsa na wani bugu da sauri ga wani ɗaci da yake ji a maƙoshinsa. Sameera ta rasu? Dama Sameera ba ta duniya? Kenan dalilin Laila na jin zafinsa kenan? Shekarun da Mama ta lissafa ai ya yi daidai da sadda al'amarin ya afku. 

Mama ta kasa gane yanayin da suka shiga, ta yi shiru da ta ji Fareed ya amsa mata da cewa ba su da masaniya. Areef dai ya kasa magana ma baki ɗaya. Ganin yanayin Areef sai ta ji bakinta ya yi mugun nauyi, ta kasa furta masa batun Haidar. 

Suka amsa addu'ar da Fareed ya yi na nemarwa Sameera rahmar Allah da 'amin.'

"Mama ni ne silar rasuwarta ko?"

Ya jefawa Mama tambayar da wani irin raunin murya. Hawayensa tuni suka sauko saman ƙunci. Mama ta ji tausayinsa ya kamata, ta daure ta haɗiyi miyau gami da girgiza kai lokaci guda tana kawar da idanunta saman fuskarsa. 

"Ai Areef babu wanda ya isa ya tsallake wa'adin mutuwarsa. Sameera lokacin mutuwarta ne kawai ya yi. Koda dalili ko babu, to babu wani abu da zai hana ta komawa ga Mahaliccinta. Don haka addu'a kawai take buƙata tunda ita kam ta dace in sha Allah. Kuma wani abu da ba ka sani ba shi ne, Sameera babu wanda ta riƙa a rai tsakaninka da iyayenka, ta saka a kai ƙaddararta ce."

Duk da jin wannan bai sa Areef ya ji sauƙin abin da yake ji ba, shi kansa Fareed gaba ɗaya jikinsa ne ya yi sanyi da batun mutuwar Sameera. Har suka bar gidan jikin kowannensu babu laka. A ɓangaren Mama, tunanin meke gudana a kwakwalwar Laila kawai take. Za ta so sanar da ita mahaifinta na raye sai dai a dole ta zaɓi yin shirun bisa dalilin Adam din da yace ta yi na ɗan lokaci kaɗan, ya sanar da ita akwai manyan dalilan da ya sa hakan. Da wannan ta bar batun a ranta har su Areef suka tafi bayan sallar Magriba. 

Ga Areef kuwa, tunanin me ya kashe Sameera kawai yake? Kenan silar fyaɗen da ya yi mata ne ko kuwa? Yayin da shi ma Fareed tunaninsa ya tafi can ɓangaren. 

Koda suka shiga jirgi zancen da suke kenan. 

"Fareed I'm lost, na rasa ma tunanin da ya dace na yi a wannan gaɓa. Laila tana da ƴancin ɗaukar kowane irin mataki a kaina idan har ni Areef sanadina ta rasa twin sistern ta. I deserve to be punished."

Girgiza masa kai Fareed ya yi, 

"Ba laifinka ba ne Areef. Ai ka ji me Mama ta ce ko? To ka saka a rai ko mene ne, it wasn't your fault please. Lokacin mutuwarta ne ya yi, kuma da bakinka ka ji Mama ta ce sun yafemaka komai. Don Allah kar ka bari wannan ya zame maka wani sabon shafi na damuwa. Ka godewa Allah ma iyayenta na raye da za ka dube su ka nemi gafararsu, za kuma ka yi musu wata kyautatawa da za su ji daɗinta har su sanyamaka albarka. In sha Allahu nan gaba farin cikin da za ka sanya iyayenta ciki, sai ya ninka damuwar da abin da ya faru ya haifar musu."

Areef ya jinjina kai. 

"Hakane, sai dai har yanzu kaina yana matuƙar ɗaurewa kan incident din Fareed, har yanzu na kasa warware ta inda aka haihu a ragaya. Na yi har na gaji, na fawwalawa Allah. Ka fi kowa sanin da ace ina aikata abin da suke zargina a kai, toh kai ne farkon wanda za ka yi shaidar hakan kafin kowa a duniya. Ba ka ji nasihar da Mama ke min ba? Shiriya take roƙa min fa, har tana min nasihar na ji tsoron Allah. Duka akan laifin da na kasa tuna yanda lamarin ya afku, a kai na samu mummunan shaida a wurinsu. Shaidar da idan ba Allah ne ya wanke ni daga wannan zargen da aka yi na faɗa ba, to fa babu ta yanda za'a yi ya gogu."

Ajiyar zuciya Fareed ya saki. 

"Ni kasan mene ne target dina ne idan Allah ya sa muka yi kiciɓus da Sameera? Kawai tambaya zan mata na yanda aka yi ta tsinci kanta a ɗakinka. Shi ne kaɗai ke ɗaure min kai." 

Shiru ya ratsa su, Areef kansa ya sani ba zai iya tuna komai ba. Wasu tambayoyin Laila ce kaɗai za ta amsa musu, amma ya sani ba zai ji komai daga bakinta a yanzu ba. Babu wani abu da za ta faɗamasa a yanda ta ƙullace shi ta kuma tsane sa. Tsana mai tsanani. 

 Kawai ya runtse idanu ya jingina kai jikin kujerar jirgin, bai ƙara magana ba, Fareed ma bai ƙara tada zancen ba har jirginsu ya sauka a filin tashin jirage na birnin Kano. 

 Daren dai bacci ɓarawo ne kawai ya ɗauki Areef a ɗakin hotel ɗin da suka kama. Zuciyarsa cike fal da tunanin marigayiya Sameera.

 ***
 Washegari da asuba suka kama hanyar Katsina don a ranar ma suna da tarin ayyuka shaƙe a ofis din nasu. 

 Koda suka isa Katsina, kai tsaye ofis suka zarce. Areef ji ya yi zai fi samun sukuni idan aiki ya ɗauke hankalinsa akan dai ya je gida zaman tunani. 

 Don haka wannan ta sa koda aka tashi har Abba ya tafi gida bai bari sun haɗu ba. Gaba ɗaya jikinsa ya yi mugun sanyi, komai kawai yana yi ne amma babu wani kuzari tattare da shi. Ƙulle kansa ya yi a ofis har kowa ya watse. Bai tashi barin Ofis din ba sai gabanin Magriba, tuni an soma kiraye-kirayen sallah, koda ya fito dama bai tsammaci ganin kowa ba. Don haka kai tsaye wurin motarsa da ta riga shi isowa ofis din wanda direban gidansu ya kawomasa ya nufa, ɗaya daga cikin masu gadin kamfanin na ganinsa ya ƙaraso da mamaki. 

 "Ah, Yallaɓai ai na ɗauka ko tare da ɗan uwan naka ka tafi. Ashe kana ciki."

 Ɗan murmushin yaƙe ya yi. 

 "Ina ciki Malam Hadi, ashe ba ka wuce ba kai ma."

"Eh nima yanzu zan tafi, dama Alaramma nake jira su ƙaraso su karɓe ni."

Areef ya jinjina kai, hannu ya sanya a aljihu ya fiddo dubu biyu ya miƙa masa. Aikuwa ya dinga godiyar nuna jin daɗi. 

Daga haka ya shige motarsa ya yi fice. Tun shigarsa ya kula windunan motar ba a rufe su dakyau ba, sauro duk ya shigo, don haka kawai sai ya zuge window gaba ɗaya saboda iska ta ɗan ratsa. Can kuma ya mayar ya rufe ruf ya kunna AC. Abin da zai iya tunawa, wata budurwa ta zo wucewa ta gaban motarsa, da sauri ya taka burki. Gaba ɗaya layin shiru, koda dama ba Magriba ba ne, wurin haka yake. Ya san dai an zuro tafin hannu ta baya an shaƙa masa abin da ya yi sanadin fitarsa a hayyaci, wannan ne kaɗai abin da Areef ya riƙe, daga nan bai ƙara sanin duniyar da yake ciki ba. 

***
  Laila ta buɗe saƙon da Suhailat ta aikomata wanda take sanar da ita Areef ya shiga hannu. Wani murmushi a take ya suɓuce mata gami da sauke ajiyar zuciya. A lokacin tana zaune saman darduma ba ta jima da idar da sallah ba. 

***
 Hajja Zayha ta buɗe ƙatuwar jakar da Zakari ya shigo da ita, suka dubi juna suka yi dariyar farin ciki da jin daɗin komai zai tafi yanda suka so. 

 "Lallai ɗan gaban goshi za'a je gidan gyaran hali. Za'a shiga hannun hukuma."

 Fadin Hajja kenan, suka tuntsire da dariya. 

***
 ABUJA

Da wani irin nishaɗi Daddy Affan ya ke sauraron wayar da suke yi da John na cewar ya yi nasarar bibiyar kayan su Areef da ya iso Lagos, har ya cimma nasara gun aiwatar da duk abin da suka shirya. 

 "Good job John! I really really appreciate your hardwork!" 

 John ya yi godiya, suka yi sallama. 

 "Time to settle the score." Daddy Affan ya faɗi a fili cike da jin wani irin farin ciki marar misaltuwa!


©Rufaida Umar