Page 1
Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuh
Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alkairi,masu saurare da masu karantawa barkan mu da sakeh kasan cewa a cikin sabon littafin mu mai suna Gaskiya dokin ƙarfe labari mai cike da dunbun tausayi,kaddara,cin amana,zalunci,tauye hakki da kuma zallar soyayya.
Kundin beenarh 🩸🩸
Toh yanzu littafin namu zai fara
Bismillahir Rahamanir Rahim da suna Allah mai rahama mai jin kai.
Page 1
A hankali motar ta fara shigowa layin,har izuwa kofar gidan alh adamu tare da ita akwai convoy na motoci kimanin guda uku cikin isa yasa driver din shi ya fara danna order,cikin kidima baba musa (mai gadi)ya fito da sauri dan gudun kar yayi laifi dan ya riga da yasan alh ja'afar ne kanin alh adamu.
Barka da zuwa yallabai an zo lafiya.baba musa ya fada cikin dar din zuciya.
Wani kallon banza yayi mashi irin baima san dashi a gurin ba.direct parking lot suka nufa da motocin,da sauri body guard din dake cikin motar da ke binsu ya fito domin bude mashi kofa ,cikin isa ya fara ziro kafarsa guda ya dauki kimani mintuna goma kafin ya fito da gudar,kafafun dauke suka da takalma na company din adidas,cikin isa yafara ta kasan tile din dake compound din,da sallama dauke a bakin shi ya shiga yana shiga ya ci karo da yaya mas'ud ko gaishe shi baiyi bah balle ya chi darajar kallo sbd a duk lokacin da yaya mas'ud ya kalli kwayar idon alh adamu da alh ja'afar babu abunda ke fado masa a rai sai cin kashin da akayi ma mahaifin su wanda aka mayar mai gadi ta karfi da yaji,sannan kuka kashe......, mgnr assadiq ce ta tsayar da shi daga fadin abunda yayi niyya.
Laa uncle ina wuni assadiq din ya fada cikin zumudi na jin dadin ganin kawun nashi.
Lafiya assadiq ya gidan uncle ja'afar din ya fada ba yabo ba fallasa.jin irin amsar da uncle din ya bayar yasa yaya mas'ud kama hannun assadiq din suka shiga ciki.
Yaya dole ne muzo mu kawar da wannan yaron,domin in har yana nan Allah ba zai zuba ido a cigaba da cii ma mahaifin shi mutumci.uncle ja'afar ya fada yana zama.
Hmm ai komi wannan yaron zaiyi saidai yayi amma wllh idan har najii wata mgn ta fita Allah sai dai su tattara shida uban nashi su tafi duk inda ma zasu su tafii,amma sauran yan'uwan shi suna nan babu inda zasu tunda shine mai baki,kuma wannan shegiyar yarinyar Fatima saina aurar da ita sai dai in tayi auren kar ta zauna,dama naga take takenta tunda safe zaka ta wani tafi gurin wancen matsiyacin wai tana taya shi hira gashi wannan shakuwar da muke gudu tsakanin ta da Zainab yanzu sai abunda yayi gaba,dan mah inda Allah ya taimake muh ko kama basuyi balle muyu tunanin koh asirin muh zai gilgiɗu wata rana,gudun haka fa yasa na aura ma ubansu wancan yar duniyar sannan na bata gudar yan biyun ta rike ta a wurin sbd naga itama yar yii ce,amma duk da haka kafin auran sai da nayi mata gargadi mai game jiki akan karta kuskura ta nuna ma zainab cewa ba ita ta haifeta bah,duk da haka kagan su nan abun da zahrar sunyi wani irin sabo na ban mamaki.alh adamu ya fada a kufuleh.(Nace ikon Allah toh wai ita wannan Zahra yan biyu ne da ita da zainab koko ya da kanwa ne,kuma minene ya faru dasu,da alama dai yaya mas'ud shine babban wansu, assadiq kuma dan karamin kaninsu,toh bari dai mu bisu mugani ai bamu yanke hukunci ba sai mun san abunda ya faru 🙄)
A haka suka zauna suna saka da war warar yanda zasuyi wani makircin har akayi kiran farko na magrib.
Zainab na zaune tana kallon wani series na turkey fassarar hausa a tashar arewa 24 mai suna tarkon kauna yadda taga ana kulle kullen makirci kawai sai faduwar gaba ya ziyarceta,tana cikin wannan halin Fatima ta shigo
Abhuh .... Abhuh...... Zainab.....ta fada da karfi sannan ta dawo hayyacin tah kyakkawar ajiyar zuciya ta safke sannan ta Maida duban ta izuwa yar'uwa kuma aminiyar ta.
A hankali cikin takunta ta isassun yan' mata masu jini ajika wanda a ko yaushe aka ga tana irin takun za'ayi zaton girman kai ne ta iso zuwa ga aminiyar tata, gefen ta ta zauna ta fara yi mata mgn cikin kwantacciyar mirya taceh.
Zainab mi kikeh tunani har haka,na shigo baki ma san da shigowa ta ba 🥺shiru zainab din tayi kafin nan taceh: Zahra ina mafarkan dana taba fada maki inayii............
Eh na tuna yau ma irin su kikayi, a'a wannan film din sai ya dinga tuna man mafarkin,kinga fa itama wai ga mahaifiyar ta amma wai sai tayi mafarkin wata mata tazo mata cikin barci tace da ita wai ta rike amanar yar uwarta, Zahra anya nida keh bah mahaifiyar mu daya bah akeh boye mana 🥺ki duba fa wannan alamarin ki gani.eh kuma da wannan amma fa kinji abunda hajiyar makwarari taceh.memah tace,ke dalla da taceh ni ina da yabbiyu kuma bani kadai umma ta rasu ta bari ba ina da kani dakuma yayye biyu daya namiji daya maceh wadda itaceh gudar tawa amma fah amana nafada miki taceh kar na bari wani yaji don zanja ma babana matsala sbd yana nan da ranshi kawai dai sunki su nuna manishi kuma sun hada yanuna min kanshi ,shiyasa har yanzu ban san shiba gashi har ana shirin yi min aure😢😥batare da sa albarkar shi ba Allah kana ji kana gani yaa Allah kayi mana sakayya daga mu har iyayen mu, Zahra tafada 😭
Kundin beenarh 🥰🥰🥰