MARYAMA

Page 37/38

by @ummufadeela01

💫MARYAMA💫

                 BY

UMMU FADEELA

TYPING📲

               EPISODE 37/38.

Sosai Jabeer ya samu shauƙi da farin ciki a kasancewarsa da Maryama yau, dan ko kaɗan bata bashi tangarɗa ba, idan baiyi mistaken ba ma kamar harda reply ta ke masa,ba shakka gangar jikinta ya amshi saƙon yanayinshi har ya isarwa zuciyarta.

Bacci ne ya kwasheta bayan lafawar komai, a hankali Jabeer ya fara ƙoƙarin rabata da jikinsa dan ya tsabtace kansa,gashinta da ya barbaje saman fuskarta ya gyara mata zuwa baya,leɓenta dake matuƙar burgeshi ya shiga shafawa yanajin wani irin ƙaunarta yana ratsa jini da tsokarshi,ranƙwafowa yayi daidai goshinta ya manna mata kyakkyawar sumba sannan ya miƙe murmushin da na kasa fassara na menene shimfiɗe saman fuskarshi.

Ruwan zafi Jay ya ɗaura mata sannan ya cika babban buta ya shiga yayo wankan tsarki.lokacinda ya fito ana ta ƙiraye ƙirayen sallar la'asar, dan haka jallabiya ya sanya ya wuce masallaci, ana idar da sallar kuwa bai ɓata lokaci ba ya dawo gida dan gaba ɗaya hankalinshi yana kanta,ruwa mai ɗan zafi ya haɗa mata zuwa bayi kafun ya koma ɗakin, har lokacin Maryama bacci ta ke yi ba alamar ma ta motsa hannu ya kai saman fuskarta yana cigaba da shafawa cike da nishaɗi bayan ya durkusa bisa guiwowinsa a bakin gadon, sannan cikin sassauta murya ya fara ƙiran sunanta, "Pretty!,Pretty!!".

Buɗe jajayen idanuna na yi wanda suka min nauyi kaɗan na sauƙe su kan hamma jay dake durkushe a kasa hannunsa na yawo tsakanin kaina zuwa fuskata,ido ɗaya ya kanne min haɗi da cewa, "Barka da tashi my SWEET WIFE!"

Turo baki na yi gaba cikin muryata da bata fita mai kyau sakamakon baccin da nayi haÉ—i da ture hannunshi na ce, "Ni ba Sweet ba ce ba".

Wani kayataccen murmushi ya yi yasa hannu kan dogon hancinta yaja kaɗan gami da faɗin, "Ke kinma fi sweet daɗi a wajena baby girl,ko in nuna maki ne practically?"ya faɗa yana miƙewa, haɗi da ɗaukata cadaƙ kamar yar baby,rufe idanuna na yi gam ina buga kirjinshi da hannayena biyu da faɗin, "Ni Allah bana so ka sauƙeni, wayyo innarmu, ni dai ka sauƙeni".

Bai dire ni ko ina ba sai bayi, "in maki wankan ne my sweet?" ya faɗa cikin kunnena bayan ya ajiye ni, turasa na yi da ƙarfi har sauran kaɗan ya faɗi kasancewar abin ya zo masa unexpected amma ya yi ta maza ya coge gami da dafa bangon bayan gidan da hannu ɗaya,"ni dai ka fita banson ganinka kuma" na faɗa ina sinne kai ƙasa.

"Yanzu kuwa sahibar ruhina" ya faÉ—a yana Æ™ara matsoni, "Ki tabbatar kinyi harda É—aya wankan fa,kin iya ai?,ko dai in koya miki yadda ake yi". ya Æ™are maganar da É—an dariya cikin muryarshi.bugunshi na fara yi da hannuna duk ta inda na samu ina binshi hale da cewa, "Allah hamma jay bana so, nidai bana so"har saida na tabbatar ya bar bayin sannan na koma ciki na zauna,haka kawai naji wani murmushi ya suÉ“uce min wanda ban shirya masa ba,lumshe idanu nayi na buÉ—e ina tuno yanayin da na shiga É—azu, 
(Masu karatu kar kuga laifina, wato hamma jay na dabanne na tabbata ko a cikin maza shi É—in Namiji ne.Duk sanda ya ke nuna min irin wannan soyayyar na kan manta da wani burina da mafarkina,shi kaÉ—ai nake iya hanga da gani a duniyata).
Wanka na yi na soso gami da na tsarki,sai da na gama na tuna banzo da wani kaya ba kuma babu zanin wanka ko hijab a tattare dani rasa yadda zanyi in fita na yi dan haka na koma na tsaya cike da rashin sanin abinyi.

Yau ya shiga cikin rana mafi farin ciki a rayuwarshi fuskarshi cike da annuri ya koma ɗakin bayan ta koroshi daga toilet,saman three seater ya kwanta haɗi da ƙurawa ceiling ɗin ɗakin idanu na tsawon lokaci, lokaci lokaci yana sakin faffaɗan murmushi wanda ke ƙawata fuskarshi,tunawa da yayi cewa bata shiga da wani zani ba yasashi miƙewa da ɗan sauri ya shiga ya ɗaukar mata zanin da yasan tana wanka dashi gami da babban hijabin da ya gani kan pray mat nata.ba tare da knocking ba kawai Jabeer ya faɗa banɗakin, wani ƙara Maryama dake tsaye har lokacin ta sake tana kaiwa durƙushe da haɗe jikinta waje ɗaya. "Wayyo Allah na, ni dai ka fita,Innarmu kizo kice mashi ya fita ni dai banaso".

Dariya ta bashi sosai dan haka ya dara abinshi, cikin son ƙara zolayarta ya ce, "Yauwa kinga na fi son ganin ta bayan dam....."Kafun ya ƙarisa ta yi wani irin miƙewa a tamanin ta maƙale shi ta baya,,ƙanƙameshi ta yi ƙam tana sakin wani kuka da faɗin ita bataso ya fita.

"To pretty ta ina zan fita bayan kin maƙalƙaleni haka". "ehh ni dai ka fita ko in haɗa ka da Daada". juyi ɗaya ya yi ya kuma ɗaukarta cidak yana kareta da kayan dake hannunshi har ɗaki sannan ya ajiyeta, cukuikuye kayan tayi ba laifi ya ɗan rufe mata jiki kaɗan.dan haka ta juyo masa baya tana cuno baki gaba.

Rungumarta ya yi ta baya yana sako kanshi saitin kunnenta ya lumshe idanu yana shaƙar ƙamshin sabulun da tayi wanka dashi, cikin wani salo da ke nuna duk abin da zai faɗa daga cikin zuciyar shi zai fito ya ce, "Thank you for today wife, yadda kika faranta min kema ubangiji ya faranta miki daga yanzu har abada,".da sauri na ja baya jin tsikar jikina tana tashi, bai yi yunƙurin bina ba ya ce yana kallon agogon dake manne ɗakin, "ki kimtsa da wuri zamuje gaida su Innarmu da kuma sallama da su Daada zasu koma gobe".

 "Da gaske ka ke hamma Jay?".na faÉ—a da wani irin farin ciki.

"Da wasa nake Sweet wife". cewar Jabeer yana mimicking muryarta,sannan ya ɗora da faɗin, " ki hanzarta kar ki ɓata lokaci,.Gaban wardrobe namu ya tsaya gami da buɗewa ya zaro kayanshi jamfa da wando na wata farar shadda da ya ɗinka lokacin aure,palo ya fita yana ƙara tabbatar min in shirya kan lokaci.

Kasancewata ba mai son yawan kwalliya ba,mai na shafa nayi yan goge gogen turaruka a jikina haɗi da shafa lip balm saman lebena,duk da banyi kwalliya ba amma fuskata tayi wani washar da ita ɗan kumburan da ta yi saita bayar da wani sirrin kyau,da ɗan sauri sauri na ke shiryawa cikin atamfata orange colour dinkin riga da zani da ya matuƙar ƙawata jikina.abin sallah na shimfiɗa na gabatar da sallar la'asar da ta kubce min,tun ban idar ba nake jiyo muryar hamma jay yana sanar dani in fito ko ya shigo ya ɗaukeni, dan haka ko addu'ar kirki ban ba na zaro gyale na mai ɗan girma shima orange colour na yafa haɗe da ƙara feshe jikina da turare ban ɗauki jaka ba sai takalmata flat baƙaƙe da na saka kasancewata doguwa ban cika sanya takalmi masu tudu ba.

"Masha Allah" na furta lokacin da na tsaya gaban mirror ina ƙarewa kaina kallo ba ƙaramar kyau nayi ba, idan banyi kuskure ba harda wasu yan kumatu naga na fitar ga wani irin sheƙi da walƙiya da jikina ke yi.

Juyowa nayi da niyyar fita amma na yi turus ganin hamma jay da ya sauya kaya zuwa farar jampar da ya ɗauka tsaye bakin ƙofar shigowa ya yi folding hannayensa akan kirjinsa,fuskar shi ɗaure tamau ba bu alamar dariya.Ɗan muskutawa yayi yana zuba hannayenshi a aljihu gami da watso min wani kallon da ya kusa tsaida min gudunar jinin jikina ya ce, "Ina zakije a haka?" ya faɗa yana nuna ni da bakinsa daga kasa zuwa sama.

"Haan Hamma Jay shiryawa na yi fa zamutafi".na faÉ—a tamkar zan fashe da kuka ganin yadda ya yi da fuskarshi lokacin tambayar.

"Canza kayan nan to, sannan ki tabbatar kin sanya hijab har ƙasa if not ba bu inda zaki bini".

Fashewa na yi da kukan da nake ta riƙewa tunda ya fara maganar,matsoni ya yi sosai har muna shaƙar numfashin juna ya fitar da hannunsa daga aljihu yasa ya dago haɓata dashi,kallon cikin ido muka yiwa juna kafun inyi nasarar janye nawa idon zuwa ƙasa.

Cikin sanyin muryar da ba ko yaushe hamma jay ya ke magana da ita ba sai in abu ya taɓa zuciyarshi ya ce, "Maryama bazan amince maki fita a haka ba,kin buɗawa kanki turare,kin sanya mayafi mai bayyana jikinki....." sai kuma ya yi shiru yana sauƙe wani irin ajiyar zuciya, a hankali ya kamo hannuna bayan ya sakar min fuska,cike da salo ya ke murza min tafin hannun yana kallona ya kuma cewa, "Pretty ina tsananin kishinki, sau tari nakanji tamkar in tsaga zuciyata in sanya ciki ko zan huta da yanayin da nake ji game da ke,pretty har kullum ina ji a raina da tabbatarwa ƙaunarki ce jarabtata,shin kin taɓa ganin inda aka ajiye zinariya tsirara? nasan baki taɓa gani ba, a auduga ake sanyata sannan sannan a adanata cikin akwatin ƙarfe mai tsananin tsaro kana a kefata a glass, iya wannan akwatin dake tabbatar da akwai zinariya a ciki ake iya hangowa ta cikin glass ɗin, to haka kike a wajena my wife, kin ma fi wannan zinariya daraja a idanuna, plsss and plsss love ki taimaka ki tayani adana kanki ba dan ni ba sai dan tarin ƙaunar da nake maki marar yankewa." Jabeer ya kare yana mai sakin hannuna da juya min baya sakamakon kaɗawa da idanunshi sukayi jajur.

Da farko kukan taɓara na keyi,amma tun bayan da ya fara magana naji kukan gaske ne ke tahomin harda sheshsheƙa, sosai maganarshi da yadda ya yi ta cikin sanyin murya mai cike da rauni ya sanyaya min jiki na.Haka kawai na samu kaina da bin umarnin shi dan kuwa wardrobe na buɗe haɗe da fitar da babban jilbab nawa har ƙasa na sanya,juyowa ya yi yana sakin murmushi mai sanyi ganin yadda jilbab ɗin yai matuƙar karɓata fiye ma da gyalen, " Ya salam!" Jabeer ya furta yana ɗaura hannu saman gashinsa gami da yamutsawa, "mu tafi to" na faɗa ina Allah Allah kar yace ya fasa,.

"Ki sanya nikaɓ" ya faɗa a can kasan maƙoshinsa, "kai dai hamma j... ".

Tun ban kai aya ba ya katse ni ta hanyat langwaɓar da kai gefe gami da sassauta murya ya ce, "Plssss mana wife". komawa na yi bakin mazubin kayana ina jin wani irin haushi haushi a raina haka na fitar da niƙab ɗin na sanya, na kama zan ɗaure amma ya yi hanzarin riga ni kama igiyar yana ɗaure min ta baya cikin salon soyayya ya kamo hannuna ya sumbata cike da shauƙi ya ce, "You look so beautifull my love". bai jira na ce komai ba ya kama hannun nawa muka fita,key ya sanyawa kofar palon sannan ya zare ya jefa a aljihunshi muka fita, kofar gidan kuwa kwado ya sanya mishi ya rufe gam sannan muka jera cike da sha'awa da burgewa muka nufi gidanmmu.

               ..........*******..........

Sake gwada layin Maryama a karo na ba adadi siyama ta yi amma still switch off ake sanar mata, lallai yarinyar nan ni zata rainawa hankali ba?, tabbas bata san waye siyama ba,nifa duk harkar da zata kawo man kudi komai hatsarinta sai nayi,ajiyar zuciya ta sauke tana tuna irin dukiyar da Sadeeq ke dashi matukar ta jefa wannan kyakkyawar Maryamar cikin rayuwarshi yadda ya kamata ba karamar ganima zata kwasa ba,sai akayi dacen tun batayi wani yunkuri ba shi da kanshi ya fada kaunar yarinyar gashi yanzu an mata aure,"what a lost?"siyama ta fada tana dafe goshinta da hannu biyu... ,yanzu haka dan shi ta canja layi tsabar yadda ya matsa mata da kira cikin sati dayan nan tun tana mashi karya har karyarta ya kare,.

Da hanzari ta daga wayarta ta tattaba kana ta karashi kunnenta,zuciyarta na tabbatar mata aikata abin da ke mata yawo a ciki.

"Barka da yammaci ranka ya dade, ka dade kayi kargo kayi shekaru irin na dabino Allah ya ja zamanin gagara badau mai ba yan maza tsoro."Siyama ta fada cike da jinjinawa da karramawa.

Daga daya bangaren dan dukununun mutumin dake zaune bisa wani buzu da shirgegen carbi a hannunsa gefe kuma kasa ne mai laushi cike da wani tray da sauran tarkace irin na malaman tsubbu, dariya yayi mai fadin gaske sannan ya ce," hajiya Siyama yau kin tuna damu kenan,kasuwar ne ta tsaya?ko bakin wasu kikeso a garkame maki?." ya fada cikin amon muryarshi marar dadin sauraro.

"Ba ki daya yallabai,wato ina yarinyar dana kawo maka sunanta kwanan baya za'ai aiki a kanta nazo na fasa dinnan?na dawo yanzu inason muyi aikin amma zamu canza ba irin na farkon bane,"

"An gama hajiya, yanzu wani iri ne kike bukatar ayi?".

Shiru Siyama ta yi cike da nazari kafun daga bisani tayi wani murmushi ta fara magana, tsawon mintuna shida tana maganar sannan ta yanke wayar gaba daya tana jin wani irin reliefe a ranta.....