Page 39
💫MARYAMA💫
BY
UMMU FADEELA
EPISODE 39...
***
Da wani irin gudu na je na rungume Innarmu da ke faman dakan kalwa a tsakar gida ta hada uban zufa na fashe da kuka,da ace da ne ko kallon inda take bazan ba tsabar yadda na tsani wannan sana'ar ta innarmu, amma abin mamaki cikin ƙasa da kwana goma kawai da ban ganta ba wani irin azababben kewarta na ke yi.
"Ƙalau kike kuwa Maryama?" cewar Inna tana ƙoƙarin rabani da jikinta,ƙara rungumeta na yi ƙam cikin kuka na ce, "Na yi kewarku Innata,shi ne ko kije ki ganni kuma".
Dariya Innarmu ta yi mai cike da farin ciki ta ce, "Tunda banje ba ba gashi ke kinzo inda nake ba".
"Haaan waye wannan kuma haka?,ya zaka tsaya wa mutane haka sandandan aka kamar dogari?" cewar Daada dake shigowa gidan ɗauke da kaya niƙi niƙi a hannunta tayi arba da Jabeer dake tsaye hannuwanshi zube cikin aljihun rigarshi sai kallon Maryama da Innarmu ya ke cike da sha'awa,haka kawai ya samu kanshi da tuna mahaifiyarshi a yau ɗin.
Juyowa ya yi yana shafa kanshi haɗi da yin murmushi,ya ce, "Kai wannan tsohuwa kin cika jarabar tsiya, daga shigowa ko sallama babu kin fara yiwa mutane hayaniya a k...." kaga jaraba can kan ubanka Hassan da uwarka Dijah ba ni ba".Kwalalo ido ya yi waje gami da faɗin, "Rufamin asiri in gama da duniya lafiya, me iyayena suka miki, a'a babu ruwansu gaskiya" ko kallonshi bata yiba ta wuce fuuu abinta,tsayawa tayi kusa da su Innarmu tana ƙarewa Maryama dake sanye da niƙab, baka ganin komai a fuskarta sai idanunta kallo, ta ce," waye wannan kuma haka kamar an ɗaure ƙyanwa a baƙar leda?. wannan dai ba halin ƙwarai bane gaskiya,yo ko shi mai ahlari ma ai da ya tashi sanar mana inda yake al'aura a jikin mace ya ce, "ko ina na jikinta al'aurace amma banda fuska da tafin hannunta",amma ke tsabar iyayi yar miji daɗi kin wani ƙaƙabawa fuskarki niƙabi kamar mai ɓoye muni,ku dai ku dinga yin gaskiya a al'amuranku wllh nidai ba ruwana." bata basu daman bata amsa ba ta shige abin ta.
Innarmu da Maryama da tun shigowar Daada suka juyo suna saurarensu da Jabeer kafun ta sauƙe masu nasu rabon ta yafito Jabeer dake tsaye har lokacin baida niyyar karasowa fuskarta ɗauke da murmushi ta ce, "Babana tare kuke tafe ashe?sai kunyi haƙuri da daada fa dan shekaru sun ja sai an haɗa mata da uzuri,ƙarasowa ya yi cike da kunyar Innarmu da ya samu kanshi a ciki yanzun ya durƙusa kusa da ƙafarta ya ce, "Barka da yammaci Innarmu".
"Barka ka dai babana ya hidima?" kara sunne kai kasa ya yi ba tare da ya ce komai ba.ganin baice ɗinba ya saata faɗin "Allah ya maku albarka baki ɗayanku,ku ƙarasa ciki ina zuwa"...
Ɗakin Innarmu suka shiga suka tadda ilahirin mutan nijar suna ciki sai haɗa manyan ghana must go suke na shirin komawa gobe wanda yawanci kaya ne yan kasuwan cikinsu irinsu inna lami suka sara a ciki dan komawa dashi nijar, ya ye niƙab nata Maryama ta yi suka gaggaisa sannan jabeer ya fita ya barta anan shikuma ya wuce wajen oga zubairu kafinta, duk da yau ba aiki zaiyi ba dan kayan dake jikinsa sai dai ya tayasu hira.
Zaune suke suna ta hira a ɗakin harda Innarmu da ta gama dakan kalwarta, yayinda Daada ke ta tsokanan Maryama wai ko tayi ciki ne daga aure sati ɗaya ta tsirar da wani uban kumatu da walkiyar da bata santa dashi ba,Inna lami ke shigar mata ita kuwa sai kumbura take tana cuno baki gaba,a ɓangaren innarmu kuwa wani irin daɗi ta ji da maganar na daada tare da addu'ar Allah yasa hakan ta kasance da sai ta fi kowa murna tuna irin shekarun da ta kwashe kafun ita Allah ya bata Maryamar.
Sallamar da Umaimah ta yi ne ya tsaida maganar da daada keyi,tana ɗaga labulen ɗakin Innarmu gami da shigowa ciki, a tsanake suka gaisa da mutan da ke ɗakin na kama hannunta muka tafi ɗakina dan ƙule nake da ita, ko zama ba muyi ba na kama ƙugu nace, "Idonki kenan Umaimah?shi ne ko ki ƙara waiwayata ko?wato duk abin da zai faru ma ya faru babu ruwanki ba?".
Dariya Umaimah ta yi sosai tana kamo hannuna ta ce, "Relax mana amaryar hamma jay,ba gashi ke kinzo ba, kuma ki tambayi innarmu kullum ta Allah sai na zo gidannan kuma sai na tambayek...."
"Ban gane ba?baki san hanyan gidana bane da bazaki je ba, gaba É—aya taku nawa ne daga nan zuwa gidan nawa fisabilillahi Umaima amma ki ka manta dani faa".cewar Maryama tana katse Umaimah daga maganar da takayi.
"Uhmmm ashe kinyi gida amarsu" cewar umaimah tana dariyar shaƙiyanci,da jana zuwa kan gado muka zauna,sai a lokacin na tuna abin da na faɗa amma sai na fuske tamkar ban ji mi ta ce ba, itama fuskewar ta yi tana canza maganar da cewa, "So me labari?" ta ƙara yin ƙasa ƙasa da murya yadda ni kaɗai zan jiyota ta ce, "Nasan zuwa yanzu hamma jay ya gama cika aiki, ya lamarin yake ɗan bani labari mana,shin ya biki a hankali kuwa yadda nag....."
Wani wawan marin da Maryama ta ɗago zata ba Umaimah ne yasata yin baya da sauri tana gimtse sauran maganarta haɗi da kwanciya saman gadon tana ƙyaƙyata dariya,zuwa can kuma ta yi shiru tana janyo filo ta matse a kirjinta ta ce, "Ohhh my dear yusuff ina kake ne."
Cike da mamaki Maryama ke bin ta da kallo, ta rasa mi Umaimah ta gani a jikin wannan soloɓiyon yusuf ɗin da ta nace masa, ita dai tasan ko a ƙafa aka ɗaure mata shi zata cire ta gudu shi ba kyau ba shi ba kuɗi ba, kai ina impossible.hira suke ta yi irin na aminan da suka daɗe basu haɗu ba, yawanci hirar kuma Umaimah ke yi haɗi da zolayar Maryama,ƙiran sallar maghrib ne ya ɗaga su suka gabatar da sallar haɗi da cin shinkafa da miyar stew da yaji nama da Inna ta girka musamman dan Maryama,ba laifi kuwa dan ta ci sosai,rabonta da abinci tun breakfast na safe.Sallama suka yi da Umaimah ta koma gida da alƙawarin zata zo mata cikin satin nan su wuni Insha Allah.
Jabeer bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha,suka shigo tare da baffanmu suna ɗan tattaunawa sama sama akan aikin koyarwar da ya fara.abinci Innarmu ta zuba musu bayan sun zauna bisa babbar tabarmar da suka shimfiɗa a tsakar gidan kamar kullum,...Maryama ta fito tazo gaban baffa ta durƙusa gami da gaisheshi tana jin wani irin hawaye yana kawowa idanunta,amsawa ya yi cike da kulawa gami da faɗin "Allah ya maku albarka mamana". sun daɗe suna tattaunawa har misalin karfe takwas da rabi sannan baffanmu ya ce su tafi hakannan dare ya yi,nan fa ake yinta domin kuka Maryama ta sanya wai ita bazata bishi ba, sai da ƙyar da suɗin goshi baffa ya rarrasheta suka tafi tana ta sauƙe ajiyar zuciya da alƙawarin gobe da asuba zasu zo raka su daada zuwa park....
Hannuna Hamma Jay ya kama bayan mun iso gida har kan kujerar mai zaman mutum uku, zama ya yi sannan ya janyo ni saman cinyarsa ya zagaye waist ɗina da hannunshi guda, ɗaya hannun ya sa yana share min hawayen dake cigaba da gangaro min saman fuskata har lokacin ba tare da ya ce komai ba,a hankali ya gangara da yatsar shi saman lips nawa ya fara shafawa yayinda idanunshi ke cigaba da rinewa,ƙoƙarin tashi na fara inajin kukan na komawa amma ya ƙara damƙeni da kyau, da wata iriyar murya yana ƙara matsoni ya ce, "Plssss wife! ki yi haƙuri da ni, i know that tun ba muyi aure ba sai kin jure da yanayi na, nasan ni ɗin mai yaw...." Bai ƙarasa ba ya haɗe bakinshi da na nata ya shiga aika mata zazzafan saƙonni...(Ni dai jan ƙafata na yi na bar musu ɗakin ina tambayar kaina shi kam baya gajiya ne?)...
*********----------**********.
A hakali ta buɗe idanunta ta sauƙe su kan Mommy dake zaune kan stool dake gaban dressing mirror ta zabga tagumi, "Mommy" ta faɗa cikin murya ƙasa ƙasa,da wani irin sauri mommy ta taso har kujerar da take kai yana ƙoƙarin faɗar da ita ta hayo gadon tana kama hannun Khadija haɗi da shafa kanta cike da tausayawa ta ce, "Sannu dota na,ina ke maki ciwo yanzu?.
"Babu ko ina Mommy, kawai zan sha ruwa".sauƙa gadon tayi ta buɗe karamin fridge dake ɗakin ta ɗauko ruwan haɗi da zubawa a cup ta dawo gareta ɗaga kanta tayi ta bata a baki sosai ta sha ruwan saida ya ƙare ta koma ta kwantar da kanta tana lumshe idanu.
"Sorry dear!tabbas Man zaisan ni na haifeshi ba shi ya haifeni ba, shi har ya isa ya ga tsabar idona yaceman wata can yar talakawan da suka kasa sata even school yake SO ba ke ba,lallai duk wacce ya yi gangancin shigar da ita cikin rayuwar mu da sunan aure ba ke ba tabbas sai ta gwammaci ɓarin cikinta uwarta tayi akan haifota duniya har ta san ɗana,ke kaɗaice matar Man kima dake zai zauna har gaba da abada idan ya nuna min taurin kai kuma wallahi wallahi kap zuriyar su yarinyar zan kulle sannan shikuma ba abin da zai hana in......."
Da sauri Khadija ta rufe bakin Mummy da hannunta tana girgiza kai hawaye na tseren gudu saman kumatunta.
"No Mommy,don't do such, wannan ba halinki bane,tunda ya ce bai sona to bai sona ɗinne da gaske, ki barshi ya auri zaɓin zuciyarshi,ko kin takura ya aureni ma daga ƙarshe zumuncin da ake son ya yi kyau ne zai ɓaci, ki barshi kawai Mom,ki barshi kawai" ta faɗa tana fashewa da kuka mai tsuma zuciya.sosai tayi kuka sannan ta cigaba da faɗin, "wannan shine tawa kaddarar mom, SON MASO WANI, da daɗewa nasan yaya Sadeeq bai sona amma na dagewa zuciyata cewa with time zai canza amm....." wani kukanne yaci karfinta, tana share hawaye ta ce, just leave him mom, leave him ya auri wacce ya ke so,matuƙar zai yi farin ciki da ita ki barshi wannan shine asalin so wllh zan tayashi ƙaunarta." Kai da kaga yanayinta kasan she's hurting inside, kawai ƴarfin hali ta ke yi.
Rungumeta mommy ta yi ta ce, iam giving you my word Khadija bazan canza akan abin da na faɗa ba, wllhi Allah ɗaya kenan duk wacce man ya kawo gidan nan da sunan aure sai ta gwammaci mutuwarta akan rayuwarta, ke nake so ya aura, ke ɗin amanata ce, ke ɗaya tilo nake gani in tuna gaba ɗaya iyayena da sauran yan uwana da na rasa sanadiyar hatsari, ƙanwata khadija kawai Allah ya barmin bata yi waccan tafiyar mai cike da tashin hankali ba saboda cikinki dake jikinta, koda ta haifeki kuwa bata shayar dake na sati biyu ba itama Allah ya amshi abin shi, taya zan maki riƙon sakainan kashi Khadija? dole in haɗaku aure da tilon ɗan da na mallaka a wannan duniyar ku haifo mana wasu zuriya masu albarka," share hawaye masu zafi mommy ta yi tana shafa bayan Khadija dake kwance lamo a jikinta sai sheshsheƙa ta ke yi, ta cigaba da faɗin, ba dai ya gudu ba, inace ba ƙasar ya bari ba,?zan wanke ƙafata inje har can wajen aikin nashi ai ba baƙona bane zai san uwa uwace. Yanzu ta shi muje in kaiki hospital dan sau biyu dr, yana zuwa kina bacci."
Cikin shagwaɓa Khadija ta dafe kanta dake sara mata ta ce, "Mommy Allah ba inda ke mani ciwo fa, kawai ki barshi sai dare, ta faɗa tana komawa ta kwanta saman gadon haɗi da lumshe ido, are sure dota?"
"Sure Mom, i just want to freshen up" cewar khadija.
"Ohk bari in haÉ—a maki ruwa to". bayi mommy ta shige ta cika mata ruwa a baho daidai yadda zata ji daÉ—insa sannan ta fito tana kamata.
"Zan iya faaa" ta faɗa tana ƙarfin halin miƙewa ita kaɗai ta wuce bathroom ɗin kamar zata faɗi,saida Khadija ta shiga ruwan ta daidaita kanta,sannan ta samu kanta da fashewa da wani irin kuka gami da toshe bakinta da hannuwanta duka biyu..tsawon lokaci ta kwashe a bathroom ɗin tana kuka har saida taji tamkar zata shiɗe kamun ta canza ruwa ta ɗauraye jikinta ba tare da tayi using soap da spounge ba.fitowa tayi daure da babban towel,ganin babu mommy a palon ta fada saman gado ta lulluba da duvet nata.
..............'''''''''''''''''''''...............
Da hanzari siyama ta kimtsa dan amsa kiran da aka mata a ranta tana fadin ba'a bori da sanyin jiki,da dan hanzari ta zari yalolon mayafinta mai kama da abin tatar kamu ta yafa hadi da daukar jakarta ta rataya ta bar gidan.
Zaune take gaban mutumin wanda kai tsaye bazamu kirashi boka ba dan yafi kama da malaman zaure duba da irin tarkacen dake dakin nasa na aiki,abin da ke hannunshi ya mika mata ya cigaba da fadin, "ki tabbata kin sanya wannan karkashin harshenki kamun ki mata magana, ina tabbatar maki idan kika aikata haka ko wuta kikace ta shiga bazata maki musu ba".
Cike da murna Siyama ta karbi dan karamin layar da ya mika mata tana juya shi fuskarta dauke da farin ciki, ta zaro wasu kudade masu auki daga jakarta ta mika mishi tana godiya ta bar gidan, abinda ya rage mata kawai yadda za'ayi ta je gidan Maryama dan harga Allah tsoron haduwarta da jabeer take dan tsab zai iya guntule mata kafafu ba mutunci ne da shi ba.
Kwanaki uku Siyama ta kwashe tana jiran jin kira daga wanda tasa aikin leken asiri, don haka yanzu da taga kira da layinshi ba karamin dadi ta ji ba,kara wayar tayi a kunnenta cike da zakuwa, daga daya bangaren yaron dake makale jikin wani lungu ya ce, "Hajiya mutumin naki ya fita fa,kuma da alama zai juma dan haka kiyi gaggawan zuw.."
Ba tare da ta jira jin karshen maganar ba ta yanke kiran tana ganin agogo wanda ya nuna mata karfe bakwai da mintuna arba'in na safiya,hijab kawai ta saka har kasa kamar mutuniyar kirki ba tare da ta bi takan wanka ba ta suri jakarta tayi gaba, mamarta na tsaida ita ta yi breakfast ma ko kulata batayi ba.
Yau na tashi bana jin dadin jikina gabadaya kasusuwana ina jin tamkar ana kwankwasa min su dan haka ko dan sharar da nake yi kwana biyun nan ban ba hamma jay ne ya yi komai na gidan sannan ya shirya ya tafi inda yake aiki, shayi kawai na iya sha dan haka tun fitarshi nake kwance saman doguwar kujera kamar kayan wanki,cikin wannan halin ne naji ana sallama a tsakar gida kamar da muryar siyama, da kyar na mike daga kwancen da nake inajin zuciyata na bugawa da sauri sauri nayi karfin halin amsawa,labulen palon ta daga gami da shigowa fuskarta dauke da murmushi, cike da zolaya ta ce, amarya bakya laifi, gaba daya kin manta damu kina nan kina kurbar romon dimokoradiyar soyayya abinki.
Dariya ta bani sosai, dan haka na saki murmushi na ce, "wace ni in manta dake Siyama,kawai dai al'amuranne suka zo a haka amma wallahi kina makale a raina,ki zauna mana?" na fada ina nuna mata kujera, babu musu kuwa ta zauna harda daura kafa daya kan daya tana taunar cingam kas kas, ta ce, "yanzu wannan akurkin gidan aka kawoki Maryama? Duk wannan kyawun a wannan gidan zai kare kenan?"
Wani irin abu naji ya soki kirjina da ban gama tantance menene ba, "Hmmm" kawai na ce ina mikewa da kyar hadi da kokarin boye hawayen da suka cika min ido na ce "bari in kawo maki ruwa Siyama" Wani irin zaro ido Siyama ta yi tana bin Maryama da bata san tanayi ba kallo har ta bacewa ganinta.
Da sauri ta zaro layarta dake cikin jaka ta makala shi kasan harshenta ta yi gum.
"Dauke da ruwa cike da jug da kuma cup guda biyu bisa tray Maryama ta shigo hadi da dire su gaban Siyama ta ce, "Bissimillah ga ruwa".
Da kallo Siyama ta bi ruwan sannan ta dago suka hada idanu da ita tana yamutsa fuska ta ce, "Yanzu fisabilillahi kina amarya amma ko dan ruwan leda baza'a ajiye maki ba balle na gora, sai dai ki kare a ruwan randa? a gida kisha na randa a gidan aure ma kisha na randa? kai ina, gaskiya maryama da sake a rayuwarki.
Wani kuka ya taho mini dan a take naji zuciyata tamin bakikirin, nace, "to ni yanzu ya zanyi?".
"Ba yadda zakiyi Maryama sai hakuri ni yanzu bama wannan ya kawoni ba, Oga Sadeeq ya takurani da kira wai lallai lallai sai na hadaki dashi." Cewar siyama tana fitar da wayarta daga jaka.
Zaro ido nayi ina dafe kirji na ce, "Sadeeq kuma Siyama? shikenan kin kashe ni, kin sanar masa an min aure ne?" ba tare da ta bani amsa ba naga tana miko min waya hadi da fadin "karbi kuyi magana,"
Haka kawai na samu kaina da kasa yi mata musu ma sa hannu na karba hadi da kara wayar a kunnena cikin sanyin murya na ce, "Salamu alaikum".Daga daya bangare Sadeeq ya lumshe idanu yana jin wani abu marar fassarawa yana mishi yawo a jikinsa, cikin kamilalliyar murya yace, " Pretty!is this you?".
Hakan kuma ya yi dai dai da shigowar Jabeer gidan yana sallama sakamakon kasa nutsuwa da yayi a makaranta tuna yadda ya bar maryama a kwance......