MARYAMA

Page 40

by @ummufadeela01

💫MARYAMA💫



By

Ummu Fadeela


Typing📲

Episode 41.

END OF BOOK ONE




Let say something about yesterdays episode kafun mu ɗora...nasan da yawanmu zamuce asirin Siyama ya kama Maryama, well,kar mu manta da waye Maryama da irin rayuwarta da tunaninta tun tasowarta,wanda shine ma dalilin da ya sa ta kai kanta wajen Siyama inda ita kuma tayi amfani da damarta wajen cimma wani buri nata itama,kunsan yadda rayuwa take yanzu yawanci mutane basa taimako dan Allah,sai sun duba idan na taimakeka ni kuma wani riba zan samu, hakance ta kasance tsakaninsu, musamman da ya zamo taimakon da Maryama ta je nema totally ya sauƙa daga tsarin yarinyar kirki.. ,kasancewar ɗan canjin da aka samu a zamanta da Jabeer kuma ba shi ke nuna tayi hankali ba, a'a ta yiwu wani dalili ne can na daban wanda ke ɓoye, so for me, ina ganin asirin ya samu halinta ne, thou an ce tsafi gaskiyan mai shi.Allah ya sa mu dace, muje zuwa my guys dan jin yadda za'a warware zaren da aka saƙa tun farkon labarin...












Tun fitar shi gidan da halin rashin lafiyar da ya barta a ciki sai hankalinshi ya kasa kwanciya,hakan yasa yana kammala period a school da shike English yake ɗauka kuma shine first period, sai ya nemi excuse ya dawo gida, kasancewar cikin kwana biyun akwai ɗan jituwa a tsakaninsu dan ta ɗan rage tsoronshi,hakan ba ƙaramin daɗi yake mashi ba,har ya ɗan fara farfaɗowa daga ramar da ya fara a kwanakin farko na auren nasu.

Da sallama ya shigo gidan...Hakan kuwa ya yi daidai da amsa ƙiran da Maryama ta yi na Sadeeq har yana tambayarta, "Pretty! is this you?".

A matuƙar firgice Siyama ta miƙe jikinta na maƙyarƙyata,sai dai abin da bata sani ba shi ne Maryama ta fita razana dan ita sumar zaune ta yi a inda take ko miƙewar ta kasa, da ace za'a tsaga jikinta a lokacin ta tabbata baza'a samu ko ɗigon jini ba.a ɓangare guda kuma Sadeeq na ta faman faɗin "Hello,hello" amma no respond.

Kamar wacce aka yiwa alluran ƙarfi ta miƙe da sauri har tana tuntuɓe ta kamo hannun Siyama dake tsaye a wajen tamkar statue kana ta rarumi jakarta fitt suka shige bedroom ɗin.

Wardrobe ɗinta ta buɗe gefen da babu kaya ta tura Siyama ciki haɗi da tura mata jakarta,duk kuwa da ya mata kaɗan amma haka ta takure jikinta ta shige tana ta zaro idanu kamar ɓera a cikin gari,take ta fara haɗa wani uban zufa numfashinta na ɗaukewa lokacinda Maryama ta tura marfin wardrobe ɗin gami da rufewa kiribb babu ta inda ɗan adam zai shaƙi numfashi.
(Wayyo Siyama ke dai kullum haÉ—uwar ki da Maryama bata zuwar maki da daÉ—i😢) 

Maryama na sanya kai da shirin fitowa shikuma yana Æ™oÆ™arin shigowa dan haka sukayi karo. A rikice take har bata kallon gabanta, kallo É—aya zaka fahimci tabbas babu nutsuwa a tattare da ita. 

Riƙo hannunta ya yi da niyyan su shiga ɗakin amma sai ita ta janyo nashi hannun zuwa palo, sosai hakan ya bashi mamaki amma sai bai nuna ba ya bita kamar raƙumi da akala,a tsakar palon ya tsaya haɗi da janyota ya rungumeta ta baya yana shafa hannayenta da suke da ɗumi kaɗan kaɗan alamar tana jin zazzaɓi. "Wife ya jikin naki. Tunanin halin da na barki ya hana zuciyata nutsuwa gami da koyar da ɗalibaina yadda ya kamata,ko dai mu tafi asibiti ne?".Ya karishe yana shafo wuyata.

"Am,ehm, ehh, a'a " birkitota ya yi da sauri suna fuskantan juna kallon cikin ido ya mata duk Æ™oÆ™arin da tayi dan janye nata idanun kasawa tayi, babu abin da Jabeer ke hangowa cikin idonta sai tsananin tsoro, tsoro mai tsananin gaske. "Wife! Are you okay?." Jabeer ya yi tambayar yana É—an jijjiga shoulder É—inta. 

Mai ke damunki duk kin birkice haka?" ya faɗa yana kai dubanshi da ƙarewa palon kallo.

Da ƙyar ta yi gathering courage ta ce,"Babu komai fa, kawai dama.. am.. shi..ƙyanƙyaso,eh yauwa ƙyanƙyaso na gani ina bacci a nan ya hau min jikina faa". sai kawai ta fashe masa da kuka.

Rikicewa ya yi sosai yana haɗata da jikinshi ya matse gam haɗi da sauƙe ajiyar zuciya ya ce, "Sorry wife, kyanƙyason nan bai kyauta mana ba, amma duk inda ya shiga yau a tsakanin bedroom da palon nan sai na fitar dashi na kashe shi yanzun nan ma kuwa, dan ya shiga hurumin da ba nashi ba ni kaɗai ke da hurumin taɓa jikinki dan haka dole in hukuntashi daidai da laifinsa, and da yamma zan siyo mana dettol da izal mu zuba musu a toilet ɗin dan nasan daga can zasu shigo mana nan," ya faɗa gami da sakin maryama ya juya zai shiga bedroom ɗin dan neman kyankyaso.

Zaro ido nayi ina dafe kirji, da wani irin speed na bishi banyi wani tunani ba na damqe shi ta baya na sanya hannuna duka biyu saman kirjinsa ina sakin wani kukan da wannan karon na shagwaɓa ne.


Cakkk Jabeer ya tsaya yana sauƙe wani irin ajiyar zuciya mai nauyi kafun ya yi ƙarfin halin cewa, "Pretty bari in nemo shi mana dan kar ya ƙara hawar miki jiki."

"To ai na riga da na kashe shi tun dazun da tsintsiya na fitar dashi ma waje na jefar kuma tun a lokacin ƙaɗangare ya cinye," na faɗa ina ƙoƙarin saisaita nutsuwata.

"Sure?" ya tambayeni bayan ya juyo yana É—aga min gira.

Gyaɗa mashi kai kawai nayi, amma deep down zuciyata tsalle take yi tamkar zata tsinke ta faɗo ƙasa, "So ya jikinnaki?" kin hana ni zama a school da tunaninki."

Cikin turo baki gaba nace "Nikam lafiyata qalau ka zo ka koma kar a nemeka, na riga da na warke," "Hmm ban yadda ba korata kike son yi da wayo kawai wife".Jabeer ya faÉ—a yana lakace hancina da yatsarshi.

"Da gaske Hamma Jay na warke faa Allah ka koma kar a nemeka", 

"Ohk zan koma amma sai kin bani wani abu mai daÉ—i wanda zan yi ta tunawa dashi a can".

"To ni mai nake da shi wanda zan baka, gashi Innarmu bata turo abincin rana ba" na faɗa ina turo baki gaba, bakin nawa yake kallo cike da sha'awa, kafun cikin nutsuwa ya ɗaura yatsarshi saman leɓena kamar yadda ya saba ya fara zagaye leɓen kamar mai tafiyar tsutsa still yana kallon cikin idona, bakinsa ya kawo daidai nawa a hankali ya furta, " wannan yafi min abinci daɗi" kamun in ankara ya bani wani sassanyan sumba a lokaci ɗaya idanunsa suna sauya kamanni.bai ƙara cewa komai ba ya juya da sassarfa har ya iso ƙofa kuma sai ya tsaya yana kallon tiren da na kawowa siyama ruwa dashi, da ido ya tambayeni "wannan fa?".

Da sauri na dawo daga suman tsayen da nayi na ce, "maƙwafta ne suka shigo min da na kawo masu ruwa shine ban fitar ba".

Yana shafa gashin kanshi ya ce, "Ya kamata mu samu ruwan leda wanda zaki ringa bawa baƙi idan sunzo ko?".

Bance komai ba sai Allah Allah nake ya tafi,shima bai ƙara cewa komai ba ya sa kai ya fice yana ƙara jaddada min cewa in kula da kaina. na kusan minti uku tsaye a wajen bayan fitarshi sannan na yi ƙarfin halin fita da sauri na sanya sakata a asalin ƙofar shigowa gidan na dawo, a bakin kofar palo na ga takalman siyama, Alhmdllh na furta ganin hankalinshi baikai kansu ba.

Da hanzari na afka ɗakin na buɗe wardrobe ɗina jiki na rawa. Gajab Siyama ta fado kasa tana zabga wani irin tari yayinda idanunta ke ƙwalalowa waje suna kakkafewa, jikinta kuwa kai kace a kogi aka tsundumata tsabar yadda ta jiƙe gajab da gumi.

Ruwa ruwa,shi ne abin da ta ke ta ambata a tamanin na koma palon,wannan ruwan dai da ta gama yi man izgili a kanshi, shi na tsiyayo cikin kofi na É—aura bisa bakinta, cikin sakan É—aya kuwa ta shanye tas tamkar zakanyar da ta shekara bata sha ruwa ba, hijab nata na zare mata haÉ—i da fara yi mata firfita da shi..

Kusan mintuna talatin sannan Siyama ta dawo hayyacinta, duk da haka dai tana bukatar hutu dan haka bance mata komai ba kamar yadda bata ce man komai ba da ƙyar ta lallaɓa muka dawo palo,hasken da wayarta ke ta faman yi ne yasata ɗagowa tana jingina da jikin kujerar da take zaune a kai, tana miƙomin wayar bayan ta yi picking gami da sanyashi handsfree ta ce, "Oga Sadeeq".

Hannu na rawa na karɓa ina karawa a kunnena ba tare da nace komai ba amma zuciyata bugu ta ke sosai tamkar ana surfa masara a turmin daka Hamma jay ne ke min gizo a idanuna, ina da ilimi na san cewa hakan is haram, amma na rasa dalilin da ya sa na kasa ƙin amsar wayar, daga ɓangarenshi ya ce, "Oh baby girl you want to kill me right?." zaro ido nayi na ce, "mai yasa kace haka?, "

Lumshe idanu ya yi ya ce, "Just forget it, bazaki fahimta yanzu ba sai kin É—an Æ™ara girma, now you're a small baby na fi son sai kin kammala degree na ki by then kin É—an Æ™ara girma kaÉ—an, atleast idan na faÉ—i maki abin da ke raina bazaki min yarinta ba." ya fada in a naughty way. "hmmm" kawai na faÉ—a ina jina tamkar wata sabuwar hallita a doron Æ™asa. Cigaba ya yi da faÉ—in, 

"Munyi maganar makarantar ki da Siyama ta ce parents naki sun amince dan haka na tura mata jamb registration fee naki sai kuje kuyi register dan kar lokaci ya ƙure and kiyi ƙoƙari kar ki bani kunya plsss,,amma kafun nan inason ki turamin layin dad naki za muyi magana dashi."

Zaro ido nayi a lokaci guda kuma ƴawun bakina ya kafe ƙam, dan haka na kasa buɗe bakin bare har in bashi amsa.

"Ki ce mashi babanki bai nan idan ya dawo zaki hadasu". Siyama dake saurarenmu tun fara wayar tamu ta faɗa ƙasa ƙasa yadda ni kaɗai zan iya jiyota. Hakan ko na faɗa mishi,baice komai ba sai jaddada min da yayi cewa da zarar ya dawo in haɗasu dan magana mai muhimmanci zasuyi.

Mun kwashe wani minti talatin ɗin muna hira da Sadeeq,tun ina amsa masa da eh a'a, har dai na sake na manta da yanayin da nake ciki na cigaba da cin amanar hamma jay ta hanyar hira da wani ƙato da ba muharramina ba har ina ƙyaƙyata dariya.

Haɗe hannaye siyama ta yi cikin juna ta ɗaura habarta bisa hannayen tana ta kallona yayin da abubuwa dayawa ke bijiro mata a kai tana ta murmushi. Da ƙyar ya yanke ƙiran bayan munyi sallama. Awajen muka hau tattauna yadda za'ayi in samu fita har muje muyi registern jamb ɗin ba tare da an samu akasi hamma jay ya sani ba...mun yanke shawara kan cewa idan ya fita aiki ranar litinin tunda sai ƙarfe biyu wataran yake dawowa zata zo da wuri ta ɗaukeni muje mu dawo tun bai taso daga makarantar ba.
*****

Hakan ko akayi kwanci tashi asarar mai rai, ranar litinin misalin ƙarfe takwas da rabi Siyama ta zo min, dama na shirya tun wajen takwas da hamma jay ya fita a gidan dan yau fitar wuri ya yi,dama shiya dafa mana shayi ya sayi bread da madara da ƙosai da shi muka karya dan zazzaɓin da na kwana dashi, gashi ya dakatar da innarmu turo mana abinci tun kwanaki huɗu da suka wuce shi ke dafamana a nan gidan watarana kuwa takeaway yake yo mana, dan haka ta na isowa bamu ɓata lokaci ba na sanya hijab tare da nikaɓ muka wuce bayan na kulle gidan da ƙwaɗo.

Ba mu wani ɓata lokaci ba acan ɗinma muka kammala muka dawo sai jiran ranar rubutawa ina ta godewa Allah, Hamma Jay bai dawo ba, a ɗaya ɓangaren kuwa wani irin farin ciki nake ji marar misaltuwa zan cika burina na tafiya jami'a, sai dai tambayar da nake yawan yiwa kaina shine 'ta yaya zan tafi makarantar?".(nima dai nace ta ya MARYAMA?).
                            *****
Haka muke ta gurgura rayuwar da kullum kwanakinmu ke raguwa aiyukkan zuciya mabanbanta kama da ga na sharri haɗe da na alkhairi suke wanzuwa a bayan ƙasa.

A cikin yan kwanakin da na zauna jiran ranar jarabawar abubuwa da yawa sun faru, ciki har da cikar wata ɗaya da samun aikin hamma jay yayin da aurenmmu ke cika wata ɗaya da kwana biyu, sai dai abin takaicin shine, wata ɗayar ta ƙare ba tare da an biya malaman primary albashi ba, kowa dai yasan yadda aka rena ma'aikatan ƙananan hukumomi a ƙasar nan, to hakance ta kasance dan haka abubuwa sun mana tsauri kaɗan, dama rufin asirin abincin da innarmu ke kawowa ne tinda ya hana kuma ɗan kayan garan da aka min shine muke ta ci har i zuwa yanzu da al'amuran ke taɓarɓarewa, da ka ga hamma jay kasan yana cikin damuwa amma babu wanda yake iya faɗawa.

Wajan aikinsu kuma ba wani abin arziƙi ake samu a can ba dama, babbar damuwar shi shine yaso yayi suprising Maryama da salary ɗinshi na farko ta hanyar yi mata registern jamb ya kuma sai mata waya ko da ko yar ƙaramace, baijin daɗin yadda take zaune haka babu waya, amma abin ya faskara and lokacin yi registern har ya wuce, ya so ace ya cika alkawarin da ya ɗaukar mata, sai gashi abincin da zai ajiye a gida ma yana neman gagararshi, don haka a yan kwanakin kullum da jan ido yake dawowa gidan na aiyukan wahalar da yake zuwa yi duk don ya samo mata abin da zata ci mai daɗi ko da ko shi bai ci ba..

Maryama kuwa a yan kwanakin sharafin soyayya take sha ita da Sadeeq É—inta thou bai fito fili ya bayyana mata yana sonta ba amma idan suna waya mantawa take ita matar aurece ya yinda shima yake mance cewa bai sanar mata yana sonta ba, kullum Æ™arfe tara na safe yake Æ™iranta kamar yadda ta bashi time wato in jabeer ya tafi makaranta, sai kuma Æ™arfe huÉ—u, ida jabeer ya dawo ya yi shirin ya tafi neman gumin halak, nan suke baje kolin hirarsu abin ba'a cewa komai. 

Itama siyama tana can tana ta bada ƙaimi wajen zuga Maryama da cewa ita ba kalan matar da za'a fita daƙo sannan a ciyar da ita bane, ita matar hutu cezugi dai kala kala sosai kuma hakan ke tasiri a rayuwar gidan nasu dan ɗan kulawar da yake samu a da sam yanzu bata bashi fuska. Idan ya zaunar da ita da nufin suyi magana sai ta hau shi da masifa tamkar ɗanta tun bata iya fitowa fili ta faɗi abin da ke ranta har ta kai ga Maryama ta dubi tsakiyar idanun Jabeer ta ce masa.

"Ni ba kalar matar talaka bace da sai ya fita ya nemo sannan ya ciyar dani ba, ni matar manya ce".

Waɗannan maganganu sun daki jabeer sosai har ta kai ga bayan kwana biyu saida ya ziyarci asibiti dan ganin likitan da ya ke bashi magani lokaci lokaci. Sai yanzu ya fahimta, sai yanzu abubuwan da suka yi ta faruwa a baya kafin auren su ya ke dawo masa dalla dallah a cikin kai tare da auna komai akan mizani sai dai hakan bai hanashi cigaba da nema ba dan ya ciyar da ita da kuma sauran buƙatun ta.

Haka kuma bai rage koda kaso É—aya cikin dari na tarin soyayyar da yake mata ba. Amma duk sadda ya tuna da kalamanta sai ya rumtse idanu tsabar yadda suke sukarshi, cikin lokaci kaÉ—an Jabeer ya bushe kamar wanda ya yi shekara yana jinya. 

Sosai hankalin Innarmu ke tashi idan ta gansa tambayar duniya ta mashi akan abin da ke damunsa amsar dai É—aya ce, "babu komai innarmu yanayi ne kawai").

Ba don ta yarda ba, sai dai kawai ta bishi da addu'a da kuma nasiha irinta iyaye masu ƙaunar ƴaƴansu. Tabbas jinyar zuciya wani lokacin tafi ta zahiri zafi da radadi.

                    ******

Yau muke rubuta jamb dan haka hamma jay yana fita nima na shirya yau ni naje wajen Siyama ba ita tazo ba muka rankaya centern da zan yi jarabawar. 

Cike da farin ciki na rungumi siyama bayan na fito a jarabawar da ta ɗauke ni 2hrs cikin murna na ce, "Siyama wallahi babu wani wahala gaba ɗaya na amsa tambayoyin har ma da ƙari Insha Allahu zanyi nasara haɗe rai siyama tayi tamau tana jin wani irin haushin Maryama mai haɗe da hassada, amma sai tayi saurin ɗagata tana ƙaƙalo fara'a gami da bubbuga bayanta tace "Insha Allah".

Bayan sati biyu sakamakon jarabawarmu ta fito a cikin wannan sati biyun sosai hamma jay ke haƙuri da ni dan ba ƙaramar wahala nake bashi ba, ko ɗan yatsata na daina yadda ya taɓa. Gaba ɗaya ya koɗe ya fice a hayyacinsa.

Haka yau ma na fita ba tare da izininsa ba ni da siyama zuwa cafe dan duba result ɗin kasancewar babu waya wajena. Alhmdllh na samu nasara fiye ma da points ɗin da ake buƙata, tun acan Siyama ta sanar da Sadeeq abin da ke faruwa cike da ƙwarƙwasar da ban san ta iya shiba. Sosai ya tayani murna da sanar min da zaran admission ɗina ya fito zai sanar min dama University of portharcourt Siyama ta cike min a first choice, ko da na tambayeta dalili mai yasa bazan nema a arewa ba sai ta ce, a can zan fi nutsuwa in yi karatu tunda babu wanda na sani sai Sadeeq a can and shikuma he's busy with his work dan haka zanyi karatu na cikin salama. And that's the begining of everything da ya samu rayuwata, wannan shi ne mafarin dukkan abin da ya samu rayuwata.

Cikin farin ciki muka kamo hanyar gida ina cike da ɗoki, tun da siyama taja ta tsaya a inda suka sauƙa daga keke napeep ɗin daya dawor dasu tana kallon Maryama da ta marairaice murya tana tambayarta, "Yanzu Siyama ya zanyi in sanar da hamma jay na yi jarabawar jamb har na samu nasara?".

ÆŠan ajiyar zuciya ta sauÆ™e sannan ta matso dai dai kunnena ta fara magana ta yadda ni kaÉ—ai zan jita,... zaro ido na yi kirjina ya bada wani irin sauti darrraammmm har saida na kusa faÉ—uwa kasa jin abin da siyama ta faÉ—a, girgiza mata kai kawai nake hawaye na silalo min cikin kuka nace , "Ina Siyama bazan iya aikata wannan ba, Hamma Jay ne fa? ina sam bazan iya ba". 

"To shikenan tunda bazaki iya ba, sai kije ki zauna da hamma jay ɗin muga idan zai iya biya maki ki cigaba da karatun sannan kin san tabbas kina karkashin wani kuma Sadeeq bazai biya maki makaranta ba, so go and think before lokaci ya ƙure maki, ba tare da ta ƙara ko kallona ba ta wuce abinta.

Da ƙyar nake iya ɗaga ƙafata zuwa gida, wata sabuwar faɗuwar gaba ce ta sameni ganin kofar gidan a buɗe bayan na rufe kafin in fita, da jan ƙafa na ƙarasa shiga har cikin palon. Tun da nayi arba da takalmin jay a bakin kofa yawun bakina ya kafe, amma sai na aro jarumta na yafa ina ɗaure fuska maganganun siyama nayi min yawo a kai...

Kwance yake kan doguwar kujera sanye da jallabiya, rigingine idanunshi a lumshe ya ɗaura hannu ɗaya saman kashi ɗaya kuma ya ɗaure saitin zuciyarsa turus na yi na ƙame a wajen ina ƙare masa kallo sai yau na lura da irin ramar da yayi.

Rinannun idanunshi da suka kaÉ—a suka yi jawur tamkar borkono ya sanya cikin nawa yana miÆ™ewa da Æ™yar, "Ina kika je?"ya faÉ—a cikin wata iriyar murya da ba tashi ba.."Ina kika je na ce!" ya kuma faÉ—a da É—an karfi. 

Shiru bance komai ba sai rawar da jikina ke yi.

Tasowa yayi zuwa inda nake yana ta rumtse idanu gami da cije lebe, ya amshi takardar da ke hannuna ya bude yana karantawa, wani irin jiri ne ya kwashi jabeer saura kadan ya fadi kasa ya dafe kujera yana fadin "Ya Allah".

Karfin jalin cewa nayi, "Wannan sakamakon jarabawar da nayi ne na jamb wani mai kudi ya biya min mai sona,mai son cigaba na, mai son inyi karatu,kuma na samu admission a university of por....


"Shuuuttt up!" jabeer ya fada da karfi yana dafe zuciyarshi.

Bazan yi shiru ba jabeer,"jabeer!" ya maimaita. Ehh bazanyi shiru ba sai na fadi abin da ke raina, na gaji, na gaji, na gaji da wannan bakar ta talaucin da na tashi a ciki sannan na tunkari karewa a ciki, bazan yadda ba, dole ne ka amince in tafi makarantar nan....Hayaniya takeyi sosai har bakinta na kumfa, ita kanta bata san abinda take fada ba, duk abin da ya zo kan harshenta furtawa kawai ta ke yi, banda rawa babu abinda jikin jabeer keyi,tunda yake bai taba ganin tashin hankali makamancin wannan ba arayuwarshi, anya wannan prettyn shi ce kuwa? any....


          ******

Cikin kuka Umaima ta fito daga gidansu kamar zata shide, har zata shiga gidansu maryama kuma ki me ta tuna ta fasa ta nufi hanyar gidanta tana kuka mai tsuma zuciyar mai saurare,a tsakar gidan ta tsaya tana sallama amma babu amsa saidai kamar tana jiyo hayaniya a cikin dakin hakan yasa batai wata wata ba ta afka ciki, aikuwa tayi mugun gani, dan maryama ce tsaye ta cakumi wuyar jallabiyar dake jikin jabeer sai masifa take, har idanunta na fitowa tamkar mai shigar aljanu.Jabeer kuwa na tsaye kikam sai kallonta yake fuskarshi yayi jajawur sai digar zufa ya ke yi labenshi yana ta rawa kar kar kar.

"Da gudu umaimah ta karaso gabansu har ta manta tashin hankalin da ta ke ciki ta fara jan maryama.

"Maryama are you mad?are out of your senses?how dare you kike aikata such things kamar baki je islamiyya ba?.

Ina maryama tayi nisa bata jin kira sai ma lumshe idanu tayi ta bude shawarar siyama na kai kawo a kwakwalwarta kamar ana buga mata karfe, cikin wani irin karsashi ta hankade Umaimah gefe sannan tana kallon cikin idon Jabeer tace, 

"Jabeer idan har ka cika dan halak cikin uwa da uba ba shege ba yanzun nan ka sake ni!"

Wani irin ihu Umaimah ta yi zata damke bakin Maryama amma ta kara hankada ta, a hankali Jabeer ya lumshe idanunshi, yana jin wani irin bugu da zuciyar shi yayi sau daya sannan ya dira ya balle daga jijiyarsa ya fada cikin cikinsa da kyar ya motsa baki ya ce. "Maryama na sake ki saki daya, tun bai gama cewa ba Maryama ta juya da sauri zuciyarta na bugawa ta fice