MARYAMA

Page 42

by @ummufadeela01

💫MARYAMA💫

     By 

Ummu Fadeela

TYPING📲

                                  

EPISODE 42.

BISMILLAHI-RAHMANNIR-RAHIM.


Wani irin ihu Umaimah ta yi ta fadi a gefen Jabeer sumammiya...

Innarmu yau ta shirya kawowa Maryama ziyara dan ganin dakinta, tunda aka yi bikin bata taba zuwa ba.

Tsaf ta shirya cikin atamfarta da babban hijab ta dan fesa turare sama sama ta fito Fati da itama ta shirya tsaf abinta tana zaune bakin kofa tana ta jiranta ta taso suka wuce.

Sallama suka dinga rafkawa a tsakar gidan amma shiru babu amsa ga ko ina a bude ga kuma takalmuna a kofar dakin wanda ke alamta cewa mutanen gidan suna nan.


"Innarmu basa nan fa watakila, ko inje in leka dakin?"

Cewar Fati. "a'a Fati mu tafi kawai ma dawo watarana kada ki tada su yanzu.."

Har Inna ta kama hannun Fatima sun fara tafiya, sai kuma ta tsaya cak tamkar wacce aka shuka wajen tana jin wani irin bad feeling har Numfashinta yana mata nauyi, haka kawai ta kasa daga kafar tata kuma.

"Inaga zo ki leka din Fatima, idan kinga suna barci kada ki tadasu sai ki dawo a hankali kinji" cewar Innarmu dake sauke ajiyar Zuciya kamar wacce tayi kuka.

Wani irin ihu Fati ta yi lokacin da ta yi arba da Jabeer kwance cikin jini ga Umaimah ma agefensa babu alamun numfashi tattare dasu.

Da wani mugun speed Innarmu ta afka dakin, kanta ne ya buga da karfi gingirigiiimmm tamkar an buga karfe da karfe.


"Hamma ka tashi dan Allah ka tashi, hamma hamma!

Anti Umaimah me ya sameku? ku tashi mana, kar ku mutu, Innarmu Jini bakin Hamma Jabeer jini baya magana."

Fatima ke ta sambatu tana ta jijjigasu.

Inna da tayi suman tsaye sai a lokacin ta dawo haiyaccinta, jiki na rawa ta nufe su, sai dai rasa abin da zata fara tayi. 

Dago idanunta da suka jike sharkaf da hawaye ta yi ta kalli Fati ta ce cikin sanyin murya "Fatima yi maza ki kira Baffanmu a kasuwa, kice ya zo da abin hawa".

To Innarmu amma ina anti Maryama take,?" sai a lokacin Innarmu ta ankare da cewa bata ga Maryama ba fa, amma sai ta ce, "Hanzarta Fati bakiga halin da suke cikiba."...

Kukan da take ta rikewa Innarmu ta fashe da, lokacin da Fati ta fita, cike da rudanin abin da ya same su take kuka hadi da fara neman Maryama a cikin gidan amma babu ita babu alamarta. 

Cikin wannan yanayin su Baffanmu da wasu maza uku suka shigo gidan dan duk fati ta mashi bayanin abin da ke faruwa.

Babu bata lokaci aka wuce da su asibiti dan tabbatar da suna raye ko sun mutu...

Emergency aka karbesu bayan sun iso asibitin. Wasu nurses ne suka fito da gadon daukar marasa lafiya aka dora su bisa gadon da dan gudu gudu suka wuce emergency ward da su. 

Ganin haka yasa su Innarmu da sauran mutanen ma binsu da gudu Suna.

A bakin ward din suka tsaya saboda ba'a isowa ciki. Iya makurar tashin hankali ne kwance saman fuskar iyayen.

Inna da Fati banda kuka babu abin da suke yi, sai zagayen wajen suke.

Awanni biyu cur likitocin suka kwashe kan Jabeer kafun Allah ya basu ikon janyo numfashin sa wanda ya yi nisan kiwo kana aka makala mashi oxygen tube.

Daya bayan daya likitocin ke fitowa, na karshenne ya umarci yana bukatan ganin makusancin majinyatan, haka yasa Inna da Baffa binshi zuwa ofishins.

Dan rubuce rubuce kadan ya yi kafin ya dago yana kallonsu ta saman farin gilashin dake fuskarsa ya ce, "Alhamdulillahi munyi nasarar janyo numfashinsa ya zuwa yanzu. Sai dai bai dawo hayyacinsa ba, ita kuma yarinyar dama ba wani abu bane suma ne tayi sakamakon ganin wani abin tashin hankali, so ta farka yanzu ita za ku iya ganinta.

Dan uwan nata ne dai yana bukatan kulawa mai tsanani dan zuciyarshi ce ta kumbura kuma ta na gaf da bugawa. Amma idan mun kiyaye Insha Allah babu abinda zai faru.

A rikice duk suke kallon likitan kafin baffanmu ya juya kan Inna ya ce.

"Ina MARYAMA?"".

A hankali Inna da ke zaune tamkar jini baya gudana cikin jikinta ta maimaita abin da ya fada.

"Ina MARYAMA?".

                     *****

Maryama da fitanta kofar gida cikin sa'a ta samu napep ba bata lokaci ta tsayar dashi ta afka ba tare da ta san inda ta nufa ba sai da ta daidaita zamanta cikin napep din sannan wani irin kuka ya taho mata har tana jin daci a makogoronta.

Kuka take yi sosai har jikinta na rawa.

(MARYAMA KIJE NA SAKE KI SAKI DAYA). 

Muryar Hamma Jay ya shiga dawowa cikin kanta tamkar yanzu yake fada mata. Da sauri ta dafe kirjinta dake bugawa da sauri sauri tana kara sautin kukanta. 

"Kukan me kike yi kuma Maryama?

Abin da kike so fa ya miki ba ke kika roki ya sake ki ba?".. Zuciyarta ta tambayeta. Jin hakan yasata saurin gimtse kukan nata amma abin ya ci tura.

"Hajiya ina mu ka nufa ne?" cewar mai napep dake ta galantoyi kan titi ga Maryama dake ta kuka bata ce mashi komai ba.

Jajayen idanunta ta dago ta fadi masa sunan anguwarsu Siyama.

A daidai kofar gidan ya tsaya ta fito tana zare idanu kamar wacce ta hadiye kunama sai yanzu ta tuna babu kudi hannunta da zata sallami mai napep dashi.

"Kudinki dari biyu ne hajiya". Muryar mai napep din ya doki kunnena, ina faman juya hannaye na nace "Dan Allah ka yi hakur...." 

"Wane irin inyi hakuri kuma hajiya, a'a karki yadda ki hadani da Allah ki cuceni a banza, kinsan baki da kudi mai ya kaiki aikata abin da kika aikata har zaki fito gari kina kuka akan titi?

Bani kudi na kawai, akan hakkina zan iya aikata komai wallah" Mai napep din ya fada cikin harzuka yana dirowa kasa tun Maryama bata gama fadin abin da tayi niyya ba. Wasu hawaye ne suka gangaro mata.

Daidai fitowar Siyama daga cikin gida waya kare kunnenta. Da sauri ta iso wajensu tana fadin, "Subhanallah, Maryama lafiya? mai ke faruwa?" ta jero min tambayar tana dafa kafadata.

"Siyama ki bashi dari biyu idan akwai canji a wajenki". Na fada muryata tana rawa.

Dari biyun ta bashi ta ja hannuna muka shige gidan nasu babu kowa a dan madaidaicin palon gidan, hakan yasa muka shige dakinta. Ina zama bakin gadon na sanya mata wani irin kuka mai shiga zuciyar mai sauraro. Cike da raunin murya da ta zuciya na ce, "Siyama hamma Jabeer ya sakeni!"

Ba Siyama da ta ke saurarona ba hatta ni da na furta kalmar saida na zaro ido ina jin kamar amai yana taso min gami da faduwar gaba.

Zaro ido Siyama ta yi ta dafe kirji baki a hangame ga wani irin faffadan murmushi saman fuskanta ta ce "Ban fahimta ba. Plsss come again"

Siyama hamma Jay ya sake ni fa nake fada maki amma kamar farin ciki naga kike yi. 

Siyama yau idan na koma gida babu abinda zai hana Innarmu ta saka ni a turmi ta min dakan sakwara ta shanya. Wllh Innarmu da Baffanmu tsinemin zasu yi Siyama do something plsss".

Na fada ina sakin wani sabon kuka.

Rufe baki Siyama tayi kafin ta daura hannu saman hancinta ta rabka wani uban gud'an da saida na toshe kunnuwata. labulen dakin aka dago Mamanta ta shigo tana zare idanu. "Me yake faruwa a nan?" cewar mamanta tana kare mana kallo.

"Kai Mama ya zaki shigo min daki haka kawai babu sallama dan kinji na yi guda." Siyama ta fada cike da raini tamkar ba mahaifiyarta ba.

"Kiyi hakuri yar albarka, na ji kinyi guda ne na ce ko wani abin arziki kika samo mana, bansan cewa tare kike da bakuwa ba," ta fada cikin rarrashi da kwantar da murya kamar ba yar da ta haifa ba.
(Inna lillahi wa'inna ilaihiraji'un, tabbas Manzon Allah SAW ya yi gaskiya.) Allah ka shirya mana zuriya badan halayenmmu ba.

Da kallo na bi ta bayan mamarta ta juya ta fita, saidai tashin hankalin da nake ciki bazai barni in ce komai ba, nima ta kaina nake yanzu. Tunanin yadda zan tinkari gida da wannan maganar nake.

Rumtse idanu na yi da karfi zuciyata da gabana suna bugawa a tare tunowa da nayi na yadda na fita na bar Jay.

Kwakwalwata ce ta fara tariyo min hoton fuskarshi da yanayin bakinsa da idanunsa lokacin da yake furta min kalmar saki.

"Dole inyi farin ciki Maryama, dole inyi farin ciki da farin cikinki. Ai ke wannan huta roro kenan. Ya miki abin da ya dace a lokacin da ya dace.

Zaki tafi makaranta ba tare da igiyar kowa daure wuyanki ba.

Ki gama makaranta ki auri Sadeeq mai kudi wanda zai iya dauke miki duk wani bukatunki na rayuwar duniya. Wannan babban abin farin ciki ne a wajenmu." Siyama ta fada bayan ta dawor dani daga duniyar tunanin da na tafi.

"Amma Siyama me ya sa zai sake ni dan kawai nace ya sake ni din,?" na tambaya ina jin wani zafi a kirjina.

"Haan Maryama ba ke kika ce ya sake ki ba. You just have to be happy cewa zaki yi free life naki a makaranta ba tare da wani damuwa ba. 

Wait Maryama ko dai kinason wancan talakan dan uwan naki ne dama ban sani ba?"

Da sauri na dago ina kallonta, haka kawai yau maganarta na ji ta min zafi a raina amma sai ban nuna mata ba na kuma fadin "but Siyama Hamma Jay ne fa.

Me yasa zai sake ni, su Innarmu zasu iya daukan ko wanne mataki a kaina saboda shi," tana kare min kallo ta ce 

" To sai me dan hamma jay ne? Duk kinbi kin daga hankalinki? Karki damu matukar zaki bani hadin kai komai zai tafi normal, and daga yanzu bazaki kara zuwa wajen iyayenki ba sai ranar da kika gama karatu kika samu aiki, kika yi kudi kika auri mai kudi. Ina tabbatar miki babu abin da zasu ce maki balle idan kinzo kin rushe wancan tsohon gidan naku kin tada sabon gini kin hada masu da kujerar hajji. Tsaf zasu mance abin da ya faru su sanya miki albarka,"

A hankali na ji damuwa ta kaso saba'in ya fita, har na fara imagination na rayuwar da zan yi idan abin da Siyama ta kirga min yanzu ya tabbata.

Wani irin murmushi na yi na ce, "Yanzu me abu na gaba Siyama, kin san dai da zarar Hamma Jay ya je gida dole zai sanar da su Innarmu komai and za'a neme ni kuma nanne first place da za'a fara zuwa." na fada damuwa shimfide saman fuskata.

"Komai da tsari na ke yinsa Maryama kar ki damu." cewar Siyama tana kama hannuna, "muje kiyi wanka" har bayin dake manne cikin dakinta ta kaini sannan ta fito gami da jan kofar ta rufe.

Wani irin tsalle Siyama tayi ta haye gadonta hannunta ta dunkule waje daya tace, "yes yess yesss,"tanajin wani irin farin ciki kamar an tsomata a aljannah.

A nan na karisa wuni ranar mai cike da bakin ciki wanda bansan dalilinsa ba,..a gefe guda kuma farin ciki ne fal raina na cewa zan cika burina a rayuwa na yin karatu da zama hamshakiya a duniya.

Wani irin zazzabi ne ya rufe ni bayan mun gama cin abincin dare. 

A hankali na rufe idanuna dan jay ne ya fado min a raina, kusan kullum ina fama da irin wannan zazzabin da daddare shike kula dani a irin wannan lokacin.

Paracetamol Siyama ta ballar min hadi da ruwan leda ina tamqe idanu na na jefa a baki,da hanzari na rike numfashina bayan na hadiye maganin, saidai duk yadda na so ganin na hanashi dawowa hakan ya ci tura yunkurin shiga toilet nayi saidai kafun in kai na fara kwarara amai anan wajen tamkar zan amayar da yan hanjina.

Sannu Siyama ke min tana shafa bayana, cikin galabaita nake gyada mata kai ina jin wani yunkuri yana zuwar min saidai babu aman dan duk abin da naci na riga da na fitar, da taimakon Siyama na kuskure baki na hadi da wanke fuskata na dawo saman gadonta na kudundune cikin bargo sai rawar sanyi na ke yi har hakwarana suna haduwa waje daya.

Ba don ta so ba haka Siyama ta nemo tsumma ta fara goge wajen da Maryama ta bata, sai yamutsa fuska ta ke tamkar dai zatai aman itama, "Shegiya tsabar jaraba har ta kwaso, zan kwashe aman nan ne kawai dan ina da yakinin zan kwashi rabona bayan an cire gantalallen cikin nan , dan ni kallo daya na san ciki gareta munafuka".

Cewar Siyama dake magana da zuciyarta tana cigaba da kwabe fuska. Tas ta goge wajen ta fesa freshner sannan ta dawo bakin gadon tana kallon Maryama dake ta makyerkyata sai sannu ta ke ta jera mata.

A nan gidansu Siyama na kwana yayin da zazzabi na ke ta gaba gaba. Ganin ina kokarin mutuwa mata a daki ne ya sa da sassafe Siyama ta kwashe ni muka tafi asibiti. 

Kati ta yankar mana muka bi layin ganin likita sai after 8 likitan ya iso ya fara aikin duba patients. Lokacin da layi ya iso kaina da kyar nake iya ganin gabana jikina ya dume zau da zafi idanuna sun kumbura suntum suntum.

Yan tambayoyi likitan ya min kafun ya tura mu lab. Sakin baki kawai na yi ina ganin likitan jin abinda ya fada na sakamakon gwajin da muka kawo masa. Ta ke na nemi zazzabin da na ke fama dashi na fara rasawa. Mayar da kaina na yi jikin kujerar da na ke zaune na jingina ina lumshe idanu na gabana na dukan tara tara.

"Ko nawa kake bukata zamu baka likita, Dan girman Allah ka taimakemu ka cire cikin nan".

Da sauri na dago kaina jin furucin da Siyama ta yi, wani banzan kallon da ta jefeni dashi ne ya sa ni maida kaina ba tare da na shirya ba wani irin mixed feeling na ratsa gangar jikina. So ina dauke da cikin hamma Jay kenan likitan nan ke nufi,? Ciki na haihuwa?.

"Dr. Kayi shiru ba kace komai ba. Dan Allah ka taimaka mana wallahi tsautsayi ne ya fada mata, idan iyayenmu suka gane zasu iya yankata da ranta, ka yi ceton rai likita" cewar siyama tana marairaice murya jin likitan baice komai ba ya harde hannu a akan table dake gabanshi sai kallonsu ya ke yi with much interest musamman Maryama.

"Dan Allah likita ka taimakemu." Siyama ta kuma katse shirun nashi. Gyaran murya ya yi ya ce, "Bama irin wannan aikin a nan, but tunda kin rokeni kin hada ni da Allah, zan taimaka in cire mata, amma da condition din cewa duk abin da ya biyo baya babu hannuna. Idan kin amince to. Thou bama fatar samun akasin ma, zaki biya dubu dari da hamsin kudin aikin"

Dam dam haka kirjina ya ke bugu jin abin da suke fada.

Jiki ya na rawa Siyama ta ce, "Mun amince dr. Allah ya kara maka rufin asiri".

Dago jajayen idanuna da suka rine na yi ina kallon dr. Na ce, "Ban amince ba".

"What? baki da hankali me? Ko kin fara hauka ne? Ya ina nemar maki mafita zaki watsa min kasa a idanuna. Kin san me barin ciki a jikin ki ke nufi da rayuwarki kuwa?".

Hannu na daura kasan marata ina jin wani irin dari kamar na zazzabi yana shigata tun daga tafin kafata zuwa tsakar kaina, "bazan cire ba Siyama, na Hamma Jay ne fa."

"Shut your mouth you fool!" Siyama ta fada cikin hargowa har tana kokarin kai mata cafka.

"Sorry madam, inaga kuna bukatan tattaunawa cikin sirri dan haka ku je kuyi shawara akwai wasu patient akan layi," likitan ya fada bayan ya mike.

Wani irin fisga Siyama ta yiwa hannuna ta jani muka fita, backyard na asibitin ta nufa dani saida muka yi nisa ta tsaya gami da jefar da hannuna ta na huci ta ce, "Maryama baki da hankali ashe ban sani ba? Yaushe kika zama haka? Ina burin naki, ohh wato ni kika mayar yar iska ko, ehh shegiya mana wato ga yar banza, ni ina can ina ta maki fafutuka amma zaki watsa min kasa a ido. 


Idan kin bar cikin nan fa hakan na nufin babu ke ba zuwa makaranta this year, ko kin dauka Sadeeq din wawa ne,? 

A ina kika samu ciki?i

Idan ya miki wannan tambayar kina da amsar da zaki bashi? ki dawo nutsuwarki Maryama.

"Amma Siyama cikin na halal ne fa, na hamma ja...." ki rufe min baki, kar in karajin kin kira sunan Jabeer a nan dole ki yadda a zubda cikin nan, idan kuma ba haka ba wallahil azeem ba bu ni babu ke. Duk yinkurin da nake na taimakonki dan ki cimma nasara a rayuwarki wallahi zan daina. 


Kuma ko a kan hanya kika ganni karki nuna kin sanni, and this is your final chance Maryama". Ko kallon inda Maryama take bata kara yi ba ta juya. 

Kamo hannunta na yi da sauri ina karya wuya na gefe yayin da wasu hawaye ke silalo min na ce, "Sorry plsss Siyama".

"Sorry for your self," ta fada tana fizge hannunta, kara rike hannun na yi ina rumtse idona dan har cikin raina na ji inason wannan cikin ba tare da nasan dalili ba. A hankali ta samu kan ta da fadin. "Na amince Siyama"....

Da wani irin farin ciki Siyama ta juyo ta bani wani irin runguma taana tsalle a wajen, "ko kefa, uyimmm yanzu zakiji dadin rayuwarki amma idan kinbar cikin nan komai tabarbarewa zai yi.

Haka inaji ina gani likita ya burge min cikina wanda ko daga riga bai fara ba, ya yo flushing nasu zuwa waje,ba karamar galabaita na yi ba dan jini na ringa zubarwa sosai saida likitan ma ya tsorata. Dole aka yi admitting nawa a asibitin ana min karin ruwa da jini a tare tsabar yadda nake bukatarsu duk biyun. kwana hudu na kwashe ina jinya babu laifi Siyama tana kula dani mamarta kuwa tana kawo abinci kullum thrice a day........

        *******

Kalmomi baza su iya expressing how happy iam ba,you people da kuka yadda kuka biyoni kuka sayi book two saidai ince Allah ya barmu tare...