SANADIN HIJIRA

Page 25

by @ummufadeela01

SANADIN HIJIRA

 By 

Ummu Fadeela


Elegant Online Writer's

 Chapter 25.



Durkushe nake a wajen hannayena duka biyu dafe da kasa kaina a dage ina kallon kofar da su Uwa suka bi suka fice daga gidan yayinda zufa ke karyo min a duk wata hudar gashi dake jikina idanuna sun kada tsabar tashin hankali.!


Na kwashe akallah mintuna goma a wannan Yanayin kafin Dakyar na iya zabura na mike dan nemar wa kaina da Mahhh mafita ganin abun sai kara kusantowa yake, ban yi taku biyar ba na ji karar shigowar su gidan da gudu ridididididi dukkansu sun hada uban zufa jikkunan su suna ta makyarkyata tashin hankali rubuce karara saman fuskokin su, suna kururuwar ihu da ambaton "Innalillahi wa Inna Ilaihiraji'una shikenan mun mutu sun mana kawanya sun zagaye gari babu hanyar fita" duk cikinsu babu wanda ya dawo da jakar kayanshi gaba daya sun zubar a hanyar gudu dan lokacin da suka fita garin ya gama daukar zafi a lokacin sojoji suka iso babu abun da ke tashi sai dirin motoci kirar igwa da manya manyan rokoki. Bouuumm wata irin kara mai tsinka yan hanji ya daki dodon kunnuwanmu tsabar rikicewa karo muka dinga yi da juna a kokarin tseren shiga daki, kuuumm Uwa ta buga kanta da jikin kofa, wani irin hajijiya taji yana dibarta dan azaba amma bata bi ta kai ba sai da ta shige dakin su Iya dake nan kasa ta kama taga gami da hayewa ta makale a ciki ta yi tsuru kai ka ce bera ce, tana share zufar dake tsatstsafo mata tana fifita da hannunta, sai a lokacin ta fara shafa bakinta da ya haye suntum a take.

"Ke Uwani kin shiga uku kwanciya ake ba'a hawa saman abu inba haka ba yanzu sai harsashi ya bi ta kanki ya wuce" cewar Iya da suka kasance karshen shigowa dakin. Wani irin tsalle Uwa ta daka gami da ruftowa kasa ta baje nan wajen dan ba karamin buguwa ta yi ba, sai a sannan ta ankara duk jama'ar gidan kusan su talatin da takwas a cikin wannan dakin suke, haka suka gwamutsu waje guda kowa yana iya addu'ar da tazo bakinsa ,yayin da karar harbe harbe da fashe fashe ke cigaba da karade ko ina..!


Da rarrafe na hau saman mu ganin duhu ya fara dan ganin halin da take ciki. Yadda na bar Maahh haka na sameta sai ma kara hauhawa da jikin nata ya yi na tsananin tashin hankalin da kunnuwanta ke jiyo mata...
                  ***___***___***

Lokacin da bataliyar sojojin suka kusanto shiga gari sai Al'ameen ya daga wani abu mai kama da kyamara wadda ke iya hango abu komai nisanshi ya saita akan idanunsa, da hanzari ya janye gabanshi yana bada wani irin sauti, mayarwa ya kuma yi dan san gaskata abun da ya gani ko dai gizo idanunshi ke mishi. Wata irin runduna ya hango na yan ta'@ddan sun durfafo garinsu Fanne gadan gadan yayin da kura ya turnuke sararin samaniya kai kace rundunar dawakai ne ke gudun tsere tsabar yawansu da ababen hawansu, wasun su akan motoci wasu akan babura ko wanne babur ya na daukan akalla mutum uku ko hudu gefe guda kuma suna dauke da manya manyan makaman yaki Wanda yafi na sojojin yawa da karfi, yawancin su yara ne da shekarunsu ke tsakanin sha biyar sha takwas ashirin zuwa ashirin da biyar, Musty ne yasauko daga motar da ya ke yanufo Al'ameen ganin yana tsaye da abun kallo daga nesa makale a idanunshi. "Ya akayi ne capt"?. Shiru Al'ameen bai amsa mishi ba yana can duniyar mamaki da al'ajabin abun da yake hangowa, 'yanzu duk wadannan yayan wasu ne, iyayene suka haife su, macece tayi nakuda ta haifa ta shayar ta ci kashi da fitsarinsu tayi kokarin tarbiyarsu amma rana tsaka aka yaudaresu aka daurasu akan keken bera da sunan Jih@di suna kashe rayukan bayin Allah n da basu ji ba basu gani ba Innalillahi wa Inna Ilaihiraji'un.'!


Fisge kyamarar da Musty ya yi ne ya farkar da Al'ameen daga doguwar nazarin da ya afka, da sauri shima Musty ya janye daga idonsa sakamakon abun da ya hango, "What"!!! Ya fada da wani irin karfi, kafin ya cigaba da cewa,"Capt, kaga abun da n...." Al'ameen bai bashi damar karisa abun da ya yi niyya ba ya katseshi, "Musty mu kara azama NO GOING BACK, lallai mu yi kokarin ganin wancan runduna basu Kai ga shiga cikin garin nan ba dan tabbas idan suka shiga ba karamar barna zasu yi ba". Amma Al'ameen kaga irin muggan makaman dake hannun yaran nan kuwa"? Musty ya tambaya cikin wani irin kidima amma kasancewarsa soja mai cikakken horo yana kokarin danne hakan. 


"Yes Musty kuma dole mu tunkaresu a hakan mu mayar dasu baya. Daga haka suma suka fara nausawa suna tunkarar rundunar yan ta'@ddar, lokacin da suka fahimci jami'an tsaro sun zo domin tare su nan fa aka fara bata kashi tsakaninsu babu abun da ke tashi sai karar harbe harbe da mabambanta sauti, a daf lokacinne kuma aka gama jana'izar su Baba Modu da su Almuhajir😭.yayin da jama'ar gari suka rude suka gigice suka dimauce kowa ya fara gudu domin ceton rai.
Ko wanne bangare a tsakaninsu sun ji jiki musamman su Al'ameen da ya kasance kayan aikinsu bai Kai na yaran ba, sun kwashe lokaci mai tsayi suna artabu lura da Al'ameen yayi yaran suna gaf da cimma su yasashi yi masu nuni da su koma baya ba Wai dan sun kasa ba sai don bukatar neman agajin gaggawa daga sama. ganin sojojin sun janye ya ba yan ta'addan damar kutsawa cikin gari cike da karfin iko da karsashi bayan sun janye kimanin mutum tara da su Al'ameen suka kashe musu su kuma a nasu bangaren ba su samu asaran rai ba sai soji biyu da suka ji ciwo.
Al'ameen yana aikin cirewa wadanda suka ji rauni harsasan da suka ma'kale a jikinsu wayar aiki (Working talking) kare a saitin bakinshi tashin hankali rubuce karara saman fuskarsa yake magana, "Hello hello, AF Almisry ke magana, hello hello. Da gaggawa MG ya dauka kamar jiran kiran yake, "Capt wani hali ake ciki.?" da sauri sauri yake magana duk da kasancewarsa nutsatstsen mutum, "Sir Lallai muna bukatar taimakon gaggawa na hadin guiwar jami'an sojojin sama da kuma karin kayan aiki..."nan ya zayyanewa MG duk abun da ke faruwa da kara tabbatar mishi bukatar kasancewar jami'an sojojin sama a tare dasu.
Lokacin da suka samu damar kutsawa cikin gari Kai tsaye Ofishin yan sanda suka nufa in da suka banka wuta a ciki dama duk yan sandar suma sun yi ta kan su kana suka nausa cikin gari suna ta harbin kan mai uwa da wabi gami da bankawa shaguna wuta, a wannan yanayi ne su Uwa da sauran jama'ar gidan suka fita da niyyar barin garin suka bar Fanne durkushe a bakin kofa cikin rashin sanin yadda zata yi da maahh wannan hali, sai dai Bata Kai ga tashi a inda sukabarta ba suka dawo a dari da tamanin sun zubar da akwatunansu sakamakon yadda yan ta'addan suka cimma garin.

           ._____*****_____*****_____.

                     *Abuja*

Baya baya Abeey ya fara yayin da mahaukaciyar dariyar da wanda ya Kira da Alburhan ke ci gaba da karade dakin cikin yanayi maras dadin sauraro saura kiris ya fada ta bayan windown Alburhan ya mika hannunshi sai ga hannun yana mikewa tamkar ana warware zare yayin da zako zakon faratan dake jikin hannun ya damki wuyan Abeey sai gashi a tsakar dakin....!
A firgice Abeey ya farka daga mummunan mafarkin da yake yi zufa na yanko mishi ta ko wanne bangare na jikinshi tamkar ya yi wanka a kogi, lalube ya fara a kan gadon wayam babu Fanta babu labarinta a inda take kwanciya wadda hakan ke nuna ta fita tunda ya san tare suka kwanta, jiki na rawa ya lalubo makunnar wuta (switch) gami da kunnawa take dakin ya gauraye da hasken kwayayen lantarki kwanyar tamkar safiya, ya jima yana zaune tsakiyar gadonsa yana kokarin rarrabe abubuwan da suka faru a mafarkin, da gaggawa ya juya gefen kujerarshi da ya ga Alburhan a Kai sai idanunshi suka dinga nuna mishi tamkar kujerar tana tashi da kwanciya irin yadda ya gani cikin mafarkinshi dan haka ya tashi da hanzari ba tare da ya bar tsoron dake cikin zuciyarshi ta bayyana a saman fuskarshi ba. Zagaye ya dinga yi a falon kafin daga bisani ya fara lalubar wata namba a wayarshi bayan ya duba time dake nuna mishi karfe daya da minti talatin da biyu na dare hakan na nufin karfe 2:32 kenan na dare a masar.


"Hosni! akwai matsala, da alamun boyayyen sirrin da aka dade da binnewa shekaru sama da talatin tana gaf da tonuwa, Wanda idan har hakan ta kasance lallai Maza zasu ji a jikinsu." Cewar Abeey bayan Hosni ya kama kiran da ya doka mishi. mikewa Hosni ya yi daga kwancen da ya ke yana mutsutsuke idanu da muryar bacci ya ce, "Fadlallah kasan bana gane yaren hausa sosai mussaman idan aka hada hausa cikin hausa, me kake son cewa ne ka tadani cikin wannan sulusin daren ban fahimce ka ba. akwai alamun rudewa tattare da Kai".


"Hosni, Alburhan bai mutu ba yana raye dan yau ma na kuma haduwa dashi".
"Mmmmmm me ka ce Fadlallah?" Hosni ya fada da hardewar harshe lokaci guda baccin dake cike a idanunshi suna washewa...abun da kaji shina fada Hosni, Alburhan bai mutu ba yau ma na hadu dashi a shataletale".


"Kunyi magana ne?" Hosni ya fada cikin firgici har yana son fin Abeey da ya ga komai rudewa."Bamuyi magana ba amma..........."nan ya kwashe komai ya sanar dashi tun haduwarsu a roundabout har zuwar mishi da yayi a mafarki da kuma yanayin da ya zo mishi. Tuni zufa ya fara wankewa Hosni fuska har yana sharcewa da hannunshi duk da cewa akwai na'urar sanyaya daki a dakin nashi, amma jin karshen zancen Abeey na cewa a mafarki ya ganshi sai hakan ya sassautawa Hosni yanayin da ya shiga har yana kecewa da dariya har da buga ciki da buga bangon gadon da yake bisa, "Hhhhhhhhhh Wannan ya kara tabbatar min da cewa lallai Fadlallah ba Safinatu kawai ke bukatar ganin likitan kwakwalwa ba, har da kai. Sau nawa zan sanar dakai cewa Alburhan ya mutu kuma tare da Kai muka kwantar da shi cikin rami, ya kamata a ce ka sanyawa kanka nutsuwa wannan hallucination ne, gizo ne, gizo yake maka amma bashi bane, me yasa ka tsawon shekara talatin bai bayyana ba sai yanzu? kawai sharrin shaidan ne. 

Wata irin ajiyar zuciya Abeey ya sauke ba don ya yadda da batun Hosni ba sai dan yana bukatar lokacin yin tunanin abubuwa masu yawa, "Anyway sai da safe kawai" ya fada yana yanke wayar. Tsaki Hosni ya yi yana magana kasa kasa gami da kashe wayar tashi ma baki daya dan bai son damuwa kuma.!
Rufe idanu Abeey ya yi ya bude a lokaci daya kana ya fara bubbuga kanshi da hannu bibbiyu, "Ko dai da gaske nima na fara haukacewa ne kamar yadda Hosni ya fada, me ke Shirin faruwa ne? Ya yi wa kanshi tambayar da babu mai bashi amsa.
       
*Washegari da wani sabon tashin hankali Badar ta tashi tun bayan da allurar baccin da akai mata ya saketa, gidan gaba daya ya rikice dan sai a lokacin suka samu labarin yan tada kayar bayan sun yi nasarar shiga garin bayan sun karkashe sojojin da suka je dan kaiwa jama'ar gari dauki,(kadan kenan daga cikin sharrin social media). a tashin farko sumewa Badar ta yi Abeey kuma a take jininsa ya haura dama ya kwana cike da firgici a gefe guda kuma wani irin gurnani mai tafe da sautin nishi Ummie ke fitarwa daga dakinta tana kwance ko yatsarta bata iya dagawa, Ummah ta gigice ta rikice da kyar ta iya kiran wayar Dr shettima dan ya kawo mata dauki. 

Saudat na Duke akan Badar sai faman shafa mata ruwa take yi,da kyar ta iya kawo numfashi, tana farkawa kuma ihu ta zunduma tana zambarmar a barta ta tafi wajen Al'ameen Saudat tana riketa, ihu take wayyo shikenan sun kashe min shi, wayyo ku barni nima in bishi, Anty nima mutuwa zan yi ku barni in bishi" take cikinta ya kara rikicewa da hautsinewa, da hanzari Saudat ta saketa ta ruga toilet dake palon a guje, gudawa ta dinga yi har karfinta ya kare, kafin Dr shettima ya iso Badar ta shiga bayi ya Kai sau shida dole da dabara ya kuma mata allurar bacci kana ya daura mata ruwa ya zuba wasu allurai na tsaida gudawa a cikin ruwan, Abeey ma dole a karshe ruwan aka daura mishi da allurar bacci inda likitan ya yi gargadin kar wanda ya tadashi har sai ya tashi da kansai dan jininsa ya Kai kololuwa wajen hauhawa

Ummah ce ta mishi jagora har zuwa dakin Ummie, tana kwance tamkar gawa babu abun da ke motsi a jikinta sai wannan gurnani mai tafe da huci dake fita, duk in da imanin mai imani yake idan ya kalli Ummie a wannan lokaci sai ya zubar mata da hawaye, itama wata allurar ya kuma yi mata a cewarshi zazzabine mai zafi ya rufeta, Ummah ta rakoshi har bakin mota sukayi magana na tsawon minti uku kafin ya tafi, kamar kar ya tafi jikin Ummie ya kuma rikicewa gurnanin da take fitarwa yafi na farko, Shigowar Ummah daga raka Dr shettima ya yi daidai da fara burarin da wayarta ya dauka, waige waige ta yi sai da ta tabbatar babu kowa wajen, da hanzari ta yi picking ta kama hanyar kitchen.


 *FANNE*

Tabbas bayyana halin tashin hankalin da muka shiga bata lokaci ne, a wannan ranar da Ubana da baffannina da kuma masoyina da sauran al'ummar musulmai suka rasa ransu, duk da haka ba'a barmu mun huta ba, ba'a barmu mun masu addu'a ba tashin hankali da harbe harbe da kone kone kawai ke tashi a garinmu, sai wajajen karfe sha daya na dare suka tsagaita, a zuciyoyinmu muna hamdala da godewa ubangiji sai dai duk da haka babu Wanda ya runtsa ko wannan barawon bacci babu Wanda ya yi nasarar sacewa.

Ana murna bako ya tafi ashe yana labe a bayan gari, domin kuwa asubar farko karar bindigu ne suka mana assalatu, gabas da yamma kudu da arewa harbe harbe ke tashi kusan minti talatin sannan aka fara kiran sallah da wasu muryoyin da bamusan irinsu ba, wannan rana ta kuma shiga cikin jerin ranakun da bazan taba mantawa dashi ba a rayuwata, tun da muka idar da sallar asubahi suke harbe harbe babu Wanda ya iya sanya ko da ruwa kurbi guda ne a bakinsa Maahh numfashinta sai hawa da sauka yake idanunta suna kakkafewa yayin da dan dake cikinta yake wani irin zillo da barazanar balla cikinta ya fito tun lokacinsa bai ba. Hannu na daura aka zan fasa ihu sai kuma na yi saurin damke bakina ina salati da Kiran suna Allah buwayi gagari misali mai kowa da dukkan komai, nasan yasan halin da muke ciki kuma shine zai taimake mu da taimakonsa, da gudu na fito daga dakin na sauko kasa, dukkan gidan suna tare a kasanmmu kowa ya yi jugum jugum cike da damuwa kar ma Uwa taji labari duk ta firgice ta fice a hayyacinta., sai a lokacin na kara tabbatar da cewa a wajen Baba da Ya Almuhajir kawai muke da tasiri a gidan nan tunda gashi kowa yana nan amma babu wadda ya tuna cewa a wanne hali muke a ciki, wasu hawaye masu masifar zafi ne suka cika min kwarmin idanu. "Haann Fanne?" cewar Ammah da sai a lokacin ta lura da tsaiwata a wajen, "Aminatu fa?" Ta tambaya a lokaci guda tana mikewa ta nufo inda nike,"Maahhh,mahhh Maahh tana bukatar taimako na fada cike da rawar harshe lokaci daya na rasa duk wata juriya da karfin halin dana arawa kaina kawai na fashe da kuka....

"Eh ba shakka, kun ga jaraba ko, yo in ban da jaraba ya muna ta kokarin takurewa waje guda dukkanmu zaki fito tsakar gida ki rafsa mana ihu salon mutanen su san da jama'a a nan, kin rufe mana baki ne ko sai na taso na lallasa ki matsiyaciya irin tsiya?" cewar Uwa tana watso min wata irin kallo daga can kurya.
"Bazai yiwu ba fa Uwani, yanzu kowa zaman kansa yake a gidan nan kina cewa kule za'a ce miki caaass dan haka ki kama girmanki tun wuri".
Cewar Iya da tayi zaraf ta mike ta iso garemu itama, shirun kuwa Uwa tayi kamar an sanya sufagulu an rufe bakinta, 

Bayana Ammah ta ke shafawa a hankali, "Muje ga Aminatun" ta fada bayan ta tusani a gaba, sai iya da yakura suma suka biyomu, mu hudu amma dakyar muka dauko Maahh zuwa kasa sakamakon yadda jikinta gabadaya ya saki, duk wani taimakon da suka san zai taimaka mata suka dinga bata duk kuwa da luguden wutar da ake a waje. a haka muka wuni a wannan wajen babu mai yin ko motsin kirki babu abinci babu ruwa dama abun ka da gidan talaka bawai abincin yana zaune bane, sai iyaye Maza sun fita sun yo fafutuka kafin ake daura sanwa to yau babu mazan babu kuma hanyar fitar Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un haka muka wuni a wajen ba tare da sun tsagaita da barin harsasai da suke yi ba. wasu daga cikinmu sun sha attempting fita amma suna dawowa a guje dan babu hanyar fitar.

Wani tashin hankalin kuma shine misalin karfe biyar na yammaci zuwa lokacin mun gama galabaita da yunwa sai ga jiragen yaki ta sama suna shawagi da barin wuta a gefe daya kuma karar harbi ya yawaita dan su Al'ameen sun dawo da karfinsu, fafatawa ake a tsakanin su bilhakki, ganin wannan jirgi ba karamar razana su Yakura ya yi ba a cewarsu wannan jirgi yafi komai muni dan harba B@mb yake ba bu ruwnshi da wannan jama'ar gari ne wannan yan ta'addane. haka muka shafe wannan dare da ya kasaance dare biyu kenan cikin mummmunar fargaba da yunwa, washegari da safe aka sake daura damarar fita muna zazzaune a tsakar gida ina ma'kale jikin Maahhh na sarke hannayena cikin nata karfin ikon Allah ne kawai ya bar min maahh raye amma ta gama galabaita, lissafi ake na yadda zamu bi ayarin jama'a dan mu bar gari mu zama y'an GUDUN HIJIRA, kamar a mafarki suka fado cikin gidan namu, duk cikinmu babu wanda hantar cikinsa bai kada ba. za su Kai akallah mutum goma sha biyar sirarane sosai wasunsu farare ne tas sun fi kama da mutanen Chadi haka sun sanya tufafi irin shigar yan Afghanistan sun zagaye kawunansu da wasu bakaken yadi kafadunsu rataye da manyan bin@digu Wanda ya kusa fin karfinsu, dukkan su sun yi datti babu kyan gani sannan akwai aalamar yunwa a tattare dasu, yara ne sosai da idan ba don bindigun dake rataye a kafadunsu ba riko daya aka musu zasu iya karyewa dan rashin Kumari.!


Tsayuwa suka yi a kanmmu suna kare mana kallo daga sama har kasa, dukkanmu babu wadda ya iya daga kanshi ya kallesu sai makyarkyata da muke yi, magana suka yi da wani yare shi ba hausa ba kana ba kanuri ba kafin daya daga cikinsu cikin ya ce, "Ina kafuran mazajenku suka buya,? ku kirasu mu koya musu addinin gaskiya"... 'Wallahi sun rasu, dukkansu sun rasu jiyan nan, jiya aka kashe su a jumma'a duk gidan nan mata ne babu namiji ko guda dukka sun yi shahada, Uwa ta fada cikin rawar baki.


Dariya babbansu ya kece dashi kamar jikan boka ya sanya hannu gami da janyo wuyar hijabin Uwa da ke maganar yana fadin, "ku kuma mata bari kuga yadda ake yi daku" duk aukin Uwa sai gata wanwar a kasa, "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'una"! Shi ne abun da Uwa ta iya furtawa jikinta na rawa kamar an jona mata shocking, caaaakk ya tsaya daga tinkarota da ya yi yana tsefe gemunshi da yatsu ya ce, "Ashe kafurai ma sun san kalmar Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, fassara min kalmar me take nufi?" ya tambayi Uwa cikin zaro idanu, a take harshenta ya daure duk yunkurin da ta yi na son bashi amsa ta kasa tsuru ta yi tana ta fitar da zufa, sululululu wani irin fitsari mara control ya kwacewa uwa sakamakon abun da ta ga ya fitar yana tunkarota.....