BIYU A ƊAYA

Chapter 9

by @barista

BIYU A ƊAYA 

Page 9

Sayyada barrister 
***
YOTA 13 
TEAM FIVE INK LEGENDS


NIGERIA Maiduguri KIRAWA'S FAMILY 

Dr Waahab yana barin side na Daddynsa ya wuce side na Mamie, yana isowa ya yi nocking ya tura ƙofar a hankali tare da sallama, Hauwa dake zaune kusa da Mamie suna tattaunawa ta amsa, tare da gaida shi 

"Barka da safiya Ya Waahab"

"Yawwa"

Ya faɗa ya zauna kan carpet tare da gaida Mamie 

"Ina kwana Mamie"

"Babangida Barka dai an tashi lafiya"

"Alhamdulillah Mamie"

Ya yi shiru, Mamie ta ta fahimci da magana a bakinsa, ta maida hankalinta gare shi tare da cewa 

"Babangida lafiya?"

A hankali ya ɗago ya yi magana cikin sanyin murya 

"Tafiyar mu gobe ne?"

"Gobe kuma?"

Cewa Mamie da mamaki, ya sauke numfashi tare da cewa 

"Eh yau ne aka sanar damu akwai taron da za ayi a Abuja, ana so mu halarta"

"To ikon Allah, za ka dawo Maiduguri bayan taron kenan?"

"A'a Mamie daga cen za mu wuce"

"To ya yi kyau, Allah ya bada sa'a, ya kai ku lafiya, ya tabbatar da alkhairi"

"Amin, ya jikin Mommie?"

"Jiki dai Alhamdulillah, Daddynka ya ce kun tsaida magana akan za a fitar da ita outside"

"Eh haka ne, Allah ya bata lafiya"

"Amin"

Ya mik'e ya yi mata sai anjima ya fice zuwa ɗakin Mommie, ƙofar a buɗe take don haka sallama yayi ya shigo, Jamila ce ke zaune ta amsa sallamar ya ƙaraso ya zauna kan stool suka gaisa yake tambayar jikin Mommie ta ke sanar dashi bai jima ba ta koma bacci, sun ɗan taɓa hira da ita don mutuniyar shi ce sosai sannan ya koma ɗakinsa ya ci gaba da shirin tafiyar....


***********

Ashfat na kwance ta faɗa a zurfin tunani game da abin da take ji akan Dr Waahab, zuciyarta ta kasa sukuni tana yi mata zafi, me yasa zuciyarta za ta yi mata haka? Me yasa zata kamu da son wanda bai ma san tana yi ba? Me yasa za ta kai kanta inda ba a san da zuwanta ba? Ita da ba kowanne namiji take kulawa ba, maso kuɗi, masu mukami, attajirai, manyan mutane duk sun nemi su haka alaƙar soyayya da ita amma taƙi shine zuciyarta ta kai ta in da ba a mara ba da ita...

To amma za tayi taga shima ya yi maraba da ita kamar sauran mazan da suke binta take watsar dasu, to ta yaya? Yaushe? A ina?

Ta sauke numfashi tayi murmushi a lokacin da ta tuno da cewa Mamie tana maraba da ita cikin rayuwarta, za tayi amfani da son da Mamie ke yi mata har ta samu ta cimma burinta....

"Ke me ye haka, ke kaɗai kina zancen zuci kuma kina murmushi?"

Danna mata bugu a bayanta Hauwa tayi sannan ta ke tambayar ta, saurin tashi tayi daga kwanciyar da ta yi ta kalle su taga dukkanin su sun kura mata ido suna mamakin sauyin da ta samu lokaci guda...

"Amma Hauwa bana son abin da ki ka yi min, me yasa za ki yi min haka?"

"Yi hakuri gani nayi kin fara haukacewa shine na dawo dake hayyacinki"

"Hauka kuma?"

Cewar Ashfat cike da mamaki take duban su, Suhaima ta ce

"Eh fah sai murmushi kike kina zancen zuci, tun ɗazu fa"

Ta sauke numfashi tare da cewa 

"Ina ruwanku da abin da nake yi, bana son sa ido, main your business"

Dariya su ka yi, ganin ta koma tayi kwanciyar ta, Hauwa ta ce

"Uhm Ya Wahaab ma gobe zai yi tafiya"

Da sauri Ashfat ta tashi ta zauna tare da cewa 

"Tafiya kuma?"

Suka tsaya suna kallon ta, Hauwa ta jaddada mata tafiya zai yi, ta sauke numfashi tana jin ƙirjinta na yi mata raɗaɗi, tana ta faman shirya plan nata akan sa, ashe ma tafiya ce a gabansa, ta koma ta kwanta...

"Ni kam sis Ashfat anya ba kamuwa da soyayyar Ya Waahab ki kayi ba?"

Ta kalli Hauwa sai a lokacin wani idea yazo mata, tayi murmushi da Hauwa da Mamie za tayi amfani dasu wajen mallakar Abdulwahab Waseem KIRAWA......

***********************************

GHANA Alaja SPECIAL RESTAURANT 

Bilqees jiki a sanyaye ta baro gida, don tun jiya har wayewar gari bata ga fuskar Alaja ba, ko biya mata da ta ke yi ta ɗaukota su taho tare ma yau bata yi ba, ita kaɗai tazo restaurant. 

Tana sauka a mashin ta sallame shi ta shigo a lokacin ma ma'aikata sun fara shigowa, jiki a sanyaye ta shigo reception gani tayi suna binta da kallo jikinta ya sake yin sanyi, har ta wuce dining areas zata wuce ciki, taji muryar Alaja na yin waya, a side room, ta dawo da baya ta shiga ganin ƙofar a buɗe take yasa ta turo ƙofar ta shigo. Ta zauna har Alaja ta kammala wayar, cikin sanyin murya ta ce

"Bonjour Maa"

Alaja ta zuba mata jajayen idanunta ba tare da ta amsa mata ba na wani lokaci, hakan ya sake ɗagawa Bilqees hankali, jikinta ya soma rawa haka ma muryarta, da ƙyar ta furta

"Na tuba Alaja, ba zan sake yi ba, kuma ba da sanina na yi hakan ba"

Gyara zama Alaja tayi ta mimmiƙe gajerun ƙafafunta wanda suke da cika ido tayi magana kamar ta tashi ta kwaɗa wa Bilqees mari....

"Hakurin da kike bani ba zai yi tasiri ba, saboda kin kai ni bango, sau nawa kike ɓata min rai nake shanye wa, ki yi duk abin da kike so bana magana, ba wai bana sane bane, a'a kawaici nake yi. Amma wannan karon ba zan yarda ba, sai na cire kuɗin plate nawa a jikin ki"

"Don Allah Alaja ki yi hakuri, kada ki hanani albashin wannan wata, na roƙe ki, Mamata za ta je asibiti follow up"

Ta faɗa tana hawaye...

"Kukan ki ba zai canza komai ba, magiyar ki ba zata sauya komai ba, abin da na faɗa shine kawai hanya mafi sauƙi da zan bi na huce da asarar da ki ka yi min"

"Alaja I'm really sorry, na san nayi laifi amma ki yi min sassauci ba zan sake ba...

"Tashi ki fice ki bani waje"

Alaja ta faɗa cikin ɗaga murya, jiki a sanyaye Bilqees ta fito ta wuce kitchen, ba tare da ta kula kowa ba ta zauna kan madaidaicin kujera ta cire jakarta dake maƙale a bayanta ta ajiye tana share ƙwalla. Farin ciki sosai ya ɗarsu a zuciyar Laraba da Jummai kamar su zuba ruwa a ƙasa su sha haka suke ji, wannan yanayin da su kaga Bilqees a ciki ya fiye musu komai farin ciki ina ma ta dawwama a haka. Amma bangaren Majada kuma sai zuciyarta ta karaya taji bata kyauta wa Bilqees ba, duk laifin ta ne, gashi Bilqees na fuskantar hukuncin da bata da alhaki akai..

Ta taso ta iso inda Bilqees ke zaune ta zauna a ɗayan kujerar tare da cewa 

"Friend me ya faru ki ke kuka?"

Haɗiye kukanta tayi, tare da cewa 

"Nothing more"

"Jikin Mama ne?"

"Majada, i need a space please"

Majada ta mik'e jiki ba kwari, ta iso inda su Laraba suke, ta zauna tare da cewa 

"Ku yi hakuri ba zan iya ci gaba da ganin Bilqees tana hawaye ba"

Jummai ta dire tare da cewa 

"To kuwa za ki ga kan ki kina hawaye, muddin kika janye daga abin da mu ka saka ki yi"

"Ke har ma kina bata amsa, ni ai ko tanka wa ba zan yi ba, batun janyewa ma bai taso ba, tun da taji sirrin mu to sai ta aikata abin da muka saka ta"

Cewar Laraba, Majada ta rafka tagumi tana kallon Bilqees cikin tausaya wa, bata san ya za ta yi ba...

Shigowar Alaja cikin madafar abinci ne yasa kowacce maida hankali kan aikin da take yi, banda Bilqees da ta rafka uban tagumi ta faɗa cikin duniyar tunani...

"Bilqees!"

Alaja ta faɗa da ƙarfi, a tsorace ta ɗago ta kalleta ta ce

"Kina nufin ba za ki yi aiki ba?"

"Zan yi"

"To menene ki ke yi a zaune?"

"Ba komai"

"Daga yau na maida ki cikin Server's, kada na sake ganin ki cikin kitchen"

Bilqees ta sauke ajiyar zuciya, bata so hakan ba, Serving akwai wahala, wuni za tayi akan ƙafafunta tana hidima da customers...

"Ki wuce bangaren su"

Ta mik'e ta fito zuwa bangaren Server's, hakan ba ƙaramin ɓatawa Laraba da Jummai rai yayi ba, Alaja ta rusa musu shiri.

Alaja ta fice daga cikin kitchen ɗin cikin ɓacin rai, Majada tayi saurin cewa 

"Yawwa komai yazo ƙarshe, shikenan tun da Bilqees bata bangaren girke-girke"

"Wa ya faɗa miki, in an kanza kiɗa haka ma rawa canzawa take yi, dole mu sake sabon shiri"

Cewar Laraba, Jummai ma ta goyi bayan haka, Majada abin bayyi mata daɗi ba, da sun kyaleta....

*********

Bilqees tana shigowa shashen masu raba abinci, ta yi musu sannu sannan ta wuce ta ɗauko rigar da suke ɗaurata kan uniform nasu ta ɗaura a jikinta, ta gyara komai yayi daidai, ta juyo ganin sun zuba mata ido yasa tayi magana 

"I'm here for serving our customer's"

Da mamaki wacce ke jagorancin bangaren masu raba abinci ta ce

"I didn't get you, what you mean?"

Take tambayar ta, bata fahimci me Bilqees ke faɗi ba, me take nufi? Bilqees cikin sanyin murya ta ce

"Alaja ce ta ce yau a bangaren ku zan yi aiki...

"Ba a yau kaɗai ba, kin koma aiki anan bangaren kenan ba ki ɗaya"

Suka jiyo muryar Alaja daga bakin kofa, Bilqees ta sauke numfashi tare da sudda kai, tana jin Alaja na ta ci gaba da yiwa Hafsu me kula da bangaren raba abinci bayani akan irin ayyukan da za ayi ta bata tana yi. Bilqees ta fito nan suka fara serving customers, tun da ta fito idanu a kanta sai ciniki aka yi wa Alaja sun fi son Bilqees ce ta yi serving nasu sai cewa suke ta basu wannan ta kawo musu wankan.....


***********************************

Ta iso wajen kamar kullum, ta tadda abokanta, sai wasa suke yi, tun daga nesa suka hango ta, a lokacin da me mashin ya sauke ta, nan suka fara murna har ta iso. Suka iso da gudu suka rungume ta, suna 

"Oyoyo kyakkyawar Aunty"

Murmushi take yi tana cewa

"Kada ku kadani"

Suka sanya dariya, tare da cikata ta zauna kan dakali tana sauke numfashi, suka gaida ta, ta amsa tare da cewa 

"Yawwa ƴan albarka, yau kun burge ni"

Nan suka shiga murna, ta zaunar da Aicha akan cinyarta tare da cewa 

"Aicha yau me ya faru, ba ki son yin magana"

"Tattawan (kyakkyawar )Aunty yunwa ne"

"Yunwa?"

Ta gyaɗa kanta alamun eh, cikin tausaya wa, ta shafa kan yarinyar tare da cewa 

"Haneef ba ku ci abinci bane"

Ya yi magana yana kallon Aicha ya ce

"Kin ganta nan, sai ta ci abinci sau uku a lokaci guda bata ƙoshi ba"

Da mamaki ta ce

"Kamar ya?"

"Ai Kyakkyawar Aunty, Aicha cikin ta kamar durum yake, tayi ta loader abinci a ciki baya isar ta"

Murmushi ta yi, tana jin damuwar ta na yayewa, tana jin ƙaunar yaran har cikin ranta, ta sauke Aicha tare da cewa su jeru kan layi ta kawo musu abin daɗi, suka jera, nan ta raba musu Alawa da biscuit, nan ko sai murna wasu suka buɗe biscuits suna ci wasu kuma da Alawa suka fara sha.

Ta kura musu ido tana kallon su, wani lokacin su bata tausayi, wani lokacin kuma su sakata dariya, ta jima a wajensu sai da ta tabbatar sun tafi sannan ta duba agogon wayar ta, ganin lokaci yaja yasa ta mik'e da sauri don barin wajen tayi karu da mutum, da sauri ta ɗago niqab nata ya yaye nan suka tsaya kallon juna. Ta matuƙar kaɗuwa da ganinsa a wannan lokacin, saurin gyara niqabinta ta yi, tare da daidaita ta nutsuwarta tana sake kare masa kallo, da kuma mamakin me ya kawo sa nan? Ba dai bibiyarta yake yi ba?..

"What brings you here?"

Shine abin da ya furta, yana da tsawo da jiki, baƙi ne ba sosai ba, ya ɗan tara gashin kai da yasha saloon, sanye yake da riga armless baƙa, bottom na ƙirjinsa a buɗe ana ganin siririyar tsarka dake maƙale a wuyarsa, wacce ke ɗauke da tambarin Cross. Sai kuma wando 3 quarter da ya saka tare da takalmi Boot....

"I'm asking you Angel"

Ya sake faɗi a karo na biyu, saboda ganin ya tambaye ta, bata bashi amsa ba, ta kura masa idanunta masu ɗemauta shi. Da ƙarfi ta sauke numfashi tare da cewa 

"I'm looking for someone"

"Someone?"

Ya faɗa da sauri, ya tari numfashinta...

A hankali tayi baya, tare da gyara jakarta, ba tare da ta ce komai ba, matsowa dab da ita ya yi tayi saurin ɗagowa tare da haɗe fuska za tayi baya ya yi saurin kai hannu zai janyo ya kusa da shi ta yi saurin ɗaga matsa hannu tare da cewa 

"Don't tried to touch me, Abraham"

Lumshe idanunsa ya yi ya buɗe su, yana jin ƙuna har cikin ransa, jikinsa ya soma rawa idanunsa sun kaɗa sun yi ja, ya furta da ƙarfi

"Daga cikin hotel kike?"

Ta watsa masa fararen idanun ta da suke cikin niqabi, irin na sharri za ka yi min. Kamar ba zata buɗe baki tayi magana ba, amma ta ce

"Shine abin da zuciyarka ta raya maka?"

"Yeah, of course yes"

"Think whatever you want"

Tana ƙoƙarin barin wajen har ta yi step biyu, jin abin da ya faɗa yasa ta tsaya Chak...


"Zan koma gida na faɗa musu cewa kin zo hotel wajen wani"

Take idanunta suka ciko da ƙwalla, ta dawo da baya zuwa in da yake tsaye tana magana muryarta na rawa 

"Kada ka kuskura ka shiga sakanina da ƴan'uwana"

Murmushi ya yi sosai, sannan ya sake gumewa kamar ba shi ba, ya yi magana yana kallon cikin idanunta 

"Ba zan faɗa ba, amma sai kin faɗa min daga ina ki ke"

Ta sauke numfashi, ta buɗe jakarta ta fiddo da Alqur'ani ta ce

"Karatu naje ɗaukawa"

Ya miƙa hannu da niyyar karɓa amma taƙi ba shi Alqur'ani, ya tambaye ta cike da mamaki

"Why?"

Ta ce

"Ba zayyu ka taɓa ba"

"Ai littafi ne shi ma"

"Eh littafi ne amma ba kamar sauran littattafai ba, whatsoever ba za ka iya taɓawa ba"

"Amma me yasa, gashi ke kin ɗauka"

"You are a Cristian, you can't touch it"

Ya sauke numfashi tare da cewa 

"However, I love you"

"That's not enough Abraham, until you combat to Islam"

"No i can't pray for five times in a day"

Murmushin takaici ta yi tare da cewa 

"Addinina ya haramta aure a sakanin mu"

"Me yasa?"

"A Muslim woman isn't allowed to marry a Christian man, but it's permissible for a Muslim man can marry a Christian woman"


"That'll not be a problem, Angel in mun yi aure kowa ya yi addinin sa"

"Wa kai ba, amma ma ni, there's a lot of problem's"

Tana gama faɗin haka ta bar shi nan tsaye tayi ba kin titi ta tari machine ta hau, nan yaja suka bar wajen...





Comments and share fisabilillah