1
by @oumfatima33
✨*ƘUNCINA* ✨
*By*
*KANSA'U BELLO*
*(OUM FATIMA)*
*PAGE 01*
*BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM*
*SHIMFIƊA*
*AURE!!!*
Aure yana daga cikin Umarnin da Allah da Manzonsa suka umarce mu muyi, sai dai yana da kyau mu sani cewa Allah daya umarce mu muyi aure shi yake da ikon tsara mana lokacin yin sa. Domin kuwa ko wane bawa yana da ƙaddararsa wacce take rubuce a cikin allon ƙaddararsa tun lokacin da aka aka halicce sa, komai da zai gudana a rayuwarsa rubutacce ne tun daga lokacin da za'a haife ka, shin musulmi ne kai ko saɓanin haka, zaka yi auren ko a'a, lokacin auren, lokacin haihuwa da dukkanin abinda zaka gudanar har ka koma ga Mahaliccinka.
Sai dai muna mantawa da cewa duka wannan ɗin tsarin Allah ne, idan Allah ya yiwa yarinya jarabawar jinkirin aure shike nan sai a tsangwame ta a riƙa goranta mata a kan abinda bata da iko dashi. Wanda idan takurar tayi yawa aka yi rashin sa'a sai yarinya ta faɗa wata rayuwar da bata dace ba, ko kuma a tilasta mata yin zaɓin wanda bai dace ba duk don a rufe bakin mutane. Da zarar anyi auren kuma sai ayi ta fuskantar ƙakubale, wanda ba ko wane auren yake ɗorewa ba, kuma a sako maka ƴar ta dawo gaban naka da kake gudu. Wanda wasu ke amfani da karin maganar dake cewa "Dariyar zawarci tafi ta budurci."
Irin wannan jarabawar nake fuskanta a halin yanzu wacce ta jefa ni a tsaka mai wuya na rasa tudun dafawa!.
___________
Sunana Nusaiba Abdulkarim Iyayena ƴan asalin wani ƙaramin ƙauyene a garin Zariya dake jahar Kaduna, amma a halin yanzu muna zaune ne a cikin garin Zariya unguwar sabon gari. Mahaifina Malam Abdulkarimu Malamin makarantar secondary ne ta Mata dake nan cikin garin Zariya, Matan aurensa biyu Mama Talatu ita ce uwar gida tana da yara Bakwai Mata biyar Maza biyu. Yaya Garba shine babba sai Muhusina, Bilkisu, Lubabatu, Aliya, Safara'u, sai Yasir auta. Sai Mahaifiyata Nazahatu wacce nake kira da Umma wacce mu biyu ta haifa, ni Nusaiba sai ƙanena Umar wanda na bawa shekaru sosai don bayan ta haifeni ta samu tazarar haihuwa har ma ta haƙura kafin Allah ya kawo rabon. Muna zaune cikin rufin asiri dai-dai gwargwado domin kuwa bayan koyarwa Mahaifina yana da shagon sayar da kayan ɗinki a Kasuwar Sabon gari wanda yake samu sosai da shi, wannan yasa yafi ƙarfin duk wasu buƙatunmu dai-dai gwargwado.
Mama Talatu da Ummata sam babu wata jituwa a tsakaninsu domin kuwa Mama Talatu mace ce mai tsananin kishi, wannan yasa duk ƙoƙarin da Abbanmu keyi don ganin ya haɗa kan iyalinsa abin ke gagara. Don yana tufka ne tana war-ware masa, ko tsakanin mu yaran babu wata kyakykyawar alaƙa tamkar ba ƴan'uwa ba kowa harkar gabansa yake yi. Yaya Garba shine kaɗai a ɗakinta baya ɗaukar shawarar da take bashi na hana shi yi mana abubuwa tamkar yanda yake yiwa ƙannen shi su Bilkisu, kasancewar Allah ya rufa masa asiri ya samu babban aiki a Kaduna a can yake zaune da Matarsa da yaransa. Duk lokacin da yazo ya kan zo mana da tarin tsaraba bayan kayan abinci da yake saya wa Abbanmu, hakan da yake yi ba ƙaramin baƙanta ran Mama Talatu yake yiba. Domin ta tsani wani daga cikinmu ya amfana da abinda ɗanta ya kawo, wannan yasa kullum idan ya sayo mana kayan sawa tayi ta masifa, gori da habaici baya ƙarewa har dai Uammanmu ta gaji wani zuwa da yayi ya shiga suka gaisa a mutunce ya bata tsarabarmu taƙi karɓa tayi masa godiya kawai. Murmushi yayi ya kalli Ummanmu yace.
"Haba dai Umma ya zaki biye abinda Mama take faɗa kice ba zaki amsa ba, kar ki manta fa su Nusaiba suma ƴan'uwana ne tamkar su Safara'u kinga kuwa babu yanda za'a yi na ban-banta tsakaninsu, don Allah kar kice ba zasu amfana da abinda Allah ya hore min ba saboda Mama." Wannan maganar ce tasa Umma ci gaba da amsar kayan da Yaya Garba yake saya mana, take share Mama Talatu duk sanda take haibaici da gorinta bata tanka mata tamkar yanda Abba yace ta daina biye mata.
Gaba ɗaya yaran Mama Talatu sun taso da farin jini tun suna yara ƙanana, wannan yasa suna gama Makarantar secondary ake aurar dasu. Haka akayi wa Muhusina aure kuma itace sa'ar haihuwata don ance wata biyar ta bani. Bayan ita aka aurar da Lubabatu da Bilkisu rana ɗaya, Aliya ma yanzu haka da Mijinta a hannu da zarar ta kammala makaranta za'a yi bikinta tamkar ƴan'uwanta. Saura Safara'u da yanzu ne take tasowa don bata fi sa'ar Umar ba.
Amma ni a ɓangarena shiru ne domin tunda na tashi koda wasa ban samu wanda ya taɓa cewa yana sona ba, kuma abin mamakin shine duk nafi sauran ƴan'uwana kyau da dirin jiki. Hakama na fisu natsuwa da kamun kai ga kwarjini da Allah ya bani, wanda ake cewa shine yasa mutane ke shakkar tarata suyi min magana bare su tare ni da maganar soyayya.
Tun abin baya damun Ummata har ya fara damunta, domin kuwa tuni Mama Talatu ta sako ta a gaba da gori da haibaici akan cewa baƙin halinmu nida ita yasa nayi bandaro na tsofe a gida ana ta aurar da ƙannen baya na. Abin bai tsaya iya ita kaɗai ba har mutanen unguwa ta fara yaɗa cewar baƙar ƙafa gareni shi yasa har yanzu bani da mashin shini an gama aurar da sa'annina har an fara aurar da ƙanne na, abin bai isheta ba sai da tabi dangin Abbanmu duk ta ɓatani a wurinsu tasa suka fara matsa wa Abba a kan ya tilasta min fitar da Miji in yi aure ko a sama min ko waye a ƙauye a bashi sadaka ta tunda ni za'a rufa wa asiri.
Umma bata da damar shiga dangi sai a fara nuna ta ana gulma, haka a ɓangarena tuni na daina zuwa sabgar dangin Abbanmu a ƙauye saboda yanda suka mayar dani tamkar wata mujiya. Haka za'a yi ta nuna ni ana cewa na rasa mashin-shini ga ƙannen bayana nan duka suna da yaransu, nayi kuka nayi kuka ban san adadinsa ba a kan hakan. Sai dai na yarda da cewa ko wane ɗan Adam yana da tasa ƙaddarar a rayuwa, ni wannan ita ce jarabawata kuma na karɓa da hannu biyu ina fata Ubangijin daya jarabceni ya bani ikon cinyewa.....