2
by @oumfatima33
✨ *ƘUNCINA* ✨
*By*
*KANSA'U BELLO*
*(OUM FATIMA)*
*PAGE 02*
*BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM*
_______ ★
Yauma kamar kullum ina kammala sallar asuba ban koma ba na fito na nufi ɗakin Ummata na gaisheta ta amsa min da kulawa, daga nan Mama Talatu naje na gaisar ta amsa da ƙyar tana bina da mugun kallon da na saba gani a gare ta. Ban damu ba na fito saboda ba sabon abu bane a gareni zagi da hantara daga gare ta, ɗakin Abbanmu na wuce shima na gaishe shi mukayi zaman karatun Alƙur'ani kamar yanda muka saba kullum bayan sallar asuba zamu zauna ya ɗora mana karatu duka yaran.
Ƙarfe 7:00am dai-dai muke tashi don haka muna fitowa na ɗauki tsintsiya na fara sharar ƙaton tsakar gidannu kamar yanda na saba, ina kallon Aliya ta wuce ɗakin Mamarta tayi kwanciyarta ta koma baccin safe, Safara'u kuwa dama a ɗakin Mama Talatu take kwana kuma ko haki bata ɗaukewa a gidan bare maganar shara. Duk da cewa nima ina buƙatar baccin safen amma bani da dama saboda Mama Talatu ta saka min dokar yin shara da wanke-wanke kullum da safe. Tace tunda naƙi aure na zauna a gida bani da amfanin daya wuce hakan.
Duk da cewar Ummata najin ciwon abinda ake min amma bata taɓa buɗe baki tayi magana ba, kasancewar tana min ƙara da alkunya na ƴar fari yasa ba sosai take magana a kan abinda ya shafe ni ba.
Lokaci sosai na ɗauka kafin na kammala share ƙaton tsakar gidan namu, kiching na nufa na riƙa fito da tarin kwanukan dake ciki ina kaiwa bakin fanfo. Sai dana kammala kwaso su duka kafin na kunna fanfon na tari ruwa na shiga wanke su, sai da na kammala tas ina ƙoƙarin kunna wuta don ɗora abin kari Ummata ta fito kasancewar ita tayi girki jiya yauma ita zata yi abin kari. Nusaiba Umma ta kalla cike da tausaya wa tace.
"Kawo na ɗaura abin karin jeki kwanta ki huta." A natse na ɗago na kalleta cike da tsananin soyayyar da nake mata da kuma tausayinta a kan halin da take ciki na tsangwama a kaina nace.
"Babu damuwa Ummah idan na kammala sai in kwanta." Bata saurareni ba ta amshi ashanar da nake ƙoƙarin kunna wa a murhun da tuni na haɗa itace a cikinsa, dole na bar mata na fito da niyar nufar ɗakinmu na ƴanmata wanda a yanzu daga ni sai Aliya a cikinsa. Wanda ita ba sosai bama take zama a cikinsa, tafi zama a ɗakin Mamansu. Mama Talatu na haɗu da ita hannunta riƙe da buta tana bina da kallon ƙyama tace.
"Ke yanzu bakya jin kunya kalle ki ganɗan-gaɗan a gida babu mashin-shini amma shine har kika samu damar zuwa ki kwanta barcin safe Uwarki tayi aiki kina kwance kina bacci. Ko dan ai a wurinta kika gada tunda itama manemin ta rasa aka ƙaƙabawa Mijina jaraba!." Ta ƙare maganar cike da izgili.
Irin waɗannan baƙaƙen magan-ganun kullum sai ta faɗa mana su yafi a ƙirga. Rintse idanuna nayi ina jin zafin magar tata wacce na kasa sabawa da ita kullum ta furta ta sai ta soki zuciyata ta bar min dafi a cikinta, zagayeta kawai nayi na shige ɗakinmu ba tare dana tanka mata ba kamar ko yaushe.
Tsaki tayi itama ta shige banɗaki tana ta ƙananan magan-ganun data saba kasancewarta Mace mai azabar mita da cira magana. Umma dake kiching ido ta runtse tana jin zafin gorin da Mama Talatu ke mata a kan liƙawa Mijinta ita da aka yi.
Ƙwarai auren haɗi aka musu ita da Malam Abdulkarimu, Iyayensu Aminan juna ne tun daga ƙuruciya har zuwa girma. Ita ɗin marainiya ce Mahaifiyarta ta rasu tun tana ƙarama a hannun Matar Babansu ta tashi wacce ta riƙeta cike da mugunta da gallazawa, ita ce tayi ta kore mata Samari don ta taso da farin jini fiye da yaranta. Baƙin cikin hakan yasa ta riƙa ƙulla mata sharri da makirci tana korar duk masu neman nata har suka daina zuwa kuma ta kafa mata a kan ta rasa Miji.
Saboda tausayinta da Mahaifin Malam Abdulkarimu keji yasa ya nema masa aurenta a wurin Mahaifinta, sanin halin Matarsa yasa Mahaifinta amincewa aka ɗaura auren cikin sirri sai daga baya aka bayyana ta tare a gidan Mijinta wanda suka kwashi rikici sosai da Mama Talatu har sai da ya mata saki ɗaya kafin daga baya aka dai-daita ta dawo ɗakinta. Wannan shine ya ƙara saka tsanar Nazahatu a Zuciyar Mama Talatu yasa bata raga mata ko kaɗan.
A ɓangaren Baba Habiba Matar Malam Musa Mahaifin Nazahatu rikici sosai sukayi kan ɓoye mata auren da yayi, don taji baƙin ciki sosai akan irin Mijin da Nazahatun ta samu wanda yafi duka Mazajen ƴaƴanta nagarta, dole ta haƙura kasancewar an riga an ɗaura aure tana ji tana gani ta tare aka kaita ɗakin Mijinta wanda ya riƙeta da amana da tausaya wa, a hankali soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu.
Ajiyar zuciya Umma ta sauke lokacin data gama wannan tunanin dai-dai lokacin da ruwan kunun data ɗaura ya tafasa ta dama kafin ta mayar da ɗumame. Sai da ta kammala ɗumama sauran tuwon dare daya rage ta zuba ma kowa nasa abin karin kafin ta ɗauki na Malam ta nufi ɗakinsa ta kai masa bayan ta leƙa dakin Mama Talatu ta sanar da ita an kammala abin kari Safara'u taje ta ɗaukar musu.
Wucewarta tayi ba tare data tsaya sauraren mitar da Mama Talatu keyi ba a kan Allah yasa dai bata kwashe abincin ba ta zuba musu kaɗan bayan kuma ɗanta ne ke kawo wa, a ɗaki ta samu Malam Abdulkarimu kishingiɗe saman katifarsa yana sauraren rediyon sa inda ake labaran safe a tashar BBC. Cikin natsuwa ta ajiye kwanonin abincin kafin ta zauna a nutse ta buɗe baki ta gaishesa, da kulawa ya amsa ya ɗora dayi mata sannu.
Ansawa tayi kafin ta zuba masa kunun tsamiyar data dama a ƙaramin kofi yana ta ƙamshin kanumfari ta miƙa masa.
"Allah yayi maki albarka." Ya faɗa yana jin daɗin yanda ta kasance mai kulawa da komai nasa, sosai yake jin daɗin zama da Nazahatun kasancewarta Mace mai tsananin biyayya a gare sa. Tana da haƙuri da sanyin hali shi yasa take jure duk abinda Mama Talatu ke mata, da wanda danginsa suke mata. Ƙaryawa ya fara yi cikin natsuwa sai da ya kammala ya shiga yi mata nasiha da kwantar mata da hankali kamar ko yaushe, sai da ya kammala tayi masa godiya ta fice da kwanonin.
A ɗakinta ta samu Nusaiba suna ƙaryawa ita da Umar dake shirye cikin Uniform ɗinsa na Makaranta, zama tayi itama ta karya fuskarta babu wal-wala sosai saboda har yanzu magan-ganun Mama Talatu ciwo suke mata a cikin rai. Sosai abin yake damunta a wannan lokacin har take jin kowa Nusaiba ta samu gwara ta aure shi ko zasu huta da gorin mutane su duka biyun, saboda a halin yanzu ita kanta zaman Nusaibar babu manemi har yanzu ya fara damunta. Kuma kullum ƙara girma take.
Maganar Umar ce dake mata sallama zai tafi Makaranta ta dawo da ita daga tunanin da tayi nisa a cikinsa, a dawo lafiya tayi masa bayan ta bashi Naira hamshin kuɗin break duk da cewar Abba na basu kullum. Shiru muka yi nida Umma bayan wucewar Umar kowa damuwa na cin zuciyarsa.
Ɗagowa Umma tayi ta zuba min ido wanda har sai da na tsargu da kallon da take min, ta jima tana kallona kafin ta buɗe baki tace.
"Ya kamata ace zuwa yanzu kin yiwa kanki faɗa ki fitar da Miji ki tafi ɗakinki kema ki huta da wannan rayuwar da kike yi a cikin gidan nan, nima ko zan huta da gorin da dangin Mahaifinku suke min a kan rashin aurenki." Ajiyar zuciya na sauke ina jin damuwata na daɗa ƙaruwa, a tunanina Umma tafi kowa sanin halin da nake ciki tunda a gabanta na taso tun ina yarinya har zuwa yanzu. Koda wasa bata taɓa ganin wani ya aiko kirana da sunan hira ba, to yanzu in tace in fitar da Miji wa nake da shi da zan fitar ɗin.
Kuka naji yana shirin ƙwace min saboda ganin Umma da nake samun sauƙi a wurinta itama ta fara gajiyawa dani, da ƙyar na iya buɗe baki nace.
"Kiyi haƙuri Ummah kici gaba da yi min addu'a Allah ya zaɓa min abinda yafi alkairi a rayuwata!." Ina gama maganar na miƙe na fita daga ɗaki na nufi ɗakinmu ina sakin kukan da nake ta riƙe wa tun ɗazu.
Ni kuma kalar tawa ƙaddarar kenan, haka zanci gaba da rayuwa a cikin gidanmu kowa yana yin aure yana barina. Ga takura da tsangwama daga wurin mutane ba damar ka shiga cikin ƴan'uwa sai a fara nuna ka ana goranta maka a kan abinda Allah ne keda ikon zartarwa. Kuka sosai nayi kafin na haƙura na share hawayena.
★Washe gari.
Yau tun da safe ake ta shirye-shiryen tarbar Yaya Garba da Iyalinsa da zasu zo anyi hutun Makaranta shi yasa zasu zo gaba ɗaya suyi kwana biyu su koma. Mama Talatu ta rasa inda zata saka kanta sai faman kai-kawo take na shirin tarbar Jikokinta da take ji dasu sosai, don haka tasa aka shirya musu abubuwan kwaɗayi wanda ta san suna so.
Tun da safe Muhusina da Lubabatu da Bilkisu suka zo don haka gidan namu a cike yake ana ta hidima, tsarabar dasu Muhusina suka zo da ita Mama Talatu ta fito da ita tana tayi wa Umma haibaici da goranta mata a kaina. Kamar ko yaushe Umma bata tanka mata ba sai dai abin yana ci mata rai sosai, lafiya lau muka gaisa da Muhusina wacce itace sa'ar haihuwata kuma muna zumunci da ita ba laifi. Su Lubabatu ne dai suke bina da kallon raini irin sun sha gabana ɗin nan.
Ban shiga sabgarsu ba kamar yanda basu sani a ciki ba, haka na gama abinda zanyi na shige ɗaki na ɗauki saƙar huluna da kayan sanyi na yara da nake yi naci gaba wacce ita ce ke ɗebe min kewa, sai kuma karance-karancen litattafai da nake yi. Ƙarfe 12:00am dai-dai motar Yaya Garba ta tsaya a ƙofar gidanmu, da gudu Umar da Yasir suka yi waje don taron su. Gaba ɗaya Mama Talatu da yaranta suka fito tsakar gida suna jiran isowarsu, Safara'u ma tuni ta kai waje ita ma. Nida Umma ma duk fitowa muka yi don yi musu maraba duk da irin hararar da Mama Talatu da yaranta ke jeho mana.
Tarin kaya aka riƙa shigowa dasu kamar ko yaushe idan zai zo sai ya ciko mota da tsarabar kayan abinci da sauransu, Matarsa mai suna Surayya ita ta fara shigowa da yaransu Uku Abdulkarim mai sunan Abba ana kiransa da Kalifa, sai Suhaila, sai Affan shine ƙarami. Da gudu yaran suka nufi Mama Talatu dake musu oyoyo suka rungumeta, sai da suka gama murnarsu kafin suka juyo suka gaishe da Umma dake musu magana cikin sakin fuska.
Barka da zuwa na yiwa Aunty Surayya wacce ta janyo hankalin yaran suka dawo wurina suna rungumeni cike da farin cikin ganina, don suna sona musamman ma Suhaila dake tsananin sona. Ɗaya bayan ɗaya na riƙa ɗaga su ina musu oyoyo ina aje wa cike da farin cikin ganinsu saboda yanda nake son yaran, don ma Mama Talatu na hanasu zuwa wurina su zauna idan suka zo. Shigowar Yaya Garba tasa duk muka juya kansa muna masa Barka da zuwa, da fara'a yake amsa wa kowa kafin ya gaishe da su Mama muma muka gaishe shi.
Juyawa nayi da niyar komawa ɗaki saboda na gama abinda ya fito dani Suhaila ta riƙo hannuna tana cewa.
"Aunty beauty zan biki." Murmushi nayi mata na kama hannunta zamu wuce muryar Mama Talatu ta dakatar dani......