ƘUNCINA

3

by @oumfatima33

✨ *ƘUNCINA* ✨

            *By*

 *KANSA'U BELLO* 

         *(OUM FATIMA)* 




 *PAGE 03* 


    *BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM*




    "Zo nan Suhaila." Mama Talatu ta faɗa tana haɗe rai sosai. Ganin duk an zuba mata ido har da Yaya Garba da Aunty Surayya yasa ta yin murmushin yaƙe tace.

    "Muje kici abinci ki huta kinji ko." Maƙale kafaɗa Suhaila tayi tace.

   "Ni a wurin Aunty beauty zanci abinci." Ƙara tsuke fuska tayi sosai tana watso min harara da kallon tsana da ƙyama. Duƙawa nayi na dafa kafaɗun Suhaila nace.

   "Kinga pretty je kici abinci tare dasu Mama idan kika kammala sai kizo zan baki abin daɗi." Dariya tayi ta gyada kai kafin ta nufi inda Mama Talatu ke tsaye tana aika min harara, tana zuwa ta kama hannunta suka nufi ɗakinta da sauran suka shige tuni.

   Ajiyar zuciya na sauke nima na juya zan shige muka haɗa ido da Umma tana kallona, duƙar da kai nayi na wuce ba tare dana ce komai ba. Ajiyar zuciya Umma ta sauke bayan shigewar Nusaibar ta wuce itama tana mata fatan samun miji itama taje ta haifi nata yaran. 

   Cike da farin ciki Mama Talatu da ƴaƴanta da ƴan Jikokinta suka ci abinci suna ta hira da nishaɗi, suna kammala cin abincin Suhaila ta gudu ɗakin Nusaiba duk irin kiran da Mama Talatu ke mata bai sa ta tsaya ba. Yaya Garba ne ya dubi Mama Talatu cikin jin-jinawa lamarinta a kan Umma Nazahatu da yaranta wanda taƙi haƙura su zauna lafiya duk tsawon shekarun da suka ɗauka tare, cike da girmamawa ya kalleta yace.

   "Wannan ta riga tayi gaba ai Mama, amma kar ki damu na san ba zata wuce wurin Nusaiba ba." Cike da masifa Mama Talatu tace.

  "Ita Nusaibar Uwarta ce da dole sai taje inda take!." Ta ƙare maganar tana manta cewar Nusaibar ƙanwar Garba ce don haka matsayin Uwa take dashi ga Suhaila. Haƙuri kawai Yaya Garba ya bata saboda ya san ko ya tsaya fahimtar da ita ba fahimtar zatayi ba, don haka addu'a kawai yake mata a kan Allah ya sanyaya zuciyarta a kan tsananin ƙiyayyar da take yiwa ƴan'uwansa saboda kishin dake tsakaninsu da Mahaifiyarsu.

   Suhaila kuwa kai tsaye ɗakin Nusaiba ta nufa da gudu don ma kar Mama Talatu ta dakatar da ita, samuna tayi ina duba wani littafi na addini da muka fara shi yau tare da Abba yana ɗora min. Ajiye littafin nayi ina miƙa mata hannu nace.

   "Zo nan." Da gudu ta ƙaraso ta zauna saman ƙafata ta shiga bani labarin School ɗinsu da ƙawayenta. Biye mata nayi muka yi ta hira bayan na ɗauko mata alewa da biscuits, cikin farin ciki take ci tana bani labari. Sosai nake jin yarinyar a cikin zuciyata don haka muka ɓata lokaci sosai ina biye wa shirmenta har sai da muka ji sallamar Abba ya dawo daga makaranta muka fito yi masa sannu da zuwa. Sosai Abba yayi farin cikin ganin su Yaya Garba duk da ya san da zuwan nasu daman, haka yayi ta yiwa su Affan wasa irin na Kaka da Jika.

   Bayan Abba yaci abinci ya huta suka zauna da Yaya Garba suna tattaunawa a kan harkokinsu da yanda komai yake tafiya, ajiyar zuciya Yaya Garba ya sauke ya dubi Abba da kyau yana son sanar dashi tunanin da yayi a kan makomar Nusaiba.

    "Abba nayi wani tunani a kan Nusaiba wanda nake ganin kamar hakan zai fi, amma nace bari na sanar da kai tukun na." Kallon sa Abba yayi yana gyara zamansa yace.

    "Ina sauraron ka."

   "Cewa nayi mai zai hana in tafi da Nusaiba can Kaduna in sama mata gurbin karatu ta fara, tunda har yanzu Allah bai kawo mata Miji ba. Kaga bai kamata taci gaba da zama haka ba bata komai, idan ta fara karatun duk sanda Allah ya kawo mata Mijin sai ayi auren, nake ga kamar hakan zai taimaka mata sosai kuma karatun zai ɗebe mata kewa ya rage mata damuwar da take ciki." Tunda ya fara magana Abba ke gyaɗa kai yana sauraren sa har sai da ya kammala kafin ya sauke ajiyar zuciya yace.

   "Wannan tunani ne mai kyau don nima na jima da yinsa har nake tunanin nema mata gurbin karatun a nan ABU Zariya, amma yanzu tunda kazo da wannan batun sai a tuntuɓi Iyayenku aji ta bakinsu. 

  "To shike nan Abba sai kayi musu bayani, idan sun amince sai in fara bincika mata admission ɗin idan na koma." Yaya Garba ya faɗa.

   "Masha Allah, Allah ya zaɓa mata abinda yafi alkairi, Allah ya maku albarka baki ɗaya." Abba ya faɗa. 

   "Amin." Yaya Garba ya amsa kafin suka miƙe don yin alwalar sallar magriba da ake gab da kira. 

   Da dare bayan su Abba sun dawo daga sallar isha'i sunci abinci tare da Yaya Garba, Abba ya buƙaci ganin su Mama. Umma ce ta fara zuwa don haka ta samu wuri ta zauna bayan ta yiwa Abba barka da dare, gaisheta Yaya Garba yayi ta amsa da kulawa. Bata jima da zama ba Mama Talatu ta shigo itama cike da son nuna wa Umma isa ta ƙarasa ta zauna gefen Abba duk da cewar taga Umma zaune a saman kujera mai zaman mutum biyu, sai Yaya Garba dake zaune a ƙasa kusa da ƙafafun Abba.

   Babu wanda ya tanka mata a kan abinda tayin sai ma gyaran murya da Abba yayi ya fara yi musu bayani a kan maganar da Yaya Garba yazo da ita. Tun bai ƙarasa rufe bakinsa ba Mama Talatu ta tari numfashinsa da cewa.

  "Ina!! Sam! Wannan maganar ba mai yiwa bace don haka ama bar ta, don wallahi ba zata bisu ba taje ta kashe masa aure da baƙin halinta ba, tunda ita taƙi yin auren tana zaune a gida a tsakanin Iyayenta jgan-ɗan-ɗan bamu da maraba da ita." Ta ƙare maganar cike da masifa da son cusawa Umma baƙin ciki.

   Ai kuwa sosai maganar ta soki zuciyar Umma harma da Yaya Garba da yake jin rashin daɗi akan kalaman da Mahaifiyarsa ke faɗa a kan ƴar'uwarsa. Cike da takaicin halinta na rashin tauna magana Abba yake kallonta yana mamakin wannan halin nata, cikin ɓacin ran da magan-ganunta suka saka shi ya buɗe baki ya fara magana.

   "Wato ke dai Talatu ba zaki taɓa sauya wannan mummunar ɗabi'ar taki ba ko? Shin ke baki san ƙaddara bane? Baki san cewa ko wane bawa da kalar tasa ƙaddarar bane, ba kuma zai taɓa tsallake taba?. Wai da take zaune gidan a kanki take zaune ne da zaki uzzurawa rayuwarta, su ƴan'uwanta da Allah ya fitar musu da Mijin kike alfahari da hakan ai ba wayo ko kuma dabararsu bace tasa suka samu lokacinsu ne yayi, itama da zarar nata lokacin yazo ba zata taɓa tsallake shi ba. To daga yau bana son sake jin magana makamanciyar wannan a cikin gidan nan!." Ya ƙare maganar ransa a matuƙar ɓace.

  Cikin ɓacin ran faɗan da Abba ya mata a gaban Umma Mama Talatu ta dubi Yaya Garba tace.

  "Kai dai na isa da kai domin kuwa Uwarka ce ni na haifeka, don haka ban yafe maka ba matuƙar ka ɗauki yarinyar nan ka kaita cikin gida ka!." Tana ƙare maganar ta miƙe fuuuu!!! Ta fice a ɗakin ba tare da an sallame ta ba.
  
  Cikin rashin jin daɗin abinda ya faru Yaya Garba ya dubi Umma ya fara bata haƙuri a kan abinda Mahaifiyarsa tayi, murmushi ta masa tace.

   "Dawo ki zauna." Muryar Abba ta fita cikin tausasawa. Babu musu ta koma ta zauna tana danne hawayen da suka cika mata ido suna son fitowa, miƙewa Yaya Garba yayi ya musu sallama ya fice bayan ya ƙara basu haƙuri a kan abinda ya farun.

   Ajiyar zuciya Abba ya sauke bayan fitar Yaya Garba ya dubi Umma da kyau yace.

   "Kar kisa magan-ganun data faɗa a ranki su dame ki har ki kasa cinye jarabawar da Ubangiji yayi maki, ki sani komai yana da lokacinsa idan har lokacin aurenta bai yi ba tofa duk irin matsuwar da muka yi don ganin hakan ba zai kasance ba har sai lokacin da Ubangiji ya tsara. Ki ƙara haƙuri kici gaba dayi mata addu'a, wai ma duka yarinyar guda nawa take da za'a ɗaga hankali har haka? A kwai da dama waɗanda suka fita nesa ba kusa ba kuma suna zaune a gaban Iyayensu lafiya lau ba tare da wata damuwa ba, ki kwantar da hankalinki don Allah saboda hakan shi zai saka nata hankalin ya kwanta itama." Ya ƙare maganar cike da rarrashi da son kwantar mata da hankali. Gyaɗa masa kai tayi kawai ta miƙe tana jin yanda ƙirjinta ke ƙara yin nauyi.

   Har zuwa yaushe zata ɗauka tana jiran lokacin, kullum fa Nusaibar girma take ƙara yi. Shekarunta fa ƙaruwa suke ba raguwa ba, ita kaɗai ta san halin da take shiga duk lokacin data ɗaga ido ta kalli Nusaibar a gabanta matsayin budurwa, bayan duk ƙannenta dake gidan an aurar dasu. Ga gori da baƙaƙen magan-ganun da kullum gari ya waye sai an ƙunsa mata su. Da wannan tunanin a cikin zuciyarta ta ƙarasa ɗakinta, a zaune ta samu Nusaiba ita da Umar tana taya sa home work ɗinsa. Cikin rufewar ido Umma ta rufe Nusaiba da faɗa a kan dole ta daina wannan haɗe fuskar da take wa mutane suke tsoron tunkarata da sunan soyayya, faɗa sosai tayi mata ƙarshe ta fashe da kuka.

  Wani irin ɗaci nake ji a cikin zuciyata duk lokacin da naga Umma ta shiga irin wannan halin a kan rashin aurena, kuka sosai na fashe da shi ina jin damuwa mai girma tana lulluɓeni. A yau yanda nake jin zuciyata koda nakasashshe yazo yace yana sona da aure zan amince masa ko don Umma ta samu salamar zuciyarta, sai dai bani da wannan sa'ar don ko kuturu bai taɓa zuwa wurina da sunan soyayya ba. Da yawan lokuta na kan zauna inyi ta tunani a kan wani irin baƙin jini ne gareni da aka rasa wanda zai furta min kalmar so koda da wasa ne. Cikin rashin sanin abin yi na buɗe baki na fara magana muryata na fitar da sautin kukan da nake yi.

   "Kiyi haƙuri Umma kiyi min addu'a." Iya abinda na iya furta wa kenan na miƙe da gudu na fice a ɗakin na nufi namu ɗakin. Cike da tausayawa Surayya ta bita da kallo, fitowarta kenan daga ɗakin da suka sauka zata je ɗakin Mama Talatu ta gitta ta gaban ɗakin Umma ta tsinci magan-ganun da suke yi. Sosai tausayin yarinyar ya kamata har take jin da za'a bata ita da ta tafi da ita Kaduna, mamaki take yi matuƙa idan ta dubi Nusaiba ta ganta kyakykyawar budurwa Masha Allah, ga kyawun dirin halitta da Allah ya mata uwa uba kuma natsuwa da kamun kanta, amma ace wai ta rasa manema. Irin su Nusaibar nefa ake rubibi idan ta kama har yaƙi ake a kan samun su. Sai dai kuma idan ta tuna da ikon Allah wanda komai ke gudana bisa tsarawarsa sai ta ture tunanin cikin zuciyarta.

   Jiki a sanyaye ta shige ɗakin Mama Talatu a can ta samu Yaya Garba da yara suna hira, zama tayi itama aka ci gaba da ita duk da jikinta a sanyaye yake har lokacin.


 ★ Washe gari...

  Damuwar dana kwana cikinta ce ta haifar min tashi da zazzaɓi, duk da dai Alhamdulillah na samu sauƙi a zuciyata sakamakon kwana da nayi ina faɗawa Allah damuwata, kwana nayi sallah da karatun Alkur'ani wanda hakan ya saukar min da natsuwa a zuciyata. Sai da nayi sallar asuba na kwanta yau ko karatu ban fita ba saboda kaina dake min ciwo, kafin gari yayi haske kuma zazzaɓi ya rufeni. Koda Abba ya aiko Aliya ta duba ni ganin ban fita karatu ba abinda ban saba ba, hasalima nike yin farkon zuwa kullum don su Aliya sai an taso su.

   Rufe ta sameni a cikin bargo ina rawar sanyi don haka taje ta sanar da shi cewar bani da lafiya.

   "Subhanallah! Mai ya sameta haka?" Ya tambaya yana miƙewa daga saman abin sallar da yake kai. Dubanta Yaya Garba dake zaune kusa da Abba yayi yace.

   "Meke damun Nusaibar?".

  "Allah ban sani ba Yaya ni dai na sameta tana rawar sanyi a cikin bargo." Aliya ta bashi amsa.

  "Allah ya bata lafiya." Ya faɗa yana mayar da kansa saman Alƙur'anin da yake karantawa a zuciyarsa yana raya cewar an jima zai kaita asibiti a dubata.

   Abba kuwa ɗakin Umma ya leƙa inda ya sameta zaune saman abin sallah tana lazumi, ɗagowa tayi ta kallesa da kumburarrun idanunta da suka sha kuka daren jiya, sai dai itama kwana tayi tana faɗawa Allah damuwarta kamar yanda Nusaibar tayi, a hankali ta buɗe baki tace.

   "Barka da safiya Malam, an tashi lafiya." Sai da ya gama kallonta tsaf ya fahimci bata cikin wal-wala da alama kuka tayi don idanunta sun nuna hakan.

   "Lafiya lau, Alhamdulillah. Yaya kika tashi." Ya amsa mata da kulawa kafin ya ɗora da ce mata taje ta duba Nusaiba bata da lafiya. Miƙewa tayi gabanta na faɗuwa a kan jin cewa Nusaibar bata da lafiya, meya sameta to? Ko maganar da tayi mata jiya ce yasa ta rashin lafiyar?. Da waɗannan tambayoyin a cikin zuciyarta ta isa ɗakin su Nusaibar ta buɗe labule ta shiga....