ƘUNCINA

4

by @oumfatima33

✨ *ƘUNCINA* ✨

            *By*

 *KANSA'U BELLO* 

         *(OUM FATIMA)* 




 *PAGE 04* 


    *BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM*





       Cikin sanyin jiki ta saka ƙafarta cikin ɗakin ta fara takawa a hankali saman shimfiɗaɗɗiyar ledar tsakar ɗakin da aka malala aka yi masa kwalliya da ita, a saman katifar dake mallakinta ta hango ta a kwance rufe cikin bargo tana rawar sanyi. Ji tayi zuciyarta ta tsinke da wani irin tausayin yarinyar tata, da ace tana da ikon canza mata ƙaddara to da tuni tayi hakan. Sai dai bata da wannan damar amma kullum tana mata addu'a da fatan Allah ya kawo ƙarshen jarabawar tata.

   Da wannan tunanin ta ƙarasa saman katifar ta zauna tasa hannu ta yaye abin rufar, wani hucin zafine ya daki fuskarta don haka cikin sauri ta ƙarasa yaye rufar tana taɓa wuyanta. Zafi sosai taji don haka ta miƙe ta fice ba tare da tace komai ba.

  A hankali na buɗe kumburarrun idanuna da suka ƙara min nauyi nabi Umma da kallo har ta fice ina jin ƙauna da tausayinta na ratsani lokaci ɗaya, idona na mayar na rufe ina jin rashin daɗi a kan yanda na zama silar damuwarta a cikin gidanmu. Sai dai nima ba laifina bane, babu wanda yazo wurina na masa wulaƙanci bare ace ko wulaƙanta samarin nake har suka daina zuwa.

   Tunanina ya katse dai-dai lokacin da naji shigowar Umma a karo na biyu, da ƙyar na iya buɗe idanuna na kalleta tana riƙe da ƙaramin baho a hannunta. Zama tayi kusa dani ta saka tsumma mai tsafta tana sawa a cikin ruwan mai sanyi sai ta matse ta goge min fuskata zuwa wuyana, haka taci gaba dayi har sai da zafin jiki na ya ragu kafin ta koma ɗakinta ta haɗo tea mai kauri a cikin kayan tea ɗin da Yaya Garba ya kawo aka raba aka bata.

  Dawowa tayi ta taimaka min na tashi zaune ta miƙa min kofin ba tare da tayi magana ba, amsa nayi ina ta binta da kallon ƙauna da tausayi. Ɗauke kanta tayi ta mayar gefe kafin tace.

   "Maza ki shanye kisha magani." Ajiyar zuciya na sauke jin fitar muryarta da kulawa a gareni, kofin na kai baki na na shiga sha a hankali duk da bana jin daɗinsa a bakina. Sai da nasha fin rabi kafin na aje kofin, kallo na Umma tayi ta kalli kofin bata ce komai ba ta shiga ɓalla magani ta bani. Bana son magani da allura duka amma haka na daure na kai bakina ganin yanda Umma ta haɗe fuska sosai don ma kar nayi mata musu.

   Ruwa na kurba na runtse ido na ɗaga kaina sama kafin na jefa maganin na haɗiye da ƙyar, sai dai ina buɗe idona amai ya yunƙuro min na sauka da gudu na fita waje. Tun kafin in kai bakin makwarara na fara kwara amai mai matuƙar wahala don har ta hanci yake biyo min. Haka zazzaɓina yake dama komai naci sai ya dawo haka ban isa in sha magani ba sai na amayar dashi, ƙarin ruwa da allurai kawai ake min a zauna lafiya duk da bana son allurar ma.

   Umma data biyo bayana tun fitowa ta da gudu ita ta bani ruwa na wanke baki da fuska ta taimaka min na miƙe da ƙyar na koma ɗaki, nida ita duk muna jiyo ƙananun magan-ganun Mama Talatu dake faɗar kar dai a dauko musu abun kunya a kawo musu cikin gida. A wannan karon kam Umma kasa shanye wannan maganar tayi sai da ta mayar mata da martani.

   "In sha Allah hakan ba zata taɓa faruwa ba har abada kuwa!." Umma ta faɗa cikin jin zafin maganar. Mama Talatu zata fara masifa Abba da fitowarsa kenan ya dakatar da ita ta hanyar yi mata tsawa, dole tayi shiru tana haɗiyar zuciya saboda duk abinta tana shakkar sa don baya ɗaukar wargi ko kaɗan.

   "Bari a kira likita ya dubata." Abba ya faɗa yana fitar da wayarsa don kiran Doctor Luswana, babban likita ne a nan unguwar gidan Iyayensa yake don abokin Yaya Garba ne, kuma shine yake duba Nusaibar idan bata da lafiya don tana yawan jinya.

   "Abba ko dai na fitar da mota a kaita asibiti?." Yaya Garba ya faɗa da kulawa. Wani mugun kallo Mama Talatu ta jefa masa tana jin tamkar ta wanke sa da mari a kan wannan maganar da yayi, ita ta rasa wane irin yaro ne shi mara kishin Uwarsa yabi ya tare a ƙarƙashin Nazahatu yana musu hidima ita da yaranta tamkar ita ce ta haifa mata shi. Maganar Abba ce ta katse mata zancen zucin da take yi lokacin da yace.

   "Ina ga a jira yazo ɗin ya san aikinsa zai duba ta yanda ya dace in sha Allah." Ɓoyayyar ajiyar zuciya Mama Talatu ta saki a ɓoye tana jin sauƙi kaɗan don ta san idan Lusuwanan yazo ma dai kuɗin ɗan nata ne dai za suyi ciwo abinda taƙi jini.

   "Shike nan to Allah ya sauwaƙa." Yaya Garba ya faɗa yana juyawa ɓangaren da suka sauka. 

   Umma dai tunda ta gama taimaka min na kwanta ta shige ɗakinta tana jin duk abinda ke faruwa, bata fito ba bare ta tanka hasali ma kayan tahafiz ɗin Umar ta shiga gogewa kasancewar ko anyi hutun makarantar boko suna zuwa tahafiz. Ba'a jima sosai da kiran Doctor Lusuwan ba sai gashi ya ƙaraso gidan yayi sallama, Yaya Garba ne ya fita yayi masa iso suka shigo tare yana ɗauke da kayan aikinsa. Har cikin ɗakin namu Yaya Garba yayi masa jagora duk da irin hararar da Mama Talatu ke jefa masa, tana kiching tana haɗa abin kari amma idonta na a kan abinda ke faruwa a tsakar gidan. Masifar ɓacin rai take shiga ganin yanda yake ta wani shish-shigewa a kan lamarin kishiyarta. 

   Ina ƙudundune cikin bargo suka shigo kujerar roba Yaya Garba ya janyo ma Doctor Lusuwan ya zauna shi kuma ya ƙarasa gaban katifar da nake kai, a hankali ya ɗan buga gefen filon da nake kwance yana faɗin.

  "Tashi Nusaiba ga Doctor nan zai duba ki." Naji saukar muryar Yaya Garba na shiga cikin kunnena. Da ƙyar na yaye abin rufar na yunƙura na tashi zaune, filo Yaya Garba ya sa min a bayana don inji daɗin zaman.

  "Sannu, ya jikin?." Ya furta min da kulawa sosai irin ta ɗan'uwan daya damu da ƴar'uwarsa. A hankali cikin tarin kasalar da ciwon ya sakar min na iya bashi amsar cewa.

   "Da sauƙi." Na ɗora da gaishe sa kafin na kalli inda Doctor Lusuwan yake na gaishe sa shima. Dukansu amsa min sukayi da kulawa sosai har ina hango tsan-tsar damuwa a fuskar Doctor Lusuwan wanda takamai-mai ba zan ce ga dalilinta ba.

   Cikin tsananin kulawa ya shiga duba ni yana yi min tambayoyi har ya kammala ya ɗaura min ƙarin ruwa tare da allurai wanda sai da aka sha fama kafin na yarda. Ba'a jima ba na lumshe ido bacci ya ɗauke ni sakamakon harda allurar bacci a cikin alluran da aka zuba min. Ajiyar zuciya duk su biyun suka sauke kafin Doctor Lusuwan ya duba Yaya Garba ya fara masa bayani.

   "Akwai maleria a jininta sai kuma high BP wanda nayi mamaki sosai a kansa, bai kamata ace ƙaramar yarinya kamar Nusaiba tana fuskantar irin hakan ba. Yanzu dai na mata abinda ya dace in sha Allah idan tayi bacci sosai ta samu isasshen hutu muna saka ran komai zai dai-daita, idan na fita zan turo da magun-gunan da zata yi amfani dasu. Don Allah a kula da ita sosai, dole ta daina barin damuwa a ranta irin haka don gudun abinda zai iya faruwa ga lafiyarta, zan shigo da dare in ƙara dubata in sha Allah." Ya ƙare maganar fuskarsa ƙunshe da damuwa sosai wacce ta bawa Yaya Garba mamaki, da kuma ya duba yaga cewar likita ne shi ɗin suna da tausayi ga patient ɗinsu sannan kuma an zauna a unguwa ɗaya kuma ana zumunci sai ya ture tunanin da zuciyarsa ta fara bijiro masa da shi.

   "Mun gode Doctor in sha Allah za'a kiyaye." Yaya Garba ya faɗa lokacin da suke fita tsakar gida, hannu ya saka a aljihunsa ya ciro kuɗi masu ɗan dama ya miƙa masa yace.

  Ga wannan ayi abinda ya dace, mun gode sosai." Harararsa yayi yace.

   "Ni zaka biya don na yiwa Nusaiba wani abu?." Idon Mama Talatu ƙyar a kan kuɗin da Yaya Garba ya fitar zai bayar a kan maƙiyanta, ji take kamar tayi fiffike ta wafce kuɗin sai kuma cikin sa'a Doctor Lusuwan ɗin yaƙi amsa duk da ƙin amsar tasa ya sosa mata zuciya saboda tunanin da yazo mata cikin rai akan dalilin ƙin amsar, don haka ta sake ƙaramin tsoki ta shiga jefo magan-ganun ɓatanci a kan Nusaibar a kai-kaice.

   Babu wanda ya tanka mata har Doctor Lusuwan yayi musu sallama ya fice yana jin rashin daɗi a kan magan-ganun da Mama Talatu tayi a kan Nusaibar. Kowa ya san cewa Nusaiba yarinyar kirki ce a unguwar tana da kamun kai sosai sannan tana girmama na gaba da ita, bata shiga sabgar da bata shafeta ba ko kaɗan. Sannan bata da rawar kai irin na ƴanmatan zamanin nan, musamman yanda take kyakykyawar nan mai kyan sura da taga dama zata iya amfani da kyawunta ya zama jarinta. Amma sai ta zaɓi suturce jikinta da ɓoye baiwar da Allah ya mata na kyan sura, wanda da yawa suke kallon ustazancinta yayi yawa. Yayinda wasu ke mata kallon rashin wayewa. Koma dai miye shi dai tana birgesa kuma har cikin zuciyarsa yake sonta, sai dai shi kansa ya rasa dalilin da yasa ya kasa tunkararta. 

   Tana da masifar kwarjini wanda ba kowa bane zai iya tararta kai tsaye da sunan soyayya bare maganar banza, shi yasa lokuta da yawa sai yayi niyar fuskantar ta. Sai dai tana tsayawa a gabansa da kamammiyar fuskarta mai cike da kwarjini sai ya kasa furta abinda yayi niyar tamkar wanda aka saka ƙwaɗo aka datse masa baki, sai dai ya ɓige da tambayarta wani abin da ban. Dalili na biyu dake dakatar dashi shine: Matarsa, Matarsa Hadiza azababbiyar Mace ce mai masifar kishi wacce kullum ake bala'i da ita a akan Mijinta. Ba zai iya irga adadin ƴanmatan data jiwa ciwo ba wanda dalilin hakan ya amsota a police station ba adadi. Hakan yasa ƴanmata ke tsoronta sosai don ko maganar Mijinta ta kama yarinya nayi yanzu zata tsige mata gashin kai, ko kuma ta zana maki tsagun goburawa a fuska babu ruwanta iyaka a kaita police station Mijinta yaje ya amso ta ko baya so don Dada ba zata barsa ya huta ba idan bai amai taba. Amma yana nan yana jiran lokacin daya dace ya fuskance ta da soyayyarsa in sha Allah don ita ce wacce zuciyarsa ke muradi.

   Bai tafi wurin aikinsa ba sai da ya biya ya haɗo duka magun-gunan da take buƙata ya aika mata sannan ya wuce wurin aikinsa cike da tunanin halin da take ciki.


**** 

  Alhamdulillah kwana biyu nayi a kwance na warke naci gaba da harkokina kamar yanda na saba, kullum zan je islamiyya da yamma inda da asuba muke yi tare da Abba kamar ko yaushe. A haka su Yaya Garba sukayi mana kwana huɗu suka koma saboda yanayin aikin Yaya Garban, ita Aunty Surayya da yake malamar makaranta ce ita bata da matsala don suna komawa ma zasu wuce Kano asalin garin Iyayenta ita da yara suga dangi.

   Sun tafi sun bar mu cike da kewar su musanman ma Suhaila da nake jin yarinyar sosai a cikin zuciyata saboda tana matuƙar sona nima kuma ina sonta sosai.

   Rayuwa taci gaba da tafiyar min cikin tsananin ƙunci da kaɗaici musanman ma da aka tsayar da bikin Aliya watanni biyu masu zuwa don ta kammala jarabawarta. Ranar da ƴan'uwan Abba suka zo daga ƙauye amsar lefen Aliya sai da na ƙwammace da ban zauna a gidan ba, daga ni har Umma sai da muka yi kuka saboda baƙin cikin magan-ganun da suka ƙunsa mana. Bayan gori da haibaici da dangin Mama Talatu suka gama yi mana suka tafi, goggo Baraka har ɗaki ta isko Umma tana zaune cikin ƙunci da baƙin cikin data gama haɗiya a kan magan-ganun da dangin Mama Talatu suka gama jefa mata.

   Da sallama ta shigo wacce tayi ta da ƙyar tamkar wacce aka yiwa dole, wuri ta samu ta zauna saman kujera tana ƙarewa ɗakin kallo da taɓe baki. Cikin isa da gadara ta kalli Umma ta fara magana.

   "To Nazahatu, mu dai ba zamu gaji da faɗa maki gaskiya ba duk da dai bakya sonta, a kan ganɗamemiyar budurwa da kika saka gaba kike zaune da ita babu aure, mu gaskiya mun gaji da yanda ake yamaɗiɗi damu a ƙauye ana cewa mun bar yarinya sangan-gam a gida tana haɗa kafaɗa da Iyayenta. Koda kuke ganin a birni kuke rayuwa mu ba zamu lamunta ba don ko a birnin an daina barin yara suna ganɗamewa a gida, yaran yanzu dake da buɗaɗun idanu ba abinda basu sani ba, in aka barsu suka riƙa ba'a musu auren ba sai su koma bin Mazan waje. Mu kuma ba zamu lamunci a ɓata mana sunan zuri'a ba, don haka ki saka yarinya ta fitar da Miji a mata aure in kuwa ba haka ba to zamu turo mata ɗan'uwanta Rufa'i ya rufa mata asiri tunda shine mai Mace ɗaya a cikin dangin." Tana gama faɗa ta miƙe ta fice tana ci gaba da mita ba tare da damuwa da halin da Umman ke ciki ba.

   Da baya Umma ta faɗa saman gadon tana fashewa da matsanancin kuka, cikin kuka take addu'a da roƙon Allah ya kawo musu ɗauki cikin wannan tsaka mai wuyar......