HASASHEN SOYAYYA

Hs 7

by @legendspen

Page 07

A Hanyar Cafeteria ne Amrah tace   "Wancan gayen mai kyau ne."

"Wane gaye kuma?." Suhaima ta tambaya its dai Bhatool ba face ko ƙala ba amma tabbas ta yarda Senate mai kyau ne.

Sai ƙarfe 06:00 na yamma suka bar YSU daman su kullum shigar 08:00 fitar 06;00 ne ko sun gama classes ɗin su haka zasu zauna suyi ta surutu.

Alla Alla take ta koma gida domin ta karɓi kuɗi wajen Abdul, wani ɓari na zuciyarta ma cewa take taje can kasuwar suyi ta ta watse, a haka ta samu ta ƙaraso gida.

Da sallama a bakin ta kamar abun arziƙi ta ajiye jakarta ta ɗauki tsintsiya tana faman shara.  "A'ah Bhatool sharan me like?." Murmushi tayi ta cigaba da sharar tana faɗin.  "Yanzu  idan ban gyara gidan nan ba wa zai gyara, idan ban taya uwata aiki ba wa zai taya ta." Kallonta sosai Mama tayi sanan face " Banbu ƙaci aikin ba Bhatool balle nan da  ƴan mintina kizo kina cemun ban riƙe amana ba nasaki aiki, idan wani abun kikeso kawai faɗi."

A jiye abun sharar tayi tana faɗin "Wallahi Mama so nake kisa yaron can Abdul yaban kuɗin ɗinki."

"Ke yanzu fisabillahi Bhatool baki da wata magana sai abaki abaki, ke ko tanadi baki iya ba?."

"Ta nadin mene, naga dai haƙƙin kune ki ciyar da ni, ku tufatantar dani sanan ku ilmantar dani haka zalika ko kaini ɗakin Miji, sanan kuma gashi Allah yabani ƙani mai mai kuɗi, Sister na tana auren mai kuɗi sabida nice Nan banza zan zauna na yi tanadi."

Baki Mama ta riƙe sanan tace "Uhm ke ba bamza bace." daga haka ta koma ɗaki, itama Bhatool ta ɗau jakarta ta shige ɗaki.




~~~~~~~Red bricks

"Mom please introduce me to her." Kallon Senate Mom tayi, wani kululin takaici kamar ta kwaɗe shi, wanan sanyi halin nashi yayi yawa.

"Senate wane introducing yarinyar da na kawo maka har gida, akwai wani introducing da make ɓukata?."

"Mom yau tayi mun magana, amma ba a soyayya ba, I want you to introduce me to her as lover."

"Senate idan nayi introducing dinka as her love, sai na dinga raka ka zance ina yi maka hira ko?,bayan kunyi aure sai na koma gidan ko?."

Girgiza kai yayi sanan yace  "Ba haka ba Mom, ina so ne tace mun tana so na" 

"Sabida ita ta rako mata duniya ko, kaine yaka mata kayi proposing da kanka, and please ka nemi Anas ya taya ka ka barni na huta." 

Shiru yayi kamar zaiyi kuka, idon sa ya ciko da ƙwalla, bakin shi ya fara rawa. "Ya Allahu." Momi ta faɗa tare da tashi ta matso inda take, hannu tasa akan ka faɗar shi sanan tace "Senate what?.".

"Mom I so much loved her, I'm always going far."

"I know kana sonta but yaka mata ka nemo soyyarta da kanka, shine zata so ka ta ga girman ka as her Husband."

"Mom taya zanyi hakan?." 

"Kabani two days kaji." Gyaɗa mata kai yayi daga man ya tashi ya nufi ɗakinshi, Anas yaje gidan su kasancewar Maman shi ta dawo daga Kano.



~~~~~Nyanya


Zaune take kan ƙaramar kujera a tsakar gida, Mama kuma na daga gefe kan abun sallah, hankali Bhatool na kan waya tana chatting tare da zaman jiran Abdul ya dawo ta karɓi haƙƙinta, ita ko acikin gadonta ne.

Sallama yayi ya shigo hannunsa riƙe da ledar da ya siyo fruit wanda wanan abu ne wanda kullum sai ya siyo, Tashi tayi tana faɗin "Yaya Abdul sannu da dawo wa." Kallon ta yayi sanan yace "Yawwa sannu Yaya Bhatool ya makaranta ya gida."  

"Ai kune manya , ya kasuwa kawo na riƙe ma." ta faɗa tana karɓar ledar, kamar abun arziƙi ta shiga kitchen ta ɗakko plate ta zuba, suna zaune ta kawo musu ta ajiye tana faɗin.

"Yaya ya kasuwa?."  

"Kasuwa mungode Allah, ya makaranta." Murmushi tayi sanan tace  "WallaHi Alhamdulilah, Yaya."

Shiru ne ya biyo baya Kafin Abdul yace "Yawwa Mama ɗazu ake faɗamun Goggo Larai ba ta ji daɗi ba, ina ga yanzu zanje na duba ta ko?." Dariya Bhatool tayi sanan face "Abdul kanada shishigi a rayuwar ka, mene haɗin ka da wanan matar?."

"Ubanki Bhatool yayar mahaifin naku, uwa ɗaya uba ɗaya zaki ce mene haɗin ku da ita, to kisani har ke za'aje dubiyar nima gobe zanje."

"Ai shikenan, da shi wanda ya bada amanar, da amanar da ya bayar aka hada aka zage, Abbana ka mutu ka barni inda ba'aso na, ina da ba ƙauna ta ko ƙaunad farin ciki na, Abbana ka mutu ka barni wajem waƴanda basa sauke hakkinka akaina, Abba ba samun sutura abinci kawai suke banI."

Kuka take sosai kamar gaske, gaba ɗaya jikin Abdul yayi sanyi, tashi yayi yadawo kusa da ita. "Bhatool kiyi haƙuri yanzu me aka yi miki." Kuka take yi sanan tace "Yanzu nazo da anko aka kasayimun aka barni, yanzu kuɗin dinki ma an hanani so ake naje titi nayi bara."

"Waye ya hanaki, kin tambaye ni ne?". Girgiza kai tayi sanan tacee
"Nasani Yaya Baza ka bani  ba."

"Yanzu tashi ki shirya muje gidan Goggo Lami ɗin sai mu biya wajen mai ɗinkin na bashi kudin.

Miƙewa tsaye tayi tare da kar ka ɗe jikinta ta shige ɗaki, Girgiza kai kawai Mama tayi sanan tace "Allah ya kyauta."

Bayan mintina kaɗan ta fito cikin wata doguwar ta wani lace, irin ɗinkin nab da amare keyi sai zuba uban kyalli take, ankon bikin wata ƙawarta ne shima da tashin hankali akayi mata shi wajen dubu saba'in amma tun da akayi bikin ta watsar ba ta ƙara ɗaukan shi ba sai yau.

"Bhatool ina zaki da wanan kayan?."  Takalmin ta mai tsini ta ajiye ƙasa tana faɗin "Zani gidan maƙiyana ai gwanda nasa ka ka ya masu kyau, yanda baƙin ciki zai ƙarasa Goggo Lami ta mutu har lahira."

"Innullahi wa inna illahir rajiun, ni Habiba wanan yarnya Allah yakawo mata sauƙi da nutsuwa da kuma hankali, walallahi ko da wasa wani yazo neman auren ki sai na bashi kuje can ku ƙara ta."

Dariya Abdul yayi yana faɗin  "Mama da ƴar ta."

"Faɗi ka ƙara Mama da Ƴar ta, ƴan bakin ciki."

Ficewa yayi itama tabi bayanshi tana faɗin "wallahi kafin mu ƙarasa sai na siya sabon cover ɗin waya mai kyalli dan wallahi so name bakin ciki ya ƙarasa munafu kar matar naman



~~~~~~ Red bricks

Senate ne zaune cikin ɗakinshi tare da wani kyakyawan saurayi wanda take sanye cikin ƙanan kaya, saurayin ne ke magana yana cewa.

"Senate you're so annoying wallahi, na dawo daga Cyprus ba ka barni na samu isashen hutu ba kace kana da magana kuma nazo kasani a gaba."

"Am sorry Juraij, Na faɗa soyayya." kallon shi Juraij, sabida Juraij ya nada baiwar Fahimatar Senate ssosai da sosai.

"Who is the lucky girl." Murmushi Senate yayi sanan yace "Sunan ta Bhatool I mate her last three months but ba mu taɓa magana da ita ba sai yau, I mean yau da kanta tayimun magana."

"Hahaha." Juraij ya faɗa sanan yace "Muga hotonta kuma yanzu me make tunanin yi."

"I don't know." Ya faɗa yana nuna mai hoton ta dake kan screen ɗin wayarsa wanda ya dauke ta a makaranta ba ta ma sani ba. "This Girl?." Juraij ya faɗa cike da mamaki.


ku yi following Page dina pls, ku yi supporting dina ta hanyar comment😭