HASASHEN SOYAYYA

Hs 8

by @legendspen


_Page 08_

"This Girl?." Juraij ya faɗa cike da mamaki,  "Kasanta." ɗaga kai Juraij yayi yana dariya 

"Uwar ƴan rigima kenan yayanta abokina nane, ina siyan shadda wajensa daga nan muka fara mutanci dashi, wanan yarinyar ƙanwar sa ce the stubborn girl I ever meet in my entire life."

"Juraij she is my future wife stop addressing her like that." Senate yafaɗa Kamar zaiyi kuka. "Okay nadaina but kana ganin haɗin ku zaiyi?." 

"Why not?." Senate ya faɗa tare da ta shi ya shiga toilet, shima Juraij ɗin tashi yayi ya fice.

~~~~~Suna cikin mota tana baza ido inda zata hango masu fruit ko provision store, dan tayi alƙawarin sai ta ƙunsa musu takaici sanan kuma tana son canja case ɗin waya, cikin ikon Allah ta hango wani kusa da shi kuma masu fruit ne sai kuma provision store.

"Abduk wai haka zamuje gidan nan hannu mu na dukan cinya?." Tsayar da tuƙin yayi ya kalleta sanan yace "Bangane ba?." Girgiza kai tayi sai kuma tace " Ai daman ba zaka ganw ba, zaka je gidan maƙiyan ka shine zaka tafi a tsiyace ƙarshen asara babu ko leda."

Kallon ta kawai Yake shi tsoron sa ma kar taje tace musu maƙiyan ta. "Kinga nutsu yanzu me kikeso ayi?."

"Kaga mu sauka muje wancan provison ɗin kasiya mata ƙwai, madara, suger  sanan muje wajen mai fruit shima kasiya ma ta dayawa ma, yanda baƙin ciki da takaici zai ƙarasa ta." Da mamaki yace "Ke Bhatool!." 

Rufe ido tayi tana faɗin "Abdul umarni na baka ba shawara ba." Shi dai mamaki ya kusa kashe shi yanda ta rufe ido tana faɗa wai ita umarni ta bayar.  "Abdul wallahi idan naƙara maimaita kaina baza kaji daɗi ba."

Parking yayi zuwa gefen titi suka fito, wajen mai fruit su ka fara zuwa "Mai fruit inaso kabani lemo na dubu biyu, kankana ta dubu biyu? Abar ba ta dubu biyu, ko kuma kabani kowanne na dubu uku uku, sai ƙabani ayaba ta dubu daya kaga yakama dubu goma."

Mamaki kam zai iya kashe Abdul a wanan lokacin, dan yanda take abu kamar itace Mama.  "Bashi dubu goma." Abdul yaji ta faɗa, hannu yasa a aljihu ya ciro kudin gaba ɗaya ya bata.

Lissafa wa tayi tabawa mai fruit ɗin 10k sanan ta shiga provison store ɗin, man madara tasa aka ɗakko mata babban gwangwani da kuma milo shima babban gwangwani sai ƙwai kiras biyu, akayi mata lissafi taba su kuɗin aka biyo ta dasu.

A wajen mai fruit ɗin ta ga Abdul Yana tsaye,"Amso fruit ɗin ka haɗa da kayan Nan kasa a bayan mota, sanan mai fruit ka ware mun banana ɗin daban, dan bazan ba taba tunda ba kuɗin ubanta ne, wanan ɗin ma Allah ya isa." Daga haka tashiga shagon masu cover ta siya wata mai ƙyalli sosai sanan ta dawo mota suka nufi hanya.

Babu wanda yayi magana a cikin motar sai Bhatool da take cin ayaban ta hankali kwance, har suka ƙarasa ƙofar gidan Abdul yayi parking.

Saida ta gama gyara jikinta sanan tafito daga cikin motar, hannun ta riƙe da Wayarta wacce cover ɗin ke ƙyalli da sheƙi, a yangance take tafiya Abdul riƙe da ledoji kamar wani ɗan aikinta a haka suka shiga cikin gidan.

Kasancewar gidan family house ne, duk ƴan uwan Abbansu na cikin gidan, ɗai-ɗai ku ne basa gidan, cike yake da hayaniyar yara kamar ba farkon magariba, duk inda sukayi binsu ake da kallo. Abdul ne ke tsugunnawa yana gaidasu, itakam daga tsaye take cewa "Ina wunin ku." su bama ta gaisuwar ta suke ba, kayan jikinta dake ƙyalli suke kallo.

A haka har suka ƙarasa ɓangaren Goggo larai wanda shima cike yake da mutane, Sallama sukayi aka fara gyara musu wahe da faɗin. "Bisimillah ku shigo." Shiga sukayi Abdul na ta washewa ƴan uwa baki, Bhatool kam ta haɗe rai a zuci kam cewa take "Kai Abdul anyi asararre waƴanan kake washe baki haka wallahi sai kaci gidanku."

"Goggo ina wuni, ya ƙarfin jikin." Abdul ya faɗa bayan sun zauna, "Lafiya ƙlau Abdul bawan Allah." Goggo larai ta faɗa murya ƙasa ƙasa. "Ai kings leda munafuka done kice bawan Allah." Bhatool ta faɗa a ranta, a fili kuma cewa tayi 

"Ina wuni ya jiki naki, Allah yasa kaffara ne."
"Batula jiki Alhamdulillahi, ya maman taku." wata uwar harara Bhatool ta maka mata "Wai Batula." Abdul ne yace tana lafiya, itama gobe zata shigo." 

"To Allah ya kawo ta lafiya." Goggo Larai ta faɗa zuciyarta cike da mamakin yanda 'ya'yan Ahmad suka samu cigaba a rayuwa, yaran da suke kira 'ya'yan mace, gashi sun sami cigaba sama da 'ya'yansu.

"To Goggo ga wanan ba yawa." Bhatool ta faɗa ta miƙo ledojin sanan ta buɗe jakarta ta ciro canjin kuɗin ta miƙawa Goggo tana faɗin "Ga wanan ma Goggo." Hannu na rawa Goggo larai ta amshi damin kuɗin tana faɗin.

"Allah ya yi muku albarka yaran nan, Allah ya yi wa mahaifinku rahama."  Miƙewa Bhatool tayi tana faɗin "Ameen."

Haka Abdul ma yatashi ya fito yana mamakin wanan Abu na Bhaool, su kam su Goggo larai mamaki ya kusan kashe su yanda yaran suka canja baki ɗaya, kana ganin su kasan suna cikin huti da jindaɗi, Furai ce tace "Ni kam kunga kayan jikin yarinyar nan kuwa?."  

Habi ce tace "Furai nagani wallahi, ke mijin karima ke mata suttura dan ubanta basu da kuɗin da za suyi wanan suttura.".

"Ba kiga wayar hannunta ba, har wani sheƙi take." Furai ta sake faɗa. "Uhm kwaji da shi nidai na samu abun duniya cansu ƙarata, idan na gama ci na tufa abinda ke bakina." Goggo Larai ta faɗa tana buɗe ledojin.

"Ni Balaraba wacce aka haifa tabawa ranar sa'a, wanan kayan duka?."Goggo larai ta faɗa tana duba kayan duka.

"Aike Goggo waɗan nan yara sun gwangwaje ki." Habi ta faɗa tana kallon kayan "Ni wallahi waƴanan kayan a banza bazan daina tsanar yaran nan ba, da uwarsu gashi yanzu sunyi arziƙi sun bar namu yaran."

Furai ce face "A'a Goggo likita yace karki saka damuwa a ranki."  Tsaki Goggo larai taja tana shan lemo tana faɗin "Banso rayuwar 'ya'yan Ahamadu tayi kyau haka ba.".

"Wai kinga wani banza kallo da wanan mara kunyar yarinyar take mana." Jumala dake gefe tun ɗazu ta faɗa, "Nagani wai its yar iska,Wallahi Goggo ki ta da bori sai anhaɗa ta aure ko da kamisu ɗan wajen Baffa ne." Jumala ta faɗa sabida ita tana mugun bakin ciki Karima ma shekara ɗaya ta bata amma gashi ita tayi sure gidan hutu amma ita auren ta biyu duk sun rabu sai yara guda uku, amma gashi wanan yarinyar ma tana cikin kuɗi.

"Nikam maganarki da gaskiyya Jumala." Furai ta faɗa tana kwance sauran kaya, ita dai Goggo ba tace komai ba.




~~~~~~Parking ya yi dai dai ƙofar gidansu bayan sun biya ta wajen mai ɗinki an bashi kuɗin, kallon Abduk  Bhatool ta yi sanan face "Allah ya isa kuɗin mu, nasan suna can suna ta zagin mu amma ko ba komai mun barsu da kayan bakin ciki."  

"Ke dai kika sani, fitar mun daga mota." Abdul ya faɗa yana koƙarin buewa ya fita "Mara kunya." ta faɗa tana fita, a haka suka shiga cikin gidan tana gaba yana baya. Kai tsaye ɗakin ta huge tana faɗin "Wanan kayan kamar huta haka nake jinsu." 

"Ke dai kika sani da wani yace ki saka su." Mama dake cikin ɗaki ta faɗa, Abdul dai ɗakin Mama ya shiga yana faɗin wanan 'yar taki halinta sai ita, yau idan ki kaga abinda tayi sai kinsha mamaki."

"Ai wallahi Bhatool bazata taɓa hankali ba, ina tausayin Wanda zai aure ta." Bhatool daga cikin ɗaki face "In Allah yayarda miji nane zai fara kaiki aikin hajji tunda wanan yaron kaiki Umara.".

      Washe gari

~~~~~~Red bricks

Ganin hae ƙarfe 08:00 babu Senate babu alamun shi yasa Mom tafiya ɗakinsho domin ganin mai ya hana shi tashi, kwance yake yana bacci fuskarshi ɗauke da murmushi da alama mafarki take mai daɗi, juyawa Mom tayi zata fita taji yana cewa "Bhatool I so much love you,please karki taɓa barina." Kallonshi Mom tayi sosai its tana mamakin yadda Senatr yafa ɗa soyayya mai zurfi da Yarinyar da ba ta masan yana sonta ba.

Komawa ɗakinta tayi ta ɗau mayafin ta ta fice zuwa gidan Karima, Yaya Karima na Zaune ta ji sallamar Momi, tashi tayi tana faɗin "Ina kwana Momi."  murmushi Momi tayi tana faɗin. "Lafiya ƙlau daughter ya mai gidan naki?."  

"Alhamdulillah Momi." Yaya Karima ta faɗa tana ta mamakin zuwa Momi ɗin, Zama Momi ta gyara sanan tace  "Karima na tambaye ki wani abu mana?."

"To Momi Allah yasa na sani." Kana jin yanda tayi maganar kasan tana cike da ruɗu da mamaki. "Wanan yarinyar da kika ce ƙanwarki ce mene alaƙarku da ita?."

✍🏼