ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

25

by @gureenjoh

"Why do you keep tailing me? Me yasa kike cigaba da bibiyata? Saka ki aka yi? Ko biyanki aka yi don ki ɓata min suna saboda already ke ba ki da wani mutuncin karewa?"


Bata taɓa tunanin zai iya gayamata hakan ba, ba kuma don ta san shi farin sani ba sai don sanin bashi da tsauri a kalamai matukar zai isar da wani saƙo mai muhimmanci ciki.


Kaman yadda ya faɗa ne bashi da buri ko nufin a ce wannan maƙiyinshi ne yana iya kokarinshi wurin ganin bai zama abokin gaban kowa ba amma this particular girl ta shigo rayuwarshi rana tsaka and abin is really getting out of minds.


Yadda yake kallonta haka take kallonshi, idanunta na nuna ɓacin ranta da kalamansa.


"Me yasa zan bibiyeka? Me zan ɗauka a tattare da kai?"


Ya ɗan yi baya da kanshi yana kawar da fuska sai kuma ya kalleta 

"Ashe kema kin san babu gami, then me zan ƙira haɗuwar mu a asibiti? Haɗuwar mu a Airport, haɗuwarmu a hotel guda? Ina kyautata zaton da gangan kika sauya akwatunanmu tunda ke ce kika fara ɗauka saboda kawai ku yi framing dina right? This is not a coincidence and no one will convince me in yarda cewa coincidence ne"


Kasa magana ma tayi don mamaki, sai ta ɗan yi murmushi tana sauƙar da Idanunta ƙasa sai kuma ta kalleshi ta ce

"Ka san mene? Ka fita a sabgata tun ban nuna maka kalolin rashin darajata ba don yanzu ka gama faɗa ba ni da mutunci, kuma a rashin sanin mutuncin kamewar ban ga abin marmari da zan bibiya a rayuwarka ba, kudi kuma sun yi kadan su sa na ɓata lokacina a kanka idan ma zargi kake to tun maza ka daina! A baya ma na bibiyeka ne saboda in ɗau fansar abin da ka min kuma mun gyarota idan ba kana son na janye ma hakurar da nayi ba ne ka daina nuna min fuskarka a tawa don babu abin burgewa a rayuwarka"


Bakin da take tsiwar yake kallo zuwa idanun da take tsayarwa cikin nashi tana rashin kunyar da ta ga dama.

Taku ya ƙara gangar ta sai ta ɗan kawar da idanun tayi baya yace 

"Ƙarya ɗabi'a ce ta duk wani ɗan maye, kalaman bakinki ba su za su sa na amince da batunki ba, kuma muddin nayi bincike na gane wallahi billahi sai na yi shari'a da ke!"

Ranshi a matukar ɓace ya ƙarasa.


Ta kalleshi suka sake haɗa idanu tayi baya baya kan ta furta...

"Then do your worst Mr. Sheikh"

Tana kai nan kawai ta juya ta bar wurin bata ƙara ba saboda idan za tayi ɗin kila wuta ne zai na fita daga bakinta, wanene shi da zai yi tunanin har akwai wanda zai biyata ta bibiyi rayuwarsa? To ta ɗauki me ciki? 


Wannan shirun da tayi sai kuma ya ji babu daaɗi, goshinshi ya ɗan shafa ya furta

"Ya Allahu ya rahman am I too harsh on her?"

Wani zuciyar yace yeah baka da hurumin zarginta akan abin da baka da tabbaci but she's in all the pictures duk wani angle da zai juya tana nan ciki Meyasa hakan?"


Ya jima tsaye nan yana saƙa da warwara, kiran da ya amsa daban daban a yau suna dawo mishi kowa kuma kokari yake ya ga ya ja hankalinshi akan faɗawa wata mu'amala ko ta kusa ko ta nesa da yarinyar nan, sai da ya samu masalaha a ranshi kan  ya koma ɗakinshi ya kwanta, da sassafe ya shirya ya tattare duk abubuwanshi ya ƙira drivern dake zirga-zirga da shi, sai da ya ce mishi ya zo kan ya janyo akwatin ya fito reception ya yi check out ya bar hotel ɗin gabaɗaya.


Sai da suka hau titi drivern ya tambayi ina zai kai shi?

Idanunsa a lumshe yana kwance cikin seat ɗin yace 

"Area 11 Garki"

Ya faɗa a hankali kila idan yayi nesa da inda take babu wani kaddara da zai sake haɗasu, akallah yana da sauran aiki a garin yadda kuma hazo ya yamutse dole zai cigaba da zama a Abujan da sanayyarsa tayi ƙasa ba kaman a Kano ba.


A irin lokutan nan da zai zama topic of discussion kowa haushi yake bashi, hakan ya sa a lokutan ya fi mayar da hankali ma kan ibada saboda shi ne kadai abin da ke sanyaya zuciyarsa tunda ba fitowa zai yi ya ce ba haka ba, hakan da zai yi ma shi zai karawa abin fetur ya cigaba da ci ya ƙi mutuwa.


Wani hotel ya kai shi a nan cikin Area 11 ɗin ya fi ma wanchan tsaruwa nesa ba kusa ba, yayi booking ya ajiye kayakinshi kan ya fito suka wuce wurin program tea kawai ya sha ya cigaba da program din yana cire duk wata 'yar Daba daga kwakwalwarsa a cewarsa.


Ta ɓangaren Diva abin da yayi mata na cin ta amma ta zaɓi shiru fiye da mayar da martani hakan ya sa ta ci alwashin kiyaye ma haɗuwarsu, wai ɗabi'ar dan maye ƙarya ita duk duniya bata ga wanda ya rainata ba ma kaman wannan Shehin akwai wanda ya isa ta masa ƙarya? Ai ko click ɗinta sun sani ba'a yi mata ƙarya kaman yadda bata yi don ta tsaneshi fiye da komai, ta yi mita ita kaɗai har ta gaji, har tambayar kanta take me ma abin bibiya a rayuwarsa mutum ina ka fito wa'azi ina za ka wa'azi? Kullum ana fama da litattafai ita Sam ba abin burgewa ba ne a gareta.

kadaici ke damun zuciyarta haka shirun yayi mata yawa don babu abin da take yi iyakaci ta ci ta sha ta sha abin maye tayi bacci in ta tashi kuma tayi exercise har ji take kaman ta kira su Shaly su zo tunda Jagaban ya ƙi amincewa ta koma, sannan anan bata rigimarta don babu wanda ya taɓota hakan ya sa tayi kewar Kano.


A chan Kano kuwa ɓangaren su Abbiey abin da suka gani din ya sa sun yanke hukuncin bin shawarar Ammiey kawai a yi masa auren hakan zai rage maganganu dayawa, don haka tuni suka fara shirin kai gaisuwa cikin farkon wata mai kamawa.


Ɓangaren Jiddah tana cikin tashin hankalin rashin sanin inda suka kai mata 'yar uwa ta yi kuka har ta gaji ta dawo shiru kawai, sai addu'a bata san wani hali iyayensu ke ciki ba suna chan cikin kwanciyar hankali ko kuwa ga hankalinsu tashe bisa rashin ji daga garesu? Tana fata su ji a jikin su su kuma dage musu da Adu'a dukda ta wani fannin ta gama karaya wannan azzalumi da ake kira J duk inda za ka zaci zalunci da rashin imaninsa ya wuce nan.


A chan cheɗiya Inna da ta zabga tagumi ta kalli malam tace 

"Malam ni dai har yau hankalina ya kasa kwanciya, a jikina nake jin yaran nan basa cikin kwanciyar hankali."


"Ba ke kaɗai ba Atika, tun daga ranar da suka bar kauyen nan hankalina yake a tashe, sai in ga kaman mun yi kuskure mai girma, layin da suka bamu na kira na kira baya shiga"


Ta muskuta

"Toh ko za mu dauki fom din a wakilta wani ya je chan Kanon ya duba mana su?"


"Zan je yanzu in samu dagaci da maganan tunda kin ga ba su Hauwa'un kawai ba ne akwai yaran jama'ar garin nan dayawa."

Haka suka tsayar ya miƙe ya fice.


Kaman yadda ya faɗa kai tsaye wurin mai gari yayi ya same shi bayan yayi gaisuwa aka tambayi me ke tafe da shi.


"Da ma akan wannan tallafi da aka mana na fitar da yaranmu koyon sana'o'i ne, wallahi daga ni har mai ɗakina hankalinmu ba'a kwance ba ya kamata zuwa yanzu mu ji ɗuriyarsu tunda wata ukun har ya wuce"


Kaman jira waenda akwai yaransu ciki suka fara gyada kai suna cewa tabbas wannan gaskiya ne shirun ya fara yawa.


Dagaci yace 

"Ban da abun ku ai tunda gomnati ce ta turo mana su na tabbatar babu cuta ko ha'inci a lamarin su kuma shiru ai wata alamar lafiya ce idan babu lafiya ba za'a ji shiru ba amma ban ƙi ta taku ba mu ƙara musu ko sati biyu ne idan bamu ji daga garesu ba da kaina zan ɗaga mutum na aika chan birnin Kanon mu ji lafiyarsu"


Ba don hankalin malam buba ya kwanta ba ya amsawa dagacin da godiya don kusan sun yi na'am da zantukanshi don baƙin ma da suka zo ai sai da suka fara mishi bayani har ma suka bashi yayi waya da ministern mata.


Daga nan dai ya tashi ya bar wurin ya koma gida bai boyewa inna Atika duk yadda suka yi ba tace Allah ya kai rai.


***


"Da gaske Mama? Da gaske wani watan za'a zo tambayar aurena daga gidan su Shehi?"


"Kwarai ai na faɗa miki ki dinga hak'uri da uzuri gashi nan komai na shirin kankama? Gaggawa babu inda zai kai ki"


Tsalle ta yi ta dire ta yi ɗakinta da gudu tana murna, mahaifiyarta ta bita da kallo tana murmushi sai ta ɗaga kai sama tayi godiya ga Allah da Babanta Ustaz Abdallah bai ƙi batun Shehi ba, shi mutum ne mai tsauri da tsanani a kan yaranshi, baya yardar musu wata mu'amala ko soyayya har sai kin kamallah jami'a da kanshi zai zaɓi wanda yake so ya aurar da ke. 


Tun Jss 2 Na'ima tayi wani saurayi da ta so aurenshi mahaifinta ya ƙi babu abin da ba'a yi akan yaron nan ba ta kai har auren mahaifiyarta sai da ya tsinke kan aka sake mayar da shi a sannan ne tana Ss3 ta hakura da zancenshi saboda ganin tana shirin shiga tsakanin iyayen ta a hakan tayi ciwo tayi kunci kaman ba zata rayu ba don bata iya saka abu a rai ba, kwatsam kuma ta gamu da sheikh ta fara sonshi, tun babu wanda ya sani har mahaifiyarta ta sani kuma dama kawar Ammiey ce ita ta nemi haɗa ya'yansu kuma Ammiey ta gamsu da tarbiyar gidan don haka hankalinta kwance take shirin auren ɗan nata na fari.


****


Yau Diva ta tashi da farin ciki bayan kusan kwana goma a Abuja Jagaban ya saya mata ticket akan za ta koma jibi, ba ita kaɗai ba har su pabloo shirye-shiryen tarbarta suke, yau da wuri ta tashi don akwai sakon da za ta karbar wa Jagaban a Apo amma bata fita ba sai da ta gama duk wani abin da za tayi a hotel ɗinta kusan uku da wani abu ta bar hotel ɗin.


Bolt ta yi zuwa unguwar sai da ta sauƙa inda aka ce mata kan ta shiga takawa da kafa kaman yadda ya ce mata har ta isa daidai wurin ta danna earpod na kunnen ta ta sanar da isowarta mintuna goma bayan nan aka sake kiranta daga cikin wayan ake bayanin kayan jikinta baƙin wando, farin top, blue and white over-size shirt, black vail and facing cap.


Kai take gyadawa a hankali ba'a katse wayan ba wani ya zo ya ajiye mata jaka a kan kafarta ya wuce, babu wani shakka ta saka a kafadarta ko kallon inda ya bi bata yi ba ta miƙe ta naushi dayan barin, bata hau abin hawa ba kawai ta cigaba da tafiya a ƙafa har ta iso wani crowded road.


Akwai holdup tsallakewa take son yi kaman an ce ta kalli motar gabanta, sak Suv ce irin nata tana iya kallon maza uku dake ciki da wata mace dake galabaice tana dukan jikin windown, har ta dauke kai sai ta sake kallon wurin a daidai nan ta ga dayan ya ja ta baya ya kai mata duka ido ta runtse kaɗan ta buɗe, ba tinted mai duhu ba ne amma idan baka mayar da hankali ba ba zaka iya ganin abin da ke wakana ciki ba hakan ya sa mutane ke ta hada-hadansu.


Jikin motar ta isa a bazata ta duka ta zare wukar dake jikin takalminta, cikin seconds tayi picking lock na jikin kofar kan su kula sai ji suka yi an buɗe na gefen kofar tayi wa wani yanka da ya sa ya kwalla ƙara kan su ankara ta fusgo wannan baiwar Allahn dake galabaice ƙasa ta ja ta baya, wukar da ta riƙe da ihun da na ciki yayi shi ya ja hankalin mutane suka fara ihu, Road safeties da police da ke kusa suka taho a guje ganin haka ya sa suka ja motar a dari sai kakkaucewa aka shiga yi.


Duk waenda suke kusa da ita da wannan mata sun gudu, waiwaye take ko akwai wanda zai zo ya taimaka a kai ta asibiti saboda bakinta da hancin ta jini yake fitarwa gata kamar matacciya, idanunsa suka sauƙa kanshi.


Ya fito daga taron su da jibi za'a rufe, a gajiye yake tilis Kasancewar anan cikin Apo din suke program din nasu zai koma hotel nashi, tsayuwarsu holdup din ya sa ya buɗe idanu yana kallon mutane na ta hada hada Kasancewar yamma ya fara wasu makarantun sun rufe kuma wuri ne mai jama'a.


Ihun da ya ji ya sa ya kai idanunsa wurin sai ga mutane sun fara gudu idanunsa suka sauka a kanta riƙe da wuka, mamaki tsantsa ne ya rufe shi, wannan kanta ɗaya kuwa? A tsakiyar mutane a tsakiyar gari irin wannan mai tsaro? Buɗe murfin motar ya tsinci kanshi da yi ya fita, sai da ya matsa dab da ita ya fahimci abin da ke faruwa ga ma'aikata sun bi wanchan motar duka.


Idanun da suka haɗa ta tsayar tace 

"Stay away!"


Ya girgiza kai yana kallon yarinyar dake kwance a ƙasan with genuine concern da Bai ɓuya ba a muryarsa yace calmly

"Saving a life comes first before everything else"

Ya fahimci tana son nuna bata son taimakon da zai yi ne saboda kar ya ce ita ta sake bibiyarsa amma ba zai tafi kaman yadda sauran mutane ke gudu wasu ma na daga nesa suna video da wayoyinsu don posting ba, ya tabbatar da iyayensu ne ko 'yan uwansu babu mai fidda waya da sunan posting amma a yadda taimako yayi karanci yanzu har tsoro abin yake bashi.


Ita ta kama yarinyar suka nufi mota da wani police ɗaya yana ta kokarin kira a kawo mota ne ma tace mishi su je kawai basu sani ba kar jinkirinsu ya ja mutuwar yarinyar a kallo biyu ta mata ma ta fahimci an ɗora ta kan mummunar drug.


A gaba Shehi ya zauna police da ita da yarinyar suka shiga baya tuni drivern ya ja yana alhinin wannan abu da ya faru yana kuma jinjinawa kokarin Diva da bata ce komai ba sai hijabin jikin yarinyar da ta cire don bata iska saboda yadda take jika da wani irin zufa.


Babu ɓata lokaci suka isa wani kyakyawar asibitin kudi aka shiga da ita police din ya tsaya cike cike inda Sheikh duk abin da aka kira kudi zai cire Atm card ɗin shi ya bayar.


Ita dai Diva wuri ta samu ta zauna sai lokacin ta ji jakan sakon Jagaban a jikinta a fakaice ta kalli police din, dole ta bar wurin yanzu amma bata son tafiya bata san halin da yarinyar ke ciki ba, dukda a yanzu ta san she's safe police za su yi duk wani abin da ya kamata, a hankali suka fara ƙaruwa damuwarta sai ya kasu biyu waennan ba police na Kano ba ne bare tayi ikirarin Jagaban zai shiga ya fita, komai zai iya faruwa don haka tana bukatar tafiya.


Tana Miƙewa tsaye police da ya kawo su ya nuna ta yana yi wa oganshi bayanin ai ita ce ta cece yarinyar.


"Za ku tafi da ita ta ba da statement su kuma za'a cigaba da neman su don sun tsere"


Ta kawar da kanta tana komawa zaune, Shehi na tsaye a gefe bai ce komai ba amma idanunsa na kanta yana mamakin damuwar na halin da yarinyar da bata sani ba ne take ciki ko kuwa wani abu daban? Yarinyar lamarinta na ɗaure mishi kaiii.