Chapter 17
Motsin shigowar da ya ji an yi ne ya sa shi janye idanunsa daga kan hoton a kaikaice, kamar ba abin da yake gani.
Mammy
ita ma a hankali ta janye idanunta daga kallonsa da take yi, ta mayar da su kan Oga Fahad, da ke tsaye a bakin ƙofa, hannunsa ɗauke da takardu, fuskarsa cike da mamakin ganin Abdul zaune a kan kujera.
Ba iyakacin mamakin ganin Aziz ɗin a kan kujeran ne ke kan fuskarsa ba, har da tsananin tsanarsa da tun a karon farko ya darsu a zuciyarsa.
Saboda a duk lokacin da zai daga kai suyi ido hudu da shi, sai ya ga wani abu mai wuyar fassarawa a cikin kwayar idanunsa.
Hakan yasa ya ji ya tsanesa, ba ma iya tsana kawai yake ji a game da Aziz ɗin ba, har da rashin gaskiya da zargin yana shirya musu wani abu.
Duk da a iya ɗan ƙanƙantar kasantuwarsu tare, bai taɓa kama shi yana aikata wani abun zargi ba, duk da yadda ya sa masa ido kuwa.
Yana bibiyarsa ta bayan fage. Dalilin ya sha kama shi yana murmushin gefen baki masu ma'anoni dewa.
Murmushin da a wasu lokutan sukan fi kama da murmushin aika saƙo ga wani, ko kuma murmushin ganin alamun samun nasara ga duk abin da aka saka a gaba.
Har yanzu yana zaune, bai tashi ba, bai kuma nuna alamar zai tashin ba. Duk da hakan doka ce ga duk ma'aikatan kamfanin, idan har oga Fahad ya zo waje dole ne a mike a gaishe shi.
Ganin Abdul bai mike ya gaishe shi ba, ya sa ya tako cikin ofishin a zafafe, duk da kuwa yadda yake jin idanun Abdul ɗin na barazanar karya masa abin da ya yi niyya.
"Ya Fahad."
Ta faɗa a lokacin da ta iso gabansa ta tsaya. Cikin shagwaɓar da ta saba yi musu magana da ita ta ce:
"Daddy ya faɗa min su Umma sun zo suna gida. I'm going. Bye, take care."
Ta ƙarasa maganar cikin jin daɗi sosai.
Bata jira ya bata amsa ba ta juya da sauri za ta wuce.
Sai dai taku biyu ta yi ta bugu da teburin da ke gefensu.
"Hey Mammy, yi a hankali mana. Duk wannan saurin na zuwa ganin Hydar ne?"
Baki ta ɗan tura gaba kamar za ta yi magana, sai kuma ta fasa. Kana ta juya ta ɗan saci kallon Abdul, da ke zaune a inda yake, ya yi shiru kamar bai san da zaman su a cikin ofishin ba.
A hankali ta janye idanunta, tare da sakar wa bayansa harara.
Oho, shi dai bai ma san tana yi ba. Aikin banza, wai harara a duhu.
Ba tare da ta yi masa magana ba, ta juya za ta fice.
Ganin tana ƙoƙarin barin ofishin ne ya sa shi ma ya mike a hankali ya shiga bin bayanta da salon tafiyarsa mai cike da nutsuwa da daukar hankali.
A hargitse ta juyo tana kallonsa, ganin yana bin bayanta ba tare da ya tashi su Afaf da ke bacci ba.
Dama da haushinsa daya cika mata zuciya.
"Saboda kai ba ka je makaranta ba, baka da ganewa, shi ne ka wani taso zeke-zeke tsaye kamar fatalwa ka biyo ni. Su kuma yaran da ka bari, waye zai ɗauko maka su?"
Da sauri ya rintse idanunsa, yana jin ihunta na shiga masa har cikin kwakwalwa. Tabbas, zuwa yanzu ya fara gajiya da ihunta, saboda shi mutum ne wanda sam baya son ihu da hayaniya. Duk da a wasu lokutan abubuwan nata kan ba shi nishaɗi, amma da za ta yi cikin kwantar da murya, da hakan zai fi masa daɗi.
Ganin za ta sake buɗe baki ta yi wani tijaran ne ya sa shi juyawa ga yaran a hankali.
Yana ƙarasa gaban kujerar yaran, kamar haɗin baki, gaba ɗayansu suka farka daga baccin da suke.
Ganin sun riga sun tashi ya sa ya mike.
Har zai fita, sai kuma ya tuna da jakar ta da Suhairat ajiye a hannun sofa.
Suna fita, ya miƙa mata handbag ɗinta da key ɗin mota. A hankali ta dakata da tafiyar da take yi.
Sai da tayi fari da idanunta kafin ta hararesa, sannan ta kalli kayan a yamutse. Murya a can ƙasan maƙoshi ta furta tambayar da ke cinta tun dazu.
"Menene dalilinka na tsatstsare hotunan da ke office da waɗannan mayun idanuwanka masu kama da na mujiya?"
Ta ƙara sa maganar tare da kafesa da nata idanun, da shi ma yake ma kallon na mujiyar.
Kadan ya ɗago idanunsa ta gefe ya dube ta a kaikaice ya yinsa fuskarsa ke bayyane da mamaki kadan, saboda bai yi tsammanin abin da zai fito daga bakinta ba kenan.
Ganin bai da alamar bata amsar da take buƙatar ji, yasa ta ce,
"Malam, da kai nake fa."
A hankali ya rintse idanunsa yana ɗaga kansa sama kamar mai neman taimako. A zuciyarsa ya ce,
"Oh ni gidado, ina ganin rayuwa ya Allah, help me."
Ya ƙarashe maganar a ransa tare da buɗe idanunsa yana kallonta.
Kamar zai share sai kuma ya yi magana cikin deep voice ɗin nan nasa, wanda a duk lokacin da ya yi magana take jin kamar a cikin kunnuwanta ya yi maganar.
"I just saw that the picture looked good. and mutanen da ke cikin hoton sun dace da juna."
Ya ƙarasa faɗin maganar yana kallon cikin idonta.
Ta dai ji shi, amma har ga Allah ba ta gamsu ba, saboda ba wannan ne ta hango a cikin idanunsa ba. A hankali ta kawar da kanta daga gare shi tana kallon wani wajen.
Jin tayi shuru yasa ya saci kallonta a hankali. Ganin wani wajen daban take gani ya sa shi tabe baki, har sannan kuma idanunsa suna kanta.
"But kin san mene, my boss?"
Da sauri ta dago ta kallesa jin ya kirata da my boss.
"It looks like babu wani soyayya ko shakuwa a tattare da su. Yanayin hoton looks kamar ita kaɗai ke faman son sa saboda na..."
"Stop this bullshit, ka yi min shuru."
Ta dakatar da shi a harzuƙe.
Muryarta kamar zai tsage ta ce,
"Dama nasan wannan kallon da kake yi musu bana tsakani da Allah bane. Amma ina son ka sani, koma menene a cikin zuciyarka game da my parent, sai na bincikosa sannan na hukunta ka."
Ta ƙarasa maganar tana jan numfashi sosai kamar mai cutar asma.
A hankali ya kawar da kansa gefe tare da sakin wani ƙaramin murmushi wanda idan ba farin sani ka yi masa ba, ba za ka iya gane abin da ya yin ba.
Ganin tsananin ɓacin rai a kan fuskarta hakan ba ƙaramin faranta masa rai ya yi ba. Ba don komai ba sai don yadda fuskarta ke zama kamar ta boss lady a duk lokacin da ranta ke a ɓace tana masifa. Kallon hakan na ba shi nishaɗi, shi ya sa lokuta da dama yake yin abin da ranta zai ɓaci, yayinda ita kuma ta kasa gane hakan.
A zafafe ta ƙwace jakanta da ke hannunsa ba tare da ta jira sun ƙarasa wajen da bodyguards ɗinta ke jiranta ba. Ta yi gaba fuu kamar zata fire ta barshi tsaye, yayinda su Afaf suka bi bayanta suna daga masa hannu.
Kafin ta isa wajen da motar ke tsaye har an wangale mata ƙofar motar. Tana isa ta shige a fusace kamar wacce aka jefo cikin motar.
Su Japhat wadanda ke jiran shigowarta suka bude mata marfin motar tana shiga kuwa suka tada motar a guje.
Da kallo kawai ya bi ta har ta shiga motar. A ransa yana mamakin yadda bata gajiya da daga muryarta, yayinda a zahiri yake jinjina irin gatan da take da shi. Saboda yadda aka haɗa ta da bodyguards kamar masu tsare mata mutuwa idan ya zo.
Ganin motarsu ta ɓace ya sa shi sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, tare da sa hannu a aljihunsa yana ƙoƙarin cire wayarsa da kullum ke cikin aljihun.
Sai dai bai yi laluben da ya fi biyu ba ya tsaya jin aljihun wayam, ba komai a ciki.
Hakan ya sa shi tuna cewa wayar tana cikin motarta. A hankali ya ɗan cije lips ɗinsa yana dafe goshinsa tare da furzar da iska daga bakinsa. kirane mai muhimmanci da yake buƙatar yi da wayar tun lokacin da yake office. Rashin samun dama ya sa shi hakura da nufin sai ya fito, gashi ya fito ma babu dama.
Sake lumshe idanunsa ya yi yana jin takaici na cika zuciyarsa. Tunani ya shiga yi inda zai samu wayar da zai kiran. Saboda dole ne sai ya yi wannan kiran a yau.