Hs 9
by @legendspen
Page 09
"Wanan yarinyar da kika ce ƙanwarki ce mene alaƙarku da ita?."
Kallon Momi tayi da mamaki sosai sanan tace "Bhatool!?." Ɗaga kai Momi tayi alamar "Eyh" Zama Yaya Karima ta gyara sanan tace
"Ƙanwata ce, itace ke bina amma kuma sakamakon amanarta da mahaifin mu yabamu kafin rasuwar shi,yasa muka mayar da ita kamar itace last born ɗin, shi Abdul ne ƙarami amma kasnacewar shi namiji ne kuma duk kasuwnaci Abban mu a wajen shi yake yasa muka bashi girman, ni kaina ganin shi nake kamar shine sama dani sai ita muka bata kankantar."
"Kunyi mata miji ne?." Momi ta tambaya, Girgiza kai Yaya Karima tayi sanan tace "Banjin ta fara kula samari yanzu fa tana 18 duk da nima bankai 20 nayi aure ba."
A jiyar Zuciya Momi ta sauke sananface "I can't hide anything for you, impact ma abun ya shafe ki, Senate ne yafa ɗa soyayya da ita tun wata rana da yaje school ɗinsu, kuma soyayyar da ya faɗa wata kalal soyayya ce ni tsoro ma take ban, yanzu haka tun dazu yakasa tashi kawai murmushi yake yana kiran sunanta, gashi kuma da tsoron mata kamar masifa bana jin zai iya tunkararta ma"
Itama ajiyar zuciya yaya Karima ta sake sanan tace "Momi Bhatool wata iriyar yarnya ce mai muguwar rigima, ta kwanta a kasa taita burgima bawani abu bane a wajenta, haka zatazo nan tai tamun ihu, last time ma da tazo kukan tayi mun kuma ga Sebate very silent anya tafiyarsu xatayi dai-dai kuwa?."
"Daughter shi yaji yagani yace yanaso, to zai iya yanzu wata alfarma nake nema wajenki."
"wace alfarma ce momi?." Dafa kafaɗar Yaya Karima Momi tayi sanan tace "Kinsan ba'a taɓayin aure sai duka ɓangare biyu sunso juna, inaso ki taimaka ki zamo tsani wanda Senate zai taka ya samu soyayyar Ummi dukda nasan abu ne mai wahala."
"Momi me kenan zanyi?." Yaya Karima ta tambaya "Daughter ki kawo Bhatool gidanki ta zama kusa da Senate." Shiru yayi Karima tayi Rigimar Bhatool ba'abunda zata iya ɗauka bane, amma kuma tabbas a karamci irin na Momi ta cancanci Karima tayi mata sama da haka, sanan Mama da Abdul zasu ɗan samu bakim su ya huta na kwana biyu, kuma tabbas Bhatool za tayi dacen sirika.
"Daughter!." Momi ta faɗa ganin tayi nisa cikim tunani "Ki yarda dani ba zan taɓa cutar da ƙanwarki ba, ko wani ma sanan bawai ina nuna son nawa ɗan bane, nasan matsalal shi sanan ko ke a ɗan shiga gidana da kikayi kinsan yana da matsala tsoron mata kuma indai har baiyi nasarar saka soyayyar a zuciyarta ba, dole ya haƙura."
"Shikenan Momi insha Allah zanyi." Murmushi Momi tayi sanan tace " Tabba gidan ku yasamu kyakyawar shaida, mahaifiyarku tayi ƙoƙari akanku bayan rasuwar mahaifin ku, a ɗan karamin binciken da nasa akayi mun, Allah yajikanshi da rahama."
"Ameen yah Allah." Yaya karima ta faɗa, ba tayi mamakin binciken da Momi tasa akayi mata ba domin dama ya dace duk wanda zai nemi aure yayi.
~~~~~ YSU
Tun wajen 10 Bhatool ke baza ido a cikin garden ko za ta hango Senate, amma babu shi babu alamun shi gaba ɗaya hirar da suke hankalin ta baya kai, Jannah ce tace "Yanzu ke Amarya ina zaki Make-up?."
"Teemarhs glow zanje, ina ga ma ta 150k za'ayi mun." Dariya sukayi sanan Amrah tace "Sai dake Suhaima Amarya, Bhatool ke fa." Sai a lolacin hankalin ta ya dawo kansu, Murmushi tayi sanan tace "Me?." kallon ta su kayi baki ɗaya "Do you mean you're not with us?." Girgiza kai tayi sanan tace "Ban dai ji mai kuka ce last ba."."Muna magana ne akan wajen kwalliya." . "Uhm ina zamu." Bhatool ta tambaya alamun dai ba taji mai suka ce ɗazu ba. Jannah ce tace "Ita dai amarya wajen Teemahs glow zata, ayi mata ta 150k." Kallon Suhaima Bhatool tayi sanan tace "Sai dake capaciteted ko ina zaku." ta ma yarda hankalin ta gasu Jannah da Amrah "Ni wallahi sister na ta iya kwalliya wajenta zani." Amrah ta faɗa alamun dai tayi broke. "Uhm nima da kaina zanzi zara abata jiya haka kawai naje nasa yaron nan yayi asarar kuɗi sanan kuma ya biya mun kuɗin ɗinki, ko bani da imani bazan ƙara amsar kwabo ba a wajen sa." Dukkanin su sunsan idan tace yaro to Abdul take nufi, haka sukayi ta hira kowa yana faɗin abinda yake bakinsa, kamar ko yaushe dai sai shida suka bar makaranta kowacce ta nufi gidan su.
A cikin gidan ta tarar da Yaya Karima, wani tsalle tayi taje ta rungume ta tana faɗin "Yaya Karimancy.". Neman faɗuwa su ka fara daga ita har Yaya Kariman da ƙyar Yaya Karima ta dafa bango tana faɗin "Ke wai mai yasa baki da kwakwalwa ne?." Cuno baki tayi gaba tana faɗin "Ke kuma mai yasa ba'a yi miki abun arziki ne?." Kallonta Yaya karima tayi sanan tace "Bhatool indai wanan ne abun arziƙi to riƙe abunki bana buƙata." Kallonta ta mayar ga Mama sanan tace "Mama nadawo.".
"Naganki." Mama ta faɗa tana mayar da kallonta ga Karima, sai bayan Bhatool ta shiga Mama tace "Anya Karima yarinyar nan tabiki kuwa, ke da kike da ƙaramin ciki." Ajiyar zuciya Karima ta sauke sanan tace "To Mama ya za'ayi su likitocin ne suka ce ina buƙatar mai ta yani aiki, kuma idan ba ita ba wa nake da ita, haka dai zanyi hakuri da ita."
"Shikenan bari nayi mata magana." Mama ta faɗa tana shiga ɗakin da Bhatool ke ciki,Zaune ta sameta tana danna waya. Zama Mama tayi kusa da ita tare da kiran sunanta "Bhatool!." Ɗagowa tayi ta kalleta "Na'am Mama.".
"Inaso ki buɗe kunanki kijini, Yayarki Karima bata da Lafiya a asibiti ance ta naimi mai ta yata aiki hakan yasa zaki bita gidanta na kwana biyu kafin ta samu ƙwarin jiki." Kallon Mama tayi sanan tace "Gidan Yaya Karima zanje na kwana biyu?." tayi maganar kamar mai tambaya. "Eyh can zaki." Mama ta bata amsa, shiru tayi sai can tace "To yaushe zandawo."
"Bayan ta samu sauƙi." Shiru Bhatool tayi tana son tace bazata ba, sai kuma ta tuna dole zata ga Senate Mutumin da kyansa da sautin muryarsa ya tsaya mata arai. "Shikenan bari na haɗa kayana." ta faɗa tare da tashi.
Cikin ƙanƙani lokaci ta haɗa kayanta da kuma jakar makarantar ta, fitowa tayi tsakar gidan ta tarar da Mama da Yaya karima, Mamace ta kalleta sanan tace "Bhatool kinga bata da lafiya ki nutsu dan Allah." Cikin sanyi murya tace "Insha Allah Mama, ki gaishe mun da Abdul ɗina." Daman haka Bhatool take tana da rigima amma tabbas bata son nisa da Mama ko Abdul, Kasancewar Yaya Karima na da mota kuma a ita tazo ba mijinta bane zaizo ya ɗauke ta kuma ga Yamma yara sun kusa dawowa daga school, daman tun safw tazo sunje duba Goggo Larai ita da Mama.
Ko a mota ma Bhatool ba tace uffan ba, har suka ƙarasa Gida tayi nisa a cikin tunani taji Yaya karima tace "Dan Allah je gidan Momi kice mata nadawo ta aiko da saqon." Tabbas Bhatool taji dadi sosai domin tunanin da takeyi kenan tinda suka tawo har tazo, "Tom Yaya." ta faɗa tare da nufar hanyar gidan.
~~~~~Yana zaune cikin gidan Yau bai samu ko yaje makarantarsu Bhatool ba sabida gaba ɗaya ita yake gani da ya rufe idonshi, bama yaso yayi tafiyar da zaiyi nisa har yakasa rufen idon, kuma abunda ke sa mai jindadi shine idan ya ganta murmushi take masa, kuma Salman ne da juraij sunzo a gidan suka yini, sun tattauna kan bikin ƙannen Salman da kuma company da zasu buɗe, Rabin kuɗin da za'a bude company ɗin Abban Senate ne ya bashi sanan shima ya haɗa da nashi, shi ke da kaso 75 cikin ɗari na campanin sai Kuma juraij da yasa kaso 25 wanda yasawa Salman ne domin Juraij Dad ɗinshi ya bashi company shi dake Cyprus shiya ba cika zama nigeria ba.
Sunyi ja'inja sosai wajen saka sunan kamfanin inda Senate yadage sai dai asa Bhatool, Shi Salman bai cika hayaniya ba Juraij ne dai yayi ta ja dashi,shima kuma wasa yake mai sabida yana so yaga Senate na doguwar hira kuma a rayuwar Senate dasu kaɗai yake iya hirar sakamakon sanin halinsa da Juraij yayi hakan yasa yake janshi da doguwar hirar, ƙarshe dai suka amince a haka.
Bayan tafiyarsu ne yadawo falo, su na zaune tare da Mom suna hira sama-sama,sai kuma Anas da bai daɗe da daowa ba, Anas ɗin ne ke tsokanar Senate yana cewa"Ango mijin Amarya." Wani kallo senate ya watsa mai ba tare da yace komai ba. "Angon Batula." kallonshi ya ƙarayi sanan yace "Stop." cikin sasanyar muryarshi. "Na batula." Anas ya sake faɗa yana dariya, kallon Mom senate yayi wacce take zaune kamad ba ta jinsu. "Mom! kiyi masa magana." Harara ta makawa Senate ɗin sanan tace "Komai ni zan maka ko?." Hannu yasa ya fara sosa ƙeya shi kuma Anas ya ƙara cewa "Senate Bhatool.".
"Mene yasa ba zaka kira ta da Anty ba."Daga Mom har Anas juyowa sukayi suka kalleshi, jin yanayin da yayi magana kamar bashi ba,Murya cike da ƙarfi da ƙwarin gwiwa da kuma kwar jini,son ƙara tabbatarwa ne yasa Anas ƙara cewa "Bhatool senate.".
"Anas ba kai naiwa magana ba?." Tabbas shi yayi maganar wallahi,Mom ce tace "Senate, daman ka iya magana haka?." cikin fushi yace "Mom mai yasa bazai kirata Anty ba,ai na girmeshi dan haka mata ta ta girmeshi." kallon ikon Allah Mom ta tsaya yi, kenan idan yana cikin ɓacin rai shine yake magana haka lallai ne. "I'm sorry." Anas ya faɗa"Sorry for your self." Senate ya faɗa tare da tashi.
Rufe idonshi yayi da ƙarfi tare da riƙe ƙirjinshi..
Ku yi following da comment dan Allah
Legend's pen ***.