HASASHEN SOYAYYA

Hs 10

by @legendspen

Page 10


Rufe idonshi yayi da ƙarfi tare da riƙe ƙirjinsa, dai-dai lokacin da tayi sallama ta shigo falon, da sauri ya bud'e manyan idanunsa yana sauke su akanta.

Momi ta mike tsaye tana murmushi ta amsa sallaman tare da cewa. " Daughter k'araso mana."

Murmushi tayi tana shigowa cikin falon, har yanzu idanunsa na kanta ya gagara daukewa.

Har k'asa ta durkusa tana fadin. " Momi ina kwana?."

" Lafiya Daughter ya gida? Kin zo lafiya? Tashi ki zauna a sama." Momi ta fad'a tana murmushi.

Da lafiya ta amsa tana zama a kan kujeran kafin ta kalli Anas ta furta. " Ina kwana?."

Washe mata baki yayi yana cewa. " Lafiya kalau Bhatool ya Makaranta? Yasu Mama da kowa da kowa an same ku lafiya? Ya..." 

Hararan da Senate ya masa ne yasa yayi dif bai ce komai ba sai dariyar da yake yi ƙasa-ƙasa, kallon Senate din tayi ta ce. " Yaya ina kwana?."

Sanyayyen murmushin nan nasa ya yi ya ce. " Lafiya." Yana komawa ya zauna yana facing nata.

Momi ce ta nufi fridge ta dauko mata ruwa da juice ta ajiye a gabanta tana fadin. " Daughter ki sha ruwa ko."

Murmushi tayi bata ce komai ba, Senate sai murmushi yake yi kamar wanda ya zauce, kafin ya ce. " Bhatool ruwan gidanmu ne bazaki sha ba?."

Da sauri ta kalle shi dan batayi tunanin zai sake yin magana ba har taji zazzakar muryansa mai kwantar mata da hankali, wani sanyi taji a zuciyarta kafin ta ce. " A koshe fa nake."

" Haba daughter dan ban dibo miki abinci bama ko?." Cewan Momi tana bata fuska.

" Momi Wallahi na koshi yanzu nasha ruwa, dama Yaya Karima ce tace nazo za ki ban sako." Ta karashe suna hada ido da Senate.

" Ok to ina zuwa bari na dauko miki." Cewan Momi ta nufi dakinta.

Tashi Senate yayi ya dawo gujeran da take kai yana fadin. " Za ki dade a nan ko?."

" Eh nazo taya Yaya karima zama ne bata da lafiya." 

Hannunsa ya saka a cikin sumarsa yana shafawa kafin ya kalli Anas ta gefen ido yana sakar masa murmushi, girgiza kai kawai Anas yayi bai ce komai ba.

Momi ce ta dawo hannunta dauke da bakin leda, mikawa Bhatool tayi tare da fadin. " Gashi nan Daughter."

Karba tayi tana mai tashi tare da cewa. " Momi sai anjima."

" To Daughter ki gaishe da Karima."

Da sauri Senate ya mike yana mara mata baya da fadin. " Momi bari na taka mata zuwa gidan." Ya fita da sauri dan ya isa gurinta.

Momi ta dubi Anas tana fadin. " Naga Senate ya canja ne lokaci kadan, daga yanayin maganar zaka gane yana magana tamkar zaki, ina nufin muryansa da kausashi." Momi ta karashe da dan mamaki, dan Senate idan zai yi magana duk a cikin sanyi yake sai dai daga dazu ya canja ya zama cikekken na miji, amon muryansa ma ya isa ya sa jikin mutum ya dau rawa.

Anas ya ce. " Momi kila dan ya fara soyayya ne ya chanzu."

" Maybe." Kafin ta nufi kitchen.

Bayan ya iso inda take suka jera suna tafiya, fuskarta dauke da murmushi haka ma nasa, kamar ba zaiyi magana ba kuma sai ya ce. " Bhatool." Ya kira sunan a wani irin voice.

Ji tayi babu wanda ya kai shi iya kiran sunan ta, a wani irin yanayi ta kalle shi ta furta. " Na'am Senate."

Tsayawa cak suka yi babu wanda ya motsa, kafin ya ce. " Kina da wanda kike so ne?."

Girgiza kai tayi, wani naunauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya saki murmushi ya ce. " Muje ko." Suka cigaba da tafiya babu wanda ya cewa wani kala.

A bakin get ya tsaya ta shiga, ganin ya tsaya yasa ta ce. " Ka shigo ku gaisa da Yaya mana."

Girgiza mata kai yayi ya ce. " A'a yanzu kunyar ta nakeji, akwai lokacin da zan shigo har mu gaisa muyi hira da ita."

" Ok nagode ka gaishe min da Momi." Ta fada tana masa bye bye ta shiga falon.

Har sai da ta bace kafin ya sauke numfashi yana furzar da iska ya ce. " Yau na mata magana, yesss God kasa kar tayi wani saurayi har ta gane inason ta." Ya fada yana tsalle da murmushi kafin ya koma gida.

Tana shiga falon ta fara ihu wanda ya tsorata Yaya Karima ta fito da gudu daga kitchen.

" Wallahi sona yake, yess na kamu da soyayyar Kyakkyawan saurayi fari ajin farko irin na fita cikin kawaye da shi, na kece raini." 

Cike da haushi Yaya Karima ta ce. " Shi ne zaki shigo da ihu?."

" What the fuck, Yaya Karima ki barni kawai." Ta fada tana fadawa akan three seater ta lumshe ido.

Filo Yaya Karima ta dauka tana buga mata, da sauri ta tashi tana dariya ta nufi dakin da ta sauka ta ce. " Sai hakuri idan zaki iya, kisan wanda ya fada soyayya baya jin shawara."

Yana komawa gida ya shigo falon da gudu yazo ya rungume Momi.

" Babana Lafiya? What's wrong?."

" Momi babu wanda ya kai ki sona a duniya, ina kaunar ki Momi." 

Dariya Anas yayi yana ciro waya ya fara musu video yana fadin. " Cigaba mana da maganar, irin yau kaga bugun zuciyarka, ai har yaran ku sai sun ga video nan In Sha Allah."

Turo baki gaba Senate yayi yana hade fuska ya nuna Anas yana kallon Momi ya ce. " Momi ki ce ya daina bana so."

" Anas ka daina baya so." Cewan Momi tana dariya.

" Ke ma dariya kike min Momi?."

" A'a kuka nake."

Juyawa yayi ya tafi dakinsa yana guna-guni kamar yaro karami.



*Bhatool*


Tun bayan da ta shiga dakinta bacci ya dauke ta, sai kusan mangarib ta fito tana bata fuska.

Yaya Karima ce da Barrister a falon yaran sun tafi wasa, kallon ta Barrister yayi yana cewa. " Yar dakina nazo kina bacci."

Sakin fuska ta yi tana cewa. " Uncle ina wuni?."

" Lafiya ya gajiya."

" Alhamdulillah." 

Tashi yayi yana cewa. " Ni kam na wuce masallaci kar na makara."

" A dawo lafiya." Yaya Karima ta fada tana masa murmushi, da haka ya fice.

Duban Yaya Karima tayi tana yamutse fuska ta ce. " Yaya abinci."

" Ni zan kawo miki kenan?."

" Ni bance haka ba, naga bakon ka Annabin ka."

Da mamaki Yaya Karima ta ce. " Ke ce bakuwar kenan?."

" Eh mana."

Jinjina kai tayi tana danna wayanta, zama Bhatool tayi a kasan tana fadin. " Nikam gurin Abbana zan tafi, duk babu wanda yake so na sai shi, abinci ma ana ma mutum yanga, abun duniya da za'a mutu a barshi ana hana ni." Ta fashe da kuka.

Jikin Yaya Karima ce yayi sanyi ta tashi tazo gurin ta tana durkusawa ta jawo ta jikinta, tana bubbuga bayanta ta ce. " Bhatool kiyi hakuri mana, ba fa hanaki abincin nayi ba, amma ai kema ba bakuwa bace."

" Babu wani nan, kawai bakya sona ne, amanan da Abba ya baku kukeson ku ci." Ta kuka take maganar.

" Wallahi Bhatool ba haka bane, bari na dibo miki abincin kiyi hakuri." Ta mike ta nufi kitchen din.

Bata dade ba ta dawo hannunta rike da tray da abinci a ciki.

Mikewa Bhatool tayi tana karba ta nufi daining table, zama tayi ta fara cin tuwo miyan egusin tana mita wai yaji yayi yawa, Yaya Karima bata kula ta ba ta nufi dakinta tana cewan Momi ta kawo mata masifa.

Tana gama ci ta tashi ta dauki ruwa a fridge ta koma dakinta, salla tayi kafin ta dauki waya ta fara charting da friend's nata kuma duk hiran akan auren da suke dashi ne, tana zaune aka kira Isha ta tashi tayi, sai kusan goma kafin tayi bacci.


*Yaya Karima*


Kallon mijin nata tayi tana cewa. " Barrister sai ina ganin kamar Senate zai sha wahala a hannun yarinyar nan, dan ko mu da muke yayunta muna shan wahala bare kuma mijinta da zasuyi zama na har abada."

" Karima bana jin zaman Bhatool dashi akwai matsala, Bhatool tana da hakuri sannan kuma tana da tsoro, kuma miji ai ba wasa ba, ni a ganina a musu fatan alkhairi idan har auren nasu alkhairi ne."

" Hmmm! Barrister Bhatool fa...." Dakatar da ita yayi yana cewa. " Karima kar baki yayi yawa a ciki, Allah ya tabbatar."

Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa. " Amen." Kasan zuciyarta kuma yana raya mata cewa akwai matsala.


✍�Legends pen ***.

Comment and vote for more please