Chapter 30
Layla na zaune a ɗakinta ita kaɗai tana ta saƙe saƙe wayarta ta fara ringing.
Sunan Hafsat da ta gani yasa ta ɗauki kiran da sauri.
Bayan ta ɗaga Hafsat ta ce " ki fito ina ƙofar gidanki, zamu koma wurin malamin nan."
Da sauri ta miƙe bayan ta ji abinda Hafsat ta faɗa mata.
Mayafin da ke nannaɗe a kanta ta warware ta yi rolling ɗinshi ta ɗauki wayarta da jaka ta buɗe bedside drawer ta ɗebo kuɗi ta zuba a ciki ta fito.
A bakin gate ta tarar da Hafsat tana jiran ta.
Front seat ta buɗe ta zauna ta ce " amma gaskiya kin shammaceni, yaushe kika dawo ƙasar ne ?"
Kallonta ta yi dai dai lokacin da take reverse ta ce " Layla to ko mu koma gida ne sai na baki amsar duk tambayoyinki?"
Dariya Layla ta yi ta ce " kin fiye masifa wallahi it's just a harmless question."
Bata ƙara ce mata komai ba ta ja motar suka bar wurin.
Kafin Jiddarh ta dawo daga kiran doctor har ya buɗe idanunshi.
Mamy ta matsa kusa da shi ta ce " Sannu ALIYU."
Kallonta kawai yake yi saboda ba zai iya cewa komai ba.
Buɗe ƙofar aka yi Jiddarh da doctor suka shigo.
Gefen gadon da HAYDAR yake kai likitan ya tsaya yana duba jikin shi.
" Doctor what exactly is wrong with him?" Mamy ta tambaya.
Bayan ta gama duba shi ya juyo yana facing mamy ya ce " har yanzu bamu san abinda yake damunshi ba tukunna."
" Sai results ɗin test ɗin da muka yi mashi ya fito sannan zamu san meke damunshi."
Jinjina kai mamy ta yi ba tare da ta ƙara cewa komai ba.
Bayan ya gama duba jikin HAYDAR ya kalli mamy ya ce " madam zan turo nurse ta kira ki idan results ɗin sun fito sai na yi maki bayanin abinda ke damunshi."
Nan ma jinjina masa kai ta ƙara yi ba tare da ta yi magana ba.
Zannur ne ya dawo ɗakin ya tarar sun yi jugum jugum kamar a gidan makoki.
Fuskokinsu gaba ɗaya babu annuri, gabanshi ya ji ya faɗi da sauri ya kalli inda HAYDAR yake a kwance, sai a lokacin ya sauke ajiyar zuciyar da bai san ma yana riƙe da ita ba.
Mamy da taga shigowar shi ta ce Usman ka dawo."
Jinjina mata kai ya yi ya ce " na dawo mamy ya jikin shi?"
" Da sauƙi, yanzu likita ya fita ya ce idan results ya fito zai faɗa mana meke damunshi."
" Tohm shikenan let's wait for the results."
Inda HAYDAR yake ya ƙarasa, ya kama hannunshi ya ce " buddy sannu."
Shima kallon shi ya yi bai ce masa komai ba.
Sa'adarh na zaune a ɗakinta tana karatu mamnsu ta kira ta.
System ɗin da take karatu da ita ta tura gefe ta sakko, house slippers ɗin dake gefen gadonta ta saka sannan ta fito ta shiga ɗakin hajiyarsu.
Gefen gado ta zauna ta ce " hajiyarmu ga ni."
Hannunta ta riƙe ta ce " Sa'adatu."
Attention ɗinta ta bata baki ɗaya saboda tunda ta ji ta kira ta da asalin sunanta ta san magana ce me muhimmanci ta ce " na'am."
" Auntyn ku ce ta turo man ankon bikin Sadeeq ta ce akwai na ʼyammata shima, ta ce man su Nafeesarh sun kasa turo maki shiyasa ni ta turo man."
Kamar sukar mashi haka ta ji maganar a cikin zuciyarta amma haka ta maze ta ce " haba su kam menene na kasa turo man, ai nasan ƙaddara kuma dama can ai ni Allah ya ɗorawa son yaya Sadeeq, shi bai taɓa cewa yana sona ba bare a ce ya yaudare ni." Ta faɗa da murmushi a kan fuskarta amma zuciyarta kuna take yi.
Duk da ta yi ƙoƙarin ɓoye hakan amma bai ɓoye akan fuskarta ba, kuma duk yanda muka kai ga nuna komai ba komai bane iyayenmu dole suna fahimar abinda muke ciki ko da kuwa bamu faɗa ba.
Muryarta na breaking ta ce " hajiyarmu bari na koma ɗaki karatu nake yi."
Tausayi ta bata sai ta ce " shikenan auta maza ki je kiyi karatu, Allah ya bada sa'a."
Jinjina mata kai kawai ta yi saboda a lokacin idan ta buɗe bakinta da niyyar magana to tabbas kuka ne zai fito."
Takalminta ta saka ta fita daga ɗakin ba tare da ta ƙara cewa komai ba.
Tana shiga ɗakinta ta kwanta akan gadon tana tana tunanin shidanunta na zubar da hawaye masu zafi.
Ƙoƙarin goge hawayen take yi amma yaƙi ya tsaya.
" Calm down Sa'adatu, ki dena damuwa, dama Allah ya tsara shi ɗin ba mijinki bane." Ita kaɗai take ta bama kanta ƙwarin gwiwa.
Hawayen sun daina fitowa daga idanunta amma kuma zuciyarta zafi take yi.
Don ta yi distracting kanta daga yin tunani ta janyo system ɗinta zata cigaba da karatu.
Da ta fara sai ta manta abinda take karantawa hakan ya sa kawai ta fita daga cikin pdf ɗin baki ɗaya ta fara game.
Abbah na zaune a parlourn shi yana duba wasu takaddu Sadeeq ya yi sallama bayan ya amsa ya shiga ciki ya zauna.
Bayan ya gaida shi ya ce " Abbah dama na zo ne muyi magana."
Takaddun dake hannunshi ya aje ya fuskance shi ya ce " ina jinka babana."
Gyara zama Sadeeq ya yi ya mashi bayanin abinda yake son yi da kuma shirye shiryen biki da yake neman shawara.
Gyaran murya Abbah ya yi ya ce " toh shikenan babana Allah ya nuna mana lokacin, kai ma ka yi ƙaƙori sannu ka ji."
Murmushi kawai Sadeeq ya yi ya ce " nagode Abbah."
13 days later
" Wai Jay ba zaki fito ba? Mutane duk sun zo ke kaɗai ake jira, ga malama can ma ta zo." Munarh ce ke ta masifa.
Zata kama handle ɗin ƙofar Jay ta riga ta daga ciki, harara ta ɓallama mata ta ce " sai kace a kanki aka fara aure kin wani je kin yi zaman ki a ɗaki kin bar mutane suna ta jira.
" Ko kallon inda take bata yi ba ta ce " ke wallahi kin fiye ta kura,amma dai kin san idan babu abinda nake yi ba zan zauna a ɗaki na bar mutane na jira na ba."
Tsaki Munarh ta yi ta ce " kya ji dashi ni mu tafi kin sa mutane sai tambaya ta suke ina amarya ni har na gaji da basu amsa."
Ba wanda ya ƙara kallon ɗan uwansa har suka fito compound ɗin gidan su Jay inda aka yiwa farfajiyar gidan decoration aka saka kujeru a wurin wanda mutane zasu zauna sai kuma wurin zaman amarya da yake daga can gefe shima an ƙawata shi da tuntu daga gefe da gefe.
Sai kuma mazaunin malamar da zata ɗan tunatar da amarya da kuma mutanen dake wurin wato malama Zainab Ja'afar.
Kafin amarya ta zauna a mazauninta sai da ta fara tsayawa ta gaishe da malama Zainab sannan ta ƙarasa wurin zamanta ta zauna.
Malama ta yiwa amarya nasiha me ratsa jiki da jijiya ta kuma nusar da ita akan muhimmancin haƙuri a zaman aure.
Bayan malama ta gama bayanin da zata yi caterers ɗin da ke ta rabon abinci suka fara rabon soveineirs ɗin da aka tanada saboda wanda suka halacci walimah.
Ummi da zuwanta kenan da safe bayan an gama walimah suka raka malama Zainab har bakin mota da ledojin soveiniers ɗin da aka raba suna ƙara yi mata godiya.
Da daddare Jay na zaune a ɗaki ita kaɗai tana ta tunanin daga gobe shikenan ta zama matar Sadeeq.
Tana cikin wannan tunanin Munarh ta buɗe ƙofa ta shigo, Munarh da taga Jay bata ma son da zuwanta ba sai ta fara tunanin me zata yi da zai ɗebe mata kewa saboda saboda ta lura a ʼyan kwanakin nan tana yawan yin tunani.
Hango tulin gifts ɗin dake ajiye a gefen drawer ɗin Jay ya sa Munarh ta ƙarasa kan gadon ta zauna a gefen Jay ta ce " amarya ba kya laifi." Ta faɗa tana dariya.
Jay da ta rasa me yake mata daɗi ta miƙe zaune ta ce " Munarh wai haka kowa yake ji idan zai yi aure?"
" Sosai ta bawa Munarh tausayi, sai ta ce " ke dalla haka kowa yake ji ni wancan tarin gifts ɗin da ke aje nake son ki zo mu buɗe tun kafin gobe ya yi a kai ki gidanki kiyi man baƙin cikin ganin menene a ciki."
Mutmushi Jay ta yi saboda ta fahimci duk wani abu da Munarh take yi tana yi ne saboda ta saka ta farin ciki ta kuma manta da damuwarta.
" Ki ɗakko su mu duba, tun lokacin da na buɗe eatry ɗina ne aka bani su ban samu lokacin da zan buɗe su ba." Jay ta faɗa saboda ita ma tana buƙatar wani abu da zai ɗauke mata kewa
Ɗaya bayan ɗaya suka fara buɗewa suna ganin abinda ke ciki, cikin lokaci ƙanƙani ta manta da damuwar da take ciki.
Haka suka yi ta buɗe gift har suka ƙaraso kan wani gift card me kyau.
Munarh na ganin shi ta ce wow this is so beautiful let's me see what's inside.
Haka kawai Jay ta ji gabanta yana faɗuwa da Munarh ta fara warware ribbon ɗin da ke jikin gift card ɗin.
A hankali ta fara karanta content ɗin card ɗin kamar haka.
" Congratulations on opening your dream eatery hazely."
" It's amazing to see something that once existed only as conversations, late-night plans, and quiet dreams finally become real. You worked so hard for this, and you deserve every bit of success that comes your way."
" I won't pretend today doesn't make me emotional. There was a time when I imagined celebrating this milestone beside you, teasing you about finally making it happen, and being your first customer. Life had other plans, I guess."
" Still, seeing you win genuinely makes me happy. Some dreams are too beautiful not to be celebrated, even from a distance."
" May your tables always be full, your kitchen never run out of blessings, and may this place become everything you prayed it would be."
" Congratulations once again. I'll always be proud of the woman who turned a dream into reality, even if my applause now comes from afar."
" Wishing you nothing but success, peace, and happiness. You truly earned this."
" Allah ya albarkace ki, ya kuma albarkaci duk wani abu da kika saka a gaba."
Tun kafin Munarh ta gama karantawa fuskarta ya jiƙe da hawaye, wani na korar wani ta kuma kasa hana su zuba.
Sai da Munarh ta ji tsoro ganin irin kukan da Jay take yi ga jijiyoyin kanta sun fito sunyi ruɗu ruɗu ana ganin su.
Ta sani kaf duniya mutum ɗaya ne zai aiko mata da irin wannan saƙon.
A baya tana ƙaryata kanta a duk lokacin da zuciyarta ta ce mata shine idan an kawo mata gifts ɗin da bata san daga ina ba.
Amma a wannan karon ta kasa ƙaryata zuciyarta.
Zuciyarta ce ta fara faɗa mata " Jaiyana kin yi gaggawa, me yasa baki ƙara mashi lokaci ba?"
" Meyasa kika yanke hukunci irin haka?"
" Kin yi wa zuciyoyinku adalci kenan?"
" Meyasa kika ƙi sauraren shi duk da kin san cewa ba haramun bane?"
Irin tambayoyin da ta rinƙa yiwa kanta kenan.
Ƙoƙarin yin magana Munarh take yi Jay ta kalleta da idanunta da suka gama rinewa suka koma kalar ja ta ce " i need to be alone Munarh."
Za tayi wata magana Jay ta daka mata tsawa ta ce " get out i said Munarh."
Tsabar rikicewa bata son ta kai ƙofar ɗakin ba sai da ta ji Jay ta rufe ƙofar da makulli sannan ta fahimci ashe ma fitowa ta yi daga ɗakin.
Bayan ta rufe ƙofar ta fashe da wani marayan kuka me taɓa zuciyar me sauraro.
Daga waje Munarh ta rinƙa knocking amma shiru taƙi ta buɗe haka ta haƙura ta wuce ta kama wasu abubuwan da ake ta yi na ɗaurin aure gobe.
Sai bayan sallar azahar sannan Hafsat ta yi parking a wani ɗan ƙaramin ƙauye dake cikin garin Zaria.
Fitowa suka yi daga cikin motar suka fara tafiya da ƙafafunsu saboda babu hanyar da mota zata bi.
Sai da suka yi tafiya mai nisa sosai sannan suka tsaya a gefen wata bishiya, iska ce ta fara kaɗawa a wurin har ta koma guguwa, can kuma sai ga wata bukka tana fitowa daga can ƙarƙashin ƙasa har ta gama fitowa.
Hannun Layla Hafsat ta riƙe suka shiga cikin bukkar, wani mutum ne baƙi mummuna me kama da gwaggon biri zaune ga wuta tana ci daga gefen shi ga kuma ƙasa a faranti.
Babu kayan a jikinshi sai wasu ganye da ya yi amfani da su wurin rufe jikinshi.
Bayan sun zauna Hafsat ta ɗan zunguri Layla da nufin ta yi magana.
Kafin Layla ta yi magana muryarshi da babu daɗin sauraro ta daki dodun kunnensu " me ke tafe da ku?"
Magana Layla ta fara kamar haka " mallam dama mijina ne nemi aure a baya amma na hana shi to kwatsam sai na ga ya fara canjawa daga yadda yake yi man shine nake tunanin ya ƙara komawa yana neman aure ne."
Hannunshi ya buga akan ƙasa sai ga hoton Sooraj ya fito yana tafiya akan titi hannunshi ɗaya akan steering wheel ɗayan kuma yana riƙe da wayarshi a kunne alamun waya yake amsawa.
" Wannan shine mijin naki?"
Da sauri Layla ta jinjina kai tana faɗin " eh shine ."
Dariya ya kece da ita ya ce " tabbas mijinki yana gab da ƙara aure kuma da a ce kin ƙara ko da minti ɗaya ne baki zo wurin nan ba, to da tabbas sai ya ƙara wannan aure."
Ƙirji ta dafe ta ce " na shiga uku."
Kallonta bokan ya yi ya ce " me kike so ayi mashi?" Ya tambaya.
" Muryarta har tana rawa ta ce " so nake kar ya ƙara kallon wata ʼya mace a matsayin mace ni kaɗai zai rinƙa gani a matsayin mace sauran duk ya rinƙa ganin su a matsayin ʼyan uwanshi maza."
Hannunshi ya miƙa sama sai ga wani kwalli ya fito daga ciki, miƙa mata ya yi ya ce " ki tabbata kin lokacin da kika saka wannan kwalli shine mutum na farko da ya ganki."
" Idan kuma ba haka ba to tabbas zaki haukace."
Karɓar kwallin ta yi ta ce " shikenan."
Kuɗin dake cikin jakarta da ita kanta bata ma san adadinsu ba ta dire mashi sannan ta yi mashi godiya suka taso suka fito.
Tafiya suka yi har suka zo bakin inda motarsu ta ke suka shiga.
Tuƙi Hafsat ta fara sai ga kiran Meenah yana shigowa cikin wayar Layla, har ta ce ba zata ɗaga ba Hafsat ta ce " ki ɗaga muji me zata ce."
Ɗaga wayar ta yi ta saka ta a handsfree sallama Meenah ta yi Layla ta amsa mata, Meenah da ke jiyo iska ta cikin wayar ta ce " ina aka je haka sarkin yawo?"
Layla da take son jin dalilin kiran da Meenah ta yi mata ta ce " naje wani ƙauye ne a Zaria."
Tana faɗin haka Meenah ta gane inda taje saboda ta san daga ita har mijinta basu da ʼyan uwa a Zaria.
Girgiza kai ta yi ta ce " Allah ya shirye ki Layla daga ke har wadda take ɗora ki a hanyar banzar duka Allah ya shirye ku."
" Kira nayi na ƙara yi maki nasiha, and ina son ki sani a wannan karon idan har baki ɗauka ba zan je har gida na samu Ammi na zayyana mata komai saboda ni nayi iya abinda zan iya amma na kasa."
Hafsat da take jin kamar ta shaƙo Meenah ta cikin wayar ta ce " dalla Layla kashe wayar."
Meenah ta ji lokacin da Hafsat ta ce a kashe waya sai kuma ƙitt ta ji kiran ya katse.
Wata zuciyar ce ta ce wa Meenah " ki je ki sami Ammi kiyi mata bayani icce tun yana ɗanye ake tanƙwara shi, idan ya bushe kuwa sai dai a ƙarya."
Shawarar zuciyarta ta bi ta yafa mayafi akan ɗinkin atamfar dake jikinta.
Bayan results ya fito doctor ya yi wa mamy da Zannur bayani cewa zuciyar shi ce ta kumbura and zata iya bugawa a kowane lokaci sai an bashi kulawa matuƙa.
Bayan doctor ya fita mamy ta fara faɗa kamar zata ari baki " yanzu ALIYU aka abinda ya riga ya faru bamu da ikon hana faruwarshi kake son ka kashe kanka?"
" Eh duk mun ji ba'a kyauta maka ba amma ita ma Safiyyar ai an ɓata rayuwarta me yasa ba zaka koyawa zuciyarka yafiya ba."
Haka ta yi ta faɗa shi dai bai ce komai ba har ta yi shiru.
Kwanan shi biyar a asibiti a aka sallame shi amma mamy bata yadda an faɗawa kowa rashin lafiyar ba.
Ana gobe ɗaurin auren Sadeeq da Jaiyana mamy ta kira HAYDAR da Zannur parlournta bayan sun zauna ta ce " Usman dama kai nasan bani da matsala da kai kana ƙoƙarin mu'amala da mutane gobe ɗaurin auren ƙanwarku ina fatan baku manta ba?" Ta tambaya.
Jinjina kai Zannur ya yi ya ce " eh mamy bamu manta ba."
" Yawwa to shikenan, ALIYU kai kuma bana son kaje cikin mutane ka rinƙa haɗe rai kamar wanda aka yi wa albishir da mutuwa, ka saki jikinka kayi mu'amala da mutane kar ma wani ya gane kayi ciwo."
Ɗagowa HAYDAR ya yi ya ce " mamy bana son hayaniya da zan bari ne bayan biki sai naje na yi wa mom Allah ya sanya alkhairi."
Kallon irin baka da hankali mamy ta yi mashi ta ce " kaima ai kasan ba abu bane da zai yiwu."
" Da lafiyarka da komai saboda baka son shiga mutane zai hana ka zuwa wurin ɗaurin auren ƙanwarka?"
Rai babu daɗi ya amswa mamy zai je, suka fito ɗakinshi ya wuce Zannur ya ɗakko wata leda daga ɗakinshi sannan ya shiga ɗakin HAYDAR.
Ledar ya aje a gefen gado ya ce " ka duba kayan nan ka gani, jiya na bada aka ɗinka mana su saboda gobe tunda dai bamu zo da shiri ba mun bar kayan a Lagos."
Kallon shi ya yi da idanunshi da suka rine suka koma ja cikin ɗaga murya ya ce " fitar mun daga ɗaki Usman."
Kafaɗarshi ya ɗaga sama ya ce " ba ni zan ɗaura mata auren ba da kake yi man ihu a ka."
Fita ya yi ya bar mashi ɗakin bai ƙara ce mashi ko uffan ba.
Ƙofar parlour ta tsaya, ta kai hannu zata yi knocking sai ta ga ashe ma a buɗe take.
Turawa ta yi ta shiga babu kowa a parlour sai sanyin AC da kuma ƙamshin turaren wuta da yake tashi.
Number Ammi ta yi dailling bayan ta ɗaga ta gaishe da ita sannan ta ce " Ammi ina parlour na zo ne muyi magana, ta cikin wayar Ammi ta ce Amina ke da ba baƙuwa ki shigo mana ina ɗaki na."
Tana kashe wayar ta tashi ta yi hanyar ɗakin Ammi tana zuwa ta yi knocking sannan ta tura ta shiga.
Tsugunnawa ta yi ta ƙara gaida Ammi sannan ta zauna a kan sofa ɗin dake ɗakin.
Ammi da taga bata ce komai ba ta ce " ina jinki Amina wani abu ya faru ne?"
Shiru ta yi ta kasa cewa komai da farko sai da Ammi ta ƙara maimaitawa sannan ta buɗe baki ta bawa Ammi labarin duk abinda ya faru tun daga neman auren Sooraj har zuwa lokacin da ta zo neman shawara da irin shawarar da ta bata da irin wadda Hafsat ta bata.
Har zuwa yau da suka yi waya.
Bayan ta gama ta ce " Ammi na yi iya ƙoƙari na amma na kasa Layla bata saurarena a duk lokacin da zan bata shawara, yanzu haka sun tafi Zaria ita da Hafsat, shiyasa na zo na faɗa maki don a yiwa tufaƙar han...." kafin ta ƙarasa faɗin hanci wayarta dake gefenta ta fara ringing.
Kallon screen ɗin Ammi ta yi ta ga sunan Layla, kallon Meenah ta yi ta ce " ɗaga ki saka ta a speaker naji me zata ce maki."
Ɗaga kiran tayi ta saka ta a speaker, muryar wani saurayi yana sallama.
Amsa sallamar Meenah ta yi ta ce " bawan Allah ina me wayar?"
Daga cikin wayar suka ji ya ce " me wayar ta yi hatsari ne, na ga ke ce mutum na ƙarshe da kuka yi waya shiyasa na kira don na sanar da ke."
Miƙewa ta yi tsaye har tana shirin faɗuwa ta fara maimaita " Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un."
Ammi ce ta karɓi wayar ta ce " bawan Allah kuna ina yanzu?"
" Muna nan a hanyar shiga kaduna daga Zaria."
Jinjina kai kawai Ammi ta yi ta kashe wayar.
Tunda Jay ta rufe ƙofa bata ƙara buɗewa ba har washe gari, Munarh ta sami mom ta faɗa mata.
Ɗakin Jay suka je mom ta bubbuga amma shiru.
Magana ta yi ta ce " Jaiyana kina ji na?"
Jin mom ce a bakin ƙofar yasa ta buɗe, sai da gabansu ya faɗi da suka ga yadda idanunta suka kumbura suka yi ja.
Da alama bata yi bacci ba jiya kwana ta yi tana kuka.
Cikin ɗakin suka shiga mom ta yi ta yi ta faɗa mata abinda ke damunta amma ta ce babu komai.
Bata matsa mata ba ta ce wa. Munarh " maza je ki kara man hajiya mama Maimunatu."
" Toh " ta ce ta miƙe ta tafi.
Can sai ga su sun dawo tare, mom ta ce " hajiya don Allah ki tambayeta abinda yake damunta kalli idunta yadda ya kumbura da alama bata yi bacci ba jiya."
Gefenta ta zauna ta ce " shikenan kuje ku cigaba da aikin da kuke yi."
Bayan sun fita hajiya mama ta ce " me ke faruwa kike son ɗagawa mahaifiyarki hankali a cikin taro?"
Kuka ta ƙara fashewa dashi ta ce " na yi gaggawar bawa wani dama ya shigo cikin rayuwata, ban yi wa soyayya adalci ba."
Tana faɗin haka hajiya mama ta fahimci inda maganar take.
Rungumeta ta yi ta ce " duk abinda kika ga ya faru a duniya tabbas a rubuce yake tun kafin a halicce mu, don haka ina son ki cire wannan tunanin daga ranki."
" Yau ɗaurin aurenki bai kamata ki kasance cikin baƙin ciki ba, farin ciki yafi dacewa da ke."
Bayan ta gama lallashinta ta ce " maza kije kiyi wanka tun safe baƙi ke ta tambayar ina amarya."
Miƙewa ta yi jiki ba ƙwari ta yi hanyar banɗaki, kallon agogo tayi ta ga ƙarfe ɗaya da minti talatin, gabanta ne ya faɗi " saura minti talatin ki zama matar Sadeeq." Zuciyarta ta faɗa mata.
Da ƙyar ta iya jan ƙafarta ta shiga banɗakin.
Bayan ta yi wanka ta ɗaura alwala sannan ta fito.
Tana fitowa ta tarar hajiya mama ta fito mata da kayan da zata saka.
Ɗauka ta yi ta saka bayan ta fesa turare, ko kwalli bata saka ba ta shimfiɗa dadduma ta tada sallah.
Bayan ta idar da sallah ta rinƙa kallon agogo, gani take yi kaman jan lokacin ake yi.
Can kuma a massalacin da ke ƙofar gidan su Jay iyayen Sadeeq suka zo, bayan an gaisa suka yi magana da su dad sannan suka wuce shiga cikin masallacin suka zauna.
Can kuma sai ga tawagar Sadeeq da freinds ɗinshi.
ʼYan uwan margayi mahaifin su HAYDAR ne suka zo suma kasancewar suna gaisawa sosai da dad, kuma ana zaman mutunci har bayan rasuwar marigayi.
Har sai da aka fara siga sannan motar da su HAYDAR ke ciki shi da Zannur ta shigo cikin layin.
HAYDAR ya saka ƙafarshi cikin masallacin a daidai lokacin da me shela yake sanar da " an ɗaura auren JAIYANA UMAR FARUQ da angonta ALIYU HAYDAR MAHMOUD SHATIMA."
Baya ya yi zai faɗi dama jikinshi babu ƙwari Zannur da yake ya riƙe ya faɗo a jikinshi.