MISTER MASHI

MISTER MASHI PART 1

by @fatimadahirufuntuwa

🌺🌺🌺MISTER MASHI🌺🌺🌺

                         NA

FATIMA DAHIRU FUNTUWA BINTA


Page        1

      2026

    *** 


     Duk kan yabo da godiya sun tabbata ga mahaliccin Sammai da  'Kassai, wanda cikin ikon shi da yassarewar shi ya nufe mu da ganin wannan sabuwar shekara, Allah ina 'kara godiya a gareka da ka bani aron numfashi da lafiya har na cimma wannan lokaci, ya Allah ka 'karfafa min gwiwa ta, ka tsarkake min tunani na, ka bani ikon rubuta Al-kairi wanda mutane zasu amfana dashi, ka hanani rubuta abinda zai zama sharri ga Al-umma.

     Masoya na ina yi mana barka da sabuwar shekara🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

       Tattare takardun dake gaban Master Mashi yayi,  cikin ladabi ya ce  "Ranka shi dad'e, game da tsarin tafiyar ta ka, bakayi mana bayanin komai ba,  kuma kace akwai odar wasu kaya da zasu iso zuwa jibi, yaya kake so a tafiyar da al-amurran bayan baka nan?"

     Dafa kafad'ar shi yayi sannan cikin fara'a ya ce  "MISTER YAHAYA SARKI, wace Irin tambaya ce wannan? Sau nawa ina fada maka cewa  kadai na yi min Irin wannan maganar, yanzun ashe idan bana raye ba zaka iya tafiyar da harkar kasuwa cin ba?  Ko da bana nan duk abinda kasan a nayi da wanda ya kamata ayi kai din mai jagorantar shi ne,  Tabbas kaya zasu iso jibi, ni kuma gobe zanyi tafiya zuwa Abuja, tafiya ta zata hana kayan su zo ne? Koko zuwan kayan zai hana tafiya ta ne? Tafiya ta tanada muhimmanci sosai, ka tsaya kayi komai a kan tsari. "

    Yana gama fadar haka ya fita daga opice  din.

  
       'Karfe Tara da rabi na dare,   Shafa'atu ta fito daga d'akin ta, a falo ta samu mai gidan nata, yana kallon tashar NTA news, wanda dama hakan dabi'ar shi ne,  gefen shi ta zauna tare da shafa gashin kanshi, ta ce love kwana biyu zanyi missing d'inka fa, ina jin babu dadi hakan, gashi zakaje ka wahalar min da wannan kyakykyawan jikin naka, don Allah love me yasa ba zakayi tafiyar nan ta jirgi ba? Haba don Allah."   Ta karasa maganar cikin sigar shagwa'ba.

    "Shafa'atu, shekara biyu muna tare dake, har yanzun kin kasa fahimta ta,  ni MASTER MASHI   ba dai-dai nake da wasu masu kud'in da suke kyamar talakawa ba, yes ina da kudi na sani, amma ina so in rika shiga cikin talakawa inyi cud'anya da su ba tare da sun fahimci waye ni ba, ta hakan zaisa inji matsalolin talakawa, koda ni ban taimaka ba, zan kai koKen su gaba inda za'a share masu hawaye, idan kuma taimakon da zan iya yine sai nayi, don haka ki daina damuwa, lafiya lau zanje kuma lafiya lau zan dawo. "

       'Dan ta'be bakin ta tayi, sannan ta ce " Karfe shidda na safe zaka fita kenan? Gashi ana sanyi, to Allah ya tsare min kai."

  
     " Amin"  ya ce tare da janyo ta jikin shi, wanda dama tuni hakan take jira, ta  'kara kwantar da kanta a kan kirjin shi, tana shakar daddad'an kamshin turaren shi.

   Dan kukan shagwa'bar da ta saba yi mashi ta fara tana fadin magana 'kasa-'kasa.  " Gaskiya zanyi kewar ka, duk da ba wannan ne karon farko daka sabayin tafiya Irin wannan ba, a wad'annan 'yan Kwanakin fa ina bu'katar ka kusa dani."

      Ya ce  "To nace ki shirya mu tafi tare kince a'a  to ya kike so inyi da ke? uhum! Ki shirya mu tafi kawai in dai kinsan akwai matsala". Ya fadi maganar yana kallon idanunta, yayin da take kara  salon sabuwar kissar ta cikin shagwa'ba.

    Ta ce  "ka barshi kawai mayi waya."

    Ya ce "Kin tabbatar ba matsala ba zaki yi kuka ba."

      Dariya ta sakar mai,    ta ce "Allah ya kiyaye hanya, to muje ka kwanta tun gobe tashin wuri zakayi.

      Mi'kewa yayi ta taimaka mashi wurin cire kayan shi, sannan ya fada toilet domin yin wanka.

    Yana shiga toilet ta dauko wayar ta, ta kira MISTER YAHAYA SARKI, Shigewa tayi d'aki tana fad'in

     "Hello Sarki Al-bishirin ka, kasan cewa gobe ne zai yi tafiyar nan?"

      Ya ce   "Nasani don munyi magana da shi a opice dazu,  ya ce wai motar KSTA zai bi.

   Dariya tayi tare da fadin 'Dan wahalar ba, shi a rayuwar shi ya fi so ya kare a wahala, yanada kud'i amma baisan yadda zai more suba, ina MASTER MASHI ina hawa motar hayar Gomnati, ina so idan mutum yafi 'karfin abu, ya ri'ka nuna yafi, amma kullun shi d'an' 'kas-'kantar da kan shi ne,   soda yawa ina rayawa a raina INAMA ACE KAI NE SHI, SHI KUMA SHINE KAI,  na tabbatar da nafi jin dadin zaman aure na, amma kai kanka Mister Yahaya sarki kasan zaman da nake da Master Mashi, kai ka sani nafi son ka fiye da shi, ina yi mashi biyayyar kud'i ne, amma ainihin soyayyar taka ce,   Karfe shidda na safe Master Mashi zai tafi Abuja domin  cike wasu tsare tsare na kamfani,   karfe bawai tayi maka a cikin gidan nan, saboda gaskiya ina bu'katar ka,
MISTER YAHAYA SARKI ainihin soyayya ta, da zuciya ta, taka ce, MASTER MASHI gangar jiki na ya aura, ina tare da shi ne Sabo da yanada kudi, kai kanka ka sani, babu wani namiji da nake so sama da kai. "

   
     "Na sani Hajiya Shafa'atu, amma ya muka iya,?  Dole ne mu jira lokaci,  ni kaina ina takaicin yadda rayuwa ta tafin mana a haka, na so ace nine nake taka matsayin da MASTER MASHI yake a kai, shi kuma yana taka Irin matsayin da nake a kai, domin kuwa ko kad'an arzi'ki Irin na kud'i bai dace da MASTER MASHI ba, amma ba komai, watan wata rana dole  Al-amurra su canza! Saiya zama nine nake da 'karfin iko! Sai MASTER MASHI ya koma  'kasan-'kasa na, in taka shi yadda nake so! Domin kuwa nine cikakken mutum mai asali wanda ya kamata ya mallaki Irin wannan arzi'kin, inba don kaddara ba, ina ke ina auren MASTER MASHI?"

     Shafa'atu ta ce  "Dole  akwai ranar da komai zai canza a garemu, akwai tsare-tsare da matakan da zamu bi domin ganin mun tarwatsa shi, ainihin dukiyar shi ta dawo hannu na! Gaba d'aya ban dace da auren wannan mutumin ba, amma ba komai lokaci na zuwa....... "

    Saurin yanke wayar tayi domin jin motsin fitowar shi daga wanka,  a hankali ta 'karasa inda yake, tare da kar'bar towel din dake hannun shi ta fara goge mai jiki.

   
    Dariya yayi ya ce  "Shafa'atu  yau ban samu wankan daga gare ki ba,  mutuniyar arzi'ki,   mai kula da mujin ta, in dai a   'bamgaren biyayyar aure ne da iya soyayya da tarairayar muji  kinci d'ari bisa d'ari,   Allah yayi maki Albarka."

       "Amin mujina, mai' 'karfafamin gwiwa mai kula dani, ban tabayin abinda bai burge ka ba, komai nayi dai-dai ne a wurin ka,  yabo na da kakeyi a kan komai shine yake' kara 'karfafamin gwiwa wurin kyautata ma ka, ha'ki'ka nayi sa'ar mujin da ba kowace mace tayi nasarar samun Irin shi ba, da yawa mata suna kuka a kan rashin yabawa da nuna ko in kula da mazajen su suke yi a garesu, a yayin da su kayi masu wani abu na kyautatawa, misalin-  kwalliya,  mace ta d'au wanka tayi kwalliya da turare, amma mujin ba zai ta'ba cewa tayi mashi kyau ba, Al-halin kuwa tayi kwalliyar ne domin shi, yau ta yi-gobe ta yi, jibi ta yi baka kula taba, baka yaba kwalliyar ba, dole za taji ta sire mata, daga nan saita daina wahalar da kanta wurin yi maka kwalliyar, a ganin ta tamkar ka nuna baka sone, amma ni muji na ba haka yake ba, komai nawa birge shi yakeyi. "

   Ta fadi maganar   tana yi mai wani Irin kallo mai cike da kissa.

   Cak! Ya d'auke ta ya zauna bakin gado, ya zaunar da ita sosai kan 'kafafun shi.

     Ya ce  "Ina Al-fari da samun ki a matsayin mata ta, mace wayayya mai ilimi da sanin abinda ya dace, Allah ya yi maki Albarka Shafa'atu, Ina son ki."

       Ita kuwa bin jikin shi tayi tana shafawa, cikin solon soyayya, tare da sauya masu firar da suke yi, ta fara jero mashi kalamai wad'anda suka ruda shi,  suka sauya mashi yanayin da yake ciki.

        'Karfe Shidda dai-dai Masa'udu Direba ya d'auke shi zuwa Tashar KSTA kamar yadda ya bu'kata,  domin shiga motar hayar gomnati  daga Katsina zuwa Abuja, kasan cewar motar sammakon tashi takeyi, idan bakayi asubanbanci ba ba zaka samu motar farko ba.

       Yayi shiga dai-dai misali, babu yadda za'ayi don ka ganshi ka gane cewa shine MASTER MASHI shahararren mai kud'in da sunan shi ya karade birnin katsina da kewayen ta, da ma kasa baki d'aya,  kai har zuwa kashashen ketare, domin kuwa kasuwancin shi, bai tsaya iya Nigeria kad'ai ba, har zuwa kashashen turawa.

     Yadin shi ya saka mai sau'kin kud'i, dai-dai da Takalmin dake   'kafar shi da kuma hular shi, a ta'kaice dai shiga Irin ta talakawa, sai dai wanda ya lura da yanayin fatar jinkin shi ne kawai zai iya gane cewa wannan mai kud'i ne, amma da yawa za'ayi mashi kallon talaka mai rufin asiri ne.

        Bayan gama cika motar misalin karfe shidda da minti goma sha biyar mota ta tashi, da yake koda yazo dama motar ta kusan cika.

   
    Gefen wata matashiyar mace ya zauna wadda take ri'ke da 'karamin  yaron ta wanda bai wuce d'an shekara hud'u ba, barci yake ta yi abin shi, a kan  'kafar maman shi,  kasancewar sammakon da aka buga, barci bai ishe ba.

       Haka suka d'auki hanyar Abuja, wasu nata firarrakin su, wasu kuma suna kan wayoyin su.

     Haka MISTER MASHI  yayi shiru yana sauraron mutane, kafin shima ya d'auko wayar shi, ya fara dubawa, sai dai shi ba chart yake yi ba kamar sauran, Application d'in dake d'auke da Complete Kur'an ya shiga ya fara karanta Alkur'ani a asirce.

   Kallo d'aya matar tayi mashi ta kawar da kanta, wani Irin yanayi ta fada na damuwa, lokaci zuwa lokaci kuwa tana satar kallon shi, shi kuwa gaba d'aya hankalin shi na kan abin da yake yi.

    Ba suyi wata tafiya mai nisa ba yaron ya farka,  ruwan tea din data zubo mai a roba ta bashi shi Kuwa ya karba yana ta sha.

      Bayan ya gama sha, sai ko ya kai idon ga kallon MISTER MASHI.

   Yayi zambarma da niyar zuwa wurin shi, maman shi tayi saurin rike shi,  tana fad'in

    "Miye haka Abdul baseer, ka tsaya mana ina zaka?"

      "Aunty  ga Abbah! Aunty mu Abbah nane, wurin shi zan tafi."

     Sosai ta rike shi, tana fad'in Abdul Baseer ka bari mana, ba Abban ka ba ne wannan,  ka tsaya me kake so in siya maka? "

      " A'a ni wurin Abbah na zani, gashi nan wurin."   ya nuna MISTER MASHI.

       Ita kuma tayi 'ko'karin hana shi kawai saiya fashe da kuka.

    Hakan ne yasa MISTER MASHI maido hankalin shi a kan su, ya ce  "menene? Me kakema kuka,  zo nan."

    Ya mi' ka mai hannu, da sauri kuwa ya tafo wurin shi yana murna.

      Maman shi kuwa kyale su tayi kawai ta juyar da kanta gefe guda.

       Surutu ya fara yi mashi,   shi kuma ya biye mashi, wadda zai iya bashi amsa ya ba shi.

      " Abba kace zaka siya min jirgi, da mota, Abba yaushe zaka zo gida?  Ni da Aunty munyi missing d'inka."

     MISTER MASHI yayi dariya dai ya ce  "Ikon Allah yau na samu d'a a sama, haka mutanen dake kusa dasu sukai ta dariya, ana lallai kam ka samu d'a.

         Sun tsaya a Hunkuyi domin karyawa, haka ya fita da yaron nan yayi mashi siyayya sosai, duk abinda ya ce yana so saida ya siya mashi, sannan  ya maido shi wurin maman shi, don ya tafi shima ya karya, amma yaron nan saida yayi rigima, wai bazai tafi ya barshi ba, dole sai dai yayi mai wayo ya bashi wayar shi, yayi games, sannan ya barshi ya tafi.

      Kafin sukai Abuja wata Irin shakuwa ta shiga tsakanin rayon nan da MISTER MASHI,  shi yaro ya ce Allan baran MISTER MASHI baban shi ne 😂.

        Aiko lokacin da suka isa Abuja sai da tayi mai wayau, ta lullu'be shi da hajabi sannan MASTER MASHI ya sauka motar.

  
      Tun kafin  'karfe bawai ta yi MISTER YAHAYA SARKI ya iso gidan.

      Zaune suke shi da Shafa'atu a gefen gadon d'akin ta, fira sosai sukeyi Musamman a kan yadda zasu ci nasara a kan MASTER MASHI da kuma dukiyar shi.

      "Abubuwa da dama zasu iya faruwa  idan har shirin da neke da shi a kan MASTER MASHI ya tabbata,  a ciki kuwa akwai sauyin rayuwar mu, tsakanin ni-da-ke ne ya kamata ace mun zama ma'aurata,  saboda munfi dacewa da juna, amma ta yaya kike ganin zamu iya mallakar dukiyar shi gabaki d'aya idan har baki samu haihuwa da shi ba? Banga dalilin da zaisa kina zubar da ciki bayan kin samu ba, wanda kuma ta dalilin haihuwa tsakanin ki da shi ne kawai zai iya bamu damar mallakar duk kan abinda ya tara ta hanyar gado, amma idan baki haihu ba, ba lallai ki mallaki duka dukiyar shi ba, ya kamata ki haihu ko da sau d'aya ne, domin cikar wannan burin namu. "

      " Hummf!! Ajiyar numfashi Shafa'atu ta yi sannan ta ce   "Babu yadda za'ayi in bar ciki a jiki na har in haife shi, domin kuwa zai d'arsa zargi tsakani na da muji na, ni kuma duk abinda zaisa MASTER MASHI ya zarge ni bana so,  ha'ki'ka da hakan zata faru sai nafi kowa farin ciki.

        'Kara matsawa jikin shi tayi,  ta ce   "Abinda baka sani ba, MASTAR MASHI ba ya haihuwa, Tabbas kuma likita ya tabbatar mana da hakan, to gaka kuwa ba bu yadda za'ayi  ya ganni da ciki bai zargi wani abu ba,  mu sandai wata hanyar da zamu mallaki dukiyar, mu kassara shi, sannan mu koma muyi rayuwar mu yadda muke so."

           MISTER HAHAYA SARKI  ya ce "Dole ne zamu bi ko wace Irin hanya, domin ganin mun tara manyan kud'ad'e,  saboda   in taka matsayi Irin na shi, amma ke yanzun wace hanya kike ganin zamu bi domin cikar wannan 'kudirin namu?"

          "Hanya  d'aya ce  tunda har wasu kadarori da kud'ad'e suna a jingine da kai, to kabi duk wata hanyar da zakabi ka salwantar da su, koda karya ne ka nuna mai cewar anyi asarar su, sai mu had'a wata shaida ta hanyar gobara ko sacewa  mu kafa mashi hujja da shi, manyan kud'ad'e sosai fa, kai kuma daga nan sai ka bi asirtacciyar hanya wurin bud'e mana wani sabon kasuwancin, kafin Master Mashi ya farga mun zama wani abu.

     Bayan mun gama gina kammu  sai kuma muyi shawarar yadda shi kuma zamu durkusar da shi."

      Kwarai Mister Yahaya Sarki ya gamsu da wannan shawarar tata, cikin jin dadi da karfin gwiwa ya ce "Kuma dur'kusar da Master Mashi ba wani abu ne mai wahala ba, domin kuwa babu wata kariya ta Addu'ar iyaye a tare da shi, ke dai kawai Allah ya kai damo ga harawa."

        "Amin." ta ce dai-dai lokacin da take 'ko'karin cire yar figigiyar rigar barcin ta, wanda dama babu wani abinda ta' 'boye daga surar jikin ta.

  
  Baiyanar nonuwan ta waje ne ya 'kara birkita mister Yahaya Sarki, duk da ba wannan ne karo na farko ba, amma sosai yaji ya   'kagu  daya kai hannun shi.

     Ita kuwa sai wani 'kara kad'a su ta ke, domin ta lura da yanayin da yake ciki.

     Janyo ta yayi ya had'a da jikin shi, ya fara sartafa ta, yana kai hannun shi inda duk yasan zai rikita ta.

    
       Rungume juna su kayi sosai, dai-dai kunnan shi tana sakar mai kalamai masu Kama da sambatu.

        "Hakika mister Yahaya Sarki   ina jin dad'in kasan cewa tare da kai, kana bani natsuwa a wannan harkar, har Allah-Allah nake Master Mashi ya yi tafiya, domin kazo mu mori juna."

    'Ko' karin cire rigar shi ya fara yi, ta sa hannu tana cire ma shi, tare da 'kara had'a jikin ta da nashi tana shashshafa shi, dayi mashi kiss, tana gama cire mai rigar ta fad'a  kanshi tana kyalkyala dariya cikin nishad'i.

 🌺🌺🌺🌺ABUJA 🌺🌺🌺🌺

       Haba Master Mashi kamar kai, ina zaune a cikin garin Abuja amma kace zaka sauka ka kwana a Hotel, to duk abinda zaka samu a Hotel zaka same shi a cikin gida na,  kazo mu zauna muyi fira mu raba dare, abota aiba wasa bace, ko kai da madam d'in ka kuka zo ai kuna da wurin kwana a gida na."

   
     Dan murmushi master Mashi yayi, ya ce "Nagode kwarai da gaske Sanater, Allah kuma ya bar zuminci ya barmu da kaunar juna. "

   Sanater ya ce   "To yaya ka baro gidan  da Hajiya Shafa'atun?

    Master Mashi ya ce    "Lafiya lau na baro ta tana ta kewa ta, na ce kuma ta biyo ni ta kiya, ai da yake ba dadewa zanyi ba................

    'Karar wayar shi ce ta sa ya dakata da yin maganar da yake yi, ba'kuwar number ya gani, hakan baisa ya fasa d'aga Kiran ba.

      " Assalamu Alaikum." 
kamar yadda ya ke amsa wayar shi da sallama.

        "Wa'alaikumussalam, ina wuni?"

     "Lafiya lau."   ya amsa, duk da bai gane mai maganar ba, sannan yayi shiru yana sauraron abinda zata ce.

        Cikin taushin murya ta ce  "Kayi ha'kuri  na san baka gane wacece ba, Allah dai yasa baka riga ka kwanta barci ba na tashe ka." 

         Ya ce   "A'a ba komai ban kwanta ba, dawa nake magana?" 

        "Suna na Shamsiyya, Maman  Abdul-baseer,  d'an da Allah ya baka a cikin mota, gashi nan ya hana ni sakat! Da rigima wai ina Abban shi, me yasa ka fita mota ka barshi, kuka yakeyi sosai, harda sarkewa, shine na lallashe shi, nace mai zan kira ka kuyi magana, ko hankalin shi ya kwanta. "

'Kasa-'kasa  MASTER MASHI ya ri'ka jiyo kukan yaron, don haka baiyi wata magana ba ya ce  "Bashi wayar."

      Cikin murna kuwa yake magana duk da sautin sheshshekar kukan shi yana fitowa.

     Abbah ina kwana ya aikin? 
Meyasa baka tsaya ni ba?
       Sai gobe ne zaka dawo gida?
       Mu na so mu ganka, kuma ka daina zuwa, Abbah munyi missing d'inka sosai, zaka siyo min jirgin? 

     Shiru MASTER MASHI yayi don bai sanma ta inda zai bashi amsa ba, yaron da bai ta'ba gani ba,  wad'an nan tambayoyi haka. 

     Cikin hikima MASTER MASHI ya ce  "Zan siya maka, amma yanzun kaga dare yayi kayi ha'kuri kayi barci,  ka daina kuka kaji." 

     "Yaushe zaka dawo?"
 
     Yaron ya 'kara jefa mashi wata tambayar, 

    Kasa amsawa MASTER MASHI yayi don bai son yadda zaice ma yaron ba, baya so kuma yayi mashi Al-'kawarin da bazai cika ba. 

    "Yanzun ka kwanta kayi barci,  idan na zo zan siya maka jirgi da mota." 

    Dariya sosai yaron yayi, tare da yin godiya. 

  MASTER MASHI ya ce  "Ba maman ka wayar. 

      Ya mi'kama ta. 

"Shamsiyya wai me yake faruwa ne? Ina mahaifin shi ya ke? "

     Kuka ya ji tanayi. 

   Ya kuma cewa "Shamsiyya lafiya? Menene? Daga tambaya? Kinga, idan ba zaki iya amsa tambaya ta ba, ki barshi kawai, ni gaskiya bana son kuka."

     "Tabbas   'Da na Abdul Baseer yayi gaskiya, ha'ki'ka yasan fuskar mahaifin shi, inda ace muji na ba rasuwa yayi a gaba na ba, akayi mashi sutura a d'aki  na, sannan aka kaishi makwancin shi. 

     Da ace muji na    
 'bacewa ya yi, ko kuma ace labarin mutuwar shi kawai aka kawo min ba tare da naga gawar shi ba,  to Tabbas idan na hadu da kai, mai raba mu sai Allah, don tunda nake ban ta'ba ganin Kama Irin taku ba, koda kuwa  'yan biyu da ake haifa, ana samun banbanci ko ya yake,  amma kai ban ganshi ba, har muryar ku Iri d'aya ce,  bari in takaice maka, hatta tabon da yake a kan goshin ka shima yana da shi,  da ace zamanin da ne, na jahiliyya, to ba makawa muji na fatalwa yayi mani, babu abinda kake dashi a jikin ka wanda muji na baya da shi. 

     Shi kuma yaro bai san mutuwa ba, kullun fad'i yake :Abban shi zai dawo, Abbah na an kaishi Asibiti ne? Allura za'ayi mashi?  An zo an d'auki Abbah na, ba'a dawo da shi. "

Akwai wani Abokin baban shi saida ya daina shigowa gidan mu,  don da ya shigo Abdul Baseer zai dame shi, 

"Kun tafi da Abbah na baku dawo da shi ba, yaushe Zaku dawo dashi........... 

   Dai-dai nan Shamsiyya ta fashe da kuka. 

   Sosai kukan yaci 'karfin ta, ta yadda duk lallashin  da MASTER MASHI yake yi mata bata saurare shi ba, a 'karshe  saidai ya yanke Kiran. 

   Ya share wasu guntun hawaye da suke 'ko 'karin 'bullowa ta cikin idanun shi. 

    Sanata  ya kalle shi, cikin nuna kulawa ya ce   "Lafiya dai ko?"
  
      MASTER MASHI Ya ce   "Lafiya lau, kawai dai wata baiwar Allah ce muka had'u da ita dazun da zanzo, shine ta kira ni yanzun. 

Abinda na manta ma in tambaye ta shine: "ina ta samu number ta, gaskiya matar ta bani tausayi, mutuwa mai yankan 'kauna, ita d'in mujin ta ne ya rasu ya barta da'karamin yaro wanda baisan me ake cema mutuwa ba..............................................................................................

   Haka yaba Sanata labarin Shamsiyya iya kar abinda ya sani, da kuma haduwar su a mota.

     "Allah sarki" Sanata ya fad'a, ita rayuwa haka take, kuma kasan ance kowa da kake gani a duniya yanada mai Kama da shi, kamannin ku ne sukazo d'aya.

  

      Haka suka ci gaba da firar su har   'karfe   11-00, sannan Sanata yayi mashi sallama ya wuce  d'akin kwanan shi.

       
         Kwanciyar shi kenan ya lalubi number matar shi  Shafa'atu,  domin jin lafiyar ta da kuma yanayin kad'aici.

      "Barka da dare sahiba ta ya gidan?"

      Ta ce  "Lafiya lau muna ta kewar ka daga ni har gidan, an sauka lafiya? Ya gajiyar hanya? Nasan dai kasha wahala, ga tafiyar motar ba bu sauri, duk ka wahalar min da ni'imtaccen jikin ka."

     Ya ce   "A'a  ba laifi, tunda ba tsaye-tsaye muke yi ba, mun sauka lafiya inata missing din ki,  inama ace tare muke."

     Dariya tayi cikin wata Irin shiga mai d'aukar hankalin wanda akeyi mawa, ta ce  "Ba najin kana jin irin yadda nake ji a kanka, kwana biyun nan da zakayi ji nake kamar shekara biyu zakayi, nayi wani Irin takura, gidan gaba d'aya ba ya yimin dad'i, gaskiya muji bango ne a cikin gida da kuma rayuwar   'ya mace,  ko ba don dawainiyar da kuke yi damu ba, mace ta ri'ka ganin ku a cikin gidan ta ma kawai ni'ima ce, Allah ya saka maku da Al-kairi, ya biya ku da gidan Al-janna."

      "Amin  mu'umina, mace mai Albarka,  mai dad'in kalamai,  da irin wad'annan dad'ad'an kalaman naki kullun kike 'kara jefa kibiyar son ki a cikin zuciya ta,  ha'ki'ka da ko wane namiji haka yayi dacen mace, da aure ya zauna daram dam! Sabo da babu namijin da zai yarda yayi asarar irin wad'an nan kalaman naki da soyayyar ki, da koda yaushe namiji ya kasan ce mai faran ta ma ta rai da ya ba mata, komin butulcin namiji bai isa ya ce ta gundire shi ba, ni kuma Allah ya had'a ni da irin matar da zata zame mani sanadiyyar farin ciki na har abada, Shafa'atu ina son ki. "

     Ta ce   Nima ina son ka fiye da yadda kake so na, adadin son ka a cikin zuciya ta da rayuwa ta, tamkar ruwan sama ne yana zuba kamar da bakin kwarya, in tara babban  roba, kasan kuwa na tara da yawa." 

     Dariya yayi kana ya ce   "Idan harke wanda kika tara shine adadin soyayya ta a cikin zuciyar ki, ni kuwa adadin mamakon ruwan daya zuba a kasan shine  adadin son ki a cikin zuciya ta, kinga kuwa nawa ya d'ara naki sau ba adadi." 

    Dariya su kayi gaba dayan su, sannan ya ce  "To kada ki manta dayin Al-wallah  tare da Addu'a kafin barci, domin tsare wad'annan zai baki kariya a rayuwar ki, daga sharrin ko wane mai sharri, Allah ya tsare min ke, mu kwana lafiya." 

      Ta amsa da Amin, sannan su kayi sallama. 

     Washe gari da safe  lafiyayyan break past aka kawo mashi, haka Sanata da zo wurin shi suka sha fira, zuwa karfe  goma kuma ya dauke shi zuwa opice d'in da zasu yi metting d'in, shi ma ya wuce nashi opice d'in. 

      Sunyi taron su cikin Kwanciyar hankali, tare da d'imbin nasarori,  game da harkar kasuwancin su, na had'in gwiwa, wanda suke so su 'kara 'karfafa shi,  tare da shigo da wasu harkokin  da kuma dabarun kasuwancin,   wanda ya had'a da fara kasuwancin   man-fetur,  da kuma  'kara  'karfafa kasuwancin su na 'karafa. 

       Bayan fitowar su mitting, ya kira number Shamsiyya, yaji yadda 'Dan yaron shi ya kwana. 

     Ta shaida mai lafiya lau, ya na ta hidindimun shi. 

   A nan ne yake tambayar ta. 

 
     "A Katsina kike zaune koko?" 

       Ta ce   "E anan cikin katsina nake, Abuja kawai dai nazo ziyara ne, amma gida na yana katsina." 

      Ya ce  "OK to shikenan, Al'kawarin da nayi ma yaron nan ne, na ke so na cika,  amma uzurori ba zasu barni in siya in kawo mashi ba, amma yanzun ki bani Account number ki sai na turo maki kud'in ki siya mashi kayan wasa masu, kamar yadda ya bukata, kuma mahaifin shi yayi mashi Al-kawari, bai samu damar cika Alkawarin ba, Allah ya d'auki rayuwar shi, to ni zan Cika mai wannan Alkawarin. "

        Ta ce  "Gaskiya   'Da na yafi bu'katar ganin ka fiye da duk abinda zaka bashi, ya fi son ka a kusa da shi,  don Allah kayi min wannan taimakon in dai har kaima a Katsina kake, ka ri'ka ziyartar yaro na a matsayin mahaifin shi, har sai ya girma ya fahimta da kanshi cewa ba kai bane, saboda yana daga min hankali, da neman mahaifin shi,  bana son kukan shi,   Tabbas kai d'in zaka zama mai share hawayen shi. "

       

       Ya ce   "Shamsiyya yanzun dai bani da wannan lokacin, ki bani account d'inki kawai, in turo maki kud'in, ki siya mai duk wani abinda mahaifin shi ya yi
 mashi Al-kawari."

          Bata cika son gaddama ko jayayya ba,  hakan yasa ta amince da tura mashi account d'in.

     Kwanan shi biyu a Abuja, sannan ya biyo jirgin yamma ya dawo katsina.

      Kamar yadda ya kwana biyu a Abuja haka MISTER YAHAYA SARKI ya kwana biyu a gidan shi, jin lokacin da zai dawo yasa ya tattara ina shi-ina shi  ya bar gidan.

     Kwalliya sosai H-Shafa'atu  tayi, da lafiyyan abinci domin tarar mujin nata, tare da tanadar mai dad'ad'an kalamai nayi mashi ban gajiya.

      
       'Karfe Bakwai da rabi jirgin su ya sauka, Mister Yahaya sarki  shi  ne ya je ya d'auko shi daga Airport.

         Saida yaci abinci sannan ya fad'a wanka,  Safa'adatu ce da kanta ta taimaka mashi wurin yin wankan, ta kuma kintsa shi. 

     
      "Gidan muji na Al-janna ta,  kaji kuwa yadda nake jin wani sabon farin ciki ya d'arsu a cikin zuciya ta,  ha'ki'ka soyayya wata aba ce wadda baka iya sarrafa ta da kanka, duk kuwa wanda yayi gangancin sarrafa ta to zaya sha wahala, domin kuwa ba lallai zuciyar shi ta amin ta  ba,   soyayya a cikin zuciya da rayuwa ta ke, kuma dole kabi abinda zuciya ta za'ba maka, ba kuma yadda za'ayi ka tursasa zuciyar ka son abinda ba ta so.

    Humf! Muji na zuciya ta da taka iri d'aya ce, domin kuwa na tabbatar kamar yadda nayi kewar ka haka kaima kayi kewa ta."

       Ya ce   "Nayi kewar ki sosai Shafa'atu,  sau'ki na d'aya baki barni da maraicin jin da d'ad'an kalaman ki ba, haka kullun kike cika ni da su, gashi kuma na dawo kin kuma tara ta da su, ina son ki mata ta.

   Ya kai hannu ya rungume ta.

         'Karfe  goma da rabi na safiyar ranar wata Al-hamis, a lokacin kwanan shi biyar da dawowa daga Abuja, hudindimu sun sha mashi kai sosai, hakan yasa ya manta da zancen Al-'kawarin da ya yi ma Abdul baseer.

     Yana zaune kawai abin ya fad'o mai, aiko nan da nan ya lalubi number Shamsiyya  ya kira ta, bada jimawa ba kuwa ta d'aga kiran. 

     Sallama ya fara yi mata, kuma ba tare daya jira amsawar ta ba yaci gaba da cewa. 

        "Baiwar Allah da kika jini shiru ba sai ki nemeni ba, hidindimu ne suka sa na shafa'a da zancen nan, don Allah kiyi ha'kuri, yaya 'Dan yaron?  Da fatan dai ya daina kuka ko?" 

        Cikin fara'a ta ce  "Ba yayi, saidai koda yaushe tambaya, kullun dai hankalin shi na kan baban shi, ya kasa mantawa." 

         MASTER MASHI ya ce   "Allah sarki ai bazai manta ba, yanzun kin dawo Katsinan ne koko?" 

         Ta ce    "E na dawo tun shekaran jiya." 

      Ya ce  "To wace unguwa ki ke? Ina so inzo da kaina in kawo mashi Al-kawarin."

     Ta ce   "Ina layin zana. "   nan da nan tayi mai kwatancen gidan ta yadda zai gane. 

     Shi kuma ya ce    "Ni  ina Arebiyan querters ne, to shikenan yanzun ina aiki ne idan na tashi Insha Allahu zan shigo in kawo Al-'kawarin." 

     Godiya tayi mashi sosai, sannan su kayi sallama. 

    Yana tashi bai d'auki mota ba, ya hau keke napep. 

    Green House ya nufa kai tsaye,  nan fa yayi mashi siyayya ta kece raini, Kama daga kan kayan wasa dana sanyawa, da kayan ciye-ciye, siyayya dai sosai yayi mashi, sannan ya dauki shatar keke Napep ya nufi gidan su Abdul baseer. 

       LAYIN  ZANA

    Wata unguwa ce mai d'auke da mutane marasa  'karfi  (talakawa)  saidai suna rayuwar su cikin kwanciyar hankali, kuma kowa na yin hidindimun gaban shi,   masu sana'a nayi, da masu shaguna da masu toye-toye, unguwar dai kwanin ban sha'awa. 

     Akwai masu zaman kan layi, rukumi-rukumi,  wani rukumin dattawa ne, wani rukumin kuwa matasa, da yawansu kuwa ma'aikatan  gomnati ne, Musamman idan an taso daga wurin aiki, sawu kuma  'yan kasuwa ne, idan sun gama cin kasuwar tasu sun dawo gida, sai kuma ayi wanka, a fito tare da abokai ana fira, wani lokacin a kan abinda ya shafi kasa ta Nigeria, wani lokacin kuma a kan Al-amurra na yau da kullun, kai! Har firar kwallon 'kafa. 

     Musamman idan a kace maka  bayan sallar la'asar, zaka samu unguwar cike da mutane. 

        Haka ne yasa  marigayi  'Dan Asabe (Baban Abdul Baseer) ya gina wani kwakwkwaran  dakali a' 'kofar gidan shi, sannan yayi mai lafiyayyar baranda saboda masu zama 

      Misalin 'karfe  biyar da rabi na yamma kuwa,  wasu ma gidan ta ne su hud'u zaune a bisa dakalin,  suna ta fira. 

     Wanda yake zaune daga gefe ne keta zuba, kamar kanyar da ba dad'i.

       "Nake gaya maku,  shifa Jamilu matsoraci ne, bawai ina yi maku magana a kan ha'k'kin shi ba, shi fa a kan komai tsoro gare shi,  ji nayi fa ance :Fitsari yazo yi a waje  wai mage ta bashi tsoro, ni Allah na tuba, akwai wani abu da zai firgita ni!  Bawai batun cika baki ba,  muda a kauyen mu wane irin abu ne bama gani, ko cin karo dashi, maganar shiga daji kuwa ba a magana, nifa gaba d'aya na tsani matsoraci, haba! Tsoro ai sai mata."

     Dai-dai lokacin da me Napep ya sauke  MASTER MASHI a 'kofar  gidan.
 Kai tsaye kuma ya nufo kofar gidan, inda wad'annan mutane suke zaune suna fira.

Sallama ya yi tare da mi'ka ma mutumin dake ta surutu hannu, da niyar su gaisa, kafin kace me! Mutane ukun da suke zaune wurin tuni sun fece,  tsabar tsorata kuwa duk sun zubar da takalman su, shi kuwa wata 'yar gajeriyar suma yayi, yana fad'in "Dan Asabe-'Dan Asabe-'Dan Asabe!! Sai liyyaaaa! Ya murgine kasa somammame.

   Nan fa MASTER MASHI ya nemi mai keke Napep din daya kawo ruwa su zuba mashi.

    Cikin sauri kuwa ya dauko ruwa daga cikin keke Napep d'in ya fara zuba mashi, tare da fadin 

   "Subhanallahi!  Ba lafiya kenan."

      MASTER MASHI ya ce "Ba mamaki."

     Bawan Allah tunda yaji ruwan sanyi a kanshi, tuni yayi zambarma, ya tashi, shima ya zura a guje.

     Shara take yi a tsakar gida kawai taji fadowar mutum gigib! A guje, yana sambatu, yana 'karasowa inda take kuwa sake zubewa 'kasa yayi, yana salati,

 Innalillahi wa innailaihirrajiun! Ladidi! Ladidi!! Ki taimake ni, kizo ki duba kiga inada rai kuwa? "

     Ganin mujin nata a rude yasa tayi saurin yadda tsintsiyar hannun ta, tana fad'in

       "Me gida lafiya, meya faru?"

    Ba lafiya ba Ladidi, kizo ki ganni inada rai ko kuwa nima gawar ce? Kinsan idan mutum ya mutu baya ganewa, ki zo ki duba ni da kyau."

      Ladidi ta ce  "Me yake faruwa ne, kanada rai mana, gaka nan har ka shigo gida."

        "To amma ya nake ta ganin gawarwaki?"

         Ta ce "Gawarwaki kuma mai gida, a ina?"

      Ya ce    "Dan Asabe na gani mujin Shamsiyya yazo, muna zaune a 'kofar gidan shi, harda su Haruna mai shayi muna ta fira, a kofar gidan shi, kwatsam! Sai gashi ya dawo zai shiga gidan, har yana mikamin hannu mu gaisa! In  'Karya nake maki ba sunana ba, na rantse maki😭. "

      "Me gida ina ka ta'ba jin ance wanda ya mutu ya dawo? Ko dai ka rud'e ne? "

     Cikin matsananciyar rud'ewa yake magana. 

   "Ladidi zanyi maki 'karya ne, na ce maki mu duka mungan shi, sun rigani duguwa ma da suka ganshi, maza kije ki rufe mana 'kofar gida."

     Me zai kawo shi nan gidan, kasan fa tun  'Dan Asabe yana raye bai ta'ba shigowa ba sai yanzun ne................

     Yayi saurin katse ta da cewa  "To yanzun baya mutu ba ya zama Aljani!  Da Allah maza - maza kije ki rufe mana  'kofar gida."

    Hakanan taje ta rufe  'kofar gidan, shi kuma da  'kyar ya shiga d'aki da rarrafe.

       Shamsiyya tayi farin ciki sosai da wannan kyauta da MASTER MASHI yayi ma 'Dan yaron ta,   haka tayi mai godiya mara adadi  tare da shi mai Albarka.

   Abdulbasir kuwa farin cikin da yayi na ganin Abbah shi baya misaltuwa, domin a ganin shi baban shine, sai da yayi mashi wayau sannan ya bar gidan.

     Su kuwa su Malam Haruna mai shayi, gidan malam liman suka nufi tare da kai mai labarin dawowar  'Dan Asabe.
      
     Ya so yayi masu dariya ya kuma 'karyata su, amma ganin da yayi masu a rud'e kuma a rikice,  da alamar abinda suke gaya mashi suna da tabbaci a kanshi, shine yasa yayi masu magana cikin natsuwa tare da nuna masu cewa lallai zai yi binceke a kan labarin,  zai aika ko kuma yaje da kanshi gidan Shamsiyya d'in don ya ganema idon shi.

      MASTER MASHI ba dad'ewa yayi a gidan ba,  shiyasa koda su Malam liman suka zo saidai shamsiyya tayi masu bayani, basu taradda MASTER MASHI a gidan ba.

       *Tsarki ya tabbata ga Allah mai tsara halitta, mai kamanceceniya da mabambanta, ha'ki'ka kamar dake tsakanin MASTER MASHI da 'Dan Asabe sai kayi tunanin duka mutum d'aya ne.*

        Washe gari misalin karfe  biyu na rana,  H-Safa'atu  na zaune a falo, ta jiyo sallamar  Ummi mai turaren wuta,  amsa mata sallamar tayi, tare da bata umarnin zama,  gaisawa su kayi, sannan Ummi ta ce

      "A kan hanya fa nake, ina sauri."

     H-Safa'atu ta ce "Kinyi sabuwar d'auka ne? Don wancen turaren dana siya ya kusan  'karewa. "

      Ummi ta ce   "A'a banyi ba, ba talla ta kawoni ba,  nazo in fad'a maki cewa ki tashi tsaye kiyi da gaske, don tunda mujin ki ya fara  zawarcin Shamsiyya mai d'inki, to ki shiga taitayinki,  don naji ance mujin ta ma daya rasu saida ta asirceshi  domin na samu shaidar cewa ko Uwar shi baya jin maganar ta sai ta matar shi, wani irin mahaukacin so yake yi mata, kuma ni da idanuna naga mujin ki an sauke shi a 'kofar gidan ta, ya shiga. "

       Wani irin kallo H-Safa'atu tayima Ummi, tare da cewa  " Bansan zancen banza! Kamar ya an sauke shi? Karki kawo min karairayin nan na ku fa."

      Wane irin karairayi  Hajiya, da idanuna na ganshi an sauke shi a Keke Napep bawai labari aka kawo min ba, kuma dai kinsan nasan mujin ki,  tunda wuri ki bincika kiji, aiko ina 'karya bazan kawo maki zancen banza ba Hajiya,  mujin ki d'in dai shine na gani a Layin Zana, me zai kaishi wannan unguwar har cikin gidan ta inba zawarcin ta ba. "

       Humf!! H-Safa'atu tayi ajiyar numfashi,   ta ce   Tab-d'ijam!! Ni Usman zai yi ma wannan cin mutumcin!  Neman aure ban sani ba,  Ummi kinada tabbaci a kan wannan maganar taki?"

      Oh! ni  Ummi mai turare, wai hajiya zanyi maki karya ne, amma ki bincika shi kiji."

       Jinjina kai tayi, sannan cikin 'bacin rai ta ce   "Tashin hankali, neman aure kuma? Ni Usman zai yi ma haka? To amma ita shamsiyyar wacece a Katsina?"

      Ummi ta ce   "Wacece fa, talaka ce, Layin zana fa nace maki, Wallahi Hajiya abin kunya ne a gareki ace mujin ki yana kula wannan, domin ba wasu masu kudi bane,  in takaice maki ma mujin ta rasuwa yayi kuma ba wani abu ya bar mata ba, sana'ar da take, take dogaro da kanta, kinga kuwa idan ta dafe mujin ki ai ita warkam! Sai jalli ya 'kara ha'baka. "

     " Talaka ce?  To amma kodai muji na yaje ne domin yi mata wani taimako, ko don maraicin su? "

       Ummi ta ce "Ki daina wannan zance,  kamar MASTER MASHI ne zaije wannan gidan domin kai taimako? Ai saidai ya aika, ni zuwan nashi, nafi dangantashi da cewa akwai wata ala'ka tsakanin su, kuma bata wuce soyayya, don haka ni zan tafi, nazo layin ne dama wucewa zanyi, nace bari inzo in sanar da ke, don kisani, kin san mazan nan ba tabbas garesu ba, kada saidai kiji ana Ayyuririri!"

       H-Shafa'atu tayi mata godiya tare da cewa  "Don Allah ki 'kara bibiyar min shi, idan har wannan abin ya tabbata, saina dauki tsatstsauran mataki."

    Sannan ta d'auko naira dubu goma  10k taba  Ummi mai turaren wuta, saboda wannan labarin data kawo mata.

           ' Karfe  Tagwas na dare MASTER MASHI ya dawo gida kamar yadda ya saba kullun, wani irin canji ya gani sosai a wurin matar tashi,  domin babu wata kulawa da kalamai ko tarba mai kyau daya saba gani daga gareta, fuskar ta a murtuke babu wata fara'a.

     Cikin hikima da taushin murya ya ke tambayata menene dalilin sauyawar ta?

     " Shafa'atu  na 'bata maki raine bayan shigowa ta?  Ban ta'ba ganin haka daga gare ki ba, ko rashin lafiya kike baki canzawa haka, meke faruwa?"

      Ta ce  "Halayyar kace take' 'bata min rai, wani abin idan nace bana so, sai kaga kamar na takura ka,  ko kuma zan cutar da kai, ni kuma inayi maka hangen abinda zaije ya dawo ne, ina so ka fahimci cewa duk abinda kafi  'karfin shi to ka tsaya a matsayin kafi  'karfin nashi,  shishshigema talakawa da kake yi wata rana zai jefa rayuwar ka cikin had'ari, ina kai ina zuwa Layin Zana kai taimako,  ba sai ka aika ba, meye had'in ka da ita da har saika d'auka da kanka ka kai mata, wannan fa ba darajar ka bane? "

       Humf! Ajiyar numfashi yayi, domin yasan Tabbas an kawo mata gulma ne, to amma tunda ta sani babu amfanin 'boye mata komai.

      Ya ce  "Wata baiwar Allah ce  mujinta ya rasu, ya barta da 'karamin yaro, na tausaya mata, yaron daya ganni saiya ce nine Abban shi, saboda kamar da mukayi da mahaifinsa, ni kuma nayi mai duk Al-'kawarin da mahaifinshi yi yi mashi, to dalilin zuwa na gidan kenan."

       Wani irin kallo  Shafa'atu ta bi shi da shi, ta ce "Ita kuma mahaifiyar yaron ta ce kayi kama da mujin ta ba? Me yasa ba zaka aika a kai mata sakon ba inhar kayi niyar taimakon su tsakani da Allah,  kasan irin mugun had'arin da kake jefa kanka kuwa,  ita matar kasan wacece ita?  Kasan Halayyar ta?"

      Ya ce  " Ki kwantar da hankalin ki kawai Shafa'atu, ba abinda zai faru, sai Al-kairi.

       "Ya zakace in kwantar da hankali na, kana neman ka  'ka'kaba min abinda yafi karfi na, ace ka shiga har cikin gidan ta, kasan mugun abinda zata hada maka? Ni gaba d'aya cikin Al-amarin nan naka akwai rashin gaskiya,  kuma tsakani da Allah bazan taba jurar Irin wannan ba! "

         Ranshi a 'bace ya ce "Shafa'atu ba ki isa ki hana ni yin taimakon da Allah ya hore mani abinda zanyi ba, maganar kuma wannan mata duk wanda ya kawo maki gulmar yana so ya hargitsa maki zaman aure ne, domin duk wanda ya fad'a maki, zai kawo maki zargin cewa ina soyayya da ita ne, wanda kuma ba haka bane, taimako ne ya kaini gidan, inna so yin soyayya da ita kin isa ki hana ne! ko kinada ikon da zaki haramta min 'kara aure ne!  Shafa'atu ki tsaya a matsayin ki, karki shiga tsakani na da duk wanda zan taimaka mawa, wannan ba hurumin ki bane, Shamsiyya da  d'anta suna bu'katar taimako na, kuma na taimake su, duk wanda ya kawo maki gulmar yana so ya Tada maki hankali ne. "

     Kallon mamaki take bin MASTER MASHI da shi, duk da tasan yanada zafi, amma bai ta'ba yi mata magana cikin tsawa da kashedi irin wannan ba. 

    Fushi tayi kawai ta fad'a d'akin ta ta rufa 'kofa.

      Number Mister Yahaya Sarki ta kira,  don fad'ama mashi abinda ke shirin faruwa a gare su.

     
       "Mister  Yahaya Sarki idan har abinda nake zargi a kan MASTER MASHI  ya tabbata to lallai shirin mu na daf! Da tarwatsewa,  an fad'a mani kuma shima ya tabbatar mani da cewa lallai yaje Layin Zana wurin wata bazawara  'yar talakawa, sai dai shi ya nuna cewa ba soyayya sukeyi ba, taimako ya kai mata, wanda ni zuciya ta bata aminta da zancen shi ba, domin kuwa idan kaga kare na shinshina takalmi d'auka zai yi.

     Abu na biyu Master Mashi ya daddamfara mani maganganun da suka 'kara tabbatar min da cewa koda yaba soyayya da ita, zancen zai iya sauyawa nan gaba ko kuma ita tayi amfani da hikimar ta da Asirin ta ganin ta mallake shi, domin kuwa babu macen da zata samu namiji irin Master Mashi tare da irin wannan damar daya bata; bata samu hanyar mallakar shi ba, saboda haka koda wane lokaci zancen zai iya sauyawa. "

       Mister Yahaya Sarki ya ce  "Duk wannan ba damuwarki bane,  damuwarki ita ce yaya zamu mallaki kud'in da zamu tsallake kangin rayuwar da muke ciki, mu wawuri dukiya fiye da kima sannan mu tsallake muje muyi aure, kishin Master Mashi a kan zai 'kara aure ba naki bane, domin kuwa kema d'in ba tashi bace, kin sani ke tawa ce, me zaisa ba zamuyi amfani da wannan damar ba,  wurin kawar da hankalin shi a kanmu mu cika burin mu.? "

      " OK kana tunanin cewa kada inyi kishi a kan muji na, in zauna insa ido ina kallon wata shashasha  'yar talakawa tayi nasara a kaina, ta auri mujina, komai nashi mu raba,
Koda ace zanyi irin wannan gangancin ba yanzu ba, domin a yanzun Master Mashi yana matsayin muji na ne, ya zama dole inyi kishin duk wadda ta ce zata kusance shi, na sani kai nake so, amma dole inyi katanga ga duk macen da tace zata ra'bi muji na, ko da bana son Master Mashi kallon muji na nake mashi,  ya kamata ka fahimci halin da nake ciki fa. "

       'Darsuwar kishin ta Mister Yahaya Sarki  yaji a cikin zuciyar shi,  tare da tunanin in har Shafa'atu zatayi kishi a kan Master Mashi  to lallai son shi yana barazanar kutsa kai cikin zuciyar ta, idan kuma haka ne tunanin shi, to shi a wane matsayin yake kenan?

     Ya ce   "Shafa'atu  kada kice zaki kawo wannan zancen,  mu juyar da hankalin mu a kan shirin mu; kada zancen wata ya tada maki hankali, karki manta matsayin master mashi a wurin mu, tamkar matacce haka muke kallon shi, to amma miye na damuwa don yana son wata, wadda ma baki da tabbaci a kan ta, ki sani ni da ke zuciyar mu da 'kudirin mu d'aya ne,  kawar da Master Mashi, koda bamu kashe shi har lahira ba, mu durkusar da shi, ta yadda yana a raye amma matacce yake, daga lokacin da muka raba shi da dukiyar shi, zai zama bashi da wata daraja a idon kowa,  duk wani kwarjini da iko zai dawo a karkashi na ne, da yuwuwar mu iya kawar da hankalin shi, sannan ke d'in zaki zama mallaki na, sai mu tsara rayuwar mu yadda muke so."

      "Duk a yaushe ne wad'annan abubuwan zasu faru? Shekara biyu ina tare da Master Mashi mun kasa samun mafita, kullun kullawa muke muna kwancewa, ya kamata a wannan lokacin ace anyi mai yuwuwa,  duk da ina jin kai nake so, amma ina ba'kin cikin wata ta kusanci mujina, domin kuwa inada tabbacin cewa ni kad'ai ce tashi. "

    'Dan jimm! Mister Yahaya Sarki yayi, sannan ya ce   "Ki kwantar da hankalin ki; komai yazo   'karshe." 
  Sannan su kayi sallama.

     

          LAYIN    ZANA

    Shamsiyya ce zaune a kan keken d'inkin ta, a lokacin Abdulbasir ya tafi makaranta, da yake ranar Monday ce, akwai yaran ma'kabtan ta da suke biyo mashi su tafi tare, misalin  'karfe takwas da rabi na safiya kuwa.

     Taji Sallamar  Gwaggo Binta,  d'an-jin fad'uwar gaba tayi, domin sanin halin surikar tata, wadda ba ta raina abin tashin hankali, don tun lokacin da   'Dan Asabe na raye take fama da wula'kanci da tashin hankalin ta, bacin ma Allah ya azurta ta da muji mai hankali da fahimta, wanda yana lallashin ta da tausar ta a kan abinda Gwaggo Binta take yi mata, duk da shima d'in ba kyale shi tayi ba.

     To a yanzun haka duk da mai rabawa ta raba, hakan baisa Gwaggo Binta sararawa da abinda take yima Shamsiyya ba.

    Amsa mata sallamar  tayi, tare da nuna mata wurin zama.

      "Ina kwana Gwaggo."

        "Ba shi ya kawo ni ba! In ban gwana ba zaki ganni? Ashe kenan duk abinda ake gaya min a kanki shamsiyya gaskiya ne,  tunda nake ban ta'ba sanin cewa tsabar iya asirin ki ya kai haka ba! Ansha kawo min zancen cewa kina yima d'ana Asiri, ina kawar da kai, saboda a zauna lafiya! Yanzun ke shamsiyya jahilcin naki har ya kai kije ki tono mutum daga makwancin shi ki dawo da shi duniya,  wannan wane irin tsabar Asiri ne, wane tantirin boka ne da wannan aikin? To bari in fad'a maki tun wuri in zaki shiga taitayinki ki shiga! Wanda ya mutu baya ta'ba dawowa, ko ni da nake uwar shi ban isa in dawo dashi duniya ba, amma ke saboda munafunci, don ace kinfi kowa son shi, shine kin bishi kabari kin ciro, to tun wuri ki fita harkar shi, inba haka ba inyi maki zagar zogalen zaliha! Don tunda nake ban taba jin irin wannan mummunan abin ba sai a wurin ki!! Eheee!!!!

      Hawaye ne suka zubo a idanun Shamsiyya ta ce   "Gwaggo ba haka bane, duk wanda yace maki na dawo da matacce 'karya yake yi mani, shi wannan mutumin kama yayi da   'Dan Asabe kawai, shine mutane suka yi zaton shine, amma bashi bane, babu yadda za'ayi wanda ya mutu a dawo dashi. "

      " Ban gane cewa sunyi Kama ba,  inba munafinci ba kuma sai ya hadu dake?  Warwaremin wace Irin kama sukayi? "

     Humf! Jan numfashi Shamsiyya tayi,  sannan ta ce
   " Tunda nake a rayuwa ta ban ta'ba ganin kama irin wannan ba,  duk abinda kika san Dan Asabe yanada shi shima yana shi, muryar su kuma iri d'aya ce, hatta tabon da yake a kan fuskar shi shima yanada shi, bansan ta yadda zan iya kwatanta maki wannan kamar ba, sai dai in kin ganshi. "

       Wata zufa ce ta fara tsatstsafo ma Gwaggo a goshi.

      Ta ce to shikenan dama ina so in dawo gidan nan da zama, ki kira min shi in ganshi, idan da gaske cewa yayi Kama da d'a na, donni bana son gutsiri tsoma.

      Kuma  gidan da  nake zaune an tada ni, ni dama na gaji da wannan yawon hayar, gara in dawo gidan d'a na in zauna, koda ba nida gado ai dai naci arzi'kin shi,  ban san ma fitinar data raba ni da gidan nan ba, ina zaman zama na na tashi na kama yawon haya, koda yake wad'an nan munafikan ma'kabtan naki ne da shegen sa idon tsiya, to zan dawo gidan in zauna dai-dai nake da kowa!"  

     Saita nufi tsofon d'akin ta da nufin ta fara kakka'beshi da sharewa, har takai 'kofar d'akin kuma ta juyo. Ta ce  " To shi yaya sunan shi? "

       Shamsiyya ta ce " "Usman sunan shi." cikin zuciyar ta cike da fargabar irin zaman da zasu sake yi da wannan fitinannar sirikar tata.


Fatima Dahiru Funtuwa Binta✍