Chapter 10
by @barista
BIYU A ƊAYA
Page 10
Sayyada barrister
***
YOTA 13
TEAM FIVE INK LEGENDS
NIGERIA Maiduguri KIRAWA'S FAMILY
Tun da Dr Waahab ya tashi sallar asuba bai koma bacci ba, ya ci gaba da shirya Luggage nasa da duk wani abin da zai buƙata, kamawa daga side bag, laptop, da duk wani abin da zai taimaka masa a wannan tafiyar da zai yi akan aikinsa.
Gari ya yi haske rana ta fara fitowa, ya faɗa toilet ya watsa ruwa ya fito ya shirya cikin suit Ash color da riga fara ta ciki, ya yi matukar kyau sai ƙamshi ke tashi, ya sanya farin glass, ya fito ba tare da ya ɗauki kaya a hannunsa ba, ya wuce side na Mamie, ya taddata zaune tana shan tea, ya yi sallama ta amsa ya zauna tare da cewa
"Barka da safiya Mamie"
"Barka dai Babangida, har an shirya?"
"Eh, na shigo ne mu yi sallama"
"To Babangida, Allah ya kiyaye hanya, ya tsare ku daga dukkanin wani sharri, bani da shakku a kanka na san ba za ka aikata abin da bai dace ba"
Ya sauke numfashi a hankali, sannan ya ɗago ya kalleta tare da cewa
"Amin Mamie, in sha Allahu ba abin da zai faru"
"To Allah yasa mu ma wannan shine fatan mu"
"Amin Mamie, zan je na yi sallama da mommy sai na wuce"
"Hakan ma ya yi, Allah ya tsare"
"Amin"
Ya faɗa ya mik'e ya fito, a hanyar shigowarsa side na Mommie ya haɗu da Hauwa, ta yi masa barka da safiya, ya amsa cikin sakin fuska tare da cewa
"Auta zan yi tafiya, zan ɗan kwana biyu in Allah ya yarda"
"To Ya Waahab, Allah ya tsare"
"Amin"
Yana faɗin haka, ya shige side na Mommie, ga mamakin sa, yau ya taddata jingine jikin bed, Suhaima na bata tea, ya yi sallama suka amsa, ya iso kusa da bed suka gaida shi ya amsa idanunsa akan Mommie, ita ma shi take kallo, ya zuwa akan stool tare da cewa
"Ma sha Allah jiki yau kam ya yi kyau"
"Jiki kam Alhamdulillah yau ta ɗan sami kuzari"
Cewar Jamila, a daidai lokacin, Suhaima ta kammala baiwa Mommie tea, Dr Waahab ya yi wa Mommie magana duk da ya san ba amsawa za ta yi ba.
"Mommie ya jikin ki?, da fatan kina jin sauƙi, mun yi kewarki sosai'
Ta kurawa bakinsa idanu kamar me karantar abin da bakin ke furta wa, ya ci gaba da cewa
"Family ya dishashe saboda babu giftawarki a ciki, farin cikin zukatanmu ya gushe saboda halin da kike ciki, Mommie ke ce za ki ceci rayuwar ta hanyar ƙarfafa zuciyarki akan ta amince da gaskiyar komai kuma ta rungume kaddara"
Shiru ya ratsa sai sautin kukan Jamila da Suhaima, a hankali ya sauke numfashi ya lumahe idanunsa, shi ma kansa juriya kawai ya yi, da ko da hali da ya yi kuka, a hankali ya buɗe idanunsa ya ci gaba da cewa
"Yau zan yi tafiya, har tsawon wasu watanni, aiki zai kai ni, ina fatan na dawo na tadda ki lafiya kin warke ba ki ɗaya"
"Ya Waahab tafiya za ka yi?"
Cewar Jamila, ya bata amsa da
"Eh in sha Allahu"
Ya duba a gogon hannunsa, yaga lokacin ya ja, ya mik'e tare da cewa
"Jamila na wuce, in kin koma gidanki ki gaida yara"
"To likita Allah ya kai ku lafiya, ya kuma yi muku jagora akan abin da ku ka je yi"
Ta faɗa tana share ƙwalla, ya amsa da
"Amin"
Haka ma Suhaima ta yi masa Allah ya ƙiyaye hanya. Yana fitowa kai tsaye ya wuce side na Daddynsa, kamar ko da yaushe ya tadda su zaune suna breakfast, Abbie, Abba da Daddynsa, ya gaida su cikin girmamawa tare da cewa
"Na shirya yanzu zan wuce airport"
Sun ɗan dakatar da cin abinci da su keyi, Daddynsa ya yi magana
"Har ka shirya, to madallah ubangiji ya yi jagora"
"Amin Daddy"
"Za mu yi kewar babban likita"
Cewar Abbie, Dr Waahab ya yi murmushi tare da cewa
"Ni ma zan yi kewarku"
Abba shima ya yi masa addu'a tare da fatan Alkhairi, ya yi godiya, ya mik'e ya fito ya wuce side nasa, a ƙofar ɗakinsa ya tadda Sa'eed a tsaye, yana isowa ya miƙa masa hannu tare da cewa
"Ina side na Daddy ne, mun yi sallama"
"Abin da ya faɗo min cikin raina kenan, kana side na Daddy ko Mamie"
Cewar Sa'eed, suka shigo ciki a tare, Dr Waahab ya ce
" Gwanda ma da ka shigo ai, sai ka taimaka min mu fidda kayan"
"Abin da ya kawo ni kenan, har airport zan yi maka rakiya"
"Thanks bro"
Sa'eed ya riƙe Luggage ɗin ya fito dashi, shi kuma Dr Waahab ya ɗauko side back da wayarsa ya fito ya rufe ƙofar a lokacin har Sa'eed ya yi parking space da luggage ɗin..
Kiran shi da aka yi ne a waya yasa ya tsaya tare da amsa kiran
"Dr Faisal how far?"
Dr Faisal ya yi magana daga ɗayan side ɗin
"Ba dai ba ka shirya ba?"
"Fitowa kenan ka kirani"
"Ok mu haɗu a airport"
"Ok no problem"
Ya sauke waya bayan Dr Faisal ya katse, yana ƙoƙarin barin wajen ya ji murya kamar daga sama an kira sunan sa
"Ya Waahab"
A nutse ya juyo yana kallonta, har ta ƙaraso kusa da shi, bai amsa ba amma kuma ya bata hankalin sa, cikin sanyin jiki ta ce
"Yanzu Ammie take sanar dani, Mamie ta faɗa mata za ka yi tafiya yau"
A hankali ya sauke numfashi tare da cewa
"Eh haka ne, mene ne?"
"Nayi tunanin za ka faɗa min"
Ya kura mata idanu ya rasa me zai ce, ya kasa gane kanta....
"Ai ko addu'a ma sai nayi maka"
"Na faɗa wa iyayen mu, no need sai na faɗa muku kuna matsayin ƙannena"
"Uhm, to yaushe za ka dawo?"
"Me yasa ki ke son sani?"
Haushi ya turniketa kamar ta ƙwala ihu amma ta jure tare da cewa
"Kawai na tambayane"
"Zan kwana biyu"
Ya juya zai bar wajen ya ji muryarta tana jero mishi addu'oin da suka saka shi tsayuwa ba shiri
"Allah ya kai ka lafi, ya tsare ka daga duk wani abin da zai cutar da kai, ya kare ka da kariyar sa, ya baka sa'a akan abin da ka je yi. In sha Allahu nasara tana tare da kai Ya Wahaab"
Tana gama faɗin hakan ta sudda kanta ƙasa tana hawaye, a hankali ya juyo, yana kallonta, ya yi taku biyu zuwa uku ya zo dab da ita, yana ci gaba da kallon ta, wulaƙanci ba ɗabi'ar sa bane amma shi ba kasai yake son yawaita magana ba, musamman abin da bai zama dole a gare shi ba, a hankali ya furta
"Ashfat"
Ta ɗago suna kallon juna, hawaye kwance kan fuskarta, yana bin fuskar da mamaki, ya sauke numfashi tare da cewa
"Ameen, na gode sosai da addu'a"
"Ka kula da kanka"
"Uhm thanks"
"Zan kira ka da kun isa"
Ya sauke ajiyar zuciya tare da cewa
"Take care of yourself"
Yana faɗin haka ya juyo, suka haɗa ido da Sa'eed da ya biyo baya don ganin jimawar Dr Waahab ta yi yawa, ya taimaka masa suka sanya kayan cikin Boot na mota, suka shiga, Sa'eed ke driving, ya tada motar Baba Musa ya buɗe musu gate suka fice, shiru ya ratsa a sakaninsu, cen Sa'eed ya ce
"Dr Waahab why not ka amince wa Ashfat"
"Akan me?"
"Na san ka fahimce ta, kuma ita ma ta san ka fahimce ta, to ka amshi soyayyar ta mana"
"Sa'eed kallon ƙanwa ta nake yi mata hakan ba zai taɓa canja wa ba"
"Ba abin da ba ya yiwuwa, in dai za ka saurareta kai ma za ka ji kana sonta"
"Mu bar wannan maganar"
Suka sauya hira, har suka ido airport, a lokacin suka tadda waɗan da za su yi tafiyar tare har sun iso shi kaɗai ake jira. Sa'eed ya taimaka masa suka fito da kayansa sannan ya yi musu addu'ar fatan nasara ya dawo cikin mota, ya tadata ya dawo gida.
Dr Waahab basu tsaya bata lokaci ba, jirgin su ya tashi kai tsaye sai Abuja.
*********************************
Ashfat Dr Waahab yana barin wajen ta juya da sauri cikin farin ciki, ko ba komai yau ya kula ta, har da cewa ta kula da kanta, tana shigowa dakin su ta faɗa kan katifar su ta rungumi pillow tana murna, zuba mata ido su ka yi tare da taɓe baki, ita kam ko a jikinta, sai murmushi ta ke yi, Teemah ta ce
"Aunty Ashfat me ki ka samu haka ki ke farin ciki?"
"Bai shafe ki ba"
Ta faɗa tana murmushi, Hauwa ta ce
"Ya Waahab ya yi tafiya maimakon ki yi kuka shine kike dariya"
"Ai mun yi kyakkyawar bankwana shiyasa nake farin ciki"
Cewar Ashfat tana kallonsu, girgiza kai Suhaima ta yi tare da cewa
"Aunty Ashfat ki dawo cikin hankalin ki, kada ki zurfafa cikin son ɗa namiji, ba wai sai Ya Wahaab ba, ko ma waye ne, ki dinga sanɗa² a soyayya"
"Suhaima ba za ki gane ba, da sauran ki, kuma babu ɗa namiji da zan so kamar na Ya Waahab"
"Uhm shawara ce na ba ki, kuma ki sani don kun yi bankwana cikin farin ciki ba haka yana nufin ya amshi soyayyar ki ba"
"Ya isa haka Suhaima ko don kin ga ina hira dake ne za ki faɗi hakan, kamar bakin ciki kike yi min, in ba za ki goyi bayana ba, ki ja bakinki ki yi shiru"
"Allah ya ba ki hakuri, me ya yi zafi shi ba wuta ba, daga faɗin gyara kayan ki"
Cewar Suhaima, Ashfat ta ce
"Komai ma zayyi zafi indai akan Ya Waahab ne"
"To shikenan Allah bada sa'a"
"Amin"
Cewar Ashfat ta koma ta kwanta, babu wanda ya sake cewa komai, ta faɗa a duniyar tunani......
********************************
GHANA
A nutse Bilqees ta shirya cikin uniform na wajen aiki, tun da ta idar da sallah asuba bata koma bacci ba, da wuri ta kammala aikin. Ta shirya ta fito parlor ta tadda Mamanta kwance, ta yi mata magana akan za ta tafi amma shiru bata amsa mata ba, har Bilqees ta iso ta ɗan taɓa ta sannan ta dawo daidai, sautari tana ganin Mamanta na shiga wannan yanayin amma ta rasa na mene ne? Wani lokacin taga Mamanta na hawaye a irin wannan yanayin, wani lokacin kuma ta faɗa a duniyar tunani...
"Bilqees har kin shirya?"
"Eh Mama, saura tafiya"
"To Allah ya kai ki lafiya"
"Amin Mama"
"Bilqees"
"Na'am Mama"
"Kwana biyu Alaja bata leƙo nan ba, da fatan ba laifi ki ka yi mata ba"
Bilqees ta sauke numfashi ta ɗan gyara zamanta tare da cewa
"Fushi Alaja ke yi dani"
Maman Bilqees ta ɗan tashi ta jingina da bango, Bilqees bata yi mata ƙarya shiyasa bata shakkan tambayar ta abu, ita ma tayi noticing kwana biyu Alaja ta ɗauke musu wuta bata san akan maye ba.
"Laifin me ki ka yi mata?"
"Na fasa mata plate a rashin sani"
"Ikon Allah, in ban da abin Alaja ma kayan Allah ai na Annabi ne, kuma tsautsayi baya wuce ranar sa, ko a hannun ta ne in Allah ya yi zai fashe babu me iya hanawa dole sai ya faru"
"Mama na bata hakuri amma taƙi hakura"
"Da kin koma ki sake bata hakuri, da kai da kaya ai duk mallakar wuya ne, mene ne aka yi plate"
"To Mama zan sake bata hakuri da na iso restaurant"
"Sai kin dawo"
"Yawwa"
Ta faɗa ta maƙale jakarta a baya ta fito, ta tari machine ya kai ta Alaja restaurant.
ALAJA SPECIAL RESTAURANT
Tana isowa ta sallami me mashin, sannan ta shigo, kasancewar da wuri ta shigo yasa ta tadda ma'aikatan basu da yawa, kai tsaye ta wuce side na masu raba abinci ta ajiye jakarta ta sanya rigar sama, sannan ta fito kasancewar babu kowa a ciki, a hanyar fitowa ta haɗu da Aunty Hafsuh me kula da bangaren masu rabon abinci ta gaida ta, sannan ta fito dining area ta tadda cleaners suna ta tsabtace wajen ta wuce ɗakin Alaja ta taddata zaune tana latse² a wayar ta, cikin girmamawa ta ce
"Maa an tashi lafiya"
"Lafiya"
Kawai Alaja ta faɗa, bata da niyyar sake cewa komai, ganin haka yasa Bilqees cewa
"I'm really sorry.....
"Tashi ki bani waje, I'm busy right now"
Jiki a sanyaye ta dawo dining areas a lokacin customers ɗaya, biyu sun fara shigowa saboda breakfast, nan ta shiga tsawon Server's suka fara saving nasu, ido ya dawo kanta, sun maida ta waiter su ce suna buƙatar ta kawo musu wannan su ce suna sun wancen, duk da ita hankalinta da zuciyarta bata tare da su bata dauki hakan a kan komai ba, duk abin da suka buƙata shi ta ke kawo musu, da ƙyar ta samu ta sarara....
*******************************
Abuja Nigeria
Dr Waahab suna sauƙa a Abuja kai tsaye daga airport aka kai su, hotel da aka tanadar musu, babu ɓata lokaci kowa ya shige ɗakin da aka kama masa, Dr Waahab yana shiga ɗakinsa ya rage kayan jikinsa ya fara da watsa ruwa, sannan ya ɗan huta, nocking aka yi ya buɗe abinci aka kawo ya karɓa ya koma ci, bai wani ci sosai ba, ya kwanta yana mik'e aka sake nocking ya buɗe Dr Faisal ne, ya sauke numfashi tare da cewa
"Ya dai Faisal?"
"Ina ka ajiye wayar ka ne, OG yana kira naka ɗauka ba'a
"Oh! Tana silent me ya faru?"
"Akwai meeting da za mu halarta ne nan da 30 minutes, be ready"
"To kaya kawai zan sauya"
"Ni ma bari naje na shirya"
DR Faisal ya koma ɗakinsa, Dr Waahab ya dawo ya shirya tare da cire wayar sa a silent yaga missed calls na Daddynsa da Mamie ya kira suka gaisa sannan ya fito suka wuce meeting...
*******************************
GHANA Alaja special restaurant
Gaba ɗaya ma'aikatan an tara su a ɗakin meeting, sun yi cirko² sun zuba wa shugabar idanu suna jiran me za ta faɗa musu, don duk lokacin da ta tara su irin wannan to babban al'amari ne ya faru ko zai faru. Taku take yi tana gaba tana baya, sai da ta ɗauki wasu mintina sannan ta tsaya ta fuskance su tare da cewa
"Kowacce ta bani hankalinta"
Nan suka nutsu suna sauraron ta, ta ci gaba magana
"Yanzu labari ya zo min, za a yi baƙi a international hotel, kun san dai duk baƙin dake sauƙa a wajen ba ƙananan mutane bane, manya ne to don haka Salmon Manager ya kira ni, kai tsaye suna buƙatar abinci da daga waje na, kuma ba wai na rana ɗaya ba na tsawon watanni da za su zauna ne"
Nan suka soma jinjina maganar ta, kuma sun san indai international hotel sun nemi haɗin gwiwa da ALAJA to ba ƙaramin kuɗi take samu ba....
"Tied your belts, and make sure everything goes well"
"By God grace Maa"
"Good, bana so naji ko naga akasin haka?"
"To Maa"
Suka haɗa baki wajen faɗin hakan....
______________________
To fah fan's yanzu za a fara wasan. Da fatan kun shirya tsab saboda tafiya Ghana. Ni dai ina sauƙa kai tsaye sai Alaja restaurant 💃💃💃😂
Ku zo mu yi wa SPECIAL Dr Waahab rakiya🥰😃
To fah me ku ke tunanin zai faru a wannan tafiya? Ga Bilqees, ga Angel ga kuma Ashfat da fatan ba ku manta da Alajar mu ta gargajiya ba😃
Comments and share fisabilillah