FITAR AMO
*SILAR HALLACI...*!
*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*
FITAR AMO..!
"Ahmed ka manta Wacece ni...? Nice fa masoyiyarka Samiha..? Ka manta alƙawarin mu...? Ka manta yadda muka tashi muna gina yadda Rayuwar Aurenmu zata kasance..? Amma yau rana ɗaya saboda wani dalilinka mara tushe ballatana makama kakeso kaƙi amfani da damar data samemu Ahmed...?"
Hannu ya ɗaga mata lokaci ɗaya yana faɗin "Ya isa haka Samiha..!Nace ya isa Haka...? Ya kikeso nayi dake ne eh..? Karki manta ke matar Aure ce yanzu duk waɗannan burunkan namu sun yanke daga Lokacin da Mahaifinki ya bada ke..! Taya ya zan iya bin Buƙatarki alhalin kina matsayin matar Uban gidana..! Kuma nima ina matsayin Surukinsa ina Auren 'ƴarsa ta cikinsa kuma sai na biye miki naci amanarshi.? A'a ba zai Taɓa faruwa ba bazan Taɓa yima Maigidana Haka ba SILAR HALLACIN da yayi min bazai Taɓa barina na iya cin Amanarsa ba SAMIHA...
Kiyi Haƙuri...!
Wani irin kallo take Jifanshi dashi Lokaci ɗaya manyan Idanuwanta na Tara ƙwallah cikin Takaici da wani taku ta ta fara takawa zuwa gabanshi shi kuma yayi saurin Juya mata baya yana Ɓoye Siririyar ƙwallar dake Cikin Idanuwansa, murmushin dayafi kuka ciwo ta saki kafin tace "Ahmed kar ma ka fara wannan ganganci... Karma ka fara Tunanin wannan karon zaka iya Guje min... Baka isa ba Wlhi Tallahi na yi ma kaina alƙawarin sai na mallakeka Ahmed a matsayin Mijina ko ta Halin ƙaƙa.." Ta faɗa Lokaci ɗaya tana Zurama bayansa Ido Cikin mamaki ya Juyo yana faɗin "Me kike Nufi Samiha..? Karki manta kefa yanzu ba yarinya bace kin zama babbar mace kin mallaki hankalin kanki..Balle nace yarinta na damunki kiyi gaggawan barin mun office kafin na saka afitarmin Dake..." Ya faɗa yana Haɗe Ransa Lokaci ɗaya yana Nuna mata hanyar waje Wani Murmushin Mugunta ta saki kafin tace "Ni kake kora Ahmed...?"
Bai mata magana ba illah Nufar Teburinsa da yayi yana danna wasu lambobi bisa Telephone ɗin dake kan Teburin Wata ƙaramar Dariya ta saki Lokaci ɗaya tana faɗin "Zan tafi... Amma ba domin zaka kira min Jami'an Tsaro ba sai domin Soyayyar da nike maka ta gaskiya ne ina sonka Ahmed kuma ina son kasancewa da kai..amma ba domin haka ba zan ƙyaleka ka kira wanda zaka Kira kafin su taho nayi Tsirara agabanka suna zuwa zan Fara kuka nace kai ne kake neman yimin Fyaɗe, daga nan in Alhaji yaji komai ya lalace maka.." Ta faɗa tana wani Sakar mai Idanuwanta.
Tsam yayi kawai yana Kallonta bai samu Zarafin magana ba ta ƙara Taku zuwa gabanshi sai ta wani juya mai kafin tace "Karka damu bazan yi haka yanzu ba...Matukar kabani Haɗin kai komai Zai tafi yarda na Tsarashi in kuma ka cigaba da Taurin kai.." Ta Ƙarashe faɗa tana Shafa Sajen Fuskarsa Saurin Kauda kai yayi Cikin ɓacin Rai jakarta ta Ɗauka da wayarta dake saman Kujera ta kama Hanyar Fita tana Kadamai Mazaunanta Saurin ɗauke kai yayi yana ta'awizi acikin Ransa Kafin ta Fita ta Waigo tana kallonsa kafin tace "Zan dawo...Akwai dawowa.." Daga haka ta Fice kansa ya Dafe yana maimaita Kalmar Innalillahi wainna illaihirraji'un...
Kan kujera ya faɗa yaraf yana Sauke Numfashi Cikin Fesar da Numfashi ya Furta "Samiha...Wani bala'i ki ke neman Jefani ciki..Allah gani gareka ka tsareni daga Sharrin mace.." Ya faɗa yana Runtse Idanuwansa Cikin Halin damuwa da Rashin mafita.
*****
Bayaso Abida ta Fahimci Akwai wani abu Shiyasa ya maida wayar a silent amma Samiha bata daina kira ba, ƙarar Shigowar saƙo yasa ya ijiye Cokalin Hannunsa ya ɗan kalli gefen Abida yaga bata kallonsa Hankalinta na wajen Kaka dake Ƙorafin Tagaji da Cin Abincin Turawa, Kai duba yayi zuwa ga Saƙon Samiha wacce bai san ina ta samu Nombar wayarsa ba kai Tsaye wata Zuciya tace "A wajen Abba mana.."
"Ka ɗauki wayata..muyi magana ko kuma na zuba ma Alhaji gubar da na siyo gata atare dani...In jami'an tsaro suka kamani zan ce kai ka sani na kashe Alhaji saboda kana sona kaga kuwa dani da kai za'a kashemu.."
Wani Rass! yaji gabanshi ya Faɗi Cikin Firgici da Tashin Hankali ya miƙe duk ya Haɗa Zufa Abida da kaka suka Bishi da kallo ganin ya Nufi ɗaki Cikin Sauri har yana cin Tuntuɓe Kaka ta kalli Abida tace "Shi kuma wannan Halan Saƙon mutuwarsa ne yaji yake ta wannan Uban Rawan Jikin har yana neman Faɗuwa.." Cike da mamaki Abida ke Faɗin "Mutuwa kuma Kaka...?"
Kaka tace "Eh mana toh in ba sakon mutuwa ba Uban me zai Firgita Ahmadu lokaci ɗaya haka.." Ta faɗa tana gyara zaman Gilashin Idonta jikin Abida na sanyaye ta miƙe tabi bayan Ahmed sai dai tana zuwa taji ya garkame ƙofan baki ta riƙe Cikin mamaki tana bin ƙofar Bedroom ɗin nasu da kallo.
Yana Shiga Cikin Bedroom ɗinsu ya maida ƙofa ya kulle saboda kada Abida tabi yo bayanshi daidai lokacin da Wayarshi ta ƙara Ɗaukan Tsuwa jikinsa na ƙara ɗaukar Rawa ya ɗaga kiran bai samu Zarafin Magana ba Samiha ta kece da wata dariyan Nishaɗi da Nasara tana faɗin "Dama na faɗa maka..Zan mallakeka Ahmed mallaka na har Abada..."
Cikin Wani irin Faɗuwar gaba Ahmed yace "Samiha...! Samiha me kikeyi hakane wai..? Samiha ya kamata ki daina Bibiyata haka nan Abunda kike nema bazai samu ba na Riga na gaya miki tun Farko.." Ajiyar Zuciya ta Sauke kafin tace "Naji Aurena dakai bazai yiwu ba Ahmed...Amma ai Haɗuwa mu zama Abu daya zai yiwu ko..?" Ta faɗa cikin Wata murya mai cike da kissa.
Ahmed na goge zufan data keto mai Bisa goshinsa yace "Ban..ga..ne Abun..da kike nufi ba...?" Ya faɗa cikin Rawan murya far tayi da ido kamar yana Gabanta kafin tace "Laaa baka gane ba..? Toh ina nufin Budurcina danake ta maka tanadi Shekara goma babu Abunda ya tabashi shi zaka iya amsanshi koda yaushe ka Shirya..." Wani zaro ido Ahmed yayi Cikin Rawan baki yace "Innalillahi..." da Sauri Samiha ta katseshi da Faɗin "Mu hadu a Hotel ɗin Tahir guest palace gobe da Misalin ƙarfe goma na Safe.." Ta faɗa kai Tsaye da Sauri Ahmed ya Sulale kan gado yana fadin "Sassamiha...Sasssmiha karki min haka..." Cikin Wata murya tace "In baka zo ba..Nikuma zan cika ƙudirina zan ba Alhaji guba yaci ya mutu..." Da sauri Ahmed yace "A'a karki haka Zanzo...Zan zo karki Bama Abba guba don Allah Samiha..."
Dariyan Jin Daɗi ta saki kafin tace "Sai da safe angona...Karka manta ɗaki mai lamba Ashirin da biyu sai mun haɗu.." Ta fada ta sakin mai kiss ta waya kafin ta yanke kiran Wani Tuma Ahmed yayi Bisa gado ba inda Jikinsa baya Rawa cikin Firgici da Tashin Hankali yake Furta.. "Na shiga uku ni Ahmed..Yarinyar nan zata kasheni Lokacina baiyi ba..Wazan kai ma kukana.? Wazai bani shawara kan wannan Abun daya Tunkaroni kaicona..Ni Ahmed kaicona...ya zanyi da Rayuwata..." Ya faɗa lokaci ɗaya wasu Siraran Hawaye suna Zubo mai Bisa Fuska gabadaya ya jiƙe da Zufa kamar wanda ya Buga wasan Tsere.
******
Tana shigowa cikin Bedroom ɗin nasu taji kukan Wayarsa Da sauri ta ƙarasa kan gado ta Ɗago wayar tana ganin Lambar dake Kira ƙurama lambar ido tayi Ranta na ƙuna gaba ɗaya acikin dan Tsakaninnan wannan Lambar take yawan kiran mijinta kuma da Zarar kiran ya Shigo Ahmed ke rasa Duka Natsuwarsa gaba ɗaya ta daina gane kanshi yana rama atsaye ya daina cin Abinci balle ishasshen barci baya fara balle wata Doguwar Hira, sauri tayi ta Ɗauko wayarta dake saman Madubi takwashe Lambar kafin kiran daya sake Shigowa ya yanke Sai da tagama ɗaukan Nombar awayarta tana danna kira acikin wayarta sai ga Suna ya Fito ɓaro ɓaro AMARYAR ABBA..." Da sauri Abida ta Zaro idanuwanta waje Lokaci ɗaya ta dafe Cikin jikinta wanda ya wani juya, jiri ta fara gani da ƙyar ta iya Laluban gefen gado ta Zauna, ƙurama Sunan ido tayi acikin Zuciyarta tana Faɗin Haba biri yayi kama da Mutum Ashe duk zargin da ake ma Ahmed gaskiya ne..? Da gaske ne dama yana bin Amaryan Abbanta...? Yaci amanarta kuma yaci na mahaifinta, Batasan Lokacin da Hawaye suka wanke mata Fuska ba tana cikin Wannan Halin ne ya Fito daga wanka sanye da Rigan wanka ajikinsa ganin Abida na kuka yasa ya ƙarasa da Sauri yana faɗin "Lafiyanki kuwa Sweetheart..?"
Wani kallo ta wurga mai Idanuwanta Sun kaɗa sunyi jajir kafin tace wani abu kawai sai ta Nuna mai wayar hannunta tana Faɗin "Nombar dake yawan kiranka a kwanakin nan na saka awayata zanyi Dailing Abun mamaki Ahmed Lambar Amaryan Abba ce ta Fito min..." Ta faɗa tana Tsareshi da Ido gaba ɗaya Ahmed yaji kamar kasa ta tsage ya Shige cikin Fitan Hayyaci yake bin Wayar Abida da kallo yana Faɗin "Me..me..me kike nufi Abida Wata amaryan Abban..?" Ya faɗa cikin son ya nuna Shi Jarumi ne.
Miƙewa tayi Da ƙyar tana cije baki tace cikin Tsawa.. "Ya isa Ahmed! Ba sai kace min komai ba...Dama ashe duk Maganar da ake agari na Ana ganinta tana Zuwa office ɗinka koda yaushe da gaske ne..? Na ƙaryata wannan Zargin a gaban Umma da Sauran ƴan'uwana saboda sanin Halin kamewarka da kuma irin Hallacin da Abba yayi maka bazaka ci amanarsa ba, Ashe ba haka bane na manta Tsintacciyar mage bata mage ko tayi Wata rana sai ta nuna Halinta na ita din Tsintacciya ce.." Ta faɗa cikin zafin Rai Lokaci ɗaya kuka na ƙwace mata cikin Wani Irin Razana Da Son Fashewa da kuka Ahmed yake ƙoƙarin Riƙo Abida yana Faɗin "A'a Abida...Karki min haka na ɗauka ko kowa bai Saurareni ba zaki Saurareni kiji Abunda zan gaya miki..."
Saurin matsawa tayi baya tana Nunashi da yatsa take Faɗin "Karka kuskura ka kai Hannunka jikina domin shine kuskure na ƙarshe da zaka sakeyi arayuwarka Ahmed...Na tsaneka..Na Tsaneka.. Ƙarshen zama na dakai yazo bazan cigaba da zama da ɗan akuya ba ka haikemin kuma kaje ka haikema matar Mahaifina Tirr dakai Ahmed nayi nadamar Aurenka..." Ta faɗa cikin kuka kafin ta juya da gudu ta bar mai ɗakin Ƙasa Ahmed ya Sulale Lokaci daya yana Dafe kanshi Cikin Wani irin yanayi yake Furta.
"Innalillahi wa'inna illaihirraju'un....."
watch out in....SILAR HALLACI...
*Janafty& Aisha Alto*